Showing 30001 words to 33000 words out of 46393 words

Chapter 11 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf

yau ni ce Aunty Nabeelah zata kai dakin miji. Mijin kuma Maccido, Maccidon ma wanda na sani, na
yi wa farin sani, wanda a baya ban taba mafarkin wata alaka a tsakanin mu bayan gaisuwa ba.
To shi sha’anin Ubangiji haka ya ke. Matar mutum kabarin sa, ashe Allah ya riga ya rubuta min Attahir a
matsayin miji, babu makawar hakan komai daren dadewa.

Ina wannan tunanin Yaya Maccido ya bude kofar da Aunty ta kwankwasa masa. Yana budewa kuma ya
koma ciki ba tare da ya dube mu ba. Wata irin kyakkyawar jallabiya ce a jikinsa kalar coffee, da alama
wanka ya sake bayan baro mu da ya yi a masaukin Aunty Nabeelah.
Ni da Aunty muka zauna a kan seater yayin da ya koma gefen gado ya zauna ya dafe kansa, da alama a
kwance yake kafin shigowar mu, Aunty ta kira sunan sa na yanka,
“Attahir, ga amanar kanwa ta Asma’u na kawo maka. Ina rokon Allah ya taya ka riko. Asma’u ga amanar
kanina Tahir na damka a hannun ki. Allah ya tallafa miki wajen yi masa biyayya, Ya ba ku zuri’a masu
albarka".
Hawaye suka gangaro daga idanu na. Na tabbata wata sabuwar rayuwa ce mai cike da kalubale zan fara
daga yau, wadda ban san me zan je in tarar a cikin ta ba, ban san ya ta ke ba. Girma ya hau ni, a lokacin
da ban shirya masa ba.
Kyale hawayen na yi suka yi ta zuba abin su, ba tare da na tare su ba. Ko na share su. Aunty ta mike za ta
fita, ai ban san lokacin da ni ma na mike na bi ta ba. Ta dakata ta kama ni tana girgiza min kai, ni ma na
shiga girgiza mata. I just cannot, bayan sani da na yi cewa shi din yanzu yana da wani mafificin matsayi a
gare ni.
“Idan ba za ki zauna a dakin mijin ki ba, gobe zan koma inda na fito in bar muku kasar gabadaya”.
Kuka nasa mata, wani irin kuka mai cin rai, wanda ya taho da karfi tun daga karkashin zuciyata, na ce,
“Aunty me ya sa za ki min haka? Yaya ne fa, shi din Yaya na ne. Ba zan iya wata rayuwa ta daban da shi ba,
bayan wadda muka riga muka taso a cikin ta”.
“Ma’u, Allah bai haramta ba, baku sha nono guda ba, na rantse ko ki zauna ko na koma Beirut gobe”.

Ina ji ina gani Aunty ta juya ta fita, tunda ta rantse min, na koma jikin kofa na jingina da ita in shesshekar
kuka. Yaya ya taso ya rufe kofar dakin da key ko kallo na bai yi ba, ya koma ya kwanta. Ya ja quilt ya
kudunduna a cikin sa.
Sai da na yi kuka na ma’ishi babu mai lallashi na. Abin da ban sani ba Yaya Maccido ta kansa yake, domin
zazzabi ne da ciwon kai suka rufe shi. Ina ji ya dauki waya ya kira Aunty Nabeelah, ya ce ta dauki ajrah ta
koma asibiti ba zai iya fitowa ba, kansa ya matsa masa.
A daidai lokacin aka kira sallar magriba, Yaya ya mike ya shiga toilet, na yi amfani da wannan damar na
tuje daurin da Aunty ta yi min, kwalliyar dama duk ta dame da hawaye da majina. Na san ta yi min su ne
don in burge Yaya, ni kuma ban shirya zama matsayin matar sa ba ma, balle in nemi kauna aminci daga
gare shi.
Ya fito ya shimfida darduma har zai tayar da sallah ya ga ba ni da niyyar tashi anan inda suka barni,
sannan sautin kuka na bai bar fita a hankali ba. Yana ci masa rai, yana azabtar da zuciyar sa. Ya dafe
goshin sa da hannun daman sa cikin raunin murya ya ce,
“Ki yi wa Allah ki yi min shiru, I’m having headache”.
Muryar sa kawai na ji na yarda ba shi da lafiya din da gaske. Amma ko kadan ban ji ya ba ni tausayi ba.
Tunda kukan ne ba ya so, ni kuma yanzu na fara shi, in yaso in ya gaji ya kira Aunty ta zo ta tafi da ni. Don
haka na kara sautin gunjin kuka na ya koma kamar na fitar rai.
Takowa ya yi a hankali ya zo har inda nake. Ga dukkan mamakina, hannuna ya ja zuwa three seater, ina
tirjewa ina komai, ya zaunar da ni sannan shi ma ya zauna gefe na, kafadun mu na gugar na juna.
“Asma’u!”.
Yaya Maccido ya kira sunana da tattausar muryar sa da ta gama yin rauni, ga ciwo ga damuwa.
“Me ki ke so in yi miki mu zauna lafiya?”
As if ba Maccido ke magana ba, the voice is so soft, babu diya macen da bazata tausasawa zuciya ba.
Na ja shessheka na fyace hanci na, na ce,
“A kan me za ka aure ni ba da sani na ba? Ni kaza ce? Ko kuwa 'yar tsana ce? Ni na ce ina son ka? You are
never my choice. Ban taba mafarkin auren mai mata ba. Kana da rayuwar ka inada tawa, don me zaka
dauko ni ka tsunduma ni cikin taka ba tare da sani da amincewa ta ba?”
Maccido ya zuqi numfashi ya fesar. Ko maganata tayi masa ciwo hakan bai nuna akan kyakkyawar fuskar
sa ba, a hankali ya ce.
“Na dauka an wuce wannan wurin tuntuni? Tunda aikin gama ya gama? Aure ya riga ya dauru, da
amincewar wanin mu ko babu. Neman maslaha ce a gaban mu yanzu?”
Shiru na yi masa. Ina tauna maganar tasa a raina.

“To in wannan ne laifi na ina ba ki hakuri. Kodayake kin ce ba kya sona ne saboda na miki tsufa, Balarabe
ki ke so ko Asma’u? Ni kuma nace mai zai hana ki ba ni dama mu gani ni da Balaraben wa ya fi iya
soyayya?"
Ya dago habata da hannun daman sa ya dubi yadda hawaye suke gudu akan kunci na, kafin in yi aune na
ji taushin bakin Yaya Maccido cikin nawa. Wani irin kissing dina ya shiga yi kamar zai cinye ni, duk
hawayen fuskata sai da ya bi su emotionally ya dauke su tas! Babu wata gaba ta jiki na da ba ta amshi
sakon sassanyar sensual kiss da Attahir ke aikawa ba. Wani yanayi ne da ban taba tsintar kaina a ciki ba,
ban san akwai shi ba. Ban san sanda na lumshe idanu na ba ina jin abinda tun da uwata ta kawo ni duniya
ban taba ji ba. Yaya Maccido ya sa hannayen sa duka ya sake rike ni da wani irin riko da na yi tsammanin
har abada ba zai sake ni ba. It was kind of gentle romance wanda ya goge duk wata hadda da ke kaina ya
soma cusa sababbin karatun da Maccido-Attahir ke kawowa.
Kiran sallahr maghriba da aka yi shi ya cece ni daga hannun Yaya, kasancewar sa mai muhimmanta kiran
sallah fiye da komai a rayuwar sa, ya bi ni da lumsassun idanun sa wadanda ba sa ko buduwa a wannan
lokacin. Mikewa na yi ba tare da na iya hada ido da shi ba sabida kunya da takaicin kaina, na yi toilet na
rufe kaina. Na jingina baya na da kofar bandakin ina hawaye. Bakin cikin kaina duk ya kama ni kan yadda
na sakarwa Yaya jiki kamar mai zaman jiran hakan daga gare shi. Tabbas in aka ci gaba da irin wannan
tafiyar ba za'a je ko’ina ba Attahir zai goge mini lissafin duk da ke kaina, in manta da duk wasu laifuka da
nake zargin shi da yi mana ni da Addah.
Cikin mutuwar jiki na daura alwala na fito. A kwance na same shi saman gado kafafunsa na kasa. Jin
motsi na ya sa ya yunkura ya mike, kallo na ya yi yana murmushi ya ce,
“Jira ni in zo mu yi jam’i tunda kin warware min alwalar kin ji dadi”.
Ban ce masa komai ba, amma na zauna jiran nasa.
Bayan mun idar da sallahr magriba da isha muka yi shafa'i da wutri. Sannan Yaya ya ce, za mu yi wata
nafilar raka’a biyu don nema wa auren mu albarka. Tunda ibada ce ai bani da ja. Da muka idar ya gama
addu’o’in shi ya ce min zai je downstairs ya samo maganin headache in na ji yunwa in jira shi yanzu zai
dawo”. Ko kula shi ban yi ba.
Yana fita na sauya kayana zuwa na barci na shige cikin quilt na kudundune. Ba jimawa barci ya yi awon
gaba da ni don gabadaya a gajiye nake. Ga kukan dana sha, wanda nima ya sabbaba min ciwon kan.
Lokacin da Yaya Maccido ya dawo samu na ya yi ina barci bilhaqqi a kan kujera yadda muka saba. Zama
ya yi a gaban kujerar ya dora hannu a kan wuya na da goshi na. Nan ya ji zafin da suka dauka. A hankali
na bude ido, sai idanu na cikin na Attahir.
“Tashi ki ci abinci”. Ya fada with care.
“Bana jin yunwa”. Na ba shi amsa ina mai turo baki, tare da sake lumshe ido na.
“To tashi ko Haleeb ki sha, sai ki sha magani, you have some fever and headache kema”.

Girgiza masa kai na yi cikin nauyin barci.
“Don Allah Yaya ka kyale ni, wallahi na koshi, kuma ni lafiya ta kalau”.
Ya rankwafo daidai saitin kunne na. Har ina jin hucin sassanyan numfashin sa. Kasa-kasa ya ce.
“To ni kuma ya ya za ki yi da ni Asma’u? Kwana bakwai ko takwas ke nan ina hakuri, ina kauda kai, alhalin
na san cewa ina tare da matata ta sunnah ne, halali na. Asma’u I will not force you to be with me, in ba ki
amince ba zan hakura, har zuwa lokacin da za ki karbe ni a matsayin miji, koda hakan na nufin zan cutu.
Fata na daya ne ki yarda cewa I really love you”.
Yadda yake maganar loving and romantic kamar ba Yaya Maccido ba. Da wata irin lallausar murya da na
kasa amincewa ta Yayanmu Maccido ce. Maccidon nan ma'abocin kasaita da fadin rai kamar na basarake.
Na bude ido a hankali, don dai in tabbatar da wanda nake magana, idanu na suka sauka cikin nasa. Yana
durkushe a gabana ina kwance saman kujera. Ko kadan ban ji tausayin shi ba duk da cewa he looked so
pale a yanayin da yake maganar.
Na ga cewa in nayi wasa, Yaya zai yi galaba a kaina, domin wani sashe na zuciya ta ya fara darsa min
tausayin sa, alhalin ko kusa ban yarda da wannan soyayyar tasa ta dare daya ba. Abinda na yarda da shi
shine Attahir ya aure ni ne don ya shirya da mahaifiyar sa, ya wanke laifin da yayi mata using me as an
instrument, amma ba don so ba.
So daya ne, kuma na san matar sa yake wa. Kowa ma shaida ne akan hakan. Cewa yana matukar son
Lubabatu ta yadda har ya zabe ta akan mahaifiyar shi. Yana da target din sa na aure na wanda bazan taba
amincewa yayi galaba da ni ba.
"Yaya in ka sake taba ni, bayan wanda ka yi dazu na kyale ka, wallahi zan haura ta taga in fada in mutu in
huta, ya fiye min da in amince ka nakasta min rayuwa. Wallahi ba so na kake ba, ka aureni ne don ka cika
burin ran ka, wanda kai kadai ka san shi. Gara in mutu, da in baka abinda kake nema daga gare ni".
Na karasa da kuka wurjanjan, Yaya Maccido ya rasa abinda zai ce min, kuma kwarai kalamaina suka yi
masa zafi. A sanyaye ya ce.
"Na ji Asma'u kuma na gode, amma ki yi min alfarma ki koma gadon, ni ki bar min kujerar. Zan tabbatar
miki ban aure ki don abinda kike tunani ba, baki da abinda zaki bani Asma'u, wanda sauran matan duniya
dana tsallake su na zabe ki basu da shi. Ki rike duk abinda kike taqama dashi, ki ajiyewa Balarabe. Tashi
koma gadon ki bar min kujerar".
Wai kuma sai na ji kalaman sa sun min zafi. Kin tashi na yi sai da ya daka min tsawa, na tashi ina cuno
baki na koma gadon dakin, gadon da ban taba hawa ba tun zuwan mu sai yau. Ya rage hasken fitila,
maimakon ya kwanta kamar yadda na yi tsammani sai naga ya koma gefe ya shimfida darduma ya tada
sallah.

Yadda ya raba daren bai yi barci ba haka nima, na kwana ina tunanin wannan al'amari mai kama da
almara da ya same ni rana daya, "auren Yaya Maccido" tamkar kiftawar ido, wanda ko cikin mafarki, ban
taba kawowa rayuwata ba.



*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*



*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*


*YIWA KAI HISABI*




((13)). Washegari a dakin ban da kuka ba abinda nake yi kwance akan gado. Tun asubah dana yi sallah
na koma gado na kudundune na bude sabon shafin kuka, zuciyata ta kasa karbar wanan al'amarin da
sauki har zuwa yanzu. A jiya na dauka mafarki nake, idan gari ya waye zan farka in ga ba haka bane.
Amma da garin Allah ya waye, na tabbatar babu zancen mafarki cikin aure na da Maccido.
Don haka na bude sabon shafin kuka. Har karfe goma na safe ina abu daya, Yaya yana kwance a
doguwar kujera yana fama da ciwon kansa da zazzabi. Ya kama kansa bai shiga sha'ani na ba. Ko asibiti
yau ya kasa fita. Banza yayi min kamar bai san ina yi ba. Daga ni har shi ba wanda ya dubi abincin karin
kumallon da aka kawo mana. Sai wajejen azahar ya ga bani da niyyar tashi balle in yi wanka, ya samu yayi

wanka ya shirya amma idanun sa jazur sabida zazzabi da ciwon kai, ya dube ni a wahale da murya mara
amo ya ce.
"In kin ga dama ki tashi ki shirya mu tafi asibiti, ina jiran ki".
Ai jin za'a tafi wajen Addah, nan da nan na mike na fada wanka a gurguje, da na fito ko mai ban
shafa ba na zuba Abayat dina baka wuluk na nade kaina da veil din ta, ina so in ce masa na shirya, amma
bana so ya ji amon murya ta, ya dauka ko na fara saduda da auren sa ne, yana zaune tallabe da kansa da
yake jin kamar zai fice daga gangar jikin sa sabida tsabar ciwo. Ko kadan ban ji tausayin sa ba, a raina
nace alhaki na ne ya kama shi yake ta ciwo ba wani abu ba. Shi da kan sa ya fahimci na shirya din ya mike
yayi gaba na bi bayan sa.
Sanda muka iso Adda na cin abincin ta na musamman wanda asibitin ke bata, Aunty Nabeelah na gefen
ta tana yi mata hira suna dariyar su, Aasim na barci a kan kujera.
Dukkan su kallon mu suka yi admiringly Aunty na fadin,
“Me ku ka zo yi? Ba na ce yau ka bari sai dare ku zo ba?”
Yaya ya karasa gaban Addah ya kama hannunta ya sumbata ya ce,
“Barka da rana Addah, ya karfin jiki?”
“Jiki sai hamdala, kullum lafiya karuwa ta ke, na gode Allah ya yi muku albarka bakidayan ku”.
Ya juya ga Aunty ya ce "nima zan ga Doctor ne, shi yasa muka fito, jiya da fever da headache na kwana
sosai, amma yanzu da sauki, bari in je in dawo". Ina ta hararar Yaya, amma ya ki yarda ya kalle ni. Aunty
ta ce,
“ko dan paracetamol baka sha ba?"
Ya ce "bana shan magani ban ga likita ba, ina zuwa yanzu". Ya juya ya fita, suka bi shi da kallo fuskokin su
dauke da 'yar damuwa.
Addah ta juyo gare ni ta ce,
“Ma’u dawo nan kusa da ni”.
Na koma kusa da Adda na zauna, na ce, “Bari in kira Muhsin ku gaisa Adda, kwana biyu ba mu gaisa da
shi ba". Na hau neman waya ta a jaka ta amma sai na tuna na baro ta a daki tana caji.
Sai da Yaya ya dawo rike da ledar magungun sa don kada Adda ta fahimci bama magana na yi ta maza na
ce.
“Yaya ba ni aron wayar ka”. Ba tare da na yarda mun hada ido ba.

Ya daga idanunsa da suka kada sabida zafin zazzabi ya dube ni, karo na farko da muka hada ido tun daren
jiya, jikina na ji ya yi bala'in sanyi, cikin sanyin murya ya ce.
“Ki shafa min maiko?”
Da sauri na nuna masa tafukan hannu na.
“Allah ka ga hannuna sumul yake”.
Addah ta ce, “In za ka ba ta, ka ba ta, bana son jan rai”.
Ya ciro ta daga aljihun gaban rigar shi ya miko min.
Ina laluben lambar Muhsin kira ya shigo wayar. ‘My Wife’ shi ne sunan da ke yawo a fuskar wayar. Ban
san lokacin da na katse kiran ba, aka sake kira na katse shi, haka ta ci gaba da jerawa mijin ta kira ina
katsewa babu dalili. Kuma da yake wayar a silent ta ke, Yaya bai san ina yi ba. Ni kaina bansan dalili na na
yin hakan ba, ji nayi nan duniya ba wanda nake jin haushi irin Lubabatu.
Yaya ya fita don ya nemo mana abinci, na ja gefe na bar Addah da Aunty suna hirar su, na tsinci kadan
daga hirar tasu hirar kayan lefe ne da kayan daki da za'a yi min wanda Aunty za ta je Abu-Dhabi ta auno
komai zuwa Nigeria. Na shiga gallery din Yaya babu komai sai hoton iyalin sa. Inda na gane shi ba mai
yawan daukar hoto ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login