Showing 39001 words to 42000 words out of 46393 words

Chapter 14 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf

hannun sa, ya ce.
"Ban san me Adda ke nufi da ni ba, ta ce sai ta ga dama zaki tare, ni kuma hakuri na ya kare Asma'u"
zamewa na yi daga jikin sa zan fice da sauri har ina tuntube. Kunya kamar in yi yaya. Da sauri Yaya
Maccido ya sha gaba na, looking at me affectionately.
"Ina alkawarin da mu kai na cewa in na zo za ki ce min Maccido?"
Tafuka na nasa na rufe fuska ta ga hawaye shabe-shabe "don Allah Yaya ka yi hakuri" ya ce " ai baki isa
ba, ba ki zuwa ko nan da can sai kin cika alkawarin nan, Maccido ko Attahir, sai kin fadi guda daya".
Ganin da gaske Yaya ya ke bazai barni in fita ba ga Adda na can tana jira na dole na runtse ido na ce
"Attahir, ka bude min kofa in fita" da murmushi mai kyau Yaya ya ke kallo na kafin ya ce "saura daya
alkawarin".

Zaro ido na yi waje don na tuna alkawarin da na yi masa, wanda giyar so ta kwashe ni na yi masa a waya
wanda sirri ne a tsakanin mu, bayan kuma alkawari ne dana san bazan taba iya cika shi ba.
Ina ji ina gani Yaya ya cigaba da hargitsa duniya ta yadda ya ke so ya ke muradi da wata irin zazzafar
soyayya. Ya dauke ni ya shilla a duniyar da shi kadai ya san irin ta. Al'amarin da ya dauke mu lokaci mai
tsaho. Gabadaya mun manta da kiran Adda, itama bata kara zuwa ba, amma tana can cike da fargaba da
tsoro, tsoron kada Attahir ya tabbatar da auren sa gaban ta. Ta dade da fahimtar ba wani abu da ya shiga
tsakaninmu a Jeddah, haka har muka je Madinah muka dawo. Soyayyah ce 'yar usli mai tsafta Attahir ke
gwadawa Ma'u, soyayyar da ya tabbatar wata diya mace bata taba samu daga gare shi ba. Shi da kansa ya ankarar da kan sa cewa... this is not the right place.... and not the right time... dole ya
kyale ni na fita wajen Addah duk ba cikin nutsuwa ta ba. Kallo daya ta yi min ta dauke kanta tace in je in
yi serving Yaya abinci tun da ya iso bai ci komai ba, daga haka ta bar mana falon da ta ga Yaya Maccido na
fitowa shima.
Adda na shiga dakin ta Aunty Nabeelah ta kira, ta ce ta zo haka su yi shirin tarewar Ma'u. Ita bazata iya da
mu ba. Attahir ya zo muna ta mata rashin kunya a gida, Aunty ta yi dariya sosai ta ce insha Allah tana tafe
sati mai zuwa.
Yaya na gama cin abinci Al-Qasim yayi sallama kan sa a kasa. "Come and join us" inji Yaya. Sosa kai ya
shiga yi cike da kunyar abinda idanun sa suka gane masa dazu "I'm okey Master". Yaya ya goge bakin sa
da tissue ya mike ya dube ni na sunkuyar da kai, ya ce.
"Zan ga Al-Qasim ki shiga daga ciki".
Har karfe goma na dare suna tare a falon suna lissafe-lissafe da kasafce-kasafcen su cikin kwamfuta. Da
barci ya fara fizga ta Yaya bai shigo ba na mike na ce "Adda zan je in kwanta barci nake ji". Gadon ta ta
nuna min "yi a nan, yau anan za ki kwana". Ban gane hausar Adda ba sai da Yaya Maccido ya zo yana yi
mata sallama zai je ya huta, ya ce "Asma'u har ta koma dakin ta ta kwanta ne?" Adda ta yi fuska ta ce
tana cikin daki na tana barci" Yaya ya tsaya ya kasa tafiya, ta sake hade fuska ta ce "wani abu?" Da sauri
ya juya yana fadin "mu kwana lafiya Adda, dama sako zan bata" Adda tayi murmushi ta ce "da safe ka
bata". A zuciyar ta ta ce "ba dai a gabana ba, ka yi hakuri har in kawo maka ita".
Ina ganin kiran Yaya nata shigowa na ki dagawa sabida kunyar Adda.
Washegari Yaya da fushi ya shigo gidan, da na gaishe shi sama-sama ya amsa, Adda ta yi masa tayin karin
kumallo ya ce ba yanzu ba. Daga baya ya kira Al-Qasim ya zo ya dauke shi suka tafi mall. Bai dawo ba sai
can yamma. Ya same mu nida Adda muna girkin dare a kicin. A jikin cabinet din kicin din ya tsaya fuska a
daure ya ce "Adda sannu da gida" ta ce "kai kuma sannu da yawo ba ci ba sha. Ma'u shirya masa abincin
gashi har na rana ya kusa tadda na dare" juyar da kai yayi gefe ya ce da Adda "ni ba na jin yunwa, gobe da
sassafe zan wuce Adda saboda Monday in shiga ofis akan lokaci". Adda ta ce. "Allah ya kai mu lafiya".

Zuciyata ta yi ba dadi da biris din da Yaya yayi da ni, da kuma jin gobe zai koma. A sanyaye na ce "sannu
da dawowa Yaya". Harara ta ya yi ya bar kicin din, Adda tace "wuce ki bishi falo ku gaisa sosai ki bar min
aikin, na ga alama fushi ya ke yi, ban san tsakanin ni da ke wa ya yi laifin ba".
Murmushi na yi. Na wanke hannu na a sink na tsane da karamin tawul, sannan na bi bayan Yaya.
Ban same shi a falo ba, haka dakin Adda na duba ban gan shi ba. Kwata-kwata ban kawo yana daki na ba,
na shiga kai na tsaye da niyyar in dauki waya in kira shi inji inda ya ke.
Anan na sameshi zaune bakin gado na ya hada tagumi da hannuwa bibbiyu. A hankali na taka na isa kusa
da shi na zauna. Lokacin da ya juyo muka hada ido, sai da zuciyata ta girgiza da abinda na hango cikin
idanun sa. It's nothing but pure love wanda babu surki a cikin sa. Gabadaya ya kara rikita mu daga ni har
shi da deep kisses din sa masu tsayawa a zuci. Al'amuran sa masu ban mamaki ne. Ban iya fadin halin da
Yaya Maccido ke ciki a wannan lokacin, gabadaya ya manta da fushin da yake yi.
Adda ta taho dauke da tray ta shiryo masa abincin ta biyo shi da shi ganin har zuwa lokacin bai shigo ya ci
ba, abin ki da uwa akan cikin dan ta. Da bata gan shi a falo ba ko dakin ta ta nufo daki na da abincin. Ai
kuwa Adda ta yi kyakkyawan gani. Mu dai sai ji muka yi an ja kofa an rufe. Abinda ya maido da hankulan
mu daga ni har Yaya. Na kife fuska cikin tafuka na na rasa inda zan sa kai na. Shi kuwa Yaya murmushi ya
yi, ya mike yana gyara karin hular sa.
"...... Asma'u that's what i want ai, ta san cewa ina bukatar mata ta...kada abin nata ya koma daukar
hakki".
Sai da ya kara jimawa kafin ya bar dakin kamar ba zai tafi ba. Ban san yaya suka kare ba shi da Adda. Ni
kam har washegari da safe da Yaya ya shigo don yi min sallama zai wuce ina cikin bargo kudundune na
kasa fitowa, balle in hada ido da Adda. Yanzu ne na san Adda ta zame min suruka ta hakika, na kuma san
abinda ya sa kunya da nauyi ke shiga tsakanin mata da iyayen mijin su.
Bayan tafiyar Yaya wuni guda sur ina kaucewa haduwa da Adda cikin gidan, na zama daga daki sai daki.
Ita da kanta da ta gaji da rashin gani na ta biyo ni da abinci har daki. Sai da na yi kwana uku ina buyar wa
Adda kafin na saki jiki na mu cigaba da harkokin mu cikin gidan kamar yadda muka saba.
Yaya Maccido in bai kira ni sau hudu ba a rana zai kira ni sau uku. A wannan dan tsukin ba abinda Adda ke
yi irin tsananta Addu'a a kai na da Maccido, tana mai godewa Allah da Maccidon ta ya dawo mata, har
ma fiye da baya. Yadda ya ke kula da ita da dukkan al'amuran ta da lafiyar ta sai ya ke tuna mata da
mahaifin sa marigayi Alh. Atiku Dogondaji. Kullum addu'a take yi tana karawa kan Allah ya zaunar da mu
lafiya, ya kara soyayyar Ma'u a zuciyar Attahir, ya kare mata shi daga dukkan abin ki, da sharrin duk wani
mai sharri.
******

Kamar yadda Addah ta ce, sai ta hada mana kasaitacciyar walima don wadanda ba su samu labarin auren
ba cikin ‘yan uwa da abokan arziki su sani. Don haka da ta fahimci Yaya hakurin sa ya kare dole ta soma
aikawa mutanen arzikin ta, ‘yan uwan su Yaya na Dogondaji, abokan arziki na Bebeji wadanda suka yi
zaman mutunci da iyaye na. Ta tada dan aike har garin Babura ta jihar Jigawa ko za'a samu saura cikin
dangin mahaifiya ta Nene Zainabu.
Dan aiken Adda ya dawo da kyakkyawan labarin an samu mata uku wadanda suka tabbatar masa suna da
alaka da Zainabu matar Adamu Bebeji, daga gidan dagacin Babura aka raka shi wajen Inna Asabe, wadda
kanwa ce ga kakar Zainabu, sai Abuwa wadda mahaifiyar su Nene ce ta rike ta har ta yi mata aure duk da
babu alakar jini a tsakanin su.
Sai Jummai matar Baban Nene, amma ta tsufa sosai ba za ta iya zuwa ba, amma Inna Asabe da Abuwa
sun tabbata za su zo in har za a dauki nauyin kai su Sokoto. Wannan bai damu Addah ba, burin ta ya
kasance ina cikin dangin uwa da uba, don haka ta yi alkawarin tura direba ya dauko su tun daga Babura
har Sokoto.
Kafin Aunty Nabeelah ta iso, kayan da ta auno ne suka fara isowa. Bayan kwana biyu ta biyo bayan su,
Yaya tunda ya tafi bai kira ni ba yana ta fushin sa amma yana kiran Adda, yanzu kam Adda har gajiya take
da wayar Yaya, Allah kenan, dama ya ce yana tare da su hakuri.
A satin nan kwata-kwata ban cika lafiya ba, ciwon fargabar aure ake cewa ko me? Kai ka ce wani waje
za'a kaini ba cikin gidan mu ba, ji nake kamar zan yi da Adda, na dai san rayuwar kuruciya ta kare mini,
ina dai daurewa ne ganin hankalin kowa yana kan hidimar da ya sa gaba. Aunty Nabeelah ke tambayar
Yaya Maccido ko ya gaya wa Lubabatu maganar auren sa? Kai tsaye ya ce, Bai gaya mata ba, ya fi so sai na
tare tukunna, sabida ya san halin ta ba za ta bar shi ya zauna lafiya ba. Shi kuma yanzu ayyuka sun masa
yawa, ga na kamfanin su ga kasuwancin malls din su. Wadda a yanzu ya fadada na Abujan ya kara gina
plaza a kusa da waccan, ya bada hayar shagunan.
Aunty ta ce, “Gara ka fada mata, in ta samo labarin a wani wuri abun ba zai yi muku dadi ba. Kuma ka
hada mata kayan fadar kishiya, ko ka ba ta kudin a hannun ta”.
Duk da haka Maccido bai yi wa Lubabatu zancen ba don suna ‘yar dadi kwana biyun nan tunda ya dawo,
ta yi missing dinsa sosai, don bai taba tafiya ya dade haka ba tare da ita ba.
Aunty Nabeelah da kawayenta na Sokoto suka shiga sassan Maccido na cikin gidan, suka sa aka fidda
komai, da ma babu abin da yake mallakin Lubabatu, ba ta zo da komai nata Sokoto ba, don ta san ba
wurin zaman ta ba ne, sai dai ta zo da yawo in ta ga dama.
Zo ki ga inda ake jere mai aji, da ma kuma Yaya Maccido ya sa an yi furnishing gidan gaba daya, har
bangaren Addah. Gida ya koma tamkar sabo, kai ka ce ba a taba zama a cikinsa ba.
Bayan sun gama kafin, Adda ta sa malamai suka yi saukar alqur’ani a cikinsa. Washegari aka yi
kasaitacciyar walimar da Addah ta shirya ta mata zallah, aka yi laccoci masu muhimmanci, sannan aka yi
ta rabon kabakin takeaway da sovaneours, kowa ya tafi gida very excited don bai taba zuwa walima mai
albarka irin wannan ba.

*YIWA KAI HISABI*


*SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)*






Bayan sun gama kafin, Adda ta sa malamai suka yi saukar alqur’ani a cikinsa. Washegari aka yi
kasaitacciyar walimar da Addah ta shirya ta mata zallah, aka yi laccoci masu muhimmanci, sannan aka yi
ta rabon kabakin takeaway da sovaneours, kowa ya tafi gida very excited don bai taba zuwa walima mai
albarka irin wannan ba.
Da daddare ne mutanen Bebeji matar Malam Ayuba, wato Inna Kubra da mutanen Babura su biyu da
aminiyar Adda Hajiya Wasila suka raka ni dakina. Ina kuka sosai kamar ba cikin gidan za a bar ni ba.
Addah don farin ciki sai hawaye ta ke yi, ta shige kuryar dakin ta ta yi wa Allah sujjada da ya nuna mata
wannan rana. Wani dadadden buri da ta ke da shi, amma ba ta taba furtawa ba don tabbacin rashin
yuwuwar sa. Yau ga Ubangiji kunfa-yakun ya ba cika mata burin ta wanda ba ta taba daga hannu akai da
nufin rokon shi ba. Sai dai ta ce ya zaba mafi alkhairi. Kowa ya watse ya bar ni ni kadai, da ma ni ba gwanar kawaye ba. Kuma ba lafiya ce ta ishe ni ba. Zazzabin
ma kara zafi yake yi. Na kira Aunty a waya na roke ta ta ba ni Aasim mu kwana tare.
Ta ce, “A’ah ba zai yiwu ba, in koyi zaman gidan miji ni kadai, kuma sun yi waya da Yaya Maccido yana kan
hanya, sai dai zai kai goma na dare bai iso ba”.
Gaba na ne naji ya yi wani mugun faduwa babu dalili, kamar yau zan fara ganin Maccidon. A daddafe na
yi sallar isha, ko shafa’i da wutri na kasa yi sabida yadda jikina lokaci daya ya rikice.
Wayata na dauko na kira Aunty Nabeelah cikin muryar rashin lafiya, na ce, “Aunty ki zo, saura kadan na
mutu”.
Ta ce, “Assha! Bar kira wa kanki mutuwa, ba ku gama cikawa Adda daki da ‘ya’yan da ku ka yi mata
alkawari ba. Sannu kin ji, stress ne kawai da fargabar da kika sa wa ran ki”.

Kafin minti biyar sai ga ta ta shigo da gorar ruwa da kwayar magani, ta ba ni na sha, ta ce in kwanta in yi
isasshen barci zuwa gobe zan ji garau.
Sai da na kwanta ta rufe ni da quilt, sannan ta juya ta fita.
Lokacin da Yaya Maccido ya iso na yi nisa a barci na, tun a cikin gida Aunty ta gaya masa ya kula da ni
bana jin dadi, amma dai ta ba ni magani na ji sauki har na yi barci. With concern ya ce, “Ko asibiti za mu
je?”
“Ba sai kun je a daren nan ba, kuna iya bari sai Monday ma in raka ta bayan ka tafi, na tabbata zata ji
sauki zuwa gobe stress ne da fargabar aure.
"Fargabar aure?" Yaya ya tambaya.
Murmushi ta yi ta ce "normally 'yammata suna yin hakan in za'a musu aure, ita bata san za'a mata auren
ba sai yanzu take nata fargaban".
Sanda Yaya ya shigo ban sani ba, ya kulle ko’ina, ya saki curtains ya je dakinsa ya yi wanka yana yaba
yadda gidan ya koma cikin ransa. Ya san duka aikin Nabeelah ne, akwai ta da iya style, ga iya zaben abu
mai kyau.
Sai da ya kimtsa tsaf shirin barci ya fesa turaren sa obsession bisa pajamas din shi, ango sosai, sannan ya
nufo nawa dakin, bayan ya kashe wutar falo.
A hankali ya zauna a gefen gadon daidai kaina, yana kallon yadda nake barci cikin nutsuwa, numfashina
na sauka a hankali. Ya dora hannu saman goshina da wuyana ya ji temperature din ya sauka. Ina jin sa ya
russuna ya sumbaci baki na softly, da murmushi ya ce “sleeping beauty”. Tare da gyara min quilt din da
nake rufe da shi, ya yi light off ya shige cikin quilt din shi ma ya kwanta, ya jawo ni a hankali ya shigar
cikin jikin sa, hancin sa yana daidai tsakiyar gashin kaina. A haka muka yi barci, wani barci mai dadin da
ban taba irinsa ba. Ya nemi fushin da yake ta yi ya rasa, tunda finally Adda ta yi masa abinda ya ke so ta
bashi Ma'un sa.
Da asubah bayan mun yi sallah Yaya bai yi la’akari da halin da nake ciki ba. Da lallashi, da ban baki da
zakakan kalamai ya samu abin da yake so, ya karbe budurci na cikin girma da daraja, komai ya faru very
soft and gentle, he didn't hurt me anymore, ya yi ta sa min albarka. Ba yadda bai yi ba mu je asibiti a
washegari ganin yadda na galabaita amma na ki. Ragowar kwanaki biyun da yayi ba abinda yake yi sai
jinya ta, hatta Adda da Aunty Nabeelah tarairayata suke ta yi, Adda da abinici mai gina jiki Nabeelah da
shigowa akai-akai tana duba halin da nake ciki da tabbatar da na sha magani. Kwanansa uku ya koma ba don ya so ba, da niyyar yau yana komawa zai gaya wa Lubabatu auren sa, kada
sai na haihu sannan ta sani, ya kara wani laifin.
****
Ba laifi ya samu tarba daidai gwargwado daga Madam din tasa, amma ‘ya’yan sa sun fi murnar dawowar
sa. Bai damu ba don ya san haka take canza fuska duk lokacin da ya je Sokoton da yake zuwa yanzu

akai-akai. Ya daga Ahsan yana sumbatar sa, yaron ya shiga ransa sosai sabida kamannin shi da ke ga
yaron. Suna cin abinci, wanda ta sa mai aikinta ta yi masa, ta ce,
“Na ga wasu kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login