Showing 27001 words to 30000 words out of 46393 words
Chapter 10 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf
share hawaye, ya hakura da cin abincin ya zura takalmin
shi tare da daukar wayoyin shi guda biyu ya zuba a aljihun shi, ya ce.
“Mu je don Allah, kada ki sa ni in kware da wadannan kananan idanun naki”.
A Ajrah (taxi) muka tafi filin jirgi bayan ya tabbatar na maka niqaabi sai ka ce mutanen takari. Muna zuwa
jirgin wanda ya taso daga Lebanon yana sauka. Sai da aka bata lokaci kafin Aunty Nabeelah ta iske mu, da
gudu na sheka na rungume ta. Aasim da ke gefe ya shiga ture ni yana kiran sunan Babar sa.
Dariya muka yi, na rusuna na sunkuce shi dan lukuti da shi, kamar ba jaririn da na sha rainon sa ba. Sai
Larabci yake yi accent din Lebanon. Yaya ya tura trolley din ta muka nufi inda taxi suke.
Yaya da mai Ajrah suna gidan gaba, ni da Aunty Nabeelah da Aasim muna baya, sai kallo na ta ke yi kamar
yau ta fara gani na. Tana yi tana murmushi. Wanda na kasa gane ma'anar sa.
Na ce, “Aunty, wannan kallon fa?”
“Ina kallon yadda kani na ya iya kiwo ne, gabadaya kin yi kyau. Kin zama kamar balarabiyar Maghrib”.
Na rufe fuska ina dariya, na ce, “Aunty ai kullum fada muke yi”.
Wani takadarin murmushi ta yi, ta ce, “za ku yi mai dalili ne, wannan na rashin dalili ku ke yi”.
Ban dai gane abinda Aunty Nabeelah ke nufi da hakan da ta ce ba.
Daidai lokacin da muka shiga farfajiyar asibitin Doctor Sulayman Faqeeh. Tun kafin Yaya Maccido ya fito
na bude kofar bangare na na fice dauke da Aasim. Ina kallon su suka tsaya gefe suna magana wadda ban
san me suke tattaunawa ba. Daga baya suka shigo muka jera gabadaya zuwa dakin V.I.P da aka sake
maida Addah.
Ina murda kofar dakin gabana ya yi wani irin muguwar yankewa ya fadi, sakamakon kalmar shahada da
na jiyo Addah na furtawa cikin wata irin murya da ban taba jinta da ita ba.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870*
```HISABIN NAFS```
(YIWA KAI HISABI)
Adda muka taras na zaune a kan gado, jingine da filo sai salati take a fili, salatin da tun daga waje ya
tsorata mu, ya sa muka karaso dakin da gudun mu. Na karasa da hanzari na rungume Addah ta. Hawayen
farin ciki na zubo min. Farin cikin ganin cewa lafiyar ta kalau. Ga ta zaune akan kafafun ta. Amma tabbas
salatin da muka tsinkayo tun daga waje tana rafkawa ya bala'in tsinka mana zuciya dukkan mu.
“Ma’u na, Ma’un Addah, sannu da kokari kin ji? Allah ya baki ladan jinya”.
“Adda, yau farin ciki zai kashe ni, kin samu lafiya, Allah abin godiya”.
Aunty Nabeelah da Yaya Maccido suka karaso gaban gadon, Aasim yana hannun Yaya Maccido, idanun
Maccido duk sun raina fata. A sanyaye ya ce,
“Addah, sannu da jiki, Allah ya sa kaffara ne, Allah ya kara lafiya”.
Ta amsa ba yabo ba fallasa tana mai kawar da kai daga gare shi. Tare da daure fuska. Aunty Nabeelah ta
kama hannun Yaya Maccido ta rike cikin nata ta ja shi suka karasa gaban gadon Addah. Su duka biyun
suka tsugunna a gaban ta bisa gwiwoyin su. Cikin sanyin murya Nabeelah ta soma magana da tattausar
muryar da duk mai imani dole ya tsaya ya saurare ta.
“Addah, Maccido ya yi laifi, laifi kan laifi kam ya yi shi. Tun kina alkunya har bacin ran ya fito fili, ya kuma
shafi lafiyar ki. Maccido mutum ne dan adam kuma ajizi kamar kowa, wanda bai fi karfin sharrin shaidan
da rudin duniya ba, har ma da iblisanci irin na mata.
Addah yau ga Maccidon ki a gaban ki, ya kawo kan sa matsayin mai laifi a gare ki, yana mai amsa dukkan
laifukan sa. Fatan sa kawai ki yi hakuri ki manta komai, ki yafe masa. Ki kuma ba shi dama ya gyara
kurakuren sa.
Tun ranar da ya iso ya same ki cikin halin da ki ke ciki, sakamakon wayar da Muhsin ya yi masa, tun kafin
lokacin dama yana cikin damuwa da nadamar da ya rasa ta yadda zai bi ya gyara wannan kuskuren na
kaurace miki, ya ce shi kansa in za'a kashe shi bai san dalili ba, ya shiga tunanin hanyar da zai wanke
zuciyar ki, ya kuma zama kullum ko ba ya nan wani bangare nasa yana tare da ke wanda zai hana ki yin
kewar sa da tunanin sa ko iyalin sa.
A kan haka ne Maccido ya yanke shawarar auren Ma’u, Asma’un ki….”.
Daga ni har Adda da ta sunkuyar da kai a firgice muka dago muka dubi Aunty Nabeelah. Wata irin firgita
da ban taba yin irin ta a rayuwa ta ba. Idanu na suka yo waje bakidaya ina son jin ainihin me Aunty
Nabeelah ke nufi???
Ba ta damu da reaction din mu ni da Addah ba ta ci gaba da bayanin ta hankali kwance, murmushi dauke
bisa kyakkyawar kamilalliyar fuskar ta.
"A ranar da ya kira ni ya gaya min, na ce ban yarda ba in har ya san ba son Ma’u yake ba, ya kyale ta a
hankali za ta samu mijin ta. Sannan Ma’u yarinya ce ba za ta iya zama da kishiya ba. Balle hamshakiya irin
matar sa, wadda uwar sa ma ba ta dauke ta a bakin komai ba.
Maccido ya gaya min duka hujjojin sa kuma na amince da su. Ya ce bai zo neman auren Ma’u don ya
faranta miki kadai ba, sai don yana bukatar karin auren sabida matsalolin cikin gida da yake fuskanta
daga matar sa, sannan ya hanga ya duba babu wadda zai aura ya wanke zuciyar ki, ya yi miki ramakon
duk abin da ki ka rasa daga suruka da jikokin da ba a bari kin shaqu da su ba irin ASMA’U.
A takaice ma dai a kan karan-kansa yana son ta Addah, tuntuni, tun tana kankanuwa. Lokacin da yake son
yin aure bata isa aure ba, shi ya sa ya nemo aure a waje, amma wannan niyyar tana nan cikin ran sa.
Na gamsu da dukkan bayanan sa Addah, ya kuma ce min zai dauke ki zuwa asibiti a Jeddah, yana so a
daura aure kafin ku tafi don Ma’u ce mai jinyar ki, kuma bai kamata ya tafi da Ma’u irin wannan tafiyar
babu aure tsakanin su ba.
Na ce hakan ba zai zamo gaggawa ba? Ya ce ai shi so yake duk ranar da ki ka bude ido, ki gan shi da Ma’u
matsayin matar sa, watakila ya ci alfarmar hakan ki yafe mishi dimbin laifukan sa gare ki.
Adda kin ji yadda muka yi da Maccido. Na amince da duk abin da ya ce, na ce ya je ya samu Baffa Bilya ya
gaya masa komai, sai su je Bebeji su nemi Malam Ayuba da ki ke yawan ba ni labari, wanda ki ka ce shi ne
aminin Baban Ma’u tun daga kuruciya har girma. Su kai masa sadaki a daura aure.
Muhsin shi ya jagoranci su Baba Bilya zuwa Bebeji, ba su sha wahalar samun sa ba duk da ya tsufa,
bayani kadan suka yi masa ya sa kukan farin ciki sabida wannan karramawa da suka yi masa na ba shi
waliccin auren Ma’u.
Shi ya ja su zuwa gidan Hakimin Bebeji ya yi masa bayanin Ma’u, shi ma sosai ya ji dadi, don ya ce Baban
Ma’u mutumin sa ne, duk Juma’ah sai ya zo ya gaishe shi. Kasancewar ranar juma’a ce sai Hakimi ya bada
sanarwa cewa bayan sallar juma’a akwai daurin auren ‘yar Malam Adamu mai goro.
Aka yi daurin auren cikin farin ciki na zukata masu yawa, Baban su Ma’u ya sha yabo da addu’a daga
bakin jama’ar garin Bebeji kamar yadda Muhsin ya labarta mini”.
Ta sa hannu cikin jakar hannunta ta fiddo wani dan akwati tana murmushi, ta dora wa Addah a kan cinyar
ta,
“...Addah ga sadakin Ma’u. Muhsin ya gaya mini kin sha ce masa 'sisinan gwal' shi ne sadakin Ma’un
ki…”.
Ta bude akwatin ta kama tafin hannun Addah ta dora mata.
Kuka ne ya kubuce wa Addah Kilishi, ta kamo hannun Nabeelah ta kamo na Maccido ta ja su jikin ta ta
rungume su.
“Allah ya yi muku albarka baki dayan ku, yau na san na haifi ‘ya’ya, wadanda ko bayan raina za su rike min
marainiyar ‘yar dan uwana da amana da daraja da kauna. Barakallahu fi-kum”. Ta sake kecewa da kukan
farin ciki.
A hankali ba tare da sun ankara ba na dinga ja da baya a hankali, har na bude kofa na fice daga dakin.
Da sauri-sauri nake tafiya a gefen titi bana ko ganin gabana, ina tafe ina kuka da hawaye shabe-shabe ban
damu in share ba. Ban damu da kallon da mutane suke min ba. Ni na ce ina son Yaya Maccido? Ko kuwa
shi ke nan don ya maida ni kaza yana neman hanyar shiryawa da mahaifiyar shi sai ya kare a kaina? Ni me
zan ci da mai mata da ‘ya’ya? Allah na tuba kuma mijin Lubabatu? In rasa wanda zan aura in auren zan yi
sai ragowar wata? Ai wallahi ko auren zan yi ni ma sai dai na auri yaro, kuma balarabe irin na Aunty
Nabeelah… mijina ni ni kadai, ba mijin wata ba. Ban da karya mai mace kamar Lubabatu, me zai ci da ni,
in ba yaudara da rainin hankali ba???
Tunanin da nake ta yi ke nan ina tafe ina gursheken kuka, ban ankara ba na ga wata farar ajrah ta sha
gabana, saura kadan ta take kafafu na.
Yaya Maccido da Nabeelah ne suka bude kofofin motar suka fito suka sha gabana, na dage riga ta zan
taka da gudu, Maccido ya damke ni.
"Ke kina da hankali kuwa? Ko kin dauka a Nigeria ki ke?”
“Daga turu na fito”. Na fada cikin karajin kuka ina fiffizgewa daga hannun sa.
Aunty Nabeelah cikin mamaki ta ce,
“Ma’u ba za ki nutsu ba? Kina so ki jawo mana jami’an tsaro ne?”
Hararar ta na yi da jikakkun idanuna, na ce, “Ai komai ke ce sila, kin bi bayan kanin ki kun zalunce ni, ni na
ce miki ina son shi? Akalla a ba ni hakki na na dan Adam a tuntube ni kafin a daura min aure? Ko kuwa
don shi shi ne shafaffe da mai, ya gama yi wa Adda cin kashin sa sannan ya zo ya yi abin da yake so a
kaina?”
Ji ka ke taaas! Yaya Maccido ya dauke ni da wani lafiyayyen mari. Na sa hannu na dafe kunci na ina jin
kamar fatar fuskata ta daye.
“Ashe ba ki da kunya? Auntyn ki ke gaya wa haka? An aure ki ba da sanin nakin ba, don Allah ki je ki maka
ni a kotu a fidda miki hakkin naki”.
Na rushe da kuka.
“Don an ga ni marainiya ce ba uwa ba uba… wayyo Nene, wayyo Baba…...”.
Yaya Maccido bai tsaya sauraro na ba da kwarmaton da nake yi, don har na fara tara musu mutane, ya
danna ni a motar da suka zo, Aunty ta shigo mai motar ya ja. Na ga za a wuce asibiti ba su shiga ba na
kara rusa kuka.
"Ni ku sauke ni wajen Addah, babu ni babu ku. Ai ba zaman ku nake ba”.
Aunty dai kallona kawai ta ke tana mamaki, in wani ya ce mata ni ce wannan ba idanun ta ne ya gane
mata ba, lallai za ta musa. Ashe haka nake??
Hotel din mu muka nufa, Aunty Nabeelah ta kama hannuna muka fito har zuwa lokacin kuka nake yi
wurjanjan. A reception muka jira Yaya Maccido ya je ya kama wa Aunty daki ya dawo muka rankaya ta
cikin lifter zuwa sama.
Ya bude dakin muka shiga dukkan mu, Aunty ta zaunar da ni a gefen gado. Ta zauna kusa da ni, yayin da
Yaya ya tafi kujera ya zauna. Ta kira sunana a tausashe,
“Asma’u!”.
Ban amsa ba, amma na dago na kalle ta da rinannun idanu na da suka kada suka yi jajawur.
“Kina so ki mayar da farin cikin Adda bakin ciki?”
Da sauri na girgiza kai ta ce, “To why this? In kin bi komai a hankali ai ni mai yi miki duk abin da ki ke so
ce. Maccido bai isa ya shiga tsakanin mu ba, ki kwantar da hankalin ki, ki gaya min duk abin da ki ke so na
yi miki alkawarin in bai fi karfin iko na ba zan yi miki”.
Ai jin haka na ce, “Aunty kawai ki ce masa ya sake ni, wallahi bana son shi!”.
Aunty tana hadiye dariyar da ta zo mata ganin Yaya Maccido ya yi tsumuu! Ta ce, “Saboda me ba kya son
nasa?”
Babu ko kunya na ce, “Ni me zan yi da shi? Mutumin da matar sa da ‘ya’yan sa watakila ma ya fara
furfura”.
Duk yadda Aunty ke hadiye dariyar ta sai da ta sake ta wannan karon. Ni kuwa na ci magani, don zuciya ta
daya nake magana, ta daura hannunta bisa nawa ta ce,
“Ma’u ba kyau cin fuskar miji fa!”.
Na zumburo baki na ce, “Kada ki kara cewa miji na, mijin Lubabatu dai, ni me zan ci da shi? Wallahi
Balarabe nake so irin naki”.
Da sauri yaya Maccido ya mike ya bar dakin, fuskar sa kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas. Aunty
Nabeelah ta dinga kyalkyala dariya, ta ma rasa me za ta ce mini. Na mike ina fadin,
“Aunty tashi raka ni dakin sa in kwaso kayana, da ma kamar a kan kaya nake zaune a dakin. Don ya raina
min hankali ya ce ba shi da kudin kama daki biyu, ina ya samo na wanda ya kama wannan?”
Aunty ta ce, “Um-umh Ma’u, an dai gama shan soyayya shi ne don an gan ni za a wani ce za'a kwaso
kaya? To ba da ni ba, ba ruwana”.
Kuka na sa mata da karfi ina fadin, “Ni wallahi babu soyayyar da mukai, kullum fada muke yi! Kuma ba
gado daya muke kwana ba”.
Ta ce, “Fadan soyayya ba?”
Na ce, “Wallahi na kiyayya”.
Aunty ta koma serious ta ce, “Ma’u, ki nutsu mu yi maganar fahimta. Maccido yanzu ko kin ki ko kin so
mijin ki ne, duk kuma abin da ki ka yi masa na kyautatawa ko akasin ta, mala’iku suna rubutawa. Don
haka ki shiga hankalin ki, in ke wata mai wayo ce wannan tafiyar dama ce ki ka samu da za ki mori mijin ki
ke kadai, ki shiga jikin sa, ki mantar da shi kowacce diya mace. Amma don sakarci har kin fara zancen a
raba daki. Ma’u miji ne Allah ya kashe ya ba ki daga sama don haka kar ki yi wa Allah butulci. Wallahil
azeem Maccido na son ki, sai da na shaidi wannan kafin in yarda in shige masa gaba ga auren ki. Ga shi
dan uwan ki, wanda ya san ciwon ki, ya san mutuncin iyayen ki. Na miki alkawarin muddin ina raye ba za
ki taba da na sanin auren Maccido ba.
Ma’u ba kya jin tausayin Addah? Ba za ki so ki zama tsanin da Dan ta zai dawo gare ta ba? Ki haifa mata
jikoki ki bata ta raina a daina yi mata rowar ‘ya’yan Maccido? Ma’u in ba ki yi wa Addah wannan aikin ba,
wa zai yi mata shi da zuciya daya?”
Jiki na ya dan yi sanyi da kalaman Aunty Nabeela. Amma hakan ba zai taba sawa in karbi wannan auren
ba. Ta dora hannu a kan kafadata ta ja ni jikin ta a hankali cikin sigar rarrashi.
“Maccido abun tausayi ne Ma’u, saura kadan mace ta kai shi wuta. Ki zama mai aikin jihadin ceton
soyayyar uwa da Da. Ba ruwan ki da matar sa, tana Abuja kina Sokoto, me zai dame ki da ita?”
Zuwa wannan lokacin Aunty Nabeelah ta dan kashe min jiki. Abin da na ki yarda da shi har yanzu shi ne
Maccido na so na. Zan yi kokari in gane hakan da kaina komai daren dadewa kafin in yarda da hasashen
Aunty Nabeelah.
Ta mike ta ce, “Ban zo don in rashe ba, na zo ne don in karbe ki jinya, ke kuma ki yi amarci yadda ya
kamata. Mu je toilet da kaina zan yi miki dilka da halawa, sannan in yi miki wankan turaren da na zo da
shi takanas, sabida ke”.
Duk abin da ta fada din kuwa sai da ta yi min. Ina kumburi ina komai sai kara kwantar min da hankali ta
ke yi da tausasan kalami da misalai kala-kala. Ta dauko wasu tablets masu kama da magungunan
supplement ta ba ni, ta ce in hadiye su. Sai da ta tsaya a kaina ta mika min ruwa, ta tabbatar na hadiye
din. Ta bude jakarta ta fiddo wani lallausan swiss lace da aka yi wa dinki senegalese ta ce su zan sanya,
sannan ta sake feshe ni da turare ta yi min daurin kai very cute da shi. Ta ja baya ta kalle ni sosai ta ce,
"saura light make up".
Dan karamin akwatin kwalliya ta dauko a kayanta ta zaunar da ni a gabanta ta yi min sassaukan make-up.
Albarka ta shiga sanya min kamar wata uwa ta sannan ta kama hannu na bayan ta rufa min babban gyale
kalar adon leshin ta kira wayar hannun ta.
“Kana ina Maccido?".
A kasalance ya ba ta amsa,
“Ina daki, kaina ke ciwo, sai dare zan maida ku wajen Addah din, may be kafin nan na samu kan ya sarara
min”.
“Nawa ne lambar dakin naku?”
“104”.
Daga haka ta maida wayar jakar ta, ta kama hannuna muka fita.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
Ta lifter muka bi zuwa kofar dakin. Ni dai kallon komai nake kamar a majigi. Majigin ma na cikin mafarki.
Wai