Showing 12001 words to 15000 words out of 46393 words

Chapter 5 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf

Aunty Nabeelah ta yarda sai gobe da asubah mu tafi ba. Sai da na
tabbatar Yaya Maccido ya bar dakin sannan na fito.
Muhsin ya bi ni da kallo har na samu gefen gado na zauna.
“Ma’u na, Ma’un Addah, wa ya taba mun ke?”
Ya yi maganar cikin raha irin tasa, amma ko kadan ba ta ba mu rahar ba ni da Aunty.
Dole ya tashi ya bar mana dakin, Aunty Nabeela ta dauki wayar ta da ke tsuwwa suka canza harshe ita da
Fa’iq din ta. Sai larabci suke zumbudawa abin ya yi matukar burge ni. Na ce a raina, ina ma ni ma in auri
Balarabe irin mijin Nabeelah? Shi ba zai yi min gorin boko da ban iya ba! Ba zai damu ba don ban iya
karatun boko ba. Duk da dai yanzu a Sokoto ba kamar Bebeji ba, ba laifi ina tsintar ‘yan abubuwa da ba za
a rasa ba sabida koyarwar Muhsin da dagewar sa wajen ganin ba a yi min maimaicin aji ba.
Sai ga Aunty na kyalkyatar dariya da mijin ta kamar ba ita ce ke kuka yanzu ba, yayin da ni kuma na shiga
hidimar Aasim. Canza masa diaper na yi na hada masa madarar sa na dauke shi na soma ba shi.
Bayan sallar isha Aunty ta ce in tattara mana komai namu tun yanzu kada mu makara da safe.
Wajen karfe tara na dare Yaya Maccido ya shigo dakin, a yanzun kananan kaya ne a jikinsa shat da wando,
samfurin Tommy Hilfiger ruwan bula mai haske da mai turuwa, duk da ya rame daga yadda yake a baya
kyansa yana nan bai je ko’ina ba, sannan daukan wankan sa sai abin da ya yi gaba. Ya dube ni ina jijjiga
Aasim, ya ce, “Ke kullum ba kya zama ne sai da yaro a hannun ki? Ki bar mata dan ta mana ko tare ku ka
haife shi?”
Aunty Nabeelah ta galla masa harara, ta ce, “Ai ita ta san darajar na gaba da ita, ta kuma san nata shi ne
nata. Hidimar da ta ke da dan uwanta ba zai gajiyar da ita ba”.

Murmushi ya yi ya zauna dab da ita, don ya san magana ta gaya masa, duk dakin ya amshi bakuncin
turaren sa obsession (by CK). Har wani lumshe ido na yi don dadin turaren Yaya. Ya san Aunty Nabeelah
bakar magana ta gaya masa, ya rasa laifin da ya yi mai zafi da yake fusata ta haka. Iyakar iyawar sa ya ba
ta hakuri dazu kuma ya amsa laifin da take tuhumar sa da shi na watsar da Addah, ya mata alkawarin zai
zo ya ga Addah, ya ba ta hakurin rashin zuwan sa da rashin kiran ta, shima ya rasa abinda ya ke hana shi
shiga Sokoto, ji yake kamar bazai gane hanyar garin ba, ya fada mata sau da dama ya sha kama hanya
amma sai kawai ya ji shi ya karya kan mota ya dawo gida, ya bata hakuri yadda ya kamata amma duk
bayan dakika Aunty Nabeelah sake sabunta laifinsa take ya koma sabo fil!
Ta lura shi sam ba ya ganin girman abin da ya yi, ya yi admitting ya yi laifin ne ganin bacin ranta mai
tsanani, ban da haka ai ya san Adda lafiya ta ke tunda yana gaishe ta a waya, ta san kuma irin
commitments dinsa. Ko ita Addar ba ta korafi sai ita sarkin fushi da fushin wani.
Ya dube ni kadan, “Ki je ki dafa mana wani abun mu ci, matar gidan ta jima da yin barci, ba zata san kin
shiga kitchen din ba, but be careful kada ki bata mata wani abun ta gane kin shiga”.
Wani bala'in haushi ya kama Aunty, ta ce, “Ba za ta dafa ba, na ce ba za ta dafa ba din balle ku ce ta lalata
muku cooker gass, ko ku ce mata bagidajiya. Ka je ka ci gaba da ci a inda ka saba ci kafin mu zo, na
tabbata matar nan azabtar da kai take da yunwa ko makaho ya shafa ka ya san wannan, mu da abincin
gidan ka haihata-haihata Maccido. Wanda muka ci ma Allah ya amfana”.
Ya jefar da kai gefe zara-zaran gassun idonsa na lumshewa, ya ce.
“Wai Yaya Nabeelah me ya sa duk kin bi kin tsane ni yanzu? A baya ba mai so na irin Yayata Nabeelah, ba
wanda ya isa ya taba mata ni. Amma tunda ki ka zo ban samu tattausar kalma ko daya daga bakin ki ba, a
haka ki ke so mu rabu ki koma inda sai na shekara ban gan ki ba?”
Zuciyar Nabeelah ta dan sassauta, kalaman bakin sa sun bata tausayi, kowa ya san Tahir is her favourite
brother, so ta ke ta fahimtar da shi kuren sa ya kuma fahimci wannan matar da ya aura ba alkhairi ba ce a
gare shi, amma ya ki ya gane inda ta dosa. Kwata-kwata baya ganin laifin matar nan tasa, ko aibun ta. Ba
kuma za ta fito fili ta fada ba, Adda ta hane ta da tada tarzoma.
Saboda Allah a matsayin ta na Yayar mijin ta uwa daya uba daya ba kanwar sa ba, wadda ba ta taba zuwa
gidan ba ko sau daya, ta cananci irin tarbar da ta yi mata?
Ko sau daya ba ta bata abinci ba, sau daya ta zo ta gaishe ta daga bakin kofa ta gaya ma Ma’u magana, ba
su kara ganin ta ba. Babban bacin ran Aunty Nabeelah irin rayuwar da ta fahimci ana yi a gidan, ko abinci
ba'a ba shi, matar gidan ce master, shi subordinate. Amma ko a jikin sa.

*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE & TAKORITES*

*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI (07030137870)*



((6))Ta sauke numfashi a hankali, yanzun a cikin kallon da ta ke yi masa akwai sassauci da kauna.
“Attahir!”. Ta kirayi sunansa a hankali.

Ya dago kyawawan idanunsa ya dube ta.
“Me ya sa ka wannan ramar?”
Dan murmushi ya yi, ya ce, “Yanayin aikin mu ne kawai da ba hutu”.
Ba tare da ta yarda ba, ta ce,
“Addah yaushe za ka je ka ganta?”
“Insha Allah idan Lubabatu ta haihu, zuwa next month za ta shiga EDD dinta, za mu taho gabadaya”.
“Allah ya raba lafiya”.
Ya amsa da, “Ameen”.
Hannu ya sa a aljihunsa ya zaro bandiran kudi har guda hudu ya dora ma Aunty bisa cinyar ta.
“Ga shi ku sha mai, wannan yarinyar a saya mata wani abu kada Adda ta ce ban ba ta komai ba”.
Aunty ta ce, “Sunanta ASMA’U ba wannan yarinyar ba. Ta gode”.
Sallamar mu da Yaya Maccido ke nan.

Bayan ya koma dakin barcin su da kamar mintuna talatin Aunty tace inje in dauko mata kofi a kitchen din
zata sha magani. A hankali na bude kofa na fita ina taku cikin sanda kada su ga na shigar musu kitchen, na

dauko kofin na dawo zan wuce ta kofar dakin da suke naji tashin muryar Yaya, kamar an ce da ni in
tsaya.... kawai na tsaya jin yana magana kamar zai yi kuka.
"Amma Lubabatu kina tsoron gamuwar ki da Allah kuwa? Tun shekaranjiya nake bin ki akan ki bani hakki
na kina wulakanta ni, kawai saboda 'yan uwa na sun zo gidan ki, ke su waye ba kya kawowa daga gidan ku
na taba nuna miki bacin rai ko bakin halin da kike nuna min?
Kinsan dai bani da kamar su duk fadin duniya dole su zo inda nake. Lubabatu in ban zo wajen ki ba
matan titi kike so inje in nema? Kin san dai ina jure komai cikin tarin wulakancin ki, amma banda wannan
horon naki.... Don Allah Lubabatu ki min rai...zan iya mutuwa kafin safe....".
Ji nayi ya karasa maganar muryar sa na rawa. Yana rufe baki ta bishi da mugun tsaki. "Ai na gaya maka
this is your punishment, gobe ka sake basu fuskar zuwar mana gida, wannan Nabilar mai idanun
munafurci a cikin idon ta na gane bata kauna ta. To sai dai ta mutu amma bata isa ta fidda ni daga gidana
ba don ni wargi ce daidai kungurun kowa, wallahi ta dade bata zo ganin kwaf gida na ba......".
"Duk na ji Sweetheart, mun yi miki laifi nida 'yan uwa na, but pls don't punish me that way......Bani da
wannan juriyar kin sani.....". Da dan banzan sauri na daga kafa na bar wajen zuwa dakin mu, jiki na babu
inda ba ya rawa, ban san me yake rokon ta yi masa ba amma na san bai kamata ba tsayawar da na yi.
Kwana na yi da abun a raina, yana ci min rai, ashe Yaya Maccido duk kwarjinin nan nasa a cikin gida
kwallo ake da shi kamar ball ko gare-gare abin wasan yara? Sai na samu kaina da mugun jin haushin
Lubabatu, don ta samu Allah ya bata miji kamar Maccido shine take wulakanta shi? To ita meye matsalar
ta da 'yan uwan sa ne? Me muka tare mata???
Bani da wanda zan gayawa abinda na ji ba tare da yayi min fada ba, don haka na bar abun a raina amma
ya kasa bace min a zuci.
Washegari ba mu sa Lubabatu a idon mu ba har muka shiga mota, Yaya kam tunda ya dawo masallaci bai
koma nasu dakin ba yana tare da mu har muka shiga mota. Kamar ba za su rabu ba shi da ‘yan uwan sa,
haka Muhsin ya ja motar ya bar Yaya with nostalgia (begen gida).
Tunda muka kamo hanya Aunty da Muhsin ke tattaunawa a kan abin da suka gano gidan dan uwan nasu.
Ina ji suna shawarwarin abin da za su fada wa Adda da wanda ba za su fada mata ba. Tunda aka fita garin
Abuja barci ya yi awon gaba da ni. Ba ni na farka ba, sai da muka shiga Kaduna.
Mun wuni sur! A kan hanya, sallah kadai ke tsaida mu. Sai kuma in mun samu gidan cin abinci mai kyau
mu tsaya mu saya. Har Allah ya kawo mu gida Sokoto lafiya.

***​***​***
Allah sarki Adda! Murnar da ta yi na dawowarmu lafiya tana da yawa.

Bayan kwana uku muka shirya muka raka Aunty Nabeelah Dogondaji wajen dangin mahaifin su, ba mu
kwana ba a ranar muka dawo, Aunty Nabeelah ta soma shirin koma wa Beirut.
Ana gobe za su tafi na sha kuka sabida Aasim, Aunty tana ta tsonakata wai ya kamata Addah ta yi min
aure in je in haifo mata yaro mu yi ta raino. Addah ta ce, “Mai auren Ma’u ai sai ya shirya, don da sisin
gwal za a biya ni sadakinta”.

Washegari Aunty ta koma Lebanon.

Ranar wata lahadi na dawo Tahfiz na ga wata bakuwar tsaleliyar mota a kofar gidan mu. Sai sheki da
daukar ido take yi. Wannan ya tabbatar min baki ne muka yi. Ban bi ta falo ba ta kofar kicin na bi zuwa
daki na na cire hijab na canza kayan jiki na daga uniform zuwa na gida, na kishingida ina hutawa kafin
lokacin sallar magriba ya yi.
Kukan jariri na ji duk ya cika gidan, ba shiri na zabura na fito don tantance daga inda nake jin kukan. A
daidai kofar shiga falon muka gabza karo saura kadan na fadi, na yi saurin kama marikin kofa. A hankali
na cira kai don ganin da wa na gabza karo, idanuna suka sauka a kan Yaya Maccido. Yana sanye da wata
danyar shadda milk colour wadda aka yi wa aiki da zare ruwan kasa turarre, kansa da hula ita ma ruwan
kasar ce. Ba laifi wanan karon ya dan yi haske, amma ramar sa tana nan, kuma kyawun halittar sa
koyaushe kamar karuwa yake. Kallon sa na tsaya yi na kasa cewa komai. It’s exactly one year rabon sa da
gidan nan, don haka zuwan na shi ya dan sa ni a kokonton anya shi ne?
Tsaki ya yi ya wuce yana fadin, “Be careful in kina tafiya mana!”.
Wani irin lumshe ido na yi wanda ban san lokacin da na yi shi ba. Kamshin turaren Yaya Maccido da nake
matukar so har cikin tsokar zuciyata. Ina nan tsaye na kasa tabuka komai, Addah ta fito za ta wuce ta
same ni a wurin a tsaye.
“Me ki ke yi tsaye a bakin kofa? Ki shiga mana? Kin yi ‘ya, tun dazu suka sauka”.
“Adda, waye ya haihu?”
Ta ce, “Lubabatu”.
Da hanzari na na fada falon Adda, ido na ya sauka a kan Aunty Lubabatu rungume da jaririyar ta. Ta sha
kwalliya kamar wata matar gwamna ba matar Maccido ba. Tana gani na ta sha bula. Na karasa da farin
ciki na ina fadin.
“Aunty sannun ku da zuwa, ba ni babyn in gan ta”.
Kamar ba za ta bayar ba, sai kuma ga Yaya Maccido ya sako kai falon, sai ta miko min ita. Na zauna a gefe
rike da cute jaririyar ina ta kallon ta. Tsabar farin ciki na manta cewa Yaya Maccido ba abokin hira ta ba
ne, amma ban san sanda na ce,

“Wallahi Yaya da kai baby ta ke kama, komai da komai”.
Zan iya cewa, wannan ne karo na farko da Yaya Maccido ya yi min murmushi a duniya, tare da cewa, “Ni
kuma tun sanda aka haife ta da ke ta ke yi min kama, musamman hancin ku”.
Na washe baki, dadi kashe ni!.
Aunty lubabatu ta balla min harara, shi ma ta balla masa tasa, ta ce, “Allah ya sauwake. Ni ‘ya ta ba ta
kama da kowa daga uwar ta sai uban ta”.
Fuskar Yaya Maccido ta muzanta da kalaman Lubabatu, amma bai ce komai ba, ni kuma uwar ‘yan
kankanba na mike zan tafi da baby daki na. Da sauri Aunty Lubabatu ta ce, “Kawo ta…”.
Yaya ya dago kai daga kan wayar sa ya dan dube ni, ya ce,
“Je ki da ita, in ta yi kuka kya kawo ta…”.
Ai kafin ya rufe baki na yi waje, rungume da baby, ina ji Yaya na fadin.
“Wannan abin da ki ke yi Lubabatu ba daidai ba ne. Kanwata ce fa!”
Duk da ban kalle ta ba na san gatsine da kyabe bakin da na lura tun zuwan mu gidan ta dabi’ar ta ce ta yi.
Ta ce,
“Ai fa na ga Muhsin ne ya sha nono ya sakar mata. Ni irin wadannan jajibe-jajiben dangin bana yarda da
su. Gara ma ka canza mata suna daga kanwar ka zuwa dangin-dangaro".
Da sauri na karasa ficewa ban san amsar da Yaya Maccido ya ba ta ba. Na wuce ta kicin inda Addah ta
tsaya tare da Hawwa mai aikinta suna hada wa su Yaya abinci. Adda ta dube ni ta ce, “Taufa! An yi ‘ya yau
raino sai inda mai ya kare”.
Dariya na yi na wuce zuwa daki na ina ta lelen ‘ya ta. Ji nake kamar ni na haife ta. Kuma wani ikon Allah
sama da wajen awanni biyu ba ta yi min kuka ba sai baccinta ta ke a gado na. Kafin uwar ta ta biyo
sawunta ta amshe abar ta wai za ta ba ta nono.
A bakin Adda na ji sunan yarinyar Ihsan. An ce tsakanin Da da mahaifi sai Allah, wannan haka yake, duk
laifin nan da Yaya Maccido ya yi wa Addah farin cikin ganinsa da na haihuwar Ihsan ya shafe komai. Sai
nan-nan ta ke da su, ta ce min sati biyu za su yi. Ni da Hawwa ne muka je muka gyara ko’ina na sassan
Yaya Maccido muka shigar musu da kayan su da duk abin da za su bukata.
A zaman nan nasu na sati biyu na aikatu sosai da hidimar abincin su da rainon Ihsan. Uwar ta na yakice
ni, tana min kora da hali, tana nesan ta ni da ‘yar ta, amma ni din kamar mayya na like wa Ihsan. Ko ba
komai yarinyar jini na ce, kuma son yara a jini na yake, shi ya sa sam bana damuwa da wulakancin
Lubabatu, har wankin kayan Ihsan ni nake yi in shanya, in sun bushe in kwashe in shigar mata da su.
Canza mata diaper akai-akai da yawan ba ta ruwan zam-zam da Adda ta ce a dinga ba ta, duk da uwar ta
bata so a bata ruwa..

Suna gama sati biyun su suka hada inasu-inasu suka koma Abuja. Dama kamar akan kaya suke. Gidan mu
ya koma yadda yake, don kewar yarinyar komawa na yi kamar an yi min mutuwa. Muhsin ya yi ta tsokana
ta, wai in rabu da Adda mu yi auren mu, mu haifo namu a daina yi mana kwalele da ‘ya’yan mutane.
Na ci gaba da zuwa makaranta da Tahfiz da yamma. Daga aji biyar Muhsin ya bar sakandire, ya zana Waec
da jamb, kuma cikin ikon Allah ya haye. Ya samu gurbin karatu a jami’ar DanFodiyo inda zai yi nazarin
tsimi da tanadi (Economics).
Ni kuma a sannan na shiga aji shidda da kyar da sudin ludayi. A wannan lokacin makerin budurci ya gama
kera ni. Na zama budurwa sosai, amma ba ni da cika ido, ga ni nan ‘yar daidai, komai nawa ya yi daidai da
inda Ubangiji ya halicce shi. Ni kaina na san babu ni a jerin kyawawan mata, amma ina kokarin gyara
kaina irin na ‘yammatan da suka san ciwon kan su.
Addah kan ce, kwarai na ke da tsafta kamar Nabeelah, kuma kamanni na da Nene yanzu sun fi na baya
fitowa sosai.
Tun zuwan su Yaya Maccido lokacin haihuwar Ihsan da komawar su ba mu kara jin duriyar su ba. Adda na
lissafe da watanni daidai har guda goma sha biyar.
Da farko yana kokarin kiran waya lokaci-lokaci ya gaishe ta har ya kanga mata gwalantun Ihsan a wayar,
amma daga baya wayar ma ta gagara.
Lubabatu kuwa ba ta taba kiran Addah ba ko don gaisuwa tun auren ta da Yaya. A yadda take-taken ta ya
nuna shi ne, ita irin matan nan ce wadanda in sun auri namiji shi kadai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login