Showing 36001 words to 39000 words out of 46393 words
Chapter 13 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf
ya dago lumsassun idanun sa muka hada ido, ya sakar min harara ganin ina dariyar su ciki-ciki,
bayan shi ya fada ne don mu ji haushi ni da Addah, yayin da ni kuma na lumshe masa nawa idanun cikin
wata irin siga wanda bansan lokacin da na yi hakan ba...
Da sauri ya juya ya fice ya bar dakin.
Washegari tun kan mu tashi Yaya da Al-Qasim wanda zai tuka shi sun yi sammako sun kama hanyar
Abuja.
Da kayan mu suka iso na ba wa Muhsin tsarabar sa tare da ta Al-Qasim, na ce,
“Ni na rasa abin da na yi wa Al-Qasim tunda muka dawo ba ya yarda mu gaisa”.
Muhsin ya dinga kyalkyala dariya, ya ce, “Kishi ya ke Ogan sa ya kasa shi. Wai ke kina nufin ba ki taba
sanin Al-Qasim son ki ya ke yi ba?”
Baki sake na ke kallon Muhsin, "So? Wane irin so?”
Ya ce, “So na aure, so na soyayya. Ya dade yana son ki, ya gama burin auren ki, ya jinkirta ne zuwa ki
gama lesson din ki ki sake waec don kar ya raba miki hankali. Sai kawai ga wannan sharp-shooter din ya
zo rana daya ya yi masa kamshin mutuwa ya sure ki kamar kiftawar ido, kin ga ko ai dole ya yi kishi”.
Mamaki ya hana ni cewa komai, don dai ni ko da wasa ban taba kawo hakan a raina ba, kuma ban taba
ganin wata alama daga gare shi mai nuna hakan ba. Sai na ji tausayin shi ya kama ni, na ce,
“Muhsin zan masa addu’a Allah ya ba shi wadda ta fi ni, kuma don Allah ka ba shi wannan tsarabar. Ba
zan taba mancewa da taimakon da ya yi min ba a rayuwa, shi ne silar da na fara gane karatu, har na yi
developing hope a cikinsa. Shi din mutumin kirki ne ko don yadda yake kula da Adda da komai na gidan
nan. Da ina da kanwa da na ba shi”.
Muhsin ya ce, “A kunnen Yaya”.
Na ce, “Ka yi sauri kada kuda ya riga ka, in ya kore shi ai komai kanka zai dawo. Yanzu kuwa ka samu kana
karatun ka a nutse babu stress a kan ka”.
Tun tafiyar Yaya na koma ba fuss ba ass! Ban san na saba da shi ba, ban san na shaqu da shi ba, ban san
zan yi kewar sa ba, bansan soyayyar sa ta shige ni a dan zamqn da muka yi tare a Jeddah ba sai da ya tafi
ya bar ni. Ya kuma daina kira na. Duk na zama wata irin sukuku! Soyayyar Yaya Maccido sai kara shiga ruhi
na ta ke a hankali tana kassara ni, tana karar da kuzari na, tana tafiyar da duk wata walwala ta a cikin
gida.
Adda ta kasa gane kaina, tambayar duniyar nan ta yi na ce ni ba abinda ke damu na, akai-akai ina ji yana
kiran Addah amma ni ko sau daya bai kira ni ba. Wannan abu ya dame ni matuka. Wani lokacin sai na
dauki waya da niyyar kiran sa sai in fasa, gudun ko yana tare da matar sa.
Yau ma ina zaune gefen Addah ina cin abincin dare Yaya ya kira wayar Addah, ina ji suka gaisa suka cigaba
da hira, har suka yi sallama ban ji Yaya ya neme ni ba, itama Addah bata ce gani a kusa ba. Hawaye ne na
ji zasu bada ni, don haka na tsame hannu na daga cikin tuwon na mike na yi uwardakin Addah, kwanciya
na yi rigingine akan gadon Addah ina hawaye, zuciyata na wani irin suya. Ban ji shigowar Addah da zaman
ta a gefe na ba, sai sunana da na ji ta kira.
"Ma'u me yake damun ki? Duka a kwanakin nan ina lura da ke cikin damuwa kike" "babu komai Addah
kai na ne kawai yake ciwo" murmushi Addah ta yi, ga mamaki na sai cewa ta yi "in shi bai kira ki ba, ke ba
saivki kira shi ba? Ba mijin ki ba ne? Maccido tun yana yaro mai son kulawa ne, mai son a bashi girma, sai
kin tashi tsaye sosai wajen kula da shi, in ba haka ba zaki sha wahalar sa. Ungo nan kira shi da kan ki ki
gaishe shi" ta miko min wayar ta.
Girgiza kai na yi "Addah in yana kusa da matar sa fa? Kika sani ko ya gaya mata auren mu ko bai fada ba?
Bana so in ja masa matsala" Addah ta daure fuska sosai ta ce "na ce ki kira shi, kada ki yi musu da ni
Ma'u".
A sanyaye na karbi wayar daga hannun Addah, bata bar wajen ba sai da ta tabbatar na kira lambar Yaya
har ta fara ringing. Kayan sallahr ta ta dauka ta bar dakin.
Ga dai waya ta shiga, kuma Yaya Maccido ya dauka, amma sai na kasa magana. Shi da kan sa ya gaji da
shirun ya gane ba Adda ba ce ni ce, ya ce "Asma'u yau kin tuno ni?" Hawaye suka ciko ido na, na ce
"kullum ma ina tuna ka" "ban yarda ba Asma'u, da kina tuna ni da kin neme ni, you don't care for me
anymore. Duk a cikin rashin son ne? Ranar da zan taho ko sallama baki zo mun yi ba, duk yadda zan yi in
ja ki a jiki don ki sake da ni ki kuma karbe ni a matsayin miji na yi Asma'u, ban san me ya sa ba kyaso na
ba". Hawayen dake cike a idona suka idasa gangarowa akan kundukuki na, sabida yadda Yaya Maccido ya ke
maganar, dole ya raunata zuciyar diya mace, balle mai saurin kuka iri na, da kyar na iya cewa "Yaya ni ban
fada ba...." "kin fada Asma'u, ba sau daya ba ba sau biyu ba akan ido na, ba kya so na balarabe kike so,
kuma na yi miki tsufa, hmmm, Nabeelah ma shaida ce kan kin fadi hakan" "ka yi hakuri Yaya na tuba,
wasa nake yi, na tuba na bi Allah na bi ka". Dariya ya yi ya ce "baki duba kan nawa kin gani ba fa ko akwai
furfura ko babu, kike saurin janye maganar ki. Ni dai na san ina son Asma'u, ko ita tafi kowa tsufa a
duniya. Zan tabbatar miki da hakan duk ranar da kika bani dama".
Zuciya ta ta yi wani irin sanyi daga kuncin da ta ke ciki a baya, sakamakon kalaman Yaya Maccido "amma
Yaya me ya sa ba ka kira na? Tunda ka tafi ko sau daya baka kira ni ba" na fada cikin shagwabar da ban
san ina da ita ba. Yaya ya ce "because i want to confirm if you care for me or not, yanzun ma ban
tabbatar da hakan ba idan ba na gani a zahiri ba" "me zan yi Yaya ka yarda na damu da kai fiye da yadda
kake tsammani?" "Ki yarda ki tare a dakin ki da zarar na zo, shine kawai zai tabbatar min kin damu da ni
Asma'u, kin kuma karbe ni a matsayin mijin da Allah ya zaba miki, kin san na yi hakuri ko? Hakurin da
maza da dama iri na ba za su iya ba".
Kunya ce ta kama ni na kai tafin hannu na na rufe fuskata tamkar Maccido yana gaba na. Domin na gane
hakurin da yake nufi ya yi, Nace "Yaya ni ba ruwa na sai abinda Addah ta ce" "ai na san bakin ku daya ke
da Addar taki, duk cikin ku babu mai tausayi na, shikenan, kada ku zarge ni in na nemo mata ta uku".
Wani dunkulallen abu ne ya zo ya tsaya min a kahon zucci, wuta ta dauke min, nace "Yaya....." "ki bar ce
min Yayan nan, ni ba Yayan ki bane yanzu, nafi so na ji kin ce Maccido" "bazan iya ba Yaya, because i
respect you much,..... don Allah kada ka kara zancen auren nan....zuciya ta za ta buga Yaya!"
Ina jiyo sautin murmushin Maccido, "Then sai kiyi kokari ki zama cikakkiyar matar aure in ba haka ba aure
ba fashi, ba daya ba har biyu. Na yi aure don ina bukatar kara aure amma sai gasa ni kuke Asma'u, yaya
kike so in yi da rai na?" Murya ta na rawa na ce "Yaya in ka daina maganar kara aure ko me kake so zan yi
maka" Yaya Maccido yayi murmushin da na jiyo tashin sa cikin wayar ya ce "promise?" "Yes, i promised"
"to ki shirya min tarba ta musamman, ranar Juma'a ina tafe insha Allah" "Allah ya kawo ka lafiya Yaya"
"call me Maccido, ko sau daya ne please Asma'u" na kai tafukana na rufe fuskata, wani irin feelings na
fizgar zuciyata zuwa gare shi, "ba zan iya ba Yaya, don Allah ka yi hakuri" "ban yi hakurin ba Asma'u, na bi
ki bashi, idan nazo sai kin fadi 'Maccido' a kunne na na ji" "na yi alkawari Yaya in ka zo ga ni ga ka zan
fada" duk dai don in samu ya zo din, na yi kewar sa yadda harshe na ba zai iya bayyanawa ba. Yaya Maccido ya ce "kina ta daukar alkawarin da ba zaki iya cikawa ba, first of all kin yi alkawarin yi min
duk abinda na ke so, sannan kin yi alkawarin zaki kira ni da sunana a gabana. Well, don ke zan kamo
hanya Asma'u don haka i expect a very warm reception from you" Murmushi na yi na canza position din
rikon wayar daga dama zuwa hagu, ji nake tamkar in shiga cikin wayar in tadda Attahir, gaskiyar sa ne ina
ta daukan alkawarurrukan da bani da tabbacin zan iya cika su ga ni ga shi, yanzu ma don ba na ganin sa
ne. Shigowar Addah ya sa nayi maza na kashe wayar ba tare da mun yi sallama da Yaya ba, ban gayawa
Addah Yaya ya ce zai zo Juma'ah ba sabida kunya. Addah ta ce
"Ma'u kashe wayar nan haka ki je ki kwanta, Allah ya tashe mu lfy".
Da wani matsanancin farin-ciki na kwana yau. Kwana na yi da tunanin Yayana-Mijina Attahir, yau na
tabbata nima ina daga cikin mata masu sa'ar zuwa duniya, ban rako sauran mata ba kamar yadda a da
nake tsammani.
Washegari da safe muna karyawa ni da Addah a dining Al-Qasim ya shigo gidan, ya dau wanka da karin
hula kamar yadda ya saba, gaban Addah ya zo ya tsugunna ya gaishe ta, Adda ta amsa cikin far'a tareda yi
masa tayin kosai da kunun da muke sha, ya dauki kosai daya a warmer ya kai bakin sa. Na ce "Yaya
Al-Qasim ina kwana?" Bai juyo ya dube ni ba ya amsa ciki-ciki. Sannan ya fadawa Adda sakon da ya kawo
shi. Ya bata wasu kudade masu yawa cikin leda da ya karbo mata daga banki yayi mana sallama ba tare
da ya ko dubi sashen da na ke ba ya fita. A rai na nace "ka mutu da bakin ran ka, ni bani da case da kai". A daren ranar ma raba dare muka yi muna hira ni da Yaya. Wani abun in ya fada kamar in nitse kasa don
kunya. A rai na in yi ta mamaki har in tambayi kai na anya Maccido ne wannan? Cikin kwanaki biyun nan
Yaya Maccido ya bi ya sukurkuta ni da soyayyar sa, ba abinda na ke so irin in bude ido in gan shi gabana.
Amma na san ganin nasa shine abu mafi wahala gare ni a halin yanzu, bani da idon da zan dubi Yaya
Maccido, idan na tuna irin hirarrakin da ke fita daga bakin sa.
Washegari Juma'ah har karfe goma na safe ban fita falo ba, Adda ta aiko Hawwa kira na in karya kumallo
har sau biyu ina cewa gani nan, amma ko motsawa daga bargo na na kasa. Fargaba ce fal a rai na game
da zuwan Yaya don na san na yi masa alkawarirrikan da na san bazan iya cikawa ba. Kuma na san rigima
ce kawai za ta kawo shi.
Wajejen karfe sha daya Adda ta shigo har dakin da kanta ta same ni, tace "Ma'u lafiyar ki kuwa? Kin san
Maccido na hanya shine tun jiya baki sanar da ni ba?" Kara shigewa na yi cikin bargo na nace "ni ban sani
ba Adda". Harara ta tayi ta ce "kada ki sani din, ki tashi a bargon nan haka ki nemar masa abinda zai ci,
kin san ba ya son abincin 'yan aiki ni kuma yau ba dadin jiki na nake ji ba" cike da fargaba na bude bargon
na ce "Adda ina ke miki ciwo?" In da abun da ke daga min hankali a duniya, to ciwon Adda ne. Ko da
kuwa na farce ne. Adda ta ce "ba wani abu bane babba, dan zazzabi nake ji, amma na yi wa Al-Qasim
waya zai taho min da magani anjima". Ta juya ta fita tana fadin "na fada miki ki bar gadon nan haka ki
tashi ki nemar masa abin da zai ci, ki kuma nemi wani abu ki sa a cikin ki".
Tsaye nake jikin island din kicin ina tunanin me zan dafawa Yaya? A karshe na yanke shawarar gasa masa
kifi manyan karfasa da Al-Qasim ya kawo jiya, nan na soma hada spices din cire karni da kayan hadin da
zan wa kifin, sannan na dora ruwan zafi a wuta da nufin in yi masa tuwon acca da miyar egusi.
Aikin da ya dauke ni awanni biyu, sannan ne na samu na yi wanka, na ci abinci, sassaukar kwalliya na yi
don kada Adda ta gane ina dokin zuwan Yaya Maccido a yau fiye da kowacce rana a rayuwa ta.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870
Maccido-Tahir ba shi ya iso ba sai gefen magriba, ya shigo a gajiye likis rataye da babbar rigar sa da
wayoyin sa biyu a hannun sa. Tun da naji muryar sa na kule a uwar dakin Adda amma har can sassanyan
masculine turaren sa obsession ya bi ni yana sanar da ni zuwan sa. Duk abin da suke fadi shi da Adda ina
ji, hirar iyalin sa suke yi da hirar 'Maccido Mall' na Abuja da plaza din sa. Yana gaya mata irin nasarorin da
ake ta samu da kalubalen da suke fuskanta. Ko motsi na Maccido bai ji a gidan nan ba don haka sai zuba
ido yake yi don ganin ta inda zan bullo, amma ya yi kawaici bai tambayi Adda ba har lokacin sallah yayi
duk suka tashi daga hirar, ya fita masallaci Adda kuma ta shigo dakin don ta daura alwalla a toilet din ta
da ke cikin dakin.
Nan ta same ni a kwance bisa gadon ta, ta ce "amma Ma'u an yi shashasha, yanzu mijin na ki ya kamo
hanya tun daga Abuja har Sokoto saboda ke, shine kika buya uwar daki? To abincin wa zai kai masa?" Na
mike daga kwanciyar na ce "Adda ni ba waje na ya zo ba fa, abincin yana dining na ajiye tun dazu" Adda
ta ce "wannan kandararren girkin naki? Maccido ba zai ci shi ba, gara ki je ki dumama masa a microwave,
na tabbata a haka kika ajiye shi" na fita ina fadin "toh Adda zan dumama, amma sai na yi sallah".
Da na idar da sallah na kwashe abincin nayi kitchen na kunna na'urar dumama abinci, ba jimawa na gama
na mayar dining. Ina kokarin barin bangaren cin abincin Yaya Maccido ya shigo falon.
Wata irin kunya ce ta kama ni kamar in narke a gun, kamar yau na fara ganin Maccido, na yi kasa da kai,
ban san yaushe Yaya ya tako ya iso gaba na ba. Ratar da ke tsakanin mu bai fi taku biyu ba. Ya kira suna
na a hankali "Asma'u" amma na kasa dagowa. Hannu ya sa ya dago haba ta ban san sanda na rufe idanu
na ba.
"Me zan samu Asma'u ga ni na zo? Kin sani kuma sabida ke na zo? Ina alkawarin mu?"
Motsin kofa muka ji duk muka juya a tare, Al-Qasim ne ya shigo da sauri ya koma yana fadin "excuse me
please......". Yaya ya yi murmushi ya ja hannu na muka bar falon zuwa daki na. Rufe kofar yayi da mukullin
dake jikin ta ya ja ni muka zauna a gefen gado na. Ni dai iya abinda zan iya tantancewa kenan sai tsintar
kaina nayi a hannun Yaya Maccido yana sarrafa ni duk ta yadda ya ke so. Al'amuran na Yaya sai gaba suke
yi suna kara rikita duk wata nutsuwa da na mallaka. Kwata-kwata ya manta a inda muke waje ne da
kowanne lokaci Adda ke iya shigowa. Ilai kuwa ba'a jima ba Adda ta soma kwankwasa kofar dakin tana
kiran suna na. Ba karamin rudewa nayi ba na kwace kai na daga hannun Yaya. A hankali ya ce "relax
Asma'u, Adda ta san kina tare da mijin ki ne, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki" Ina! Mikewa na yi jiki na
rawa har sai da na baiwa Maccido dariya. Da gudu na shige toilet don bazan iya facing Adda ba despite all
those hot kisses daga Dan ta Maccido. Gani na ke kamar da ta ganni zata hango abinda ya faru. Shi kuwa
Yayan kansa tsaye ya karasa ya bude kofar.
Hararar sa Adda ta yi sannan ta ce "turomin Ma'un" daga haka ta bar bakin kofar.
Da kuka na fito ina fadin "Yaya me yasa ka shigo min daki? Yanzu da wane ido zan dubi Adda?" Dariya
sosai na bashi ya kwaikwayi murya ta ya ce "da idon da kika sanya mata Da a daki kina ta sumbata" na
kara rushewa da kuka, Yaya ya janyo ni a hankali ya sanya cikin jikin sa, ya lullube ni da tsayi da fadin sa.
Ya dora habar sa tsakiyar kaina. A hankali ya ke bubbuga baya na da