Showing 33001 words to 36000 words out of 46393 words

Chapter 12 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf

ne. Duk wani hoto na Lubabatu sai da na goge shi tas, amma ban goge na yaran
ba, haka wanda suka dauka shi da ita duk sai da na bi na yi marking na goge tas. Cike da mamakin karfin
hali irin nawa. Yaya ya shigo da ledojin abincin 'Mud’am Furouj Faqeeh', Aunty ta karba ta shimfida ledar cin abinci a
kasa wadda suke hadowa cikin abincin, ta juye komai bisa ledar ta ce mu zo mu ci mu duka.
Ita da ma Addah ba ta cin komai sai wanda aka ba ta a asibiti bisa ka’ida.
Muka sauka mu uku muka zauna bisa kilishi muna cin abinci, Addah sai kallon mu ta ke yi zuciyar ta na yi
mata dadi. Haka take so ta gan mu, haka take buri. Wato Allah ya hada mata kan marayun ta. Ta roki
Allah cikin zuciyar ta ya kara hada kan mu, ya kara soyayya da kaunar juna a tsakanin mu.
Aunty ta ce da Addah, “Auren Maccido da Ma’u shi ne YI WA KAI HISABI. Maccido ya yi laifi, kuma ya yi
wa kansa hisabi da auren Ma'u. Hisabin da ya yi wa kowa dadi. Allah ya sa albarka a auren ku, Ya kade
fitina, Ya hada kan matan ka, Ya ba ka ikon yin adalci a tsakanin su”.
Yaya da sauri ya amsa, “Amin-amin Yaya Nabeelah. Kin manta ba ki ce Allah ya kawo wa Addah yara
kurkusa ba”.
Da sauri na bar cin abincin na sunne kaina cikin gwiwoyi na, Aunty ta harare shi ta ce,
“Ai muna da yara, Ihsan da Ahsan, duk da rowar su ku ke yi wa Addah”.
Ya ce, “Ai shi ya sa na ce ki yi addu’a Allah ya kawo wadanda za su zauna kusa da ita, har sai tana korar su
tana cewa, sun ishe ta”.

Addah ta ce, “Ni ba zan taba korar su ba”.
Haka suka yi ta hirarsu suna nishadi, Yaya ya sha magungunan sa bayan mun gama cin abinci, na yi addu’a
cikin raina, Allah ya sa wannan farin cikin da ke kan fuskokin su ya dore har karshen rayuwar su, don na
lura wannan shine farin cikin Addah, wato hadin kan 'ya'yan ta.
Tunda Yaya ya dawo sallar isha Addah ta ce mu tashi mu tafi, duk wannan sakewar da ke tsakani na da
Addah yanzu ta kau, kunyar ta nake ji sosai. Muka yi musu sallama, sannan muka fito muka tari Ajrah
muka koma hotel.
Ina tsaye jikin mudubin dogon yaro ina kallon ramar dana yi cikin kwana daya kacal, na ji shi yana waya
yana fadin,
“Na kashe miki waya? Da yaushe aka yi hakan? To shi ke nan tunda haka kika ce na kashe din, don Allah
kada ki fasa tafiyar, dawowa ta kuma babu rana sai uwata ta samu lafiya”.
Ya jefa wayar gefe yana tsaki. Sai kuma ya dauko ta ya shiga binciken ta, ya shiga call log din sa, gallery din
sa da akwatin sakonninsa nan ya fahimci komai.

Kaina a kasa irin na marasa gaskiya na bi ta gaban sa zan wuce, sai ji na yi Yaya ya damko ni, na ce,
“Wayyo Allah na, zaka karya ni" Ya ce, “Sannun ki, wato shi ne ki ka hada ni fada da matata ko? Ki ka goge
min texts din ta da hotunan ta masu sanyaya min zuciya daga bakaken kalaman ki, bayan ke kin ce ba kya
so na? To a wane dalili? Ina son sani".
Na yi fuska sosai, sai ka rantse da Allah ba ni na yi ba, nace "a wane dalili kuwa? Kawai gani na yi sun cika
wayar ba space. Amma ka yi hakuri, ni daga kai har ita ba kwa gaba na". Wani irin miskilin murumushi
Yaya Maccido yayi. Ya girgiza kai yana ta mamaki, wai ‘yar wannan Asma’un ta san kishi, tun yanzu ma ke
nan, ranar da suka hadu ashe ya shirya abin da a baya bai taba tunani ba. Bai ce min komai ba ya sake ni
yana ta murmushi wanda na kasa gane dalilin yin sa.
Irin kwanciyar jiya, ita aka yi yau ma, yana kujera ina gado, ya tada kai da hannayen sa. Ya lumshe ido
yana tunanin ta inda zai bullowa wannan hutsuwar Asma'un.


***​ ***​***
Yau ma sai azahar muka shiga asibiti, jikin Addah sai hamdala yau ta sauko daga gadon ta je toilet da
kanta, duk da har yanzu a zaune ta ke sallah.
Yaya Maccido ya ce da Addah da Aunty tunda jikin Addah ya yi kyau gobe ni da shi za mu tafi ziyarah
Madeenah. Za mu yi kwanaki bakwai. Aunty na dariya ta ce, “Ka fadi gaskiya dai, ziyara ko
honeymooning?”

Ba kunya Yaya Maccido ya ce,
“Duka biyun, ai ana jifan tsutsu biyu da dutse daya”.
Na dago kai gabana na dukan uku-uku jin abinda Yaya ya ce, bansan sanda na ce "gaskiya Adda ni ba inda
zani". Addah ta ce "ba'a kin zuwa Ziyarar Ma'aiki, burin kowanne musulmi kenan, kiyi hakuri ku je".
Haka tayi ta lallashi na har na amince zan je amma ta gargadi Yaya kan kada ya takura min kan duk abinda
na ce bana so.

A daren Yaya da kansa ya hada mana gabadaya kayan mu, don ba lallai in mun dawo mu sake sauka a
dakin ba. Yaya Maccido ya yi mana shatar lafiyayyar mota, wadda za ta kai mu har Madeenah.
Tafiya zuwa Madeenatul Munawwarah daga birnin Jeddah ba tafiya ce mai sauki ba, mun wuni sur a
hanya, sai dai dadin abun akwai mud’ams (gidajen cin abinci) a kan hanya ta yadda matafiyi ba zai jigata
ba.
Sai dare muka shiga Madinah, yaya Maccido ya kama mana masauki a hotel din Dar At-Taqwa wanda ke
kusa da Masjid Al-Nabawy.
Ba abin da muka iya sai ramuwar barci sabida gajiya, kasancewar mun yi duk sallolin mu a kan hanya, sai
asubah muka taka a kafa zuwa masallaci mai alfarma, muka samu sallar asubah. A kan idona aka bude
Raudha na kukkutsa yadda kowa ke yi na gabatar da sallar nafila raka'a biyu. Allah ka kara wa Manzonmu
darajah da fadhilah da waseelah, ameen.
Kasancewar wajen maza daban na mata daban, ba mu kara haduwa ni da Yaya ba. Sai bayan sallahr
azuhur a daki. Ya shigo mana da shinkafa-kaza da juices, laban da haleeb muka ci muka yi kat, sannan ne
muka sake wanka muka koma masallaci muka samu sallar la’asar. Karfe hudu da rabi muka koma hotel
Yaya ya ce, yanzu za mu kai ziyara ne wurare masu albarka, masu tsohon tarihi a musulunci.
Mun je Masjid Quba, Uhud Mountain, Baqi’a, da Masjidil Qiblatayni, sannan muka je Dar Al-madinah
Meseum muka ga kayan tarihi. Washegari kuma Yaya ya kai ni shahararren shagon sutturar nan na manya
da yara, wato Majma’al Qimmah. A kokarin Yaya na ganin ya faranta min, na daina kumburi da fushin
dana ke yi masa ya ce in sayi duk abin da nake so a shagon.
Da farko na ce bana son komai, daga baya na yi wani tunani. Kayan yara na fara dauka masu kyau da
nagarta, mace da namiji, Ahsan da Ihsan na sai wa, sai kuma Aasim din Aunty Nabeelah. Na daukar wa
Muhsin jallabiyyu masu kyau da turare irin wadanda na ga Yaya ya saya yana sakawa. Har Al-Qasim na yi
wa tsaraba.
Yaya bai san me na debo ba sai da aka zo biyan kudi.
Ya ce, “Duk wadannan uban kayan ina za ki kai su?”

Nan na dan saki fuska nayi masa bayani, don dai in samu ya biya duka, amma ban gaya masa da na
Al-Qasim ba, na ga alama ya ji dadi sosai da tsarabar su Ahsan, amma sai ya ce,
“In suka haura kilo din kayan da aka yarje miki ke za ki biya kudin awo ba ruwa na”.
Zumburo baki na yi, na ce masa, "na yarda"

Tun daga ranar ba mu kara zuwa ko’ina ba sai Masjid Nabawy, kowacce sallahr farillah ba ta wuce mu a
masallaci. Zaman mu Madinah kadaran-kadahan tsakani na da Yaya Maccido, duk yadda Yaya ya so ya
rarrashe ni ya samu kaina mu shirya mu mori amarcin mu kamar yadda ya zo da niyya na ki yarda da
hakan, ba na tashi tada bori da kuka na sai dare ya yi, abinda na san Yaya ba ya so ko kadan, kuma yana
kokarin kiyaye umarnin Addah da ta ce kada ya sake ya takura min. Sannan da kokarin sa na son nuna
min ba dalilin da yasa ya aure ni kenan ba kamar yadda ya fada min a baya. Shi yasa Yaya ya saka min ido
na cigaba da yi masa duk abinda naga dama.
Tare da wasu dalilan da dama bayan wadannan, su suka taru suka sa Yaya ya daga min kafa, ya kyale ni
bai kara bijiro da neman wani abu da ya danganci aure daga gare ni ba. Duk wani sauke kai da namiji zai
iya don ya samu hadin kan matar sa da yake matukar so Yaya Maccido ya yi a Madinah, sai dai ba ya
samun martanin komai daga gare ni ko kadan. Banza na ke masa har sai ya gaji ya rabu da ni. Da rana
zamu wuni lafiya wataran har 'yar hira ina yarda mu yi, musamman in su Aunty Nabeelah sun bugo waya.
Sai dare yayi zaka gane ba masoyan gaske bane, domin kuwa kai da kafa muke kwana, har gobe kallon
Yaya Maccido nake matsayin Yaya na yadda yake a baya ba abinda ya canza a idanu na. Kuma na gaya
masa, na kara gaya masa ba zan taba son shi ba, so irin na aure, he's never my choice. Balarabe na ke so
kuma yaro. Ba zan taba son shi ba.
Tun kalamai na suna baiwa Yaya haushi har sun koma bashi dariya, wani lokacin in muna tafiya a cikin
gari, ya ga wani kyakkyawan balaraben sai ya ce
"Asma'u to ko wannan ya yi? Tunda Maccido bashi da sa'a?"
Hararar sa nake kawai in kau da kai, don na lura ya maida ni mahaukaciya.
Daga ni har Yaya mun yi sumul a kwanaki bakwai, kamar da ka taba mu jini zai yi tsartuwa, mun zama
wanke hannu ka taba, tabbas kasar Saudiyyah rahma ce ga kowanne musulmi.
Kwanan mu bakwai muka tattaro kayan mu muka dawo Makkah. Wannan karon a hilton na kusa da
haraam Yaya ya kama mana karamin daki kwana uku. Muka sake yin umrah muka yi dawafin godiya ga
Allah a bisa duk rahamomin da ya yi mana, muka gode maSa lafiyar da ya dube mu Ya baiwa Addah.
Muka kara rokon Sa Ya rufa mana asiri duniya da lahira, Ya dawwamar da mu cikin kwanciyar hankali,
arziki da zama lafiya.
Mun ziyarci Abraj Al-Bait Towers a Makkah. Kwanan mu uku muka dawo Jeddah, muka samu Addah ta
murmure tana harkokin ta kamar bata taba kwanciya ba.

Tun daga ranar da muka dawo na ki bin Yaya mu koma masaukin mu nace ni jinya na zo kuma ita zan yi
da Addah zan zauna, Addah bata yi wata-wata ba ta ce Yaya ya kyale mata 'yar ta, dama bata shirya
tarewa ta nan kusa ba. Yaya Maccido ya yi fushi sosai ya rabu da ni ko dakin ya shigo baya kula ni balle ya
kalli inda nake. Wai kuma sai hakan ya soma sanya ni a damuwa. Duk da haka ban bishi ba, na cigaba da
zama na wurin Addah. Nabeelah bata ce komai ba.
Bayan sati daya da dawowar mu muka soma shirin dawowa gida, bayan an baiwa Addah sallama. Da
sharadin zuwa check-up bayan watanni shidda. Saura kwana biyu mu taho Aunty Nabeelah ta koma
Beirut.
Inda bayan sati biyu za ta tafi Abu-Dhabi ta hado lefena da kayan daki, kamar yadda Yaya ya bata
kwangila, sannan ta iske mu a gida da kayan. Adda dai ta ce tarewa ta ba rana ba wata.
Ranar laraba ta shekarar dubu biyu da goma (2010) jirgin Emirate ya dawo da mu gida, ta Abuja muka
sauka, da Addah cikin koshin lafiya mu kuma cikin kwanciyar hankali.



**SADAUKARWA GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*



*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*



*07030137870*
*

SOKOTO, NIGERIA.

Mun dawo mun samu gidan tsaf! Hawwa ta gyare ko’ina, Muhsin da Al-qasim su suka dauko mu daga
filin jirgi. Muhsin na ta kururuta tsabar canzawar da muka yi daga mu har Addah. Al-Qasim ya canza min
bakidaya domin ko gaisuwa ta da kyar ya amsa, sai da Addah ta ce da shi,
“Ana gaishe ka”.
Bayan na tabbata ya ji din.

Abin bai min dadi ba ko kadan, domin akwai sabo a tsakanin mu a baya. Daga baya na ga to me zai dame
ni don Al-Qasim ya ki amsa gaisuwa ta? Ai da da yanzu ba daya ba ne. Ni din yanzu matar aure ce ina da
special miji na a gefe.
Murmushi na yi wa kai na ni kadai, a rai na na ce "kamar gaske" mijin da ko gaisuwa babu tsakanin mu???
Ni kaina na san ba zan iya cewa bana son Yaya ba, na laluba a fadin kirji na da zuciya ta na rasa space na
kiyayyar Maccido, sai dai wani kwantaccen so wanda ban taba sanin da shi ba sai yanzu dana ke da
tabbacin ni matar sa ce, domin ba tun yau ba Maccido ke burge ni, na ke yiwa kai na addu'a da fatan
samun miji kamar sa.
Baya ga laifin da ya yi min na aure na ba da sani da amincewa ta ba, na kasa manta biris din da yayi da
Adda akan mace, duk da ita ta yafe masa suna sabgar su ta Da da uwa kamar da. Sannan wani irin kishi ke
nukurkusa ta a kan Maccido, wanda ban taba sanin ina da shi ba, sai yanzu da ya zama miji na na zama
matar sa. Kishin Lubabatu! Tunda kuwa ta riga ni mallakar Attahir da komai nasa. Ta riga ni haifa mishi
'ya'ya, shi yasa na tattara kishin hakan da haushin hakan da bacin rai na duka na dora akan Maccidon, ta
sigar kafewa akan ni bana son shi ko kadan.
A ranar da muka dawo da daddare bayan mun ci abincin da Hawwa ta tanadar mana Yaya ya dube ni
kadan ta kasan ido ina zaune jikin Addah. Ya ce.
“Asma’u, dauki kayan mu ki shigar da su sassan mu, da wuri zan kwanta, don gobe sammako zan yi zuwa
Abuja, ayyuka sun tarar min fiye da kima, ga wadancan sun dame ni da waya”.
Na gane matar sa yake nufi, ban ce komai ba na yunkura da nufin daukar babbar jakar sa.
Addah ta ce, “Ke Ma'u, koma ki zauna, in ga kafar ki ta taka sassan nan, sai ran ki ya baci. Babu wanda ya
san da auran ku, ba'a yi miki jere ba, ba'a shirya ki ba, ba a raka ki gidan miji ba, kawai sai ki kwashi jiki ki
shiga dakin miji don ke akuya ce ko? Ko don kin ga na bar ki kin bi shi Madinah? Wannan ai ibadah ce, ba
kuma wanda ya isa ya hana ibadah musaman ta hajji da umarah”.
Na koma na zauna cike da kunya ina fadin,
“Da ma fa kayan zan kai masa kawai Adda ba zama zan yi ba”.

Addah ta harare ni, “Sannu tattabara sarkin soyayya, Muhsin ya kai masa, ke da shiga sassan nan sai
Nabeelah ta dawo, ta yi miki jere. Mun shaidawa 'yan uwa da abokan arziki auren ku. An yi ko walima ce.
Wuce daki na ki kwanta kafin in bata miki rai”.
Ta gaban Yaya Maccido na wuce ina zumburo baki, Adda bata yi min adalci ba, ni kwata-kwata ba nufi na
kenan ba, na yi niyyar kai masa kayan ne ma albarkacin idon ta, kada ta gane ba wani shiri tsakanin mu,
ba nufi na in tare dakin Yaya ba, ina ganin yadda ya sunkuyar da kai, na wuce, ya bi ni da kallo, a karo na
farko duk sai ya ba ni tausayi.
Addah ma ba ta wani jima ba ta shigo, sabida duk a gajiye muke. Muna shirin kwanciya Yaya Maccido ya
kara shigowa, daga bakin kofa ya tsaya hannayen sa cikin aljihu, fuskar sa dauke da damuwa tsantsa
domin shi yau ya shirya angoncewa. Bai taba tsammanin hukuncin da Addah zata yi kenan ba, Allah ya
gani ya yi hakurin da ba duk maza ne zasu iya ba. Amma Addah na kokarin karya masa juriyar sa. Da ya
san hukuncin da zata yi kenan, ai da bai yi hakurin da ya yi ta yi ba.
“Asmau ina ki ka saka min cajar waya ta ne?”
Ya fada daga bakin kofa hannayen sa zube cikin aljihu, looking upset. Na rasa wacce cajar waya yake nufi,
don ni ban dauka ba, don haka na ce,
“Ka duba cikin karamar trolley din ka, can na zuba komai".
Ya ce, “Ni ban san wata karamar trolley ba, in za ki dauko ki dauko min, ina falo”.
Addah ta ce, “Maccido ko ka fi kowa naci, yau ba kai ba hada daki da Ma’u, ka bace min da gani ko in
sabar muku dukkanin ku”.
Cikin kunkuni ya ce, “Haba Addah? Daga neman charger? Na tafi ku kwana lafiya. Ba nufi na kenan ba".
Addah ta yi murmushi ta ce, “Allah ya tashe mu lafiya”.
Sosai Yaya Maccido ya shaqa, yayi fushi sosai, ya juya yana fadin, “Na tafi Addah, ki yi ta ajiyar 'yar ki a
daki, in na ga ta uku sai in kara, tunda Allah ya bani dama”.
Ta kara sakin murmushi ta ce, “ko biyu ne ma ka karo, ni dai tunda Ma'u na ta shiga, kowa ma kake so
kayi ta kawowa’.
Attahir

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login