Showing 3001 words to 6000 words out of 46393 words
Chapter 2 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf
zauna a wajen
ta, ba don ba ta da ‘ya’ya ba. Ta yi min nuni da halin da Adda ke ciki, tana son wani makusancin ta ne a
kusa da ita. Ta ce in zauna gaba gare ta in hidimta mata, in mata biyayya iyakar iyawa ta, don ba ni da
wanda ya fi-ta a duniya bayan mahaifi na.
A bayan Nene na kwana, manne da jikin ta. Da asuba ma bayan mun yi sallah sai da ta kara lallashi na
tare da jaddada min yi wa Adda biyayya da hidimta mata, ta sa min albarka ta ce, “In kin kasa karatun
boko kada ki damu, ba shi ne tikitin shiga aljanna ba, wanda ki ka iya shi ne wanda zai tserar da ke ranar
gobe kiyama”.
Wadannan kalaman na Nene a kan karatu na na boko kullum ina tuna su, suna cire min damuwar nakasu
na a kai, suna zame min fitilar rayuwa. Baba ya ce da Adda shi ko su Nabeelah sun dawo, ya riga ya
mallaka mata ni har zuwa ranar da za ta yi min aure.
Maganganun su duka shi da matar sa Nene masu karya zuciya ne. Amma a wannan lokaci daga ni har
Adda ba mu ankara da muhimmancin su ba. Sai a lokacin da aka shimfide mana gawarwakin su a gaban
mu. Sun yi hatsari gab da za su shiga garin Talata-Mafara, Malam Hussaini direba hatta kafarsa da
hannayensa sun fita daga jikin sa.
Sabon tashin hankali irin wanda zuciya ba za ta iya fassarawa ba. Rana ce da ba zan taba mancewa da ita
ba a kundin tarihin rayuwata. Ranar da na tabbata marainiya ba uwa ba uba, har fiye da su Muhsin.
Rayuwa ta dandana mana wani irin daci ni da Addah, da babu madacin da ya kai dacin sa. Hankali na ya
bar jiki na, nutsuwa ta kau mun, kadan ya rage in rasa hankali na. Kwana na uku ina sambatu wanda babu
komai a cikin sa sai "Nene da Baba". Shekaru na goma sha hudu a daidai wannan lokacin, ranar da na
amsa sunan ‘MARAINIYA’ gaba da baya a cikin wani dan takaitaccen lokaci mai kama da kiftawar ido.
*********
Aka ce mutuwa mai tonon asiri, ba mu tabbatar da wannan ba sai lokacin da kannen mijin Adda su biyu
Malam Ilya da da Malam Bilya suka zo addu’ar arba’in din dan uwan su. Bayan an shafa addu’a suka kira
Adda falon marigayi. Babu kwane-kwane suka ce ta fiddo duk wata takarda da kowanne kobo da ta san
marigayin ya bari za su alkinta wa ‘ya’yan sa, har su yi hankalin daukar takalihun dukiyar su. Sannan in ta
amince shi malam Bilya zai aure ta don bai kamata a bar gidan ba namiji ba, in yaso sai ya kwaso sauran
iyalin sa daga Dogondaji su dawo gidan da zama. Hajiya Kilishi ta dade kanta a kasa ba ta ce komai ba, har suka gama duk wani tsare-tsaren su, wanda
babu komai a ciki sai hadama da babakere a cikin rigar zumunci. Lokacin da suka matsa da son jin amsar
ta sai ta ce, ita a yanzu ba ta da magana, tana cikin alhinin rashin mijin ta da tilon dan uwanta, babu wani
rabon gado a gaban ta, tunda gadon nan dai babu mai shi daga ita sai ‘ya’yan ta. Maganar aure kuwa ita
da kara yinsa har abada! Shekarun ta arba’in da takwas ta kusa isa ‘menopause’ ba ta bukatar wani aure
a rayuwarta. Za ta yi zaman ‘ya’yanta ne kawai da zaman jiran nata wa’adin. Ba ta da sauran muradi a duniya.
Wadannan dattijai ba su hakura ba, bayan wata uku sai da suka sake dawowa suka ce ba ta isa ba, sai ta
fiddo komai sun raba wa ‘ya’yan su gado. Saboda gudun rigima da tashin hankali, Adda ta fiddo kananan
kadarorin marigayin ta ba su. Suka dauko malaman karya suka yi kasafce-kasafcensu inda suka samfe
komai suka mike, suka ce sai yaran sun yi aure sun zauna waje daya za su ba su.
Aure kuma tunda ta ce ba a yi ita ta jiyo, da ma taimakon ta za su yi. Su rike mata marayun ta a gaban su.
Abin ya hada da rashin ilmi, ban da haka ‘yar dukiyar da suka gani suka gigice ba ta kai ko kwatan-kwatan
abin da mutum irin Alhaji Atiku ya mallaka ba.
Sun yi waya da Nabeelah a ranar ita da mahaifiyar ta suka yi ta kuka kamar ran su zai fita. Nabeelah ta ce,
ita tashin hankalin ta shi ne Maccido na kan hanya, wai surprise zai yi wa Adda shi ya sa bai gaya mata zai
zo ba.
Duk halin da Adda ke ciki dole ta murmure ta aro juriya ta dora wa kanta. Ta shiga shirin tarbar Maccido.
Watanni uku da sati biyu kenan da rasuwar Alhaji Atiku Dogondaji, wanda ya yi daidai da cikar Babana da
Nene watanni uku cif a gidan da ke jiran kowanne dan Adam. Har zuwa wannan lokacin ban koma daidai
ba, bana doguwar magana daga eh sai a’ah, abinci sai Adda ta sani a gaba shi din ma sai mai ruwa-ruwa
idan na ji hanjin cikina na raurawa. Duk wannan lukutin jikin nawa ya zaizaye na koma kamar a bushe ni
in fadi.
Ni dai na san ina wanka, amma bayan shi ko mai bana shafawa, balle a je ga zancen kwalli da hoda. Adda
ce ke takaba, amma kusan tare muke yi. Sati biyu ke nan da gama takabar ta.
Sai da ta tabbatar abincin da ta sa mai aikinta Halima ta taimaka mata ta shirya ya kammala a kan tebir
sannan ta fada wanka, ta fito ta sanya kaya masu dan haske wadanda rabon ta da sanya su tun mijin ta
na raye. Ta fito falo inda ta tadda mu zaune ni da Muhsin, dawowar sa ke nan daga makaranta ko
(uniform) bai cire ba ya ce,
“Addah, unguwa za ki ne?”
Fuskarsa ta nuna jin dadin ganin ta cikin kyakkyawar kama yau. Ta zauna tana fadin, “Ma’u miko min
carbi na”. Ba tare da ta bai wa Muhsin amsa ba.
Ko gama rufe bakin ta ba ta yi ba suka tsinkayi sautin sallamar sa cikin muryar sa mai kurdawa har cikin
kwakwalwar mutum, ta haifar masa da canjin yanayi. Idan diya mace ce ta rikitata, ta haifar mata da
kasala wani lokacin har ta rasa control din kanta.
(Maccido-Attahir).
Gaba dayanmu muka daga kai muka dube shi. Maccido ne daga Cuba, Maccido (Tahir) Atiku Dogondaji,
kamar yadda cikakken sunansa yake. Fari ne ba sosai ba, ya fi kyautuwa a kira shi wankan tarwada. Akwai
abubuwa da yawa a tare da Maccido da ba duka maza Allah ya mallakawa ba. Yana da wani irin
sassanyan kyau, wanda a kallo na farko ba za ka ganshi ba, abin da za ka gani shi ne, ilhama da cikar
halitta.
Duk inda ake neman maza su amsa sunan su, to a sanya Maccido cikin su, ko shi kadai zai wakilci guda
dari.
Maccido mutum ne wanda ba shi da fara’a ko kadan, sannan ba ya wasa ga na kasa da shi, very
responsible person, sannan ba ya son duk wata harka in dai akwai shiririta a cikin ta. Shi din wani irin
mutum ne mai matukar tsantseni da taka-tsan-tsan cikin mu’amalarsa da kowa. Ba ya shiga sabgar da ba
tashi ba, kuma ba ya son a shiga tasa.
Babban sirrin Maccido shi ne iya daukar wanka da iya diresin, wadanda suka taru suka cakude suka ba shi
wata irin kyakkyawar suffa wadda kafin ka samu mai irinta sai an tona. Maccido Taheer ya mallaki duk
wasu nagartattun halaye da ake so namiji ya siffantu da su, kai dai barshi da shan kamshi da rashin fara’ar
sa.
Wani tsalle da muhsin ya yi daga kujerarsa sai ga shi makalkale da Yayansa Maccido,
“Brother da ma kana hanya amma shine ba ka gaya mana ba?”
Dan murmushi ya yi yana yi wa Adda sannu da gida kamin ya samu gefen kafafun ta ya zauna, ya dora
hannunsa kan tafin kafar ta.
“Ka sauka lafiya Maccido, ya ya hanya kuma ya ya karatun?”
Ya dukar da kai ya ce, “Na zo lafiya Addah, da fatan na same ku lafiya, saidai karatu akwai matsala. Adda
na samu carryover har biyu, abin da ban taba samu ba a tarihin karatu na. Wani irin faduwar gaba nake
yawan yi. Ga yawan yin zurfi a tunani. Sannan Adda haka kawai sai nake fama da anxiety wanda ban san
dalilin sa ba”.
Hawaye suka ciko idon Adda, ta kauda kai daga kallon Maccido. Cikin sanyin murya ta ce, “Ka je ka yi
wanka da sallah, ka zo ka ci abinci sai mu tattauna ko?. Yanzun akwai gajiyar zaman jirgi tare da kai na
sani”.
Sai da Maccido ya yi duk abubuwan da Adda ta lissafa sannan ta runtse ido ta gaya masa duk abubuwan
da suka faru a bayan sa.
Maccido shidewa ya yi na wucin gadi, iyakar firgita da tashin hankali irin wanda dan Adam ke kasancewa
a ciki, a lokacin da ya samu labarin gushewar mahaifi. Mahaifin ma irin Alhaji Atiku, wanda shakuwar da
ke tsakanin sa da ‘ya’yansa ta zarta ta uba da ‘ya’ya kadai, su ne abokan sa kuma aminan sa. Sannan ya
bugu da mutuwar Uncle din sa da maidakin sa Nene, wadanda akwai kyakkyawar alaqa ta soyayya
tsakanin su da shi tun haihuwar sa.
Adda har zuwan kawunninsa daga Dogondaji da yadda ta kare da su sai da ta labarta masa. Maccido ya yi
kuka har ya ba uku-lada. Kwanan sa bakwai ya kulle kan sa a daki, ba ya zuwa ko ina, abinci ma can
Muhsin ke kai masa.
Hakika ya shiga wani hali wanda biro ba zai iya rubutawa ba. Nabeelah kan kira shi su yi kukan su mai
isarsu. Komai na duniya ya fice masa a ka, karatun ma ya soma tunanin kin komawa. Gani yake a yanzu
shi ne gatan uwar sa da ‘yan uwan sa. Ga marainiya Ma’u wadda ta karu a cikin su, takalihun ta dole ya
dawo hannun sa. Ya kan tuna soyayyar mahaifi na gare shi don haka ya sha alwashin rike ni cikin su
kamar yadda zai rike Muhsin.
Da kyar Adda ta lallashi Maccido ya koma makaranta bayan karewar hutun sa. Da lallashi da ban-baki, da
kalaman karfafa wa Adda tasa shi ya gyara takardun sa.
Ya kuma ci gaba da karatu da wata irin himma wadda a baya ba shi da ita. Apart from course din da yake
yi, watau "Architecture" sai ya kara da Business Administration, ba don komi ba sai don ya samu sani kan
ilmin kasuwanci, ya zo ya tallafi dukiyar da mahaifin su ya wanzar da rayuwar sa ya tara musu. Gaba daya
rayuwar sa ya fuskanci neman ilmi ka’in da na’in, don ya san yanzu shi ne kadai gatan da zai yi wa kansa
da mahaifiyar sa da marayun ‘yan uwan sa.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE*
10/09/2023
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870
~HISABIN NAFS~
((3)) *BAYAN SHEKARU UKU*
Abubuwa da yawa na ci gaba sun faru cikin shekaru ukun da suka biyo baya ga iyalin marigayi Atiku
Dogondaji. Aunty Nabeelah ta kammala karatun ta da ta ke yi a Beirut (Lebanon) ba ta tashi dawowa ba
sai da guzurin miji balarabe dan asalin kasar Lebanon. Sunanshi Fa’iq, malaminta ne a makaranta wanda
soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su, wannan ya samo asali da matukar kokari irin na Aunty Nabeelah.
Ya biyo ta har Sokoto tare da waliyyansa.
An kai ruwa rana da su Baffa Bilya kafin su amince su aurar da Nabeelah ga Fa’iq don cewa suka yi
in ta tafi bata za ta yi. Sai da Fa’iq ya alkawarta kawo Nabeelah gida duk karshen shekara, haka duk mai
son ganinta zai dauki nauyin zuwan sa gare ta, sannan suka amince aka daura auren. Fa’iq ya dau
Nabeelah suka koma Beirut.
Yaya Maccido ma ya gama nasa karatun ya samu tayin aiki iri-iri da construction companies daban-daban,
amma a karshe ya zabi ya yi aiki da Julius Berger Nigeria, suka barshi a babban reshen su na birnin
Tarayya, Abuja.
Tun daga lokacin ne ganin sa ya yi mana tsauri. Ya tattara duk dukiyar da mahaifin su ya bar musu ya
bude musu wani katafaren shopping mall kusa da Al-madina, ya dauki amintattun yara ya zuba, Muhsin
ne manajan wajen duk da karancin shekarun sa. Ko dama can Muhsin haziki ne kuma yana da sha'awar
kasuwanci. Shi yasa nauyin da Yaya Maccido ya dora masa bai gagare shi ba.
Duk wata ribar shagunan na tafiya kai tsaye account din kowannen su adadin hannun jarin sa. Babu abin
da ba a samu a mall din tun daga suttura da kayan abinci na kwalam, da duk abin da Dan Adam ke
bukata, kasancewar wajen fuskar jama’a ne, nan da nan sunan MACCIDO MALL ya yi fice a garin Sokoto,
kayan su unique ne don Adda ta sa hannu tunda tuntuni ta saba da kasuwanci.
Allah kuma ya sanya musu albarka a cikin neman su, asirin wannan family a rufe yake ruf, duk yadda suka
yi tunanin rayuwa za ta juya musu baya a bayan ran Atiku Dogondaji hakan bai kasance ba, Allah ya bawa
Adda Da daya tamkar da goma, wato Maccido (Attahir), wanda a shirye yake ya sadaukar da rayuwar sa
don ingantuwar rayuwar mahaifiyar sa da ‘yan uwan sa.
A wannan shekarar ne Yaya Maccido ya zo wa da Adda bukatar yana so ya yi aure. Adda ta tambaye shi
ko ya samu matar ne? Ya ce, eh, ya samu a can Abuja kanwar abokinsa ce Usman, sunanta Lubabatu.
Adda ta ce, “Yan wane gari ne?”
Ya ce, “'Yan Birnin Kebbi ne”.
Shiru Adda ta yi na dan wani lokaci tana nazari kafin ta ce.
“Maccido ba mu da kowa ni da ‘ya’yana, daga Allah sai kai. Matar duk da za ka aura ya kamata ka
tantance ta, ka yarda da tarbiyyar ta da dattijantakar gidan da ta fito. Wadda za ta so mu ta zauna da mu
tsakani da Allah. Wadda za ta taimaka maka wajen kula da marayun ‘yan uwanka. Ba wadda za ta kawo
canji komai kankantar sa cikin abin da ta zo ta taras ba. Idan ka yarda ka amince ita Lubabatun ta mallaki
duka wadannan, to muna maraba da ita”.
Ya dade yana tauna magananun Addar sa, yana aunawa a bisa ma'auni na hankali da tunanin sa, don
ganin ko Lubabatun sa ta mallaki wadannan qualities da Adda ta jero? Ba zai iya cewa ba! Abin da ya sani
kawai shi ne, Lubabatu ta yi daidai da ra’ayin sa, ta mallaki duk abubuwan da yake so a diya mace. Ga
kyau ga aji, ga gayu kamar rainon sarauniyar Ingila.
Sannan ga ta da ilimi don masters ke gare ta. Ba ya tunanin tana da wani aibu don kuwa abotar su da
Usman ta dade. Ya san gidan su babban gida ne, sauran halin mutum ai ba za ka sani ba sai in ka zauna da
shi.
Gadan-gadan Yaya Maccido ya sa kai ga neman auren sa. Har ya je Dogondaji ya gaya wa su Baffa Bilya.
Kafin ka ce me ye wannan magana ta kankama. An kai kudi an yi tambaya, har an ba shi mata. Tsakani na
da Yaya Maccido da ma tun fil’azal babu sakewa, babu sabo, babu wata doguwar mu’amala mai nisa.
Iyakaci na da shi in ya shigo cikin gida ne mu gaishe shi ni da Muhsin ya sa kai ya wuce dakin Adda, in
kuma tare da Addar ya same mu, sai in ba su wuri bayan mun gaisa. Wani lokacin Adda kan sa ni in dauko
masa abinci daga dining don ba ya son zama a kan tebir ya ci abinci, ya fi so ya zauna gaban Adda yana ci
suna hira. Wannan ita ce alakar da ke tsakani na da Yayana Maccido.
Shekaru biyu baya, Adda ta sa ya kai ni wata sakandire ta kudi na dora karatu na. A halin yanzu ina aji
biyar na babbar sakandire.
Kada ku dauka ko yanzu akwai soyayya tsakani na da boko, har yanzu ina nan jiya i yau, don ma dai
Muhsin ba ya bari na haka. Kullum da yamma sai ya sa na dauko littafi na ya tisa min abin da aka koya
mini. Amma kan ba ya daukar komai. Kullum ni ce ta karshen aji ko ta biyun karshe. An so a yi min
repeating a shekarar da zan shiga SS 2, Adda ta je har makarantar da kanta ta bude bakin jaka, ta kuma
ba su hakuri. Ita dai burin ta in samu ko da kwalin kammala sakandire ne, ko da ba zan shiga jami’a ba.
Bikin yaya Maccido ya zo, aka yi biki na kece raini a Sokoto da Abuja. Bikin diyar Sanator Abdu
Gwadabe.... Lubabatu Abdu Gwadabe da Arch. Attahir Atiku Dogondaji. Yaya Maccido ya sayi apartment
a Gwarimpa mai daki uku da falo. Ranar na ji yana gaya wa Adda iyayen amarya sun ce gidan ya musu
kadan, ya je ya kama haya a Maitama mai faluka uku suke so.
Adda ta kalle shi a shekeke! Ta ce, “Ko bayan raina ban yarda ka zauna gidan haya ba, alhalin kana da
naka. Ni ban yarda da rainin arziki ba. In za su zauna a wanda Allah ya ba ka shi ke nan, in bai musu ba, to
fa babu dole ta yi ta zama a gaban iyayen ta”.
An kai ruwa rana kafin su yarda su je su yi jeren. Muna kitchen ni da Addah muna hada abincin dare, na ji
Adda tana kwafa. Kafin cikin takaici ta ce,
“Ma’u, tun ba a je ko’ina ba na fara sunsuno gagarumar matsala cikin auren Maccido, sai