Showing 42001 words to 45000 words out of 46393 words
Chapter 15 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf
yara msu kyau a cikin kayanka, a ina ka saya musu?”
Ya dan dube ta yana son tuno wane kaya ne? Lokaci daya zuciyar sa ta hasko masa Ma’u a shagon
Majma’al Qimmah. Tana zabowa Ihsan da Ahsan kaya. Wani ni'imtaccen murmushi ya yi wanda bai san
ya yi ba, sannan ya sosa kansa yana ta murmushin dai ya ce.
“Nasu ne”.
"Wa ya ba su? Gaskiya ko waye ya iya zaben kayan yara, i'm sure ba kai ka zabo ba”.
Ya sake sakin murmushi, ya ce, "Ko? Ashe ni ma na iya zabi?”
Ba ta gane me yake nufi ba, ta ci gaba da cin abincin ta. Sai da suka kammala ya dauko wayar sa yana
danne-danne. Ba jimawa Lubabatu ta karbi alert din kudi masu yawan da bai taba ba ta kamar su ba. Da
mamaki ta dago tana masa murmushi.
“Sweetie, wannan kyauta haka? Lallai an bude sabuwar plaza da kafar dama, sai kawai in sayar da motata
in cika in sayi latest model.
Yana mamakin ta ya ce, “Ba kya tambayar ko na mene ne kawai daga ganin kudi ba neman karin bayani
sai kashewa?”
Ta ce, “Bayanin me zan nema? Na san dai ba mistake ka yi ba”.
Ya gyada kai, “Eh ba mistake na yi ba, naki ne, na fadar kishiya ne, ki sayi duk abin da ki ke so, na ga ya fi
in sayo miki kaya tunda ba kya rabo da dinkin sabon kaya”.
Lubabatu ta yi tsai da iadanunta tana duban shi, sai da ya yi shiru sannan ta ce, “Attahir, me ka ke fada
ne? Kamar kishiya fa ka ce?” With affirmation ya gyada mata kansa,
“Eh na yi aure Lubabatu, kusan wata uku da suka wuce”.
Lubabatu ta yamutsa fuska, ta ce, “Idan wasa ka ke ka bari, bana son irin wannan wasan ka sani”.
Ya dauko wayarsa ya shiga lalube a gallery har ya budo hoton da yake so ya tura mata wayar gaban ta.
Da farko kamar ba za ta dauka ba, sai kuma ta sanya hannu ta dauka.
Hotonsa ne shi da Ma’u, selfie ne ya dauke su a Hilton na makka, hannayensa zagaye da wuyanta,
fuskokin su na nuna irin farin cikin da suke ciki, sannan akwai alamun soyayyar da ke cikin idanun Attahir
dadaddiyar ajiya ce, wato ba ta yau ba ce.
Wani irin ihu Lubabatu ta saki tare da hada wayar Attahir da bango, ta kuwa tarwatse nan da nan
kowanne part ya kama gabansa.
Ba karamar razana Ihsan da Ahsan suka yi ba. Lubabatu ta yi kukan kura ta yi kan Attahir,
“Gara in kashe ka kafin ka kashe ni…”.
Wuyansa ta kai wa damka, duk kokarinsa na bambare hannayenta daga jikinsa ya kasa. Ya ce, “Lubabatu
kashe ni, ya fi min alkhairi da inda ki ke leading rayuwata… kin raba ni da uwata kin raba ni da ‘yan
uwana, kina kokarin ja na jahannama. Kada ki dauka duk shige-shigen da ki ke yi domin ki halakar da ni
ban sani ba. Na yi shiru ne ba don tsoro ba sai don ni ma ina da nawa target din. Wanda shi ne auren ‘yar
uwata, yawon bin bokaye don Allah kar ki fasa ki ci gaba, wa man yatawakkal alallahi fa huwa hasbuhu.
Na auri ‘yar uwa ta Asma’u, ruwan ki ne ki kama girman ki mu zauna lafiya ruwanki ne ki hana kanki
kwanciyar hankali, ki ci gaba da shige-shigen da zai fishshe ki. Rana dubu ta barawo… rana daya ta mai
kaya.
Ban auri Asma’u da nufin tozarta ki ba, sai don ra’ayin kaina da samawa mahaifiyata farin cikin da ki ka
kasa bata, girman da ki ka kasa bata, da ‘ya’yan da ki ke rowanta mata.
For your good information ku biyu ne matana yanzu. Ba ni da niyyar hada ku gida daya a halin yanzu,
amma ban san me gobe za ta haifar ba…”.
“Ubanka za ta haifar Attahir, na ce ubanka za ta haifar. Ka yi kadan ka yi min wannan tozarcin. Ka je gida
an tsaface ka an hada ka da wannan dangin dangaron don a ga bayana, to uban kuturu ya yi kadan
wallahi. Na fi karfin in hada miji da kowa balle wanan ‘yar matsiyatan.
Ban da soyayya kai ka san ba ka isa ka aure ni ba. To haka nake so ka sa a ranka ni kadai za ka rayu da ni
da an ki da an so. Ka gaya wa Nabeelah ni murucin kan dutse ce, ban fito ba sai da na shirya, don na san
duk wannan munafurcin nata ne.
Idan ka ga ka rayu da wata mace ba ni ba, to ka tabbata a lahira ne, in ka yi dacen shiga aljanna kenan...”.
Hankade ta ya yi ya mike don ya lura ta soma fita daga saiti, kwayar idonta bakidaya sun juye. Taku ya
soma yi zai wuce zuwa dakinsa don ba ya so ya sake tanka mata. Ya gama fadin mata duk abin da yake
son fada mata shekara da shekaru ya kasa. Tsoro da dabaibayin da ke kansa bai ba shi dama ba.
Yanzun ma har mamakin kansa yake, yadda rana daya ya juye ya koma Maccidonsa na ainahi. Bai san
cewa sujjadar UWA ba ce cikin talatainin dare da zafin hawayenta da jajircewar ta wajen kai wa Allah
kukanta ba tare da gazawa ko gaggawa ga son saukar ijaba ba.
Lubabatu ta dauki kofin da ya gama shan shayi da shi ta wulwula shi zuwa ka Maccido. Bai same shi a
ko’ina ba sai a keyarsa. Ya tarwatse a wajen wanda hakan ya yi sanadiyyar nutsewar wani bangare na
kwalbar cikin tsokar naman kansa, jini kuma ya balle kamar an kwance famfo.
Ihsan ta saki kuka ganin jini na zuba daga kan Babanta, ta yi kansa tana kiran sunansa. Hannunta ya kama
sannan ya kai hannu ya dafe wajen ya juyo ya dubi Lubabatu.
“You are just wasting your time, bakin alkalami ya riga ya bushe, don kuwa Asma’u da kusa haifa wa
Ahsan kannai”.
Ya suri mukullin motarsa kan kujera ya sunkuya ya dauki Ahsan da ke ta kuka ya kama hannun Ihsan suka
fice. Bangaren mai rainonsu ya kai su, ya ce ta kula da su zuwa safe. Sai salati ta ke ganin jini na malala
daga kansa. Take ta hada biyu da uku ya ba ta ma’ana, ko dai Madam zai yi wa kishiya ne? A kan yadda ta
san uwar dakin nata a kan kishi har da su ‘yan aiki za ta aikata fin haka.
Ya dauki mota jiri na dibansa zuwa private clinic mafi kusa, aka yi masa treating ciwon aka cire wadda ta
nitse, sannan aka yi masa dinki.
Kin komawa gidan ya yi sai sha biyu na dare, a tunaninsa ta yi barci, amma yana shiga falo ya jiyo tashin
muryarta tana waya cikin kuka…
“Yadda ki ka rusa rayuwa ta Allah ya rusa ta ki Nabeelah. Allah ya sa balaraben ya sako ki. Ki gaya wa
uwarku na ci dubu sai ceto, na dade da sanin mugun nufinta a kaina da wannan mummunar yarinyar da
ta ajiye a gabanta… to na ga aure na shaida ina jiran ganin ranar shigowar ta gidana, wallahi sai dai ku
dauki gawar ta inyaso ni ma a kashe ni…”.
Banka kofar ya yi ya shiga dakin, wayarsa ce a hannunta. Ya fizge wayar ya duba ya ga kiran na tafiya,
kuma sunan Aunty Nabeelah ne. Ya daga hannu ya wanka mata mari, ya sake wanka mata.
“Nabeelah sa’ar ki ce? Yayata uwa daya uba daya?”
Ya kankance ido yana mata wani kallo da ba ta taba gani cikin kwayar idon sa ba.
“Uwata ki ke bai wa wannan sakon Lubabatu? Uwar da ta kawo miki ni duniya na shagaltu wajen bauta
miki na manta da ita, amma ba ta taba korafi a kanki ba, sai ni don na yi auren da duk cikin su babu
wanda ya sanya ni? To ina so ki sani na auri Asma’u ne don ina sonta ba don wani cikin su ya cusa min ita
ba. Ke kuma na aure ki ne don kare kaina daga zina, amma tun farko Asma’u nake so ba ta isa aure a
sanda ni na isa ba. Hope this information is enough and clear ki yi deciding za ki iya ci gaba da zama da ni
ko a’ah?" Lubabatu ta yi masa wani sakaran kallo, “Ina zan je? Ai aurenmu takalmin kaza ne, da ma haka ake so in
tafi, don na tsokale wa kowa ido, to ba inda zan je, zama daram. Zaman yakin kwatar kai, inyaso mai karfi
ya kwace Maccidon. Kada ka dauka soyayya ce za ta zaunar da ni. Zan zauna ne don in hana ku kwanciyar
hankali in kuntata rayuwar ku yadda ku ka kuntata tawa…”.
Murmushi ya yi irin na mazan da suka san kansu.
“Karyar banza karyar wofi, kin ce soyayyar ta kare ko?” Ya fada yana takowa zuwa inda ta ke. Ta gane abin
da yake shirin yi wanda kuma a take zai wargaza dukkan karfin zuciyar ta. Sai ta yi wuf! Ta kasan
hannunsa ta fice dakin da gudu tana kuka. Attahir ya yi murmushi wa kansa ya daga murya yadda za ta
jiyo shi.
“Ai na so ki tsaya a tantance aya da tsakuwa, ta nan za mu gane ta inda karewar soyayyar ya fara. Kin ci
darajar haihuwar ‘ya’ya biyu, wallahi yau da sai na kumbura miki mukamikin da ke wa Yayata rashin
kunya”.
Tun daga wannan ranar gidan ya rikice ya koma wani dan karamin sansanin yaki. Lubabatu ta hana shi
kwanciyar hankali ko na second daya. Duk kayan amfaninsa ta lalata, ta kwankwatsa kayan kallo da
glassan windows, ta zama kamar wata sabuwar mahaukaciya. ‘Ya’yanta ba ruwan ta da su, komai nasu ya
koma hannun mai rainonsu, abinci sai dai ya saya a waje ya kuma ci a wajen in yana so ya tsirga masa.
Abubuwa suka taru suka addabi Attahir, ga hidimar mall ga ta Maccido Plaza, ga ta ‘ya’yansa in ya dawo
gida, sannan ga tarin ayyuka a ofis. A daidai wannan lokacin ne kuma Julius Berger Nigeria suka kara
masa matsayi zuwa construction manager, ya ga cewa in ya ci gaba da rayuwa da Lubabatu a haka
watarana stress za ya kayar da shi, don haka ya gaya wa yayanta Usman duk halin da yake ciki da ita, shi
kuma bai yi wata-wata ba ya gaya wa Baban su.
Lubabatu ta gama tsiyatakunta na yau inda ta debi ruwa bokiti-bokiti ta kwara a gadon Attahir ta fito za
ta koma dakinta, ta ji sallamar Babanta da yayanta Usman.
Tana ganin su gabanta ya fadi, don ta san Babanta ba ya zuwa gidajen su. Jikin ta ya ba ta Attahir ya gaji
ya kai karar ta ne. Ilai kuwa, Usman ya fiddo sharbebiyar bulala daga leda ya mika wa Baban, za ta gudu
Usman ya damko ta. Baban ya yi mata dukan kawo wuka, ya lallasata ko’ina a jikinta ya yi birdin-birdin,
sannan ya koro mata warning din cewa, idan ta kai Attahir bango ya sake ta, kada ta sake ta doso gidansa.
Daga wannan lokacin ne Maccido ya samu saukin Lubabatu, amma sai ta daina shiga duk wata sabgarsa,
ta maida shi shi da babu duk daya cikin gidan, sannan ta guntule alakarta da ‘ya’yanta, ta bar wa mai
raino.
Don haka ne gidan duk ya zame masa kurkuku, Allah-Allah yake ya samu sarari ya arce Sokoto. Ni ma din
ba ya samun wata kulawa daga gare ni a waya, ina can ina fama da kaina, imagine laulayin ciki mai
wahala, gaskiyar Muhsin Yayan sa is a sharp shooter. Karshe sai dakin Adda na koma da zama gabadaya,
don Aunty Nabeelah ta dade da komawa Lebanon.
Kafin ta tafi ta ba mu labarin wayar cin mutunci da Lubabatu ta yi mata, duk da Maccido ya ba ta hakuri,
Adda kuma ta ce kada ta kula ta zafin kishi ke damunta, ta yi haushin kaza huce kan dami.
Ranar wata juma’a ya samu sararin ayyukansa. Ya sa Nanny Maria ta hada masa duka kayan yaran a
babbar trolley dinsu. Lubabatu na daki tana ta kitsa sharri a waya da kawaye ya kwashe yaran ya taho da
su Sokoto ba da saninta ba.
Ba ta gane ba sa gidan ba sai yamma lis, jin shirun su ya yi yawa, da ko ba za ta kula su ba sai sun shigo
inda ta ke. Ta kwala wa Maria kira ta zo,
“Ina yara ban ji motsin su ba?”
Maria ta ce, “Oga ya kwashe su ya tafi da su tun safe ba su dawo ba, kayan su duka ya kwashe”.
Lubabatu ta zame wa Maria kamar zautacciya, Maria ta sha mari hagu da dama kan don me tun lokacin
ba ta zo ta gaya mata ba ta bari aka kwashe mata ‘ya’ya aka kai wa makiyanta? Ta je daga yau ta sallame
ta.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
SOKOTO
Ihsan ce a gaba, Ahsan ya biyo bayanta sanan babansu. Suka yi sallama a dakin Adda. Zaune nake
tsakiyar gadon Adda na yi rashe-rashe ina cin gugguru. A tare ni da Adda muka dubi kofa don ganin masu
shigowa. Yaya Maccido da na yi masa kallo daya kasa dauke ido na yi a kansa. Gabadaya ya rame ya yi
duhu, mutumin da watanni uku da suka gabata kamar ka taba fatarsa jini ya yi tsartuwa.
Hannu na bude wa Ihsan ina kiranta, Adda kuma Ahsan ta ke kokarin dauka. Farin cikin ta ya gaza
boyuwa. Ta kara amincewa Allah sami’ud du’a’I ya dawo mata Maccidon ta da ta haifa, ba mai kama da
shi a baya ba.
Yaran duk suka lafe jikin Baban su alamar ba su zuwa ba su san mu ba. Da wayo da cakulet da pop-corn
na samu Ihsan ta yarda ta zo kusa da ni, na jawo ta jiki na zuciyata kamar takarda. Yau ba ni da abin da
zan biya Yaya Maccido. Ahsan kuwa da Adda ta matsa da son daukarsa, kuka ya saka yana kiran
Mamansa. Yaya ya ce, “Ahsan my mum? Ba za ka je wajen Mamana ba?”
Adda ta mike ta soma hidima da su, shayi ta fara hada musu mai kauri kafin ta cika gabansu da lafiyayyen
abinci wanda na dafa wa Yaya domin ya yi waya ya ce yana hanya, amma bai gaya mini tare da yaran yake
ba. Ya ce "Surprise yake so ya yi wa kowa”.
Hawwa Adda ta tura ta gyara sashenmu tun kafin isowar Yaya, don ba ta bari na in yi aikin komai. Girkin
ma don na Yaya Maccido ne shi ya sa ta bar ni na yi da kaina.
Yaya Maccido da Adda sai hira suke cikin nishadi. Na kama hannun Ihsan na dauki Ahsan wanda zuwa
yanzu ya soma warewa. Na ce, “Addah za mu je a yi wanka, Hawwa ta shigo min da jakar kayan su”.
Addah ta ce, “A dai yi wankan a dawo min da su nan, yau ga kafada ta ga tasu za mu kwana, ki je ki ji da
mijinki ya debo hanya ya zo ki ce rainon ‘ya’ya za ki yi, shi kuma wa zai yi nasa rainon?”
Kunya ta kama ni na fice da sauri tare da yaran.
A falo muka yi karo da Muhsin ya ce, “Lallai yau za a yi ruwa da kankara ‘ya’yan Abuja ne a gidan mu?”
Na ce, “To ga su dai ka gansu, ka zo ka sayo musu pampers”.
Na yi musu wanka da ruwa mai dumi, Ihsan na ta yi min hira. Shi Ahsan bai iya magana sosai ba. Hawwa
ta kawo min kayansu na sa musu, na gyara wa Ihsan gashinta, nan suka yi shar duk suka yi kyan gani.
Muna hira da Ihsan barci ya dauke su a jikina.
A haka Yaya Maccido ya cimmana. Daga bakin kofa ya tsaya yana bina da wani sassanyan kallo. Yafito ni
ya yi da hannun sa, ya yi min alamar in zo gare shi. Na yi masa nuni da yaran da ke jiki na. Karasowa ya yi
ya dauke su su duka biyun a kafadunsa yana fada kasa-kasa don kada ya tada su,
“This is cheating!”.
Na ce, “Don Allah Yaya ka bar su mu kwana”.
Hararar da ya yi min ta nuna ina bata baki na ne kawai.
Wajen Adda ya kai su ya dawo. Kafin ya gama abin da yake a falo na hada masa ruwan wanka na zuba
turaren wankansa a ciki na desire dunhill.
Muna kwance kalmashe cikin jikin juna bayan al’amura sun daidaita a tsakanin mu, na kai hannu cikin
sumar Attahir ina cakudawa sannu a hankali. Cikin muryar da ke nuna damuwa na ce,
“Yaya ka rame, at the same time ka yi baki”.
Idanunsa a lumshe ya ce, “Don ma ba a kawo miki gawa ta ba? Amma Lubabatu kashe ni ne kawai ba ta
yi ba, in haka ake kishi Allah wadaran kishin mata. This is insane. Ranar da zan miki taki kishiyar ashe ke
ma daina so na za ki yi?”
Hannu na ya kai kan tudun wani dinki a kasan kansa.
Cikin damuwa na ce, “Wannan fa?”
Ya ce, “Duk a cikin punishment dina na kara aure ne”.
Cike da tausayi na ce, “Yaya kishin mata kala-kala ne, I can never hurt you like this don ka yi min kishiya,
zan yi fushi da kai for the mean time in daina yi maka magana, but I can never ever hurt or insult you…”.
Yaya Maccido ya shigar da ni cikin jikinsa sosai ya rungume ni.
“Balle ma ba zan yi ba Asma’u. Da a ce ke na fara samu ba zan yi mata biyu ba. You are more than
enough to every husband. Darajar yaran nan nake dubawa shi ya sa har na daure na ci gaba da zama da
Lubabatu cikin mugun yanayin da ko makiyana bana masa fatan auren mace irin