Showing 6001 words to 9000 words out of 46393 words
Chapter 3 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf
dai Allah ya
kade fitina”.
Nan ta ke ba ni labarin maganar gida.
Na ce, “Ni kuwa tunda na ga matar rai na yake son ta Adda, kyakkyawa ce sosai, ga ta da gashi har
kafadun ta”.
Adda ta harare ni, ta ce,
“Ai nan ku ka fi kauri ‘ya’yan zamani, kyale-kyalen duniya, wanda dukkan shi mai gushewa ne. Amma
mutanen da suka fito fili suka raina arzikin ka, ai babu alamun alheri a tattare da su”.
Ranar lahadi aka kawo amarya Sokoto. An yi wa baki abinci na alfarma wanda zai ishe su komin yawan su.
Bangaren Maccido na gidan aka sauke su wanda Yaya Maccido ya gyara sosai. Sai dare suka shigo da
amaryar wajen Adda tana tare da abokan arzikin ta da mutanen Dogondaji, aka yi abin da ake kira
‘amana', aka yi addu’o’i na nema wa ma’auratan zaman lafiya da zuri’a dayyiba sannan suka koma sashen
Yaya Maccido.
Washegari ‘yan rakiya suka juya Birnin Kebbi, sai amarya da ‘yar aikin ta wata budurwa banufiya. Kwana
uku na yi ina hidimar su don duk abin da za su ci Adda ta dora shi a wuya na. Ta kan ce "in dai a kan girki
ne ba ni da haufi a kanki Ma’u. Ko Maccido ya sara miki duk miskilanin sa, ya ce, kin iya girki sosai”.
Da daddare bayan na shigar musu da dinner na yi sallama dakin Aunty Lubabatu. Tana gaban madubi
tana kwalliya, da alama daga wanka ta fito. Gashin nan da nake so ya sha gyara sai sheki yake a dokin
wuyan ta. Ta amsa min sallamar ba tare da ta juyo ba daga shafa hodar da ta ke yi. Na ce,
“Aunty zan je in kwanta ne, ban sani ba ko da abin da ku ke so bayan abinci?”
Ta ce, “Ina son gasassun ‘yan shilla wallahi, bana son cin abinci da daddare”.
Na yi dan jim! Kafin na ce, “Ga shi ba mu da ‘yan shilla sai manyan kaji, ko in nemi karama a ciki in gasa
miki?”
Ta yamutse fuska, ta ce, “Kai anya? Barshi kawai in Tahir ya dawo ya nemo min. Na gode”.
Na koma sassan mu can na samu Muhsin yana kallon kwallo a falo. Ya ce, “Ma’u me ku ka dafa ne?”
Na ce, “Sai abin da ka ke so. Abinci har kala uku na yi wa amare”.
Ya kyabe baki, ya ce, “Ni fa sam wannan matar Yaya Maccidon ba ta yi min ba. Mace ba fara’a ba
haba-haba da jama'a. Ko da na kissa ne. jiya fa da na shiga ina jin shi yana yi mata bayanin ko wane ne ni,
amma sai cewa ta yi, "sannu fah!" (Ya fada yana kwaikwayon muryar ta), daga haka ta ta kara kallona ba”.
Na yi dariya na ce, “Yanzu kuma duk abin da na sha wahala na girka mata ta ce ba ta so, ya yi nauyi,
gasassun ‘yan shilla ta ke so, kuma ba mu da su”.
Ya ce, “Mijin ta ya zo ya nemo mata. Ni gara su tattara su tafi su bar mana gida. Haka kawai a dinga sa ki
wahala, ke girkau ce?”
Adda ta leko daga kofar dakinta da hijab a kanta, da alama sallah ta idar, ta yi masa dakuwa, ta ce, “Ungo
nan. Kun zauna kuna gulma, akwai sa’anku cikin su? Na ce akwai sa’an ku?”
Ba shiri daga ni har Muhsin muka bar falon, kowa ya yi dakin sa.
Na canza kayan jiki na na sa na barci na canza bedsheet dina, ina kokarin bude labulaye don rage karfin
A.C da ta cika dakin, na ga Yaya Maccido na shigowa cikin motar sa kirar Cadillac. Sai na samu kaina da
son tsayawa in ga fitowar sa don ni dai haka kawai yake burge ni, ga kyau ga wata irin nutsuwa, ga aji,
sannan ga wani irin kwarjini na musamman da Ubangiji ya mallaka masa.
Ya fito sanye cikin shadda filtex fara kal! Sai walainiya ta ke yi cikin hasken farin kwan fitilar da ya haske
harabar adana motocin, hannayen sa rike da fararen ledoji. Kai tsaye cikin kasaitaccen takun sa ya wuce
ta gefen tagar daki na zuwa cikin gida.
Wajen Adda ya fara zuwa kamar yadda ya saba bai jima ba na ga wucewar sa zuwa nasu sassan, wanda
dole ta gaban tagar daki na za'a wuce. Iska ta kado min sassanyan turarensa Escada Magnetism. Na samu
kaina da fadawa bisa kwayar kujerar sofa da ke daki na yayin da wani tunani ya bakunce ni.
“Matar sa ta yi sa’a”.
“Matar sa is a lucky person”.
“Matarsa ta ji dadi a rayuwar ta”.
A lokaci guda na tambayi kaina dalilin wannan bahagon tunanin? Inda ba tare da bata lokaci ba zuciya ta
ta halarto min da amsa;
“Yaya Maccido yana BURGE NI!”.
Kwan fitilar da na kashe aka kunna, haske ya gauraye dakin. Adda na gani rike da daya daga cikin ledojin
da Yaya Maccido ya shigo da su. Ta ce, “Ma’u, kin yi barci ne?”
Na yunkura na tashi zaune, na ce, “Ina shiri dai Addah”.
Ta miko min ledar hannun ta, “Ungo nan ki ci, gasassun ‘yan shilla ne Yayan ku ya kawo min. Ni ba iya cin
su na yi ba, ko za ki iya ci?”
Na karba tare da yin godiya, ta juya ta fita tana jaddada min yin addu’o’i kafin na kwanta.
Na bude ledar kamshin naman ya buge ni wanda ya ji kayan kamshi. Wato shi auren haka yake da maida
mace ‘yar gata, ko me ta ke so mijin ta zai mata, zai nemo mata komai runtsi.
To ni yaushe nawa auren zai zo?
Wane ne nawa mijin?
Yaushe zan isa auren?
Tambayoyin da nake yi wa kaina ke nan wadanda ba ni da amsar su. Na san dai rayuwar Yayan mu
Maccido da matar sa Lubabatu ta darsa min kwadayin yin aure a zuciyata.
*****
Satinsu biyu suka tattara suka wuce Abuja. A satin nan guda biyu mun fahimci da yawa daga halayen
amaryar tamu. Don kuwa ba ta zuwa ta gaida Adda in har ba Maccidon ne ya sako ta a gaba suka shigo
tare ba. Sannan ni da Muhsin da muke matsayin kannen mijin ta ba mu ishe ta kallo ba. Ni ta ma fi ba ni
matsayin ‘yar aikin gidan ganin yadda ta ke sa ni ayyuka cikin gadara da bada umarni. Mun fahimci dai
tana da girman kai, sannan ba ta shigo gidan da niyyar gina kyakkyawar mu’amala tsakanin ta da mu ba.
Adda ma bayan gaisuwa babu abin da ke hada su. Gane hakan da Muhsin ya yi sai ya yi gaggawar janye jikin sa daga gare ta. Ni da alhakin kula da abincin ta
ke wuyana dole na ci gaba da shiga sashen nata akai-akai har suka gama kwanakinsu suka wuce birnin
tarayyah.
Ranar da suka tafi Muhsin ke fadin, shi wallahi gidan ya fi masa dadi. Na ce, “Ni kuma kewar su nake, ko
banza ina koyon dressing, ina kallon gayu ina kwaikwaya”.
Tsaki ya yi, ya ce, “Allah ya sauwake miki Ma’u”.
Tunda su Yaya suka tafi tsakanin shi da kowa sai dai waya. Adda ta ke kokanta min rannan muna girki,
“Yayan ku yau watannin shi hudu bai zo ba, shi da a da karkari ya yi sati biyu, kodayake ya yi aure, nauyi
ya karu masa, kuma dai yana kiran waya. Amma ya dace ya zo haka don lissafin mall ya fi karfin Muhsinu,
jiya yake gaya min an samu batan wasu kudade masu yawa, kuma yana zargin akantocin mall don sun ga
yanzu babu idon Maccido”.
Yadda ta ke maganar cikin sanyin jiki da sanyin murya dole ta ba ka tausayi. Na rasa abin da zan ce wanda
zai kwantar wa da Adda hankali, amma tabbas Yaya Maccido tunda ya yi aure ya manta da mu, ya dauke
kafar sa daga cikin gidan su. Ban san dalili ba, amma na san hakan is unfair don ka yi aure ka daina zuwa
ganin mahaifiyar ka da marayun kannen ka.
Wasa-wasa sai da Yaya Maccido ya kwashe watanni tara ba zuwa ba aike. Wayar ma da yake kira sai ya yi
sati bai yi ba. Ba dama Muhsin ya yi korafi, yanzu Adda za ta ce tunda yana lafiya cikin iyalin sa
alhamdulillah. Amma ni na sani Adda na cikin matsananciyar damuwa, ba ta son dasa wa Muhsin
damuwar da za ta sa ya daina girmama Yayanshi ne.
Duk ta rame ta rage walwala. Sai dai kuma ta kara karfi wajen ibada. Sosai Muhsin ya zage ya dora wa
kansa nauyin da Yayansa ya sauke na kula da mall da duk wasu kudi da ke shigowa. Kuma akantocin da ya
kama da yi wa shagon almundahana ya sallame su nan take, don haka sauran suka shiga taitayin su, duk
da haka abubuwa da yawa na fin karfin sa in aka yi la'akari da karancin shekarun sa.
Aunty Nabeelah ce ta kira Adda a waya daga Beirut, bayan sun gaisa sai ta kanga mata kukan jariri a
waya. Zo ki ga farin ciki wajen Adda a fili ta dinga fadin, “Masha Allah, tabarakallah. Mace ko namiji?”
Nanilah ta ce "namiji ne, Atiku (Aasim)".
Wani hawaye ya digo daga idon Addah, kewar Baban nasu ta zo mata. Tun tafiyar Maccido da kin
zuwansa sai yau ne ta san hawayen da ta zubar a kan Maccido ne. in lissafin da ta ke yi daidai ne
watannin auren Maccido goma sha daya, wanda a ciki bai fi sau uku ta sa shi a idanunta.
Nabeelah ta ce, “Adda ya wajen su Maccido? Ni tunda ya yi aure ya manta da ni, ya daina kira na, ni in na
kira shi koyaushe ya ce min yana kan uzuri zai kira ni, kuma a karshe sai dai ni in kara kiran, amma ba zai
taba kira na ba. Matar kuma sau uku ina kiran ta, amma yadda ta karba min ban ji dadi ba sam, shi ya sa
ban sake ba”.
Adda ta nisa ta ce, “Allah ya raya min maigida na. Maccido kuma ki yi masa uzuri kin san yanayin aikin
nasa, ba waje daya yake zaune ba, koyaushe yana kan furojat (project)".
Nabeelah ta bar zancen don bai gamshe ta ba, ta ce, “Muna kan hanya zuwa jibi insha Allah, gara in zo in
wankan ganyen runhu da darbejiya hankalina zai fi kwanciya duk da a asibiti an ce ba sai na yi ba”.
Adda ta ce, “Rabu da su, ku zo ku yi wankanku ku sha ruwan zafi ku gasu. Allah ya kawo ku lafiya”.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE*
Nan muka shiga shirin zuwan Aunty Nabeelah, hatta ganyen da za ta yi wankan da shi an tsinko an jibge,
an sayo runhu da duk abin da za su bukata, tare za mu zauna a daki na in ji Addah, don tun asali da ma
dakin ta ne na gaje.
Aunty Nabeelah ta iso da kyakkyawan balaraben jaririn ta. Tun ranar da suka zo yaron ya shiga raina
sabida kyawunsa, kai ka ce ni aka haifa wa jaririn nan, koyaushe yana bayana a goye. Sau uku kawai Adda
ta yi masa wanka na koya na karbe ni nake yi masa safe da yamma, in cancara masa kwalliya da kayan sa
masu kyau. Aunty Nabeelah na kiranshi Aasim, to sai mu ma duka muka kama.
Satin su biyu Aunty Nabeelah na lura da abubuwa. Babu Maccido babu wayar sa bayan ta gaya masa ta
haihu, kuma ta zo gida. Sannan ta lura komai Muhsin ke wa Adda wadanda a baya Yayan ke yi. Sannan
Adda ba ta yi mata zancen sa, ko ita ta dauko zancensa Addah za ta waske. Me za ta ce wa Nabeelah?
Maccido tunda ya yi aure ya samu mata ba ta kara ganinsa ba tun watanni ukun farko, ko me? Ba ta so ta
zama uwar miji mai korafi, sannan ta san Nabeelah na da zafi ba ta so ta fahimci komai.
Ina goye da Aasim ina zagaye dakin da shi don mu samu ya yi bacci sai rigimar dare yake yi. Aunty
Nabeelah da ke zaune gefen gado tana gyaran kayan Aasim ta ce,
“Ma’u zo nan”.
Na karaso inda ta ke, ta ajiye rigar yaron da ke hannun ta, ta ce, “In tambaye ki mana? Za ki gaya min
gaskiya?”
Na ce, “In har na sani Aunty Nabeelah zan gaya miki”.
Ta ce, “A wata sau nawa Maccido ke zuwa gida?”
Na jinjina kai ina dan tunani cikin lissafi.
“Auren Yaya Maccido ai ya shekara, amma sau uku ya taba zuwa ba, shima bai kwana ba, tunda suka bar
nan da amaryar sa, kuma yanzu an doshi watanni goma da zuwan nasa”.
Nabeelah ta zaro ido a kaina kamar ni ce Maccidon, sai kuma ta boye razanar ta da mamakin ta, ta
hanyar lumshe idanunta, ta ce,
“Kada ki gaya wa Adda na tambaye ki komai”.
Kai na girgiza, “Insha Allahu”.
Daga ranar Aunty Nabeelah ba ta kara kiran Yaya Maccido a waya ba, sannan ba ta kara yi wa Adda
zancen sa ba. Na ga dai suna yawan kebewa ita da Muhsin suna magana. Wankan wata daya ta yi sun
murmure sun yi kyau da kiba, ita da Aasim.
A ranar da suka cika kwanaki talatin ta ce da Adda ita fa ta gama wanka, za ta je yawon arba’in Abuja,
tunda ta zo ba ta ga dan uwan ta ba.
Za ka iya ganin yadda Adda ta sunkuyar da kai, tsufan ta ya fara bayyana sakamakon damuwar da ta ke
ciki. Ta kasa ce da Nabeelah kada ta je tunda Nabeelah za ta nemi ba’asin hakan, amma a zahiri ba ta so
ta je din. So ta ke ta ci gaba da sanya wa Maccido idanu ba tare da sun bibiye shi ba har ta ga iya gudun
ruwansa.
Ashe da ma a wajen ‘ya’yan yanzu mace na maye gurbin mahaifiya da shakikai?
Adda ta ce, “Da ma Dogondaji ki ka tafi wajen dangin ki, da ya fi miki, bana so ki je ki dora musu hidima”.
Aunty Nabeelah ta yi wani irin murmushi ta ce da Addah, “Can din ma zan je in na dawo kafin in koma.
Bar ni in duba dan uwana rabin raina”.
Adda sai ta mike da nufin barin wajen, Aunty Nabeelah ta ce, “Ina neman alfarmar rakiyar Ma’u, kin san
ta fi ni iya kula da Aasim”.
Addah ta ce, “Lala-lalah! Ma’u ba ta taba tafiya mai nisa ba, kuma kin sani ba hutu suka yi ba”.
Aunty ta marairaice, “Don Allah Addah wallahi zan kular miki da Ma’un ki, insha Allahu lafiya za mu je mu
dawo, kuma gobe juma’a za mu tafi mu dawo lahadi. Zan koya mata karatun da ya wuce ta na
islamiyyar".
Muhsin ma ya saka baki.
“Ai ni in babu Ma’u babu ni a tafiyar, na fi so kullum tana gefe na in ina tuki, don ma ba ni da kudi ne da
na fara biyan Adda toshin Ma’u”. Ya fada yana sosa keya da mukullin motar shi.
Dariya Aunty ta yi, ta ce, “Da kun bada perfect match gaskiya. Kai 18 years, ita 16 years, ku tara ‘ya’ya
before 20 years ku cika wa Addah daki da su su taya ta hira”.
Na galla masa harara tare da zumburo baki, “Allah ya sauwake in aure ka, me zan yi da dan ball?”
Ya ce, “Yarinya ball aji ce yanzu, da Adda za ta ba ni dama da har Manchester sai na je na buga ball”.
Adda ta yi tsaki, “Ku bana cikin shiririta, kada in kara jin wannan maganar, dukkan ku yara ne kuma karatu
nake so ku yi, in ba za ka taimaka mata wajen ganin ta maida kai ga karatu ba, to kada in kara jin wannan
maganar”.
“Mun tuba Adda, mun bi Allah mun bi ki!”. In ji Muhsin.
“Addah, don Allah mu tafi da ita?” In ji Aunty Nabeelah tana marairaicewa.
“Ku je Allah ya kiyaye hanya. Amma don Allah Nabeelah ki kama girman ki, kada ki je ki yi halin yara na
sanki sarai”.
Murmushi mai ciwo ta yi, ta ce, “Insha Allahu Adda zumunci ne kawai zai kai mu”.
Tuni na tsallake su na tafi na soma hada mana kaya. Aunty Nabeelah ta shigo ta tadda ni har na zuge
jakar ta da tawa da ta Aasim.
Ta ce, “Aiki ga mai kare ka…”
Dariya na yi, na ce, “Don ba ki san yadda nake son zuwa Abuja ba ne Aunty Nabeelah, in ga Aunty
Lubabatu mai gashi. Sosai nake son ta wallahi”.
Aunty ta ce, “Wace ce haka?”
“Matar Yaya Maccido mana!”.
Tsaki ta yi, ta ce, “Allah ya shirye ki Ma’u”.
Ba mu isa Abuja ba sai yamma lis, duk da cewa mun yi asubanci, kuma gudu sosai Muhsin yake yi. Gaba
daya mun yi wujiga-wujiga. Aasim sai tsala kuka yake yi sabida gajiya da ciwon jiki.
Muhsin ya dauke kan motar ya shiga unguwar Gwarimpa, gidajen su Yaya Maccido na daga farko-farkon
unguwar. Bai tsaya ba sai a kofar apartment din wanda ke dauke da fenti ruwan madara da ruwan kasa.
Kananan gidaje ne a cikin estate masu kyau da tsari. Kusa da Cadillac din Yaya Maccido Muhsin ya adana
motar sa, sannan ya kashe. Gabadaya muka yi hamdala ta godiya ga Allah da ya nufe mu da isowa lafiya.
Aunty ta ciro wayar ta a jaka saura kadan cajin wayar ya muta, ta kira lambar Yaya Maccido. Sai da ta yi ta
burari tana sake kira ba tare da ta kosa ba, kamin ta samu ya daga wayar da sassanyar sallama a bakin sa.
“Ga mu a kofar gida”.
Kawai ta fada ba tare da ta amsa sallamar da ya yi mata ba.
Ya ce, “Kofar wane gidan?”
A gajarce ta ce, “Naka”.
Ta kashe wayar tare da jefa ta cikin jakar