Showing 21001 words to 24000 words out of 46393 words

Chapter 8 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf

Kin ga dukkan ayyukan da ke gabansa ya ajiye su ya
taho, kuma za ku kwashe a kalla wata guda bayan aikin Addah kamar yadda likitocin suka ce.
Ke dai tsakaninki da shi ai gaisuwa ce, sai kuma ki yi masa biyayya tunda gaba yake da ke”.
Na so in ce, “Aunty dazu ba rungume ni ya yi ba… kuma hakan haramun ne”. Amma ina dago idanuna na
dubi saitin da yake, sai na ga ya kafe ni da ido yana min kallon mind yourself. Kafin ma in yi magana Aunty
Nabeelah ta ce, “Baban Aasim ya shigo, zan kira ki gobe insha Allahu”.

**SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870
*

*YIWA KAI HISABI*


((9)). Na mike na kai ma Yaya Maccido wayar sa, ya ce, “Gobe zan hada miki waya, way ata ta daina shiga
hannun ki bakauyiya kawai, kada ki lalata min. Dubi duk kin shafa min maiko a jiki”.
Ni dai ban ce komai ba, na je toilet na wanko hannuna da bakina. Sanda na fito yana shirin barin dakin.
Ya ce, “Zan je supermarket me ki ke so?”
Kaina a kasa na ce, “Sai dai in rubuta maka”.
Ya jingina da kofar dakin, ya ce, “Ok, hurry”.
Jakata na jawo, na dauko jotter da biro. Da rubutuna mai kama da na ‘yan firamare na rubuta masa duk
abin da nake bukata, pad ce ta karshe wadda na rubuta ina runtse ido cike da kunyar kaina.
Ya karba yana dubawa, sai da ya tattara hankalin sa ya gane abin da na rubuta. Ya sa takardar a aljihun sa
ya fice.
Niki-niki ya dawo da ledoji, har ma abin da ban ce ba in dai ya san zai min amfani a zaman da za mu yi, ya
siyo min. sannan ya sayo min ice-cream.
Hannuna da nashi ya miko min ledar ice-cream din, ya ce, “Ki sha, ko ki sa a fridge kada ya yi melting
(kada ya narke)”.
Har raina na ji dadin karamcin da ya yi min, na kuma ce a raina, ashe Yaya in ya ga dama yana da kirki?
Har karfe goma sha dayan dare yana zaune yana ta buge-bugen waya, har Ihsan sai da ya yi magana da
ita. Kamar in ce ya ba ni yarinyar, sai kuma dai na yi shiru.
Ina ji ya yi magana da Al-Qasim da Muhsin. Ban san me Muhsin ya ce masa ba, ya ce, “Wallahi ba zan ba
ta waya ta ba, maiko ta ke shafa min, gobe zan hada mata tata sai ku yi ta yi”.
Ya mike yana kallo na kai tsaye daga tsakiyar idanun sa.
“Zan je na kwanta Asma’u, sai da safe”.

Yadda ya siranta muryar shi ya ba ni mamaki. Na dago a hankali sai ido na cikin nasa. Da sauri na kawar
da kai sabida ba zan iya jure kallon da nake gani cikin idon sa ba. Mamaki da tu’ajjibi kamar su kashe ni.
“Sai da safe Asma’u”.
Ya sake fada da irin muryar dazun, sannan ba tare da ya jira amsawa ta ba ya juya ya fita, ya rufe min
kofar.
Gani na yi in na zauna ina mamakin Yaya Maccido mai halaye irin na wahainiya, to kuwa zan kwana a
zaune. Yau na wuni da Maccidon da ban taba wuni da shi shekaru goma sha tara ba. Yau na ga bangarori
da yawa na Maccido, wadanda ban taba sani ba. Karewa ma yau har a jikin Maccido na kwanta. Na
girgiza kai tare da mikewa na dauro alwala, na zo na dasa sallah, sai dai kuma na rasa abu na biyu da zan
roki Ubangiji bayan samun lafiyar Addah. Sabida tunani na na yau bakidaya Maccido Tahir ya cukurkuda
shi. A gaban Addah na kwana, zaune a kan kujera kaina bisa gadon ta, hannu na rike da hannun ta. A haka
barci mai nauyi ya dauke ni, sai kiran sallar asubahi na tsinkaya daga dan nesa da mu. A hankali na zame
hannuna daga na Addah wadda ke ta barci, amma ta kan motsa lokaci zuwa lokaci. Na gyara mata
kwanciya sannan na dauro alwala na tada sallah.
Da na fito na tadda nurses da doctors sun shigo suna kanta, don haka sallahta na tayar. Fatan mu Allah ya
sa a yi aikin nan cikin sa’a.
Sai karfe takwas Yaya Maccido ya shigo, a hannunsa ledojin karin kumallon mu ne. Ciki-ciki ya yi sallama,
ni ma ciki-cikin na amsa masa. Kai tsaye wajen Addah ya dosa wadda ta bude ido tana kallon mu tarr!
Amma ba ta iya ce mana komai, sai wasu siraran hawaye da suka biyo ta gefen idon ta.
Gaba dayan mu muka yi kanta da sauri ni da Yaya, ya ce, “Addah, me ki ke so?”
Ni kuma na ce, “Addah, ina yake miki ciwo? Ko in kira likita?”
Girgiza kai ta yi, sannan a hankali ta lumshe idanun ta. Kafin ta kai hannu ta kama hannuna ta dauke
kanta daga duban Maccido. Ya kara dawowa saitin da ta maida fuskar ta. Addah ta sake dauke kai daga
gare shi, wannan abu ya tada hankalin Maccido kamar ya fashe da kuka. A kan gwiwoyin sa ya gurfana ya
kama hannun Addah ya kankame ya soma magana cikin rawar murya.
“Addah…. Na sani… ni din mai babban laifi ne… laifin da ya cancanci kowanne irin hukunci daga gare ki.
Sai dai kuma ina so ki sani, na gane kure na, a yau kuma ga ni na zo na gurfana a gaban ki ina mai neman
yafiya da afuwar ki. Ina mai daukar miki alkawarin ba zan sake yin nesa da ke ba. Na sani cewa, na ba wa
neman duniya da hidimar iyali na muhimmanci fiye da ke a baya. Ina rokonki Addah ba don hali na ba, ki
yi duba ga dumbin alfarmomin ku na iyaye ga mu ‘ya’yan ku ki yafe min Addah, ki ba ni dama in gyara
kuskurena ta hanyar da hakan ba za ta sake faruwa ba. Na zo miki da kyakkyawan albishir Addah, wanda na tabbata zaki ji dadin sa, duk don in wanke laifi na
daga zuciyar ki, wanda nake so ki dubi alkhairin da ke cikin sa ki yafe min Addah…”

Hawaye ya zubo daga idanun Addah, ba ita kadai ba, dukkan mu babu wanda hawaye bai zubowa ba. Ni
dai nawa na tausayin su ne su duka, da farin cikin kalaman da yake gaya wa Addah a yau, na kuma
tabbata nadamar nan da yake fadin ya yi, da gaske ya yi ta. Domin za ka iya ganin ta zane baro-baro cikin
fararen kwayar idanun sa, wadanda suka rine da hawaye suka koma light brown masu sheki, sai walainiya
suke cikin duhun labulayen dakin da kuma hasken fitila da ba a kunna ba.
Addah ba ta yi wani nuni da ke nuna ta yi na’am da kalaman bakin sa ba, ko ta san me yake fadi, a hankali
ta lumshe idon ta ta koma barci. Ni kuma na koma gefe na dau daya daga cikin ledojin abincin da ya zo da
su na soma ci. Ina ganinsa ya ja kujera gaban Addah ya zauna yana kallon ta with so much affection, ba ya
ko kiftawa. Sai da wayarsa ta yi kara ya tashi, ya fita don ba ya so maganar sa ta tada Addah daga barcin
da ta samu.
Sai bayan azahar ya fita, ya dawo sanye da jallabiya mai gajeran hannu ruwan madara, wadda na tabbata
a nan garin ya saye ta. Kamshin jikin sa ya canza daga turaren obsession ya koma amfani da oud abyad.
Bakin balaraben Saudiyyah Yaya Maccido ya koma daga zallar baturen sa na baya. ‘Yar farar ledar da ke
hannunsa ya miko min.
Hannu biyu na sa na karba da na fahimci kwalin karamar waya ce iphone mai shegen kyau da tsada.
Na ce, “Yaya, na gode. Amma ban san ya ake amfani da ita ba”.
“Ki koya a hankali". Kawai ya ce ya karasa yana taba wuyan Addah.
Sai juya waya nake a hannu na, ina mamakin wai wannan tsaleliyar wayar tawa ce ni Ma'u. Ko Muhsin da
Al-Qasim tasu ba ta kai aji da mukamin tawa ba.
Sai ji na yi kira ya shigo cikin wayar. Da sauri na ce, “Yaya…”.
Sai kuma na yi shiru ganin ya juyo yana harara ta. Wayar na mika masa ya nuna min inda zan danna, na yi
maza na amsa fuskata fal murmushi da na ji Aunty Nabeelah ce.
“Larabawan Jeddah, ya ku ka kwana? Kaifa haalikum! Ya jikin Addah?”
Na ce, “Alhamdu lillah aunty, bikhairin wa aafiyah, ya ya Aasim?”
Ta ce, “Ai ya shiga kindergarten yanzu ba zaman gida. Maccido ya gaya min ya saya miki waya”.
“Eh Aunty, ki taya ni godiya, ni in na yi masa magana harara ta yake yi”.
Dariya Aunty Nabeelah ta yi, ta ce, “Harara as in how?”
Na ce, “Harara sosai, kamar wadda ta yi masa laifi”.
A hankali nake magana yadda na tabbatar ba ya ji na. A rashin sani na yana da karfin ji, tsaf yake jin duk
abin da nake fada a kansa.

Aunty dai ba ta bar dariya ba, ta ce, “Ina fata dai yana kyautata miki, duk abin da ki ke so yana sayo
miki?”
Na san in na ce Yaya ba ya yi min abubuwan da ta ambata din na yi masa karya, watakila har Allah ya
tsaida ni hisabi da shi a kan hakan. Don haka na ce da Aunty Nabeelah,
“Ba ni da wannan matsalar da shi, ya sayo min komai har da wanda ban ce ina so ba, yana da alkhairi
sosai”.
Murmushi Nabeelah ta yi, ta ce, “To masha Allah, don’t mind hararar sa tunda dai ita ce kadai matsalar
sa”.
Ba jimawa kiran Muhsin ya shigo, na amsa da kaina don na rike inda Yaya ya nuna min dazun.
Ya ce, “Ma’u na ta yi waya, ta zama babbar yarinya, ya jikin Addah kuma ya aka ji da sabon wuri?”
Na ce, “Wato da karamar yarinya ce tunda ba ni da waya ko?”
Ya ce, “Eh mana!”.
Na yi dariya na ce, “Addah gobe da safe za a yi aikin ta, sai a ci gaba da taya mu addu’a. Ashe Baban Ihsan
ba laifi yana da kirki, kai dai bar shi da harare-harare”.
Dariya Muhsin ya saki, ya ce, “Allah ko? In ya ji ki ya kwace wayar sa babu ruwa na”.
Na ce, “Ina Al-Qasim?”
“Ga shi a gefe na”.
“Ba shi mana mu gaisa”.
“Ya ce ba zai yi magana da ke ba”.
Cikin mamaki na ce, “Sabida me?”
Muhsin ya yi wani irin murmushi, ya ce, “Abin sirri ne. Ki shafa min kafar Addah in samu albarkar ta”.
Har muka kashe waya ni da Muhsin ina ta mamakin wai yau Al-Qasim ne ya ce ba zai yi magana da ni ba,
ni din da a da ba wanda yake son kulawa iri na. Duk da share shin da na ke yi. To me na yi masa???

Haka muka kare wunin ranar ni da Yaya kowa na danne-danne a wayar sa. Idan mun yi kuskuren hada ido
ya harare ni. Sosai na takura da zama da shi a dakin. Lokaci-lokaci nurses da doctors na shigowa su yi
aikin su a kan Addah.
Da aka kira magriba ya fita, bai dawo ba sai da aka idar da sallar isha. Hannunsa rike da abincin da za mu
ci. Ya zauna yana cin nasa, ni kuma na adana nawa don bana jin yunwa.

Sai karfe goma na dare ya mike zai tafi. A lokacin ina waya da Muhsin yana ta ba ni labarin abubuwan da
ke faruwa a gida da mall. A fusace Yaya Maccido ya ce,
“Wallahi in ba ki daina hirar wofi da Muhsin ba zan raba ki da wayar nan, don shi ba shi da hankali gobe
za'a yi wa uwar sa aiki mai matukar hatsari, amma ya zauna yana surutun banza maimakon ya je
masallaci ya yi ta addu’a. Ke kuma shashasha shi ne ki ka biye masa. Kashe wayar nan ki je ki yi alwallah ki
kama abin da ya fi alkhairi”.
Da sauri na kashe ba tare da na yi wa Muhsin sallama ba.
Yaya Maccido bai san halin Muhsin ba ne. Shi ba shi da sa abu a rai, ko sanda mahaifin su ya rasu
makokin kwanaki biyu ya yi ya ci gaba da harkokin sa da abokan sa. Har polo suka je ranar sadakar ukun
Baban su. Naturally haka halinsa yake, ba abin da ke daga masa hankali.

Washegari tun karfe bakwai na safe Yaya Maccido ya iso, ya yi wanka ya yi fresh da shi. Ya zuba wata farar
voile mara nauyi, wadda aka yi wa dinki tazarce, links din hannunshi da botiran kayan na silver ne, ya yi
matukar kyau kamar saurayi mai tashen ashirin da takwas. Ni ma na shirya cikin bakaken jallabiya na
nade kaina da mayafin su.
Karfe takwas daidai na safe aka shiga da Addah dakin tiyata inda za'a yi mata aiki don raba ta da kidney
stones. Ni da Yaya dafe da gadon da aka gungurata a kai har zuwa kofar theatre room din. Muka dawo
jikin tagar dakin muka jingina, zuciyar kowannen mu ta yi nauyi.
Ban san tunanin da Yaya ya yi ba, sai ji na yi ya kama hannu na ya rike gam! Kafin ya ja ni mu soma tafiya.
Sai bin sa nake tamkar rakumi da akala, mamaki na neman zauta ni. Ajrah (taxi) ya tare mana a bakin titi,
ya ce a kai mu birnin Meccah.
Muna bayan mota mai Ajrah na ta sharara gudu daga Jeddah zuwa Meccah. Ban tambayi Yaya komai ba
don na fahimci yana cikin wani hali na aikin nan da za'a yi wa Addah. Na fahimci babban tashin hankalin
sa bai san matsayin sa ba, Addah ba ta yafe masa da bakin ta ba, idan ta mutu ta bar shi, ina zai sa
ransa?
Sai da muka isa Haraam yake gaya min dawafi za mu yi, bakwai sau bakwai, mu roka wa Addah samun
lafiya.
A sanyaye na ce, “Mu yi umrah kawai gabadaya mu huta”.
Ya ce, “Na fi so in yi umrah tare da Addah, amma mu fara din, in Allah ya tashi kafadun ta sai mu dawo
tare mu sake yi”.
Mun yi umrah, mun yi safah da marwah, mun yi nawaafil a maqama Ibraheema Musally, sannan mun yi
dawafi bakwai sau bakwai mun yi wa Addah addu’a wadda muka sakankance an amsa kawai, sabida
alkawarin Ubangiji ne, duk wanda ya zo da bukatar sa wannan wajen ya sakankance cewa an amsa.

Ko abinci ba mu iya mun ci ba muka sake hawa Ajrah muka dawo Jeddah.
A lokacin muka samu an yi aikin lafiya. A fili na saki hamdala, Yaya ya yi wata irin ajiyar zuciya. An kai
Addah daki na musamman inda za ta zauna tsawon kwana bakwai ba tare da kowa ya shiga ba sai
likitocin ta. Duka kulawar ta tana wuyan malaman jinyar asibitin. Mu da ganin Addah sai bayan kwana
bakwai.
Dakin mu na farko muka koma inda Yaya Maccido ya umarce ni da in tattara komai nawa mu wuce
masaukin sa. Mu da dawowa nan sai bayan kwana bakwai din, amma zai dinga zuwa kullum da safe ya ji
ci gaba da ake samu a lafiyar Addah.
Ina tattara kayana, amma hankali na ya rabu biyu. Hotel fa za mu koma daga ni sai Yaya! Wannan ko a
musulunci ba mu da hurumin sa ko da ciki daya muka fito, dukkan mu baligai ne. Dai-dai misali inada
ilmin addini na. To bai ba ni damar da zan yi masa tambaya ba, don haka na rika bin umarnin sa in ga irin
hankalin sa.
Ai kuwa na ga abin da ya hargitsa min hankali domin kuwa na fahimci dakin da ya sauka a Al-Jamjoum
Fundak nan ya kawo ni. Ya aje jakunkunan mu ya juyo ya dube ni na ci uban birki a bakin kofa. Wani
miskilin murmushi Attahir ya yi, ya ce,
“In kin gaji da tsayuwar, sai ki shigo ki rufe kofar”. Ya shige toilet abinsa.



*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* *07030137870*





```HISABIN NAFS```

((10)). Da na ga tsayuwar ba za ta kai ni ba, duk kafafuna sun sage, dole na ja jiki zuwa cikin dakin.
Kujerar farko na samu na dofana jikina kamar a ce kyat! In zura a sittin. Da na ji motsin kofar toilet har
wata irin firgita na yi. Wai an ce makaho bai san ana kallon sa ba sai an taba shi, ya kamata in yi wa Yaya
magana watakila ya manta cewa, dukkannin mu baligai ne, sannan kuma ba muharraman juna ba.
“.....Yaya sai na ga kamar bai dace mu sauka daki daya ba”.
Na fada a matukar darare, kamar wadda ke tsoron furta maganar tata.
Yana shimfida darduma zai tada sallah ba tare da ya juyo ba, ya ce, “Allah koh?”
Sai kawai ya kabbara sallahr sa.
Na yi mutuwar zaune da al’amuran Maccido Taheer, masu neman hauhawar da jini na. Domin bayan ya
idar da sallah abinci ya ja ya soma ci, bayan ya gama ya nufi closet yana kokarin sauya kayan jikin sa.
Da sauri na mike na yi hanyar kofa a lokacin da na fahimci Yaya Maccido rigar sa yake cirewa. Runtse
idanu na na yi, wani irin gam! Na karasa ga kofar da lalube. Maccido na kallona yana murmushi sosai, ya
ce,
“Asma’u!”.
Tsayawa na yi daga tafiyar laluben da nake yi, amma ban juyo ba. illahirin jikina rawa yake yi. Ban san
sanda ya tako ya cimmani ba daga shi sai farar singileti da dogon wando. Hannaye na biyu ya kama da
duka hannayen sa hagu da dama, ya ce,
“Bude idanun ki ki dube ni”.
Na dan motsa idanun yayin da yawu ya kafe a baki na.
“Open your eyes ki dube ni”.
Girgiza kai na shiga yi, hawaye na zubo min.
“Bai kamata ba Yaya!”.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login