Showing 1 words to 3000 words out of 46393 words

Chapter 1 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf

*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*





*SHIMFIDAR LABARIN*



((1)). Sunan da na taso da shi tun haihuwata shi ne MA’U. Cikakken sunana na usul Nana Asma’u
Adam Bebeji. Ma’u ya bi ni ne daga bakin mahaifiya ta Nene tun ina karama. Mahaifi na Malam Adamu
bafullatanin garin Bebeji ne, wata babbar alkarya a kananan hukumomin jihar Kano. Yayin da mahaifiya
ta Nene Zainabu ta fito daga kauyen Babura ta jihar Jigawa.
Nene baka ce amma doguwa kyakkyawa, wadda ta yi tashen manema a zamanin kuruciyar ta, a
karshe dai Allah ya yi ta zama rabon mahaifi na, wanda cin kasuwa ne ya kai shi Babura kamar yada ya
saba duk ranar kasuwar garin. Ya ganta a kasuwa tana tallan fura, farat daya ta shiga zuciyar sa, ya sa kai
da gaske wajen neman aurenta da karfin sa, har Allah ya ba shi sa’a, ya sure ta zuwa mahaifar sa, Bebeji.
Sana’ar mahaifi na shi ne kasuwancin goro, da wannan sana’ar ya dogara tun yana saurayi har zuwa
shekarun girman sa. Sana’ar goro ta karbe shi don har Shagamu yake zuwa ya auno goro, ya kai shi
kasuwannin gari-gari, kuma da ita ne ya raine mu ni da kanwa ta kwalli daya, Arifah. Mu biyu Allah ya bai
wa iyayen mu kamar yadda shi ma mahaifinmu su biyu ne kacal a wajen iyayen su, shi da Yayar sa, Adda
Kilishi.
Tsakanin mahaifi na da Adda Kilishi akwai ratar shekaru masu dan dama, sai da ta yi shekaru bakwai a
duniya sannan aka haife shi.
Ba zan manta ba Baba ya sha gaya mana yadda Adda ta yi ta wahala da shi yana yaro, duk inda za ta goya
shi ta ke ta tafi da shi, sannan ba yaron da ya isa ya taba mata shi. An yi mata auren wuri, wanda ya janyo
rabuwar su domin shekarun ta goma sha hudu ta yi manemi daga garin Sokoto, mai suna, Atiku, abokin
sa ya zo gani a garin Bebeji suka hadu kuma cikin dan lokaci suka aminta da juna. Iyaye kuma suka
amince da nagartar sa bayan dogon bincike suka aura wa Adda Kilishi Atiku Dogon Daji, ya tafi da ita
Sokoto garin iyayen sa. A lokacin yana aiki da ma’aikatar sadarwa ta kasa, wato Ministry of
Communication and Digital Economy .

Alhaji Atiku Dogondaji ya dade yana aiki a can, ko da suka maida shi jihar Rivers, wato Port-Hearcourt bai
tafi da iyalin sa ba, a Sokoto ya bar su, Adda ta ba ni labari cewa duk karshen shekara yana daukar hutu
ya zauna cikin iyalin sa kuma duk bayan watanni ukku yake zuwa Sokoto.

Tun ina goye Adda Kilishi ke hidima da ni, sutura da kayan wasa kamar ba a kauye nake rayuwa ba.
Akai-akai Adda ke zuwa daga Sokoto ta yi wa iyayena goma ta arziki, ni kuma ta yi min sayayyar suttura
da kayan wasa da ta saba kawo min duk zuwan ta Bebeji. Adda ba ta dogara da mijin ta kadai ba, tunda
ya kasance ba ta yi zurfi a karatun zamani ba, tana aji uku na karamar sakandire aka cire ta aka yi mata
aure, kuma mijin ba ya bukatar ta ci gaba, ya ce nashi karatun ya ishe su, sai ya ba ta jari ta ke kasuwanci.
Sana’ar Adda atamfofi ne da lesissika da mayafai na mata, sana’ar ta karbe ta don har shaguna gare ta
manya guda biyu a kasuwar (Dan Jabalu). Tana yo odar kayanta ne daga waje ta zuba a shagunan ta,
kuma Allah ya ba ta nasibi sosai a wannan harkar.
Iyakar kulawa da tarbiyya muna samunta ni da kanwata Arifah a wajen iyayen mu, da yayar mahaifinmu
Adda Kilishi. Kuma haihuwar Arifah bai ture gwamnati na daga wajen Adda ba, gatan da nake samu a
wurin ta Arifah ba ta samu. Allah bai yi Arifah mai tsawon rai ba ce, shekarun ta biyar ta kamu da cutar
kyanda (bakon-dauro) wadda ta yi ajalin ta.
Duk shaquwar da ke tsakani na da Adda ba abin da na tsana irin zuwa wurin ta a Sokoto, ba don komai ba
sai don halin ‘ya’yan ta. Babbar wato Nabeelah cin zalina ta ke yi, shi kuma Yaya Maccido (Attahir) mai
bin Nabeelah yana da tsanani akan ilimin boko, daga ni har Muhsin autan Adda wanda shi ne tsara na
cikin ‘ya’yan ta don shekaru biyu kawai ya bani bakar wuya muke sha a hannun su.
Don haka ne daga baya da na yi wayau idan Adda ta zo ta kuma fara shirin tafiya, to fa za a neme ni ne a
rasa har sai ta bar gari. Tun ba ta gane ba har ta gane gudun zuwa gidan ta nake. Rannan ta zaunar da ni
don jin dalili cikin lallashi, inda na sadda kai na gaya mata gaskiya, karatun Yaya Maccido ne bana so.
Maccido ga bulala in ya koyar ba ka iya ba. Ni kuma a rayuwa ta Allah ya halicce ni da kin karatun boko.
Ranar da na gaya wa Adda dalili na na kin gidan ta ta dade tana jan hankali na cewa; Maccido so yake mu
zamo masu hazaqar karatu irin nasa, mu dinga ciyo kyaututtuka na ban mamaki a makaranta irin
wadanda kullum yake ciyowa, mu zamo zakaran gwajin dafi cikin tsararrakin mu kamar yadda yake. Ba da
nufin takura mana yake yi ba.

Sunan Sultan Of Sokoto Mohammad Attahiru aka sa wa Yaya Maccido, dalilin da ya sa iyayen ke kiransa
Maccido ke nan. Mohammad Attahiru shi ne Sarkin Musulmi na goma sha uku a Seat of Caliphate. Iyayen
sa na fatan ya dauko halayen sa da soyayyar sa da gudummuwar sa ga addinin musulunci, shi ya sa suka
sanya masa sunan sa.
Kamar yadda na fada a baya, daga Adda har mahaifina Malam Adamu Allah bai ba su yawan haihuwa ba.
Daga ni sai Arifah Allah ya nufe su da haifa wadda ita kuma ba ta yi tsawon rai ba. Ita kuma Adda daga
Nabeelah da muke kira Aunty Nabeelah sai Yaya Maccido, bayan haihuwar Maccido sai da Adda ta

kwashe shekaru goma sha biyu ba ta sake haihuwa ba, har ana tunanin haihuwar shi ke nan ta kare, sai
kuma Allah ya kawo, Muhsin.
Duk cikin ‘ya’yan Adda Muhsin shi ne mai kirki, shi ne bai yo halinsu na mugunta, cin zali da takura wa
dan Adam ba. Watakila wannan ne dalilin da ya sa na fi shakuwa da shi, watakila kuma don shi ne kusan
sa’a na (tsara) na shi ya sa na fi son sa da kaunar sa.
Na taso a gaban iyaye na cikin samun ingantacciyar tarbiyyar addinin islama, da kuma samun cikakken
gata wanda bai sa ni na kauce wa tarbiyya ba.
Allah da ya halicce ni shi ya sanya min kin karatun boko, wahala yake ba ni, bana fahimtar sa ko kadan,
kullum ni ce ta-kashin aji, ni ce mai daukar ta karshe a duk jarrabawar da ake yi mana tunda na fara
firamare har na gama ta.
Kuma da ya kasance iyaye na ma ba masu ilmin zamanin ba ne sai hakan bai taba damun su ba, domin
kuwa ina bada himma a karatun islamiyya, itama ban iya hada baki ba saidai hadda, shekaru na goma sha
biyu na haddace rabin Alkur’ani. Sauran littattafan addini kuwa idan ina ja ina tarjama a haddace
tsammani za ka yi diyar wani shehin malami ce ni.
Idan ana maganar kyau na san ba za a lissafa da ni ba. Kyawu na kadaran-kadahan irin na mahaifiya ta.
Babu muni, sannan babu kyau na bada labari. Baka ce ni, doguwa, mai dan kauri, wanda kalar fata ta ya
fiddo zahirin kasancewa ta cikakkiyar bahaushiyar Kano jikar Barbushe da Tsimbirbira.
Gashin kaina yana da cika da karfi, amma babu tsayi, idan aka yarfa min kitso yana da ban sha’awa,
domin ba ka ganin kyawun gashina sai idan an yi min sabon kitso kanana. Babu wanda nake bari ya taba
min kai sai Nene (sunan da nake kiran mahaifiya ta Zainabu) kuma sunan ya bi bakin kowa, duk shiyyar
mu da Nene ake kiranta.
Lokaci-lokaci mu kan je Babura inda dangin mahaifiya ta suke, iyayen ta sun dade da rasuwa, amma
akwai birbishin dangi na iyayen nata da iyalinsu a raye.

Na taso cike da dokin, ranar zuwan Adda Kilishi. Ta kasance uwa mai yawan kyautata mini ta kowanne
fanni, ta kasance ‘yar uwa ta gari ga dan uwan ta, wato mahaifi na. Ta zame masa uwa da uban da ba su
tashi da su ba. Zumuncin ta abin a bada labari ne, domin ba ta bambanta ni da ‘ya’yan da ta haifa, tun ina
mitsitsiya ta na fahimci wannan bangaren na Yayar mahaifi na Kilishi.
An ce akwai wadanda zumuncin su shi zai kai su aljannah, bana tantama ciki har da Adda da mahaifina
malam Adam, don dai ni tun da nake a duniya ban taba ganin ‘yan uwa masu son juna fisabilillahi kamar
su ba. Duk da mahaifi na ba mai karfi ba ne wannan ba ya hana duk sallar idi ya dinka wa Maccido kayan
sallah irin wadanda ya dinka wa kansa. Haka nan yana yi masa kiwon tumaki garke guda a nan kangon
bayan gidan mu, wadanda ya fara ne da ba shi tunkiya mai ciki, ta yi ta hayayyafa, Maccidon ya ce Baba
ya kiwata masa ita, don gidan su ba wajen kiwo.

Baba ya soma yi wa Yaya Maccido wannan kiwon ne tun yana da shekaru goma a duniya, Allah kuma ya
albarkace su, domin a yanzu sun zama garken awaki na raguna da tunkiyoyi da ‘ya’yan su. Har zuwa yau
Baba bai taba gajiya da kiwon da yake yi wa Yaya Maccido ba. Baba ne kurum yake kiransa da sunansa na
asali, wato Attahir, amma a bakin ‘yan gidan su da iyayen sa da abokan sa "Maccido" ne a bakin kowa.
Ina aji daya a babbar sakandire wadda sau biyu ana min maimacin aji (repeating) kafin in samu in shiga
siniya sakandire, a hakan dai nake kukkulla makarantar maganin zama a gida, kada a ce bana karatu. Ni
tunda nake ban taba daukar littafin makarantar boko da nufin in duba abin da aka koya min in na dawo
gida ba, sannan bana yin aikin gida (home work ko assignment) yadda aka ba ni shi haka ake karbar
littafin ba tare da na rubuta ko ‘alif’ ba.
Duka na sha shi wajen malamai har ya yi yawan da bana jin shi a jikina, sai a yi min bulala bakwai a tafin
hannuna ban yi ko hawaye ba. Sau ba adadi hukumar makarantar mu ta sha kiran mahaifi na a kan
matsala ta, abin da yake cewa kullum shi ne,
“Watakila Ma’u ba ta da abinci a boko, tunda ta shiga firamare ma har ta gama haka ta ke, ku yi min
alfarma ta ci gaba da zuwa makaranta tana shiga aji, in ba ta koyi karatu ba, ta koyi rayuwa da cudanya da
jama’a”.

Ina mamakin saukin hali irin na mahaifi na. Idan na duba sai in ga ita ma Adda Kilishi ai haka ta ke. Saukin
kansu yayi yawa akan 'ya'yan su. A fili suke nuna mana soyayyar su garemu.
A daidai wannan lokacin ne rannan na taso daga islamiyya, tun daga nesa na ga santaleliyar motar da ta
sanar da ni cewa, Adda ta zo gari, don haka na kara da gudu-gudu, sauri-sauri na isa gida. Amma abin
mamaki direban ta Malam Hussaini ne kawai a zauren gidan mu babu walwala ko ta kobo a tare da shi. A
gurguje na gaishe shi na afka tsakar gida ina kiran,
“Oyoyo Adda”.
Sai dai a raina na yi mamakin dalilin da Malam Husaini yau bai yi min kirarin da ya saba yi min ba cikin
raha a duk lokacin da muka hadu, wato; “ASMA’U FARA ‘YAR SHEHU”. Ni kuma na kan amsa masa da
cewa, “Wannan Asma’un baka ce. Babu digon fari ko dis a jikin ta”. A duk lokacin da na fadi hakan,
Malam Hussaini ya yi ta dariya ke nan.
Turus! Na ja na tsaya ganin Nene na zuge katuwar jakar matafiya, Baba ma yana tsaye da tasa dirkekiyar
jakar yana kara gyara kayan ciki. Fuskokin su sun yi min kama da na Malam Hussainin Adda da ke soro.
Wato fuskokin su dauke suke da matukar alhini. Na karasa jiki a sanyaye na ce,
“Nene, ina za ku? Ina kuma Adda?”
Nene ta dago ta dube ni, fuskarta ba yabo ba fallasa, ta ce, “Ba ta zo ba, mu ne za mu je mata. Je ki ajiye
jakar makarantar ki canza kaya ki zo mu tafi, yanzu za mu dauki hanyar Sokoto”.

Tunda muka dauki hanyar Sokoto daga Bebeji babu mai magana a cikin motar, Nene da Baba jan carbi
kawai suke yi, yayin da Malam Hussaini ke tuki cikin kwarewa da kula da ladubban tuki. Ni dai sai
sake-sake nake, ina so in tambayi abin da ya faru, babu fuska, don ko a junansu ba sa hira. Wani
mummunan tunani ya fado min a rai, ko dai wani abu ne ya samu Adda? Abin da zai taso Nene da Baba a
wannan yammacin zuwa Sokoto, hakika ba karamin abu ba ne.




*KYAUTA NE GA TAKORI'S LOUNGE*
*SUMAYYAH ABDULKADIR* *(TAKORI)*



TUKUICI NE ga makaranta littatafai na.
```Yiwa Kai Hisabi```
((2)). A wancan lokacin Najeriya lafiya lau, babu matsalar ‘yan fashi, babu ta ‘yan garkuwa da mutane,
babu ire-iren wadannan abubuwan. Ina miki bayanin abin da ya faru ne ga ni Asma’u shekaru ashirin da
biyu a baya, wani lokaci ne da kasarmu ke zaune lafiya cikin lumana da kwanciyar hankali.
Babu irin tunanin da ban yi ba, amma na kasa rike kwakkwara guda daya in ce shi ya faru, wanda ya janyo
mana tafiyar dare haka zuwa Sokkoto birnin Shehu. Tsananin addu’ar da Baba da Nene ke yi, shi ya kawo
mu Sokkoto lafiya.
Addar da nake tunanin wani mummunan abu ya same ta da ita na fara yin tozali a makeken falon ta, sai
dai da ganin ta ta ci kuka har ta gode Allah, ta rame ta yi fiyat cikin kwana daya. Sai da muka kwana muka
wuni na fahimci abin da ya faru, Baban su Muhsin ne ya yi hatsarin jirgin sama daga Port-heartcourt zuwa
Sokoto, ko gawarsa ba su samu ba, an tabbatar yana cikin fasinjojin, jirgin nasu ya fado ne ya kone
kurmus.
Ya tafi ya barta da marayu guda uku, da tarin dukiyar da ba su san ya ya za su yi da ita ba. Maccido karatu
yake a kasar 'Cuba' (country in the Carribean) yayin da Nabeelah ta ke Beirut din Lebanon tana nata
karatun, Muhsin ne kawai a gaban ta.

Da wannan tashin hankalin su Adda suka wayi gari. Lokacin da ta ga Baba na sai ta daura kai a kafafun sa
ta yi ta rasgar kuka. Kuka ta ke mai tsuma zuciya, mai dauke da amon girman maraicin da ya same ta.
Alhaji Atiku Dogondaji, miji ne wanda har a aljannah ta ke fatan Allah ya tashe su tare. Ya rike Adda da
daraja da mutunci, bai taba la’akari da zurfin ilminsa ya wulakantata ba, ko ya ce zai auro wadda ta yi
boko ta fi ta wayewa ba. Ya yi musu komai a rayuwa ita da ‘ya’yan ta, don haka rashin sa tamkar faduwar
wani babban gini ne wanda yake katanga abar jingina a gare ta da ‘ya’yan ta.
An yanke shawarar ba za a gaya wa Maccido rasuwar mahaifinsa ba, saboda a daidai lokacin jarrabawa
yake yi. Amma ranar kwana biyar da afkuwar al’amarin Nabeelah ta iso. Suma ta rika yi ana yayyafa mata
ruwa tana farfadowa. Ko ba ka yi wa wannan family din farin sani ba, dole in ka ga halin da suka kasance
a wannan loakcin ka tausaya musu.
Mai rangwamen damuwa a cikin gidan, Muhsin ne. Ya yi damuwar, amma ta kwana biyu ya ware ya shiga
harkokin sa. Duk inda ya yi muna tare, kamar tip da taya. Tun sati daya da rasuwar su Nene suka so
komawar mu gida Bebeji, amma Adda ta hana, sai da muka kara sati. Da za mu koma kuma ta ce, ni a nan
za'a bar ni. Gidan ya yi mata fadi da yawa, don washegarin ranar Nabeelah ma za ta koma makaranta.
Ai kuwa ba kunya na sa kuka kan ba zan zauna ba. Aka yi a ka yi na ce kafata kafar Nene. Da haushi ya ishi
Nene, sai ta tsinka min mari. Na kuwa bare baki ina kara rusa kuka. Adda ta jawo ni jikin ta tana lallashi
na a lokaci guda kuma tana yi wa Nene fadan saurin hannun ta. Mene ne abin duka? Ta ce, “Ma’u ba za ki
zauna da ni ba?”
Cikin kuka na ce,
“Adda, to yaushe za ki maida ni wajen Nene?”
Tana goge min hawaye ta ce, “Insha Allahu idan Nabeelah da Maccido sun gama karatu sun dawo gida
zan maida ke wajen Nenen ki Asma’u. Kadaicin ya min yawa, ina bukatar mai debe min kewa, ba kya
tausayi na ne Ma'u?”
Duk sai jiki na ya yi sanyi, duk da nake yarinya karama na san Adda abin tausayi ce a wannan lokacin,
amma na fi so in yi zamana gaban iyaye na, duk da na san zan samu gata da jin dadi ne fiye da wanda
nake samu a gidan mu. Ni wannan ba ya gabana, na fi so kullum na bude ido in gan ni gaban Nene na da
Baba.
A daren ranar a dakin da Nene ta sauka na kwana, mun raba dare tana min fada, ta bari ta koma nasiha.
Ta ce, Adda ba ta cancanci abin da na yi mata dazu ba, kauna ce da soyayya ta sa ta ce in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login