Showing 96001 words to 99000 words out of 121454 words

Chapter 33 - MUWADDAT Complete book Hausa Novels by Aysha Bagudu .pdf

03 Oct 2025

6507

riko tafin hannunta,
take taji wani irin zafi ya ratsa tafin hannuta cikin tsarkewar murya tace " sunnu baby duk gajiyar
hanyar ce haka,ko daman baki da lafiya ne ?
Da kyar ta iya bud'e baki cikin tsantsar jin kunyar ummi ta tsinci kanta da cewa "eh" yayinda
gabad'aya ta kasa sakin jikinta daita tana jin kmr zata fahimci abinda ya faru ne a tsakaninta da

bunayya .

ummi tayi shiru tana nazarinta na wani lokaci sannan tace "to shikenan ki tashi kiyi wanka kiyi
sallah dan nasan yanzu haka ko sallar azahar bakiyi ba ko?
Ta d'aga mata kai ala'mun Eh .

gabad'aya jaruntar da tayi saura atattare daita, ta tattaro ta sanyawa gangar ajikinta da niyyar
tashi da kuzari ,sai dai me tana gama ziro kafafunta daga Kan gadon ta ji
bazata iya d'aga kafafunta ba ,saboda wani irin tsami da ciwo da cinyoyinta suka d'auka,
,hatta gabobin jikinta jin su take tamkar an sassare mata su, take jikinta ya d'auki rawa .....

a matukar tsorace ummi ta matso gareta sosai tana binta da wani irin kallo, bakinta na rawa
tace "ke lafiyarki kuwa, me ya samu kafafunki suke rawa haka ?

rud'ewa muwaddat tayi har tsayuwa ta nemi gagareta ta soma yin kasa tana lumshe
idanuwanta , ummi tayi saurin tarota zuwa jikinta tana furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi
rajiun "me zan gani haka ni mukarama?
"hubbey ...hubbey !! ta shiga kiran abi da iyakacin karfinta, kmr an jeho shi ,ya banko kofar da
karfi yashigo a matukar firgice yana tambayarta "lafiya?
"ina fa lafiya ta yani gani hubbey ,ta fad'a tana sake duban muwaddat dake k'ok'arin tsaitsaita
tsayuwarta ta karfin tsiya jikinta na rawa ..
abi yace "me zan gani?

ummi ta kamo hannun muwaddat dake lummmmmm da idanuwanta tace "ke ki yi tafiya yaga
yadda kika dawo ?
numfashi muwaddat ta janyo ahankali ta fesar tana lumshe idanu, kana bud'esu da kyar
sannan ta soma ta kawa sannu ahankali da niyyar shiga bayi ..har ta gama shigewa bayi
idanuwansu na kanta .

da sauri ummi ta juya ta dubi gefen da abi ke tsaye ,tana jujjuya masa hannu tare da
marairaicewa "hubbey kaga yadda tafiyarta tayi ba?
"na gani menene ya samu tafiyartata?

jikin ummi na wani irin rawa ta janyo hannu abi sukayi hanyar fita daga d'akin ,kai tsaye d'akinsa
ta nufa hankalinta a matukar tashe, idanunta sun cicciko da ruwan hawaye "wai hubbey meye
haka ne?
abi ya fad'a shima hankalinsa a tashe.
"duk kin bi kin wani tayar da hankalinki ,ni fa gabad'aya ban fahimci komai ba.

ummi tace "bazaka fahimta ba tana kuka "wai meye hk ne hubbey nifa banason irin haka ,"ki
fito ki fahimtar dani, idan wani abu ne ya sameta ,bawai ki dinga min irin haka ba,
ya fad'i yana kamota suka zauna abakin gado "ki fad'a min abinda kika gani ...ko na samu
natsuwar zuciya ? muryarta na rawa tace "wallahi gani nayi kmr an ta'ba min yarinya ........

ta k'arasa mgn hawaye na gangarowa bisa kuncinta ...

"what..? "when?
"ban gane an ta'ba miki yarinya ba ?
"wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba an ta'ba min yarinya.. ....
abi yayi shiru yana kallon yadda take zubar da hawaye had'e da nazarinta, kana daga baya
yace " haba mukarama ,haba mukarama wannan wace irin magana ce haka ?
"a tunanina irin tarbiyar da mukabawa baby ko kuda ne zai zama mutun ajikinta bazata ta'ba
amincewa dashi ba bare ta bawa wani kanta, sannan ki dinga kyautata zatonki..
" hakika manzo Allah tsira da amincin Allah shi tabbata agareshi yace" *iyyakun wazzana,
"kashedinku da zato, "fa inna zanna akzabul hadis," domin zato shine mafi karyar labari*
dan haka ki tsarkake zuciyarki ,ki sanya ikilasi acikinta ,sannan ki cire wannan zaton aranki,
babu mamaki ko gajiyar hanya ce ,ta maidaita haka, tunda ki rigada kinsa yadda baby take , a
duk sanda tayi tafiyar hanya irin hk ,a galabaice zaki ganta, sosai abi yashiga kwantar mata da
hankali, har dai taji ta d'an samu natsuwar zuciya, tare da k'ok'arin kawar da abinda taji.
bangaren muwaddat kuwa cike zuciyarta take da matsanancin fargaba abayi, ban da tsinkewar
zuciya babu abinda take ji ajikinta , jikin kofar bayin ta dawo ta jingina jikinta tana leken fuskar
ummi, har sanda suka bar d'akin , ta sauke naunauyen ajiyar zuciya, jikinta na sake d'aukar
rawa "ya Allah ka rufa min asiri...kada kasa ummi ta fahimci wani abu atare dani.. ..ya Allah ka
taimakeni, ka taimakeni kada ta gano komai .....
cikin sanyi jiki ta had'a ruwan zafi tashiga gasa jikinta kmr yadda matar nan tayi mata d'azu da
safe ,ta dad'e cikin ruwan zafin har sai da taji tsamin da gabobinta jikinta sukayi sun ragu
sannan tayi brush da wanka ,had'e da d'auro alwala ta fito ta iske Muhammad auwal zaune a
gefen gadon ya kwanta flat ,kafafuwansa duka a kasan tayis yana girgizasu , sannan yayi
sama da rigar dake sanye ajikinsa har ana iya hango farar singlet din dake cikin rigar .

Kamar ta juya ta koma cikin bayin taji, sai kuma ta k'araso saboda tasan kota juya ta koma
ciki ,hakan ba zai sa ya fita daga cikin d'akin ba, matukar ba shine yaga dama ba .
kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta daga garesa tana jin wani irin tuttukin bakinciki mara
misaltuwa ,ta k'arasa ta tsaya gaban mirrow tana goge jikinta da towel tayi tamkar batasan da
wani halitta a kwance agurin ba .
bata shafa komai ajikinta ba, illa kwalbar turaren data d'auka ta fesa a gabadaya ilahirin jikinta
,sannan ta nufi wardrobe dinta ta d'auko doguwar riga material wacce ta sha tsone work a iya
ratsin brest dinta ta sanya .

Ta d'auki sallaya ta shimfid'a ta fuskanci gabas ta tada sallar azahar ,bayan ta idar , ta sake
mikewa domin gabatar da la'asar d'an lokacinta tayi , duk yana nan kwance shima da ala'mun
bashi da niyyar ce mata komai, cikin haka wayarsa ta d'auki k'ara ya bud'e idanunsa dake
lumshe ,kana ya zaro wayar daga aljihun wandonsa ya d'auka yasoma amsa waya "shikenan
okay i will try ..." shine kawai abinda kunnuwanta suka jiyo mata .

Bayan ta idar da sallah ,ta waigo ahankali inda yake kwance, nan taga wayam babu shi babu

alamunsa, ta dad'e agurin zaune tana neman gafarar ubangijinta bisa abinda ta aikata a daren
jiya tana kuka tana sake maimata , *allahumma anta rabbi laila a illa anta, khalaqatani wa'ana
abduka, ana ala ahduka wa wahduka masta'atu auzubika min sharri ma'hsanahtu, abuhu laka
bi nihmatika alaiya wa abuhu bi zanbi ,faga firli, fa inahu la yagfuruzzuba illa ant*
byn ta gama, mikewa tayi tsaye ahankali ta koma Kan gadonta ta jingina bayanta da pillow
had'e da kallon ceiling d'akin still tana cikin fargaba,shigowar ummi yasa taji gabanta ya sake
bada wani irin sautin bugawa, take yanayinta ya sauya, ta shiga kokuwa da numfashinta
,yayinda zuciyarta ta dinga dokawa tana tsalle tmkr zata fasa kirjinta tayo waje , ummi ta k'araso
ta zauna kusa daita tana ta'ba gefen wuyanta , zuwa lokacin ba taji zafi kmr d'azu ba, dan hk ta
sauke naunauyen ajiyar kana ta kira sunanta "muwaddat hakika d'azu naji matsananci tsoro
,har ma da faduwar gaba, nayi zato akanki wanda har yanzu hkn yaki barin zuciyata, sai dai
wani bangare na zuciyata na karyata min hakan, sbd nasa ba zaki ta'ba aikata hkn gareni ba,
duba ga yanayin tarbiyarki, "amman na rasa me yasa zuciyata tayi zargin wani abu attare
dake, wanda ban ta'ba jin hkn ba sai yau....
" ko dan yanayin tafiyarki dana ga ta canza ne ban sani ba ...

da sauri ta had'eye abinda taji ya tsaya mata a makoshinta a tun shigowar ummi sannan ta
yunkura ta sauko daga kan gadon tana takawa ahankali tace " ummi ki kwantar da hankalinki
babu abinda ya samu tafiyata fa , kawai dai haka nima naji kafafuna sun rike d'azu , amman nafi
tunanin zaman mota ne kalleni yanzu kigani ,ummi ki cire tunanin komai aranki domin bazan iya
aikata hkn gareki ba ta k'arasa maganar cikin sheshekar kuka... .. ..

"numfashi ummi ta sauke tace "to shikenan bance min ki min kuka ba muje ki ci abinci , koma
dai bari nasa baba mairo ta kawo miki nan ki ci Allah ya hutar da gajiya ,amman wallahi sai
yanzu na d'an samu natsuwar zuciya, ta mike ta fice daga cikin d'akin zuciyarta na dokawa ,
ita kuma muwaddah ta sauke wata siririyar ajiyar zuciya tana godewa Allah daya rufa mata asiri.

kan gado ta fad'a tana mai runtse idanunta saboda azabar zafi , dauriya kawai tayi ta tsaya
bisa kafafunta agaban ummi dan kawai ta kawar da zargin ummi akanta, dan tasan muddin bata
daidaita yanayinta ba, ba k'aramin aikin ummi bane tayi asibiti daita domin duba lafiyarta ,
kafafunta ta mike ahankali kana ta janyo wayarta domin kiran 'yan gidansu, dan tunda ta shigo
gidan batayi tunanin nemansu ba ,sai yanzu da taji abinda ummi tace , bayan mumy ta d'auki
wayar suka gaisa tayi mata ya gajiyar hanya had'e da cewa "ai tun d'azu nake neman layinki
ban samu ba" muwaddat ta numfasa kana tace "wallahi mumy wayar ce a kashe tun bayan da muka dawo .
bayan sun gama gaisawa da mumy ,ta mikawa kanneta waya ,haka suka yita gaisawa d'aya
bayan d'aya , eiman ce ta amshi wayar daga karshe tace "big sister ......,ina nan nayi tabaje,
babu matsi balle takura ,sai dai duk da haka nayi kewarki sosai ,amman dan Allah next time
idan zaki sake zuwa mana hutu ,dan girman Allah karku zo tare da yaya bunayya ,wallahi ya
cika matsi da takura mutane, ga shegen miskilancin tsiya ,har ma gara naki miskilanci akan......
"ke dan Allah malama ban son shirme.... ta katseta ta hanyar fad'ar hk, ni da kike Allah Allah mu
rabu, shine yanxu dan gulma da munafurci zaki ce wai kinyi kewata "kai aunty muwaddat kefa

matsalata dake kenan har yanzu bakije Ghana ba,da wasa fa nake miki "ai kuwa bazan ta'ba
zuwa ba ,kinga sai anjima ta katse kiran ....

tun bayan da muwaddat ta gama waya da yan gidansu ta tsakuri abincin da baba mairo ta kawo
mata sama sama ,tayi kwanciyarta a d'aki har dare taki fitowa sai nan mairo mai aiki ta sake
biyota da abinci .

bangaren bunayya kuwa bai sake shigowa d'akin ba, dan haka ta samu damar sakewa sosai
,tana tunanin abinda ya dace da rayuwarta ,domin nemawar kanta mafuta dangane da
halakarta da bunayya ,dan kasancewarsu tare guri daya ,babu abinda zai sake haifarwa facce
dagula mata lisafi,tare da d'aga mata hankali ,haka dai tayita juyi akan gadonta tana tunani ,
har lokacin hoton abinda ya faru tsakaninsu yaki 'bace wa acikin kwalkwaluwarta ,sai da lokacin
sallah magrib tayi sannan ta yunkura ta Mike ta sake shiga bayi ..

************

washegari tana zaune a inda ta idar da sallar azahar yashigo ,ko ba'a fad'a mata ba tasan
shine yashigo d'akin, juyowa tayi a sukwane suka yi 4 eyes dashi, tsaye sanye ciki wasu
had'd'un bakaken kanana kaya ,riga t shirt da wandon baki iya gwiwa, idanu suka tsurawa
junansu tamkar ranar suka fara ganin juna , take zuciyoyinsu ya sake dilmiya cikin tafkin
kaunar juna , hk nan ta tsinci kanta cikin sabon tafkin kaunarsa shima kusan yana jin irin
abinda take ji ajikinta ,sosai tayi nisa cikin kallonsa, laulausar tafin hannunsa da taji akan
kafad'arta ne yasa ya dawo daita daga duniyar data Lula, kusa daita ya matso sosai yana
kallon fuskarta, lumshe idanunta tayi ahankali saboda bazata iya jurar kallonsa ba ,kusan minti
goma yana durkushe a gabanta yana kallon fuskarta, cike da matsanancin so ya kira sunanta
cikin sanyayiyar muryarsa mai shiga jiki " "muwaddat dina ...
Tana jinsa taki motsawa ya kamo hannuta ya Mikar daita tsaye ,ba tayi masa mutsu ba ta Mike
ya soma tafiya daita har suka k'araso bakin gado ya zaunar daita, d'an k'aramin ajiyar zuciya ta
sauke tana bud'e shanyayyun idanunta ahankali while zuciyarta na dokawa ,idanunta ta
lumshe tare da bud'e su fess akan fuskarsa , suka sake had'a ido ,take suka shiga wani yanayi
Wanda hkn yasa suka tsurawa kwayar idanunsu ido suna kallon juna, gabad'aya ya gama
karantartar halin da take ciki, har lokacin tana cikin tsananin tsoro da fargaba ne.
Haka nan shima ya tsinci kanshi cikin damuwa sosai saboda yanayin da take ciki "muwaddat
dina.....ya sake kiran sunanta
ta sake kallonsa tana kawar da idanunta batare data amsa ba ,ya kamo fuskarta da
hannuwansa duka ya had'e fuskokinsu guri daya tare da sanya kwayar idanunsa cikin nata
yana kallonta, har bai son d'auke idanunsa cikin nata "am really sorry my muwaddat i really
sorry for what I did .... bazan gaji da baki hakuri akan abinda ya faru a tsakaninmu ba .
ta sake kawar da kanta gefe idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye "kiyi hkr ki daina kukan
nan, sannan kice kin hakura plz shine kawai kwanciyar hankalina....

muryarta na rawa tace "ba..babu komai ya wuce , had'e da sake kawar da fuskarta ta sunkuyar

da kanta kasa, "to me ye kuma abun sunkuyar da kai bayan kince babu komai ,dan Allah ki
saki jikinki kinji aunty nah.......
ta d'ago da sauri tana dubansa cike da matsanancin mamaki ,sbd wannan shine karo na farko
daya furta hk gareta ,wani irin kallon yake mata kai tsaye batare daya sake ce mata komai ba
,babu zato taji ya janyota tare da sanyata ajikinsa ya rungumeta tsam yana furzar da numfashi,
yana jin kmr su tabbata a haka ,ahankali ta soma k'okarin fixge jikinta ,amman ta kasa sbd irin
kalar rungumar da yayi mata ,babu yadda zatayi ta raba jikinta dana shi, tsawon minti goma
suna haka suna sauke numfashi ,tana cigaba da mutsu mutsun raba jikinta dana shi,saboda
yanzu wani irin mahaukacin tsoronsa take ji ,dan ya shata mamakinsa da bazata ta'ba
mancewa ba har karshen rayuwarta .....
cigaba da mutsu mutsu tayi wanda hkn yasa ya barta ba dan yaso ba .

saukowa yayi gabadaya daga saman gadon ya tsaya bisa kafafunsa "ni zan koma d'akina ki
saki jikinki plz ,babu abinda zai faru sannan rashin kusantar inda ummi take zai sa tashiga
damuwa sosai, ko yanxu da zan shigo naji suna maganar da abi ,wai tunda muka dawo ta rasa
gane kanki ko parlour'n baki sake fitowa ba ,ki taimakeni ki saki ranki da zuciyarki plz karki bari
ta fahimci komai ya fad'i hk yana had'e hannuwansa guri daya, shiru tayi tare da kafe shi da
idanunta..

gbdy ta rasa ma abinda zatace masa ..
"dan Allah nace "muyarta sanyaye tace "naji amman kai ma zan roki wata alfarma agurinka, ka
daina shigo min d'aki kai tsaye ,ko nuna ka damu dani akan idanunsu ,kai bama hk ba, ni.. ni.
na yanke duk wata halakata da kai har karshen rayuwata , ka tsaya matsayinka na tsaya nawa,
banason kusancina da kai ......
"shine kawai alfamar ?
Ta d'aga masa kai "shikenan angama yana gama fad'ar haka ya juya yasoma k'ok'arin barin
d'akin tana kallonsa ya fice zucuyarta na wani irin harbawa ...

***********
bayan sati biyu da faruwar hk atsakaninsu, muwaddah ta warke sumul ta dawo normal saboda
idanun ummi dake kanta amman sam bata cikin kuzari da walwalarta,tare da farinciki tmkr
yadda take ada , tana dai fitowa ayi hirar barkwanci daita da sauransu kmr dai yadda suka saba
dan duk kar ummi ta fahimci tana tare da damuwa, cikin satin ta koma makaranta.
shi kuwa bunayya ya d'auke mata wuta kmr yadda ta bukata, ya daina shiga tsabgata da
shishige mata, ya daina nuna kulawarsa gareta tsakaninsa daita ido ne ,wannan sharewar da
ummi ta fahimci suna yiwa juna yayiwa mata , sannan hankalinta ya kwanta tare da d'aukar ko
ya watsar da kudirinsa akanta ne akan muwaddah ,bunayya kuwa hakurinsa ya gaza yasoma
bibiyar d'akinta cikin dare ,kullun sai sun sha dambe bala'i dashi akan sai ya kusanceta, ko
kuma ta fito ta sanarwa iyayensu, cewar itama tana son shi, ta nuna musu tana bukatashi ,bashi
kad'ai yake bukatarta ba.

*********

zaune take a gefen gado ta rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafar tunaninta, abu
daya tasani har lokacin tana jinsa ajikinta, musamman yanzu datake sake hango tsananin
soyayyarta acikin kwayar idanunsa,sai dai duk wannan bai sa ta amincewa zuciyarta ba, zata
rusa soyayyar zuwa kiyaya tunda iyayen goyonta basu bukatar wata halaka atsakaninsu,, ta
koma ta kwanta lamo tana sauke numfashi sama sama, har bacci barowa yasoma fixgarta.

karfe shad'aya daidai ya shigo d'akin ya tarar daita kwance sauran kad'an ta zamo kasa, ya
k'arasa da sauri ya gyarata ,yana gyara gashinta daya baje bisa fuskarta, bakinsa ya kai ya
tsotse lip's dinta yana shafo kirjinta, ta bud'e idanunta ahankali tana yatsina fuska dan baccin
bai yi nisa ba, bata ma san lokacin data d'auketa batare da ta kulle d'akin ba, yace "meye abun
wani yatsina fuska kmr kinga wani abun kazanta?
lumshe ido tayi tace "bunayya i don't like all this nonsense...girgiza mata kai yayi "you must like
it , as far as bazaki fito da tarin soyayyar da kike min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login