Showing 66001 words to 69000 words out of 121454 words
Chapter 23 - MUWADDAT Complete book Hausa Novels by Aysha Bagudu .pdf
karfin halin cewa karka yarda da zanceta makaryaciya ce da sauri ta kallesa cike
da matsanancin mamakin tare da tsaresa da fararen idanunta "yaushe wannan ya fara
atsakaninsu da har zaice mata makaryaciya? kalmar datafi tsana kenan a rayuwarta sai gashi a
karon banza a kirata dashi, hisham yayi saurin cewar karyar me tayi maka ?
"Ranar da mukaje gidanka muna dawowa gida sai naji tana bada labarin karya wai taga gidan
sarkin garin nan taga gidan gwana kai har gidan zoo tace munje ....
sukayi Dariya hisham yace "ina laifi data kareka.
"ta dai kare kanta dai nasan tayi haka ne Dan kar gaba a sake tursasata fita..
Muwaddat ta d'an Mike tsaye saboda shirmensu ya fara cika mata kunne dole daman tasan
hisham zai kasance kmr ala'meen gurin zuba tmkr ruwa ,tunda sai hali yazo daya abota kan zo
daya ..hishsm yace "ya kuma kika tashi ana hira ?
"Ni zan koma ciki idan kaje ka mika min gaisuwata gurin madam"
Ala'meen ya fahimci shi take son ta gujewa saboda kallon dayake mata hisham yace "amm
madam fa tabani sako a amsar mata number wayarki a she Ranan nan har kuka rabu baku
amshi number juna ba muwaddat tace "mantawa muka yi saboda hira ta d'auke mana hankali
anan take ta gaya masa number ya shigar dashi cikin wayarsa yace "baki gaya min sauran
lambobinki ba dan naji ance layuka uku gareki cikin yatsina fuska tace "ka manta da sauran
tunda za'a iya samuna Akan wannan layin ,hisham yace "haba muwaddat ina ganin ko mutun
yana rowar number baya yiwa kawarsa ba ,duk yadda yayi muwaddat ta tsare gida ta hanna
sauran number's dinta Wanda tabashi din ma ta karamar wayarta ce datake amsa kira Wanda
abi ya tsiya mata ,wai saboda koda cajin babbar wayar ya kare, Dan bayason yakirata bai
sameta ba ..
shi kuwa hisham Dan dai yajata da hira sai cewa yayi "ke din da nake son ki zama surukata sai
gashi kun kulla kawance da daman ..
Da sauri tace wace irin suruka kuma ?
"Au baki da labarin ina rikon ihsan ko?
Cikin dariya tace "da dai faiza kace me yuwa na Dan tsaya maka tunda ita ihsan ai uban
gidanta na hannun damanka ne ..
Hisham ya jiyo ga ala'meen dayazamanto tamkar sauna a zaune yana kallonta ",kai maigidana
kaji abinda surukata ta fad'a....
Ala'meen yayi murmushi yace ",ai ina ganin ko ita surukar taka a halin yanzu bata isa aure ba
bare aje ga faiza ko ihsan, hisham yace "haba babban yaya karka raina min hankali mana
kawai saboda ba'ason bani kanwa sai kuma ace yaya ma bata isa aure ba ,kina jinsa dai big
sister ya fad'a tare da kallon muwaddat.
Ta d'an kawar da fuskarta gefe "eh to abinda ya fad'a gaskiya ne, sai kaje kayita jiran lokacin
idan kaji zaka iya "kenan idan na fahimci ki kenan kin goya masa baya akan maganar sa na
cewa kema baki isa aure ba ballanata kanwarki?
Ta sake had'e rai "wannan ai maganarku ce ni dai na tafi ka gaida gida tana shirin fita daga
parlour'n sai ga eiman ta biyota da wayoyinta big sister an damemu da kiran wayarki muna
cikin kallo an hanamu jin gari ya Auwal yakira wasu ma duk sun kira ni dai nace musu kina
d'akin yaya ..........
Cikin matsanancin jin haushi muwaddat tace ",to d'an me zaki biyoni da waya d'akin mutane ,ko
ance miki dadewa zanyi ,Muje gani nan saukowa eiman na shirin fita aka sake bugowa ta juyo
da sauri "to ga Auwal nan ya sake kiranki .
Cikin tsawa tace dan rashin da'a kai tsaye kike kiran sunansa bako rusunawa ?
Bata amshi wayar daga hannunta ba har kiran ya sake katsewa "oya maza ki koma da wayar
idan na sauko zan kirasa ..
"Ni gaskiya ki amshi wayar a hannu , ni yanzu meye laifina bayan agabansa bazan kira
sunansa kai tsaye ba "ki ma yi kiga yadda zai yi kaca kaca da namanki Dan kinsan shi baya
d'aukar shirme ..
eiman ta marairace" murya big sister Dan girman Allah ki taimaki rayuwata ki amsa kinga na
rigada na d'auka da farko ,kinsan Halinsa zai d'auka ban kawo miki bane ...
Gabad'aya daga muwaddat din har eiman a tsorace suke ita eiman najin tsoron kar idan yazo
yaci ubanta, Dan bai mantuwa, sannan bai yafiya duk dadewar Abu zai hukuntaka akansa, sai
dai idan yagadamar Kyaleka, ita kuma muwaddat rashin sanin abinda zata fad'a masa idan ta
ashi wayar take, cikin haka ya sake kira "kin gani ko big sister ya sake Kira Dan girman Allah ki
rabani da wayar nan .
Ala'meen kasa d'aurewa yayi yace "shi din waye da baza iya amsa wayarsa anan ba ?
"Batare data juyo ba cikin tausashiyar murya kmr zatayi kuka tace "auwal kanina ne fa,
sannan ta amshi wayaoyinta ta bar d'akin cikin 'bacin rai , itama eiman sai lokacin ta saki ranta
,tana sakawar a'lameen murnushin Wanda za'a iya kiransa,Dana mugunta ...
Hisham ya juyo ya dubi ala'meen "ina ganin fa yarinyar nan ta gane kana son yayarsu "kai haba
bana ji wannan shirmammiyar yarinyar zata fahimci wani abu ,ita kanta uwar gayyar batasani
ba .
"Kana son kace min ita makauniya ce shiyasa bata lura da irin mayataccen kallon da kake yi
mata ba ko? Sannan me ka fahimta a yanzu da aka kawo mata wayoyinta ?
"Na fahimci kmr tashiga firgice gabadaya dai ta tsorata "shine abinda na gani gaskiya ka tashi
tsaye kar hasashenka yazamo gaskiya,kar yaron yazo yayi kuli kulin kubura da kai akasa..
hisham ya k'arasa mgnr yana dariya ala'meen yace "Allah ma bazai sa ba InshaAllahu rabona
ce ...
Hisham ya Mike " to Allah yasa, nima bari tafi Dan na fara tunanin madam Dina nasan tana can
tana jirana ala'meen ya hararesa nima dai zanyi madam Dina kodan rashin mutuncin da kake
min babu ikon ayi cikakkiyar hira da kai sai ka tsiri cewa madam na Jira .
"to ai gara ni da matar tawa ma ina fitowa kai fa tunda bakuwar gidanku tazo aka daina ganinka
,ai ina jin duk ranar daka mallaki yarinyar nan ,an daina ganinka gabadaya suka kwashe da
dariya har da tafa hannu sannan suka Mike tare suka sauko zuwa kasa al'amen yayi masa
rakiya ya shiga mota ta tafi shi kuma ya dawo gidan har zai hau samansa sai yaji hayaniyar
kannensa acan bangaren dady , sai ya tsinci kansa da nufar bangaren ba Dan komai ba sai
Dan ya kalli muwaddat yana shiga ciki ya iske gabadaya yaran gidan suna ciki hjy hajara tacel
kardai abokin naka ya tafi tun ba'a kai muku abinci ba yace mumy "ai kinsa halin hisham in da
yana son ci da kansa zai tambaya..
Idanuwa yashiga budewa yaga ta inda zai ganta ,babu ita babu alamarta a parlour'n Dan haka
ya juya ya wuce ya koma samansa hankalinsa a matukar tashe saboda yasan watakilla tana
can tare da Auwal a waya
Ilai kuwa abinda zuciyarsa ta kissima masa ne ke faruwa acikin d'akin muwaddat, domin kuwa
fad'a ne sosai yashiga tsakanin Auwal da muwaddat ta inda yake shiga bata nan yake fita ba
"Dan wulakanci da iskancin banza me ya kaiki d'akinsa ?
Kika bar ni ina kiran wayarki how many hours "wato kin fi damuwa dashi akaina, ke wai ma
meye atsakaninki da shi ,?
"waye shi da bazaki d'auki wayata agabansa ba?
"Ni ina nan an tsareni ganina,gani wawa bansan abinda nakeyi ba ke kuma kina can kina
shirme da katon banza , Dan haka gobe goben ki shirya zan zo na d'aukoki ki dawo gida
zuciyata baza iya d'aukar nauyi nan ba, gara kina kusa dani daman nasan saiko ake son yiwa
rayuwata shiyasa aka tsiro da zuwanki wannan hutun ..
"Kema dayake kinsa mugun nufin dake ranki shiyasa kika yi zamanki, bakya ko tunanin dawowa
maza daman tun da wuri idan ma sonki yake kice masa kina da miji Dan wallahi babu mai auren
ki matukar ina raye ya karasa mgnr yana furzar da iska ..
shiru tayi har yagama balainsa batace masa komai ba ...
Gashi kuma dai suna rike da wayar ,yadda bai yi yunkurin cewa daita komai ba haka zalika
Itama bata ce masa komai ba, illa Kunar zuciyar da take, hakika Auwal yayi bala'in rainata
wannan wulakanci ko iyayen da sukayi silar zuwanta duniya a yanzu basa mata fad'a irin haka
ballanatana shi datake masa kallon kani gareta amman babu Wanda ya janyo wannan tozarcin
kamar ita itace silar faruwar haka ta bashi abinda bai cancaci yagani ba ,banci haka tasan babu
yadda zai dinga yi mata irin wannan matsefar kamar wani ubanta ..
Ganin tayi shiru taki cewa komai ta barshi shi kadai sai balai yake yi yasa yaja dogon tsaki har
sai data yi saurin cire wayar a kunnenta ya fillingin da wayar akan gado batare daya kasheta ba
ya sauko daga Kan gadon ya fito kai tsaye part din ummi ya wuce yana shiga ya isketa zaune
ita kad'ai tana kallon labarai sallama yayi aciki sannan ya haye sama inda d'akin mahaifinsa
yake ,tabi shi da kallo duk yadda akayi ransa a bace yake ",to waye ya bata masa rai ?
Ta tambayi kanta tana runtse ido ,kamar ta Mike ta bi bayansa sai kuma ta fasa tasan da
matsalar data shafeta ce dole zai tsaya gareta Amman tunda ya nufi gurin mahaifinsa a sauka
lafiya ...
A bakin kofar abi ya tsaya yana kwankwasa kofar abi dake cikin d'akin yana duba wasu
mahimman takardun kasuwancinsa yace" waye ?
Muryarsa can cikin makoshi tamkar bai so ta fito tace ".ni ne "abi najin haka yasan kowaye Dan
haka ya bashi umarnin shigowa ya tura kofar d'akin yashigo da sallama aciki ,abi ya d'ago ya
dubesa yana nazarinsa kallo daya yayi masa yasan yana tattare da damuwa kuma duk abinda
ya kawoshi a daidai wannan lokacin mai mahimmanci ne, Dan haka ya tattara takardun dake
zube agabansa gefe ya nuna masa gurin zama "ka zauna fatan dai kana lafiya ?
Muryarsa tamkar Wanda zaiyi kuka Dan ma dai nmj duniya ne, kawai ya waske yace ",abi kana
son nayi yawanci rai a duniya ?
Da sauri abi ya gyara zama yana girgiza masa kai ",kwarai kuwa Auwal meyasa zaka fadi irin
maganar da tasanya gabana faduwa?
"Akan muwaddat ne abi ina sonta kuma da aure, wannan shine karo na karshe da zan furta
hakan gareka ka aura min ita ka daina duba kankantar shekaruna, ni aure nake so a halin
yanzu "abi ya numfasa yana cigabada dubansa yana nazarinsa tabbas yana hango gaskiyar
abinda ya fad'a Amman ta yaya kamar Auwal zaa ace zaa aura masa muwaddat ?
Amman saboda ya kwantar da hankalin yaron yace "shikenan zan duba lamarin sai asan abun
yi "zuwa yaushe kenan zaka nemeni kan mgnr, saboda ina son muce tare da ita ne?
"abi yabi shi da wani kallon mamaki kafin daga baya ya kira sunansa "bunayya kasamu
natsuwa nace zanyi wani abu akai "bunyya ya ciza gefen lips dinsa kad'an yace "abi to kace ta
dawo gida hakan nan nasan kun tura can ne saboda ni ,to wallahi idan bata dawo ba komai zai
iya faruwa dani . ya kamo hannunsa ya d'aura daidai saitin zuciyarsa "abi kaji bugun da zuciyata take ?
"Abi ya runtse ido saboda yaji yadda zuciyarsa ke bugu fastly "shikena zansa ta dawo gobe
InshaAllahu zanyi waya da alhji Muhammud yanzu kaje ka kwanta kasamu natsuwa ..auwal ya
Mike tsaye yana layi tamkar wani mashayi ya nufi hanyar fita..
Mmn sudais ce
2/4/20, 8:39 PM - imusamuhd(professor):
MUWADDAT
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_
~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~
alhamdullahi am back again.
warning!!!
don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for
mature people , if you read it, is for your own risk ......wannan shine.
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
page 17
....da sauri ta tashi zaune sosai tare da gyara zamanta ,basu daina kallonta ba hakan ya
ankarar daita a she fa kanta babu d'ankwali sai lokacin tayi hanzarin d'auka ta d"aura gaskiya
irin gyaran da muwaddat takewa gashinta ba namiji ba hatta mace 'yaruwarta zai iya burgeta
bare nmj .
Hisham ya d'an juyo ya kalli abokinsa ya lura shima ita yake kallo minal ce ta katsesu ta hanyar
yi musu sannu da zuwa sai da kowa ya zauna sannan muwaddat ma tayi musu sannu al'ameen
ya amsa idanunsa akanta yace "yau dai kun sha hira ,tun sanda suka shigo muwaddat bata
sake yin magana ba saboda tsarguwa datayi da irin kallon da al'ameen ke binta dashi haka
minal ta fahimci muwaddat batason yin magana agaban al'ameen da tunda suka shigo ta kasa
sakewa hisham ne ma yake d'an janta da magana amman Sam taki saka bakinta acikin surutun
da suke .
Al'ameen ya Mike da kanshi ya nufi fridge ya bud'e ya d'auko lemo mai sanyi ya zauna yana
sha, sai da ya gama sannan ya sake dubanta "mu tafi ko kar muyi dare ,batayi magana ba sai
kawai mikewa datayi ta lalubi Jakarta ta rataya minal ta dubi al'ameen "gaskiya banso
dawowarku da wuri ba domin hirar da muke bamu gama ba "to ko zama zanyi ku karasa ?
"Kai ma kasan bakuwa bazata iya sakewa a gabanku ba ,gashi daga shigowarku ta d'auke wuta
ko magana bata iya yi ..
Muwaddat dai gaba tayi abunta har gaban mota suka yi musu rakiya minal tayita rokon
muwaddat akan ta dinga zuwar mata hira muwaddat tace "bazan iya miki alkwari ba amman
idan nasamu lokacin da kuma mai kawoni zan dinga zuwa ...
Hisham ya d'an kalli inda Al'ameen yake yana.dariya domin jin abinda muwaddat tace shi kuwa
al'ameen shiru yayi kmr bai ji ba d'an Jan ajinta yasoma bashi haushi ya bud'e mota yashiga ya
juyo ya d'n zubawa muwaddat ido domin yaga inda zata shiga amman sai yaga hisham yana
k'ok'arin bud'e mata gidan gaba shiru yayi bai yi magana ba sai data shiga ta zauna sukayi
sallama dasu minal har ya tadda motar sun fara tafiya sannan yace "na d'auka direban zaki
sake meidani irin na d'azu"haba dai ta yaya zan maida kai diteba"eh mana gashi nan da zamu
zo kin wani kwanta abaya ina janki tayi shiru ,da yaga bazata yi mishi magana ba sai cewa yayi
"halan nayi miki kama da direbanki ne da d'azu ki wani rashi rashi abaya ?
"Ba kayi kama ba, tabashi amsa a agajerce dayake bata fiyye son doguwar magana kamarsa
ba ,sukayi shiru gabad'aya can kuma ya sake janta da wata hirar da alamun muryata yake son
ji, kallonta yayi tare da cewa "amman fa nayi mamakin yadda kuka dade kuna hira da minal
musamman yadda kike ba ma'abociyar son magana ba ,"kasan ita magana zuwa take bawai
ayita zuba kmr ruwa ba yace "ko ?
"Tace kwarai kuwa tun daga nan basu sake magana ba har suka iso wani katafarin mail na sai
da kayan makulashe yayi parking din motarsa acikin harabar wajen sai daya bud"e ya fito kana
ya zagaya ya bud'e mata yace "bismillah fito mu shiga ko, ta d'an yatsina fuska kmr kar ta fito
sai kuma taga hakan bai dace ba ko babu komai d'an'uwanta ne yakamata ta nuna kulawarta.
ta fito tana yatsina fuska saboda kai tsaye gida taso taje ta kira bunayya dan tun safe take
expecting kiransa amman ko miss call dinsa bata gani ba .
Duk yadda taki son jerawa dashi sai daya saita kafad'unsu suka jera suka nufi kofar shiga mail
din suna gota wasu matasa da suke tsaye kusa da kofar shiga mail din ,dayan ya zunguri
sauran da suke tare yana yi musu nuni da muwaddat.
"kai kai kai had'uwa ji wata hadaddiyar zalziyya suka kalleta gabad'aya, dayan yace "gaskiya
da ba dan wancan gayen da suke tare ba, da sai na d'an latsa ko zan yi sa'ar ta sairareni ,daya
daga cikinsu yace "kai tafi can kana ganin yarinya wata muguwar yar hutu amman har kake
zaton zata iya sauraronka ..
"Ai ba'a anan take ba ,su irin wad'an nan yammata da suke furgitamu in akayi sa'a sunfi saukin
kai in Allah ya doraka akansu ,babu wuya sai kaga kun daidaita "kai dan Allah karya ne ba dai
irin wannan kalar ba wannan ko acikin yayan talakawa ta fito bazata saurareka ba bare kana
ganinta kaga masu gidan Rana kaga mace na takun kasaita, ko gwal din dake wuyanta ya isa
ya sayi motarka .
Suka kyalkyale da dariya yayinda duk maganar nan da sukeyi acikin kunnen al'ameen amman
baya zaton muwaddat taji su ,saboda ita tarigashi shiga ciki, da sauri ya k'arasa ya sameta suka
jera tare "ki shiga ciki sosai ki duba abinda kike bukata kai kawai ta gyada masa sannan ta fara
zagayawa tana bada baya, wasu samari suka shiga dubanta suna magana kasa kasa "kai
Anwar dubi yarinyar dake gabanka kaga wata halitta da kyan diri mai d'aukar hankali ,cikin
hanzari wanda aka kira da Anwar ya d'aga kai yana duban muwaddat" kai gsky cikar nan ta
hadu da yawa Allah yayi halitta a wannan guri