Showing 6001 words to 9000 words out of 121454 words

Chapter 3 - MUWADDAT Complete book Hausa Novels by Aysha Bagudu .pdf

03 Oct 2025

6604

akai mutun
wani gari, sai dai hkn bai hanashi jajircewa na ganin kanwarsa tasamu karatun ta kowani
bangare ba.

bayan mahammud ya gama makarantar gaba da primary, ahankali ahankali yake sanarsa ta
kwadago ta hanyar kasuwanci,da farko dai gyaran agogo yake har Allah yasanya masa albarka
ya bunkasa arzikinsa ya zamo wani abu ..
adalilin wannan sana'ar tasa yasa yayi suna ciki da wajen kauyen har ake kiransa da muhamud
mai gyaran agogo, wanda duk inda zaka shiga a fad'in kauyen nemansa, matukar baka sanya
lakaninsa ba ,sai dai ka gama karad'e kauyen babu mai ce maka yasanshi.

bayan wani lokaci sai mahaifiyarsu ta kamu da ciwo ajali ta sha jinya sosai ,suka rasa yadda
zasuyi, gashi ciki da wajen kauyensu babu asibiti sai anjen wani gari mai kuruna dake
makwabta taka da kauyensu ,idan akace za'a kai mutun asibin ma zai iya yiwuwa ya rayu
domin kafin akarasa mararrabar garin mutun zai iya mutuwa , nawa nawa akayi akan idanunsu
suka gani ,dan haka addua suke kullun Allah ya kawo musu d'auki daga gwanati mai ci alokacin
data tallafi rayukansu ta gina musu asibiti da makarantar gaba da primary .

tunda mahaifiyarsu ta fara ciwon take barwa d'anta wasiyya a kullun bakinta baya shiru da
mgnr diyarta mukarama ta kance "mahamud ko na mutu dan Allah ka kular min da 'yar'uwarka
kaga bata da kowa sai kai," kai ne uwarta kaine ubanta domin zan tafi na barta acikin lisafi na
kurciya Muhammad ka rike zumunci ,mukarama amana ce a hannunka ina son ka kaunaceta
fiyye da komai ka kula da maraicinta da rayuwarta karka bari ta zubda hawayenta akan
damuwa kowace iri ce ..


duk sanda mahaifiyarsu ta tasa shi gaba tana bar masa wasiyya ya kan share hawaye yace "ki
daina furta wannan kalmar inna cuta ba mutuwa ba,sannan ba'a san inda rai yake ba, babu
wanda yasan gawar fari ban da Allah, baki sani ba ko mune zamu rigaki mutuwa.


"kayya d'an nan dayake hk take kiransa kasancewarsa d'an fari , "wannan ciwon bana tashi
bane, ni kaina ban sa ran zan warke ba har in tashi ba, domin wannan ciwon bai kamani da
wasa ba, ni dai fatana ko na tafi na barku ka rike 'yar'uwarka da daraja kada ka auri macen da
zata shiga tsakaninku, duk abinda, zata maka kayi hakuri kamata uziri, ku had'e kanku ka aurar

daita ga mutumin da kasan zai riketa da daraja sannan ka inganta rayuwarta da karatun addini
dana boko tak'arasa mgnr tana janyo numfashi da kyar wasu zafafan hawayen tausayin
ya'yanta yashiga gangarowa bisa kuncinta.

haka ma duk sanda mukarama ta kunsantota mgnrta kenan "mukarama ki rike d'anuwanki, ki
rufa masa asiri a duk sanda hkn takasance, ki d'auke shi matsayin uba, domin hausawa sunce
babban wa uba ne, ku rike zumunci atsakaninku, duk abinda kika samu nashi ne hk shima, ku
zamo tsintsiya mad'aurinku daya Allah yayi muku albarka.

tunda inna ta kwanta ciwo bakinta baya shr da barwa mahmamud da mukarama wasiyya da
amanar junansu ,su rike junansu , ciwon dai na ajali ne rana daya zazzabin ya tashi zanga
zanga suka nufi asibiti Daita ,akan hanya kmr ko wani lokaci Allah ya amshi rayuwarta batare
dataga auren ya'yanta ba.
bayan rasuwar mahaifiyarsu sun shiga damuwa kwarai da gaske kar ma dai mahamud yaji
labari musamman idan yaga mukarama tana yawon kukan mutuwar innarsu ,duk sai tausayinta
ya kamashi domin yasan dole kewar inna ta dameta, wani lokacin da kansa yake bata umarnin
tashiga gidan mukotansu gurin hajara .
hajara kawar mukarama ce tare suka taso tun innarsu tana da rai, basa rabuwa tare suke
al'amurasu tare sukayi makarantar boko haka islamiyya ,idan bakaga mukarama ba tana gurin
hajara akwai sabo da shakuwa mai tsananin atsakaninsu dama kuma can iyayensu aminan
juna ne, byn rasuwar mahaifinyarsu, mahaifin hajara na d'aya daga cikin wanda ya taimakawa rayuwarsu dan haka shima mahamud lokacin
daya samu rufin asiri bai manta dasu ba hatta karatu hajara shi yake biya musu kudi tare da
kanwarsa ,komai ya tashi yiwa mukarama ya kan had'a da hajara yayi musu tare irin karar
dayake musu , yasa iyayen hajara suke matukar jin dadi sosai, kullun cikin yabonsa suke.

wata rana mahamud na gida yana wanke mashin dinsa sai kuwa hajara tashigo gidan da gudu
tana huci ,sauran kiris tayi karo da machine dinsa, ganin mahamad tsaye yana kallonta sai tayi
saurin komawa da wani gudun a kunyace ,ya kwalla mata Kira ta dawo da baya yace "zo nan
sai kin gaya min dalilin gudun naki, bana hanaku irin wannan guge gujen ba, hajara tasa
hannuwanta duka ta rufe fuskarta dashi tana dariya shima diriyar yayi kana yace "wai hajara in
tambayeki shin me yasa kike jin kunyata ne?
tayi shiru kanta a sunkuye yace "ko nayi miki kama da surukinki ne?
nan ma shr tayi yace "ni na lura duk sanda kika shigo gidan nan bakya sakewa ko kuma
tsorona kike ji.?

hajara ta girgiza kai yace "to me yasa bakya iya kar'bar abu agurina sai dai mukarama ta
kar'ba muku?
nan ma shiru tayi mukarama ce ta fito daga cikin d'akin tana dry,mahamud ya kalli mukarama,

sannan yace"wai me ya sa kawarki take jin kunyata?

mukarama tace "inajin kodan taji goggo tace.... ya d'an dubeta da sauri yace "me goggon tace ?
mukarama tayi shr tana kallon hajara tana dry kuma taki k'arasawa, dayake yasan halin
shirmensu kurun sai ya rabu dasu yace "ku wuce kubani guri Allah yasa na sake ganin kuna irin
wannan guje gujen sai kace wasu kanan nan yara.

ranar wata litinin da safe mahamud yashiga gidansu hajara domin ya gaida su, hajara najin
muryarsa taki fitowa daga cikin d'akin, byn sun gama gaisawa da mutanen gidan baban hajara
yace"wai shin mahamud kai har yanzu baka fara tunanin aure ba ne?
tunda Allah ya amshi ran mahaifiyarku ,ai sai ka d'aure ka nemi abokiyar zama kodan ka
ragewa 'yaruwarka kewar innarku data rasa.


yace "wallahi baba nima nayi wannan tunanin to sai dai ina kan dudubawa in samo wacce ta
mallaki kanta, baba yace "naso ace ina da 'ya babba da zan kulla zumunta atsakaninmu
amman tunda banida ita ga hajara nan na baka, sai a wanketa akai maka.

abin yabawa mahamud mamaki ya danyi driya kana yace "lallai baba kanason ka had'a rigima
kasan kuwa yadda hajara take tsananin jin tsorona ?
bama haka ba baba yaushe za'a ce za'a yiwa hajara aure yarinyar da sai ma yanzu zasu kare
primary, nima kuma dakake ganina karatu zan koma.

mahaifin hajara yayi dry sannan yace" duk wannan bawani abu bane in dai kana sonta tunda
kana son bokon itama sai ka barta tayi karatu agidanka.
mahamud ya sake yin dry"amman baba baka ganin irin shirmen da zasu ta min acikin gida.

"duk babu komai sai ka jure har zuwa lokacin da zasu yi hankali mahamud ya d'an dubi babar
hajara yace "kin dai ji goggo ,baba yana neman ya had'ani da rigima.
cikin murmushi tace "to idan haka ne ai nice na fara furtawa kai dai tunda ance anbaka ba sai
kayi fatan alkhairi Allah ya tayaka riko ba, babu yadda mahamud ya iya dan haka yace shikenan
goggo na karba Allah ya rika min .

a daidai wannan lokacin mahamud yasamu gurbin karatu a jamiar d'an fodio dake jahar sokoto
inda zai karanci kasuwanci.

zance aurensa kuwa da hajara abu kmr wasa, abu ya kankama yana da shekara biyu a jimi'a
aka soma shirye shiryen aure cikin kankanin lokaci aka saka hajara lalle agama biki aka kaiwa
mahamud amaryarsa .
ba k'aramin raino mahamud yayi ba ,kafin hajara ta zama cikakkiyar mace ba, ya dai sha
shirmensu ita da mukarama, haka nan ya dage da kyautata musu kullun yana tsaye akansu
komai suke bukata zai siyo ya kawo musu da yake yara ne masu hankali da natsuwa sukayi
zamansu lafiya su fad'i tare su tashi tare suna harkarsu su duka suna jin dadi zama da junansu

ahankali ahankali rayuwarsu ta cigaba da gudana cikin jin dadi har sanda mukarama tasamu
karatu a makaranta kwana dake aleiro government girl's comprehensive secondary school
aleiro, yayinda hajara kuma ya samammata makaranta anan cikin garinsu, dan Allah ya tallafisu
ya amshi rokonsu yasa aka bud'e musu jeka ka dawo.
kullun zata makaranta idan ta tashi ta dawo gidan mijinta, tayi girki da sauransu hidimomi gida,
rayuwarsu dai gwanin sha'awa in kaga yadda mahamud yake tattalin hajara sai ka rantse wata
shararriya soyayya sukayi kafin aurensu.

shi dai mahamud mutun ne mai son mace taji dadi gashi da busha sha, ga sakin fuska da
saukin kai ,hajara dai ta samu soyayya da kulawa agurin mijinta, kullun babanta na saka masa
albakar saboda ya rike amanar da'aka bashi kuma gashi da zumunci domin mahamud ya
maida iyayen hajara tamkar nasa komai zaiyi ya kan nemi shawararsu haka suka cigaba da
rayuwa ganin sha'awa .

ta bangarensa karatunsa ma bashi da wata matsala komai na tafiyar masa yadda yakamata
idan ya dawo hutu kuwa zai kama kasuwancinsa na siye da siyar, sannan ya bud'e k'aramin
shago a kofar gidansu wanda yake gyara agogo.

******
lokaci zuwa lokaci idan mukarama tazo hutu hk samari ke yi mata caaaa amman sam mahamud
ya kekashe kasa yace "bai san da wannan zance ba, karatu zatayi duk wanda yaji zai iya jiranta
to ya jira ,wanda ba zai iya ba, ya k'ara gaba ya nemi matarsa, cikin haka ya kammala da
karatunsa ,kasuwancinsa ya k'ara bukasa, komai yana gara masa domin zuwa yanzu ya fantsana cikin
duniya neman arziki, dan har sun bar kauyensu zuwa cikin birnin ilorin state .

byn wani kankanin lokaci sai gashi ya zama matashi attajiri dake da mallakin gidaje, ya sayi
motaci baya ga yaran kauyensu daya Diba suke karkashinsa.
zuwa lokacin yana da yaro daya mai sunan Ibrahim ,suna kiransa da akram da yake sunan
mahaifinsa garesa ..

mukarama ta tagama karatunta na gaba da primary, ta zama cikakkiyar budurwa sosai gata da
kyau da gogewa da iya tsara kwalliya ,cikin wannan lokacin ishaq abokin Muhammad wanda ya
kasance abokin kasuwancinsa ne ya dawo daga kasar maleshia akan harkan kasuwanci da
karatunsa .
ishaq hadadden matashi saurayi ne tsayaye mai zati da haiba uwa uba naira ta zauna ajikinsa
asalinsa dan Kano ne amman babu inda baya shiga adalilin kasuwanci.

wata rana ya kawowa Muhammad ziyara,inda Muhammad yace "mukarama ta kawowa
abokinsa abun motsa baki,tashigo parlour'n cike da natsuwa da kamewa uwa uba kunya, ai
kuwa ishaq yana d'aura idanunsa akanta yarasa tsukuni amman dayayi wani tunani sai yayi

saurin kawar da abinda yaji akanta, ta ajiye tire ishaq yace "ga leda nan ta wuce dashi
tsarabarsu ce aciki, sam mukarama taki d'auka, ya d'auka ya mika mata nan ma taki amsa
yace" haba kanwarmu ina ganinki mai kalar wayyayu, a wannan zamanin yaushe ake kunya
hk? mukarama ta juya akunyace zata fice daga parlour'n, 'yar drya Muhammad yayi yace "to in kin
shiga ki turomin hajara kawai ,tana fita ishaq yace "amman wannan wani irin kunya ce hk sai
kace ba yar zamani ba?

alhj Muhammad yace" ina ruwan mukarama haka Allah yayita komai nata sai ta had'a da kunya
yarinya ce mai tsananin kawaici babu ruwanta.
yace "da kyau hk nake son naga mace nada kawaici da alkunya a dukkanin al'amuranta da
ganin kanwar tamu mijinta ya dace kwarai ya fad'i hk saboda tunaninsa ko tana da aure.

alhj Muhammad yace"kuma ka gani bata da miji har yanzu bata tsaida miji ba karatu take domin
ina da burin akanta,ina son na ingata rayuwarta da karatu boko domin a dama wannan duniyar
daita, shiyasa duk masu kawo hari nake katse masu hanzari har sai ta gama, yanzu haka tana
matakin diploma .
ishaq ya d'an dubesa a razane domin yasan asaninsa mutane karkara haka ,basu fiyye barin
yaransu su jima hk batare da yin aure ba ....
"gsky abokina kayi nmj k'ok'arin gurin ingata rayuwarta ,yanzu dai kace babu kowa akasa masu
neman aurenta?

"babu kowa ina suka ga fuska, ai sai sunga fuska tukun zasu zo, ni dai burina tayi karatu mai
zurfi ta yadda zata taimaki al'umma da ita kanta, nan dai suka bar zance suka shiga hirar
kasuwanci dayake daman harkar kasuwamci ne ta had'asu har suka zama abokai, acikinsu duk
wanda wata harka tashigo hannunsa daya san za'a samu alheri y kan janyo dan'uwansa ciki, su
samu alkhairi tare kasancewar dukansu ba masu kyashi ko bakinciki bane ,kowa yana k'aruwa
da kowa suna harkar arziki tare gwanin sha'awa.

tunda ishaq yakoma gida sai ya kasa samun sukunin zuciya duk yadda ya runtse idanunsa
mukarama yake gani tana yi masa gizo ,haka nan abin mamaki jiyayi gbdy ya tsinci kanshi da
matsanancin kaunar mukarama ,ganin dayayi mata ya gigita kwalkwaluwarsa ,sosai yarinyar ta
rikitashi ,ya rikice akanta har tunaninta na neman hanashi sukuni yin barci, shi kansa sai juya
al'amarin yake aransa yadda farat daya ya gigice akanta gashi dan'uwanta na da buri akanta,
dan hk ya danne abun aransa yacigaba da hakuri ,haka soyayar mukarama yayita cinsa arai
har sai da aka samu wasu yan watani.

************
ran nan dai ishaq ya kasa hakuri adalilin soyayyar mukarama da kullun take sake huda kahon
zuciyarsa, dan hk a zaunen da yake agaban mahamud yasoma maganar yadda yake son
mukarama.
mahamud yayi shr yana sauraron abokinsa har yagama zayyana masa irin kaunar dayake yiwa

mukarama,Muhammad yace "naji dadi kwarai kuma ina matukar farinciki da wannan bayani
naka ,sanin kanka ne kafi karfin komai agurina ,zai yi wuya ka nemi wani abu a wurina na
hanaka, musamman ma irin wannan alfarma ta aure, to amman akwai wani hanzari ba gudu ba
kmr yadda kasani, bazan aurawa mukarama mijin da bazai barta tacigaba da karatunta ba,
matsawar ka amince zata cigaba da karatunta agidanka shikenan na amince kaje ka nemi
yardarta matukar ta amince da kai zan aura maka ita.

ishaq ya sauke naunauyen ajiyar zuciya kana yace "wannan ba wata matsala bace ni kaina har
yanzu akan karatu nake kasan da haka ,domin lamarin kasuwancinmu na bukatar ilimi mai
zurfi,bugu da kari ilimin mace nada matukar mahimmanci arayuwa.

"haka ne kam Allah yasa mu dace kana iya turo magabatanka idan ta amince , ishaq yace
"ameen had'e dayiwa abokinsa godiya " domin sosai yaji dadin lafazinsa mahamud na gama
fadar hk ya bari parlour'n.

ishaq ya nemi ganawa da mukarama ,byn tashigo parlour'n suka dan yi shru kad'an sannan
yakira sunanta "ko kinsan zuwan nawa na yau dominki ne sabanin sauran lokuta?
ta d'an kalleshi cikin natsuwa, yayinda ta zuba masa idanu tana kallonsa da sauraren abinda
zaice dan gabad'aya zuciyarta ta matsu da son jin abinda ke cin ransa akanta, domin itama tana
jin wani abu a game dashi .
yacigaba "hakika mukarama dazaki min alfamar dana dan gutsara miki abinda ke cin raina a
game dake, Allah yasamin tsananin kaunarki tun ranar farko dana d'aura idanuna akanki
dayake nasan ba aure yayanki zai miki a wannan lokacin ba sai nayi kokarin danne sonki cikin
zuciyata har sai yanxu ,a yanzu dai ina gabatar miki da kaina amatsayin wanda yake son
aurenki amman menene ra'ayinki akaina ?

mukarama dai tayi shiru saboda batasan amsar dazata bashi ba, domin mutumin yana yi mata
kwarjini ganin bata da niyyar bashi amsa yace "haba mukarama ya kikayi shr ai gara kiyi
magana shi sha'anin aure ai ba'a yinsa da wasa zan so jin ta bakinki koda bakya sona barema
bana fatan haka nafi son kiyi min alfarma bisa soyayya kar ma ki tsaya duba alaka don ba itace
tasani sonki ba.

" kyawawan halaiyenki da dabi'unki na kirki ne suka janyo zazzafar kaunarki ,ki taimawa
rayuwar wannan tsohon tuxuron ki aureshi domin idan kika ki aurensa ina tabbatar miki hk zai
k'arasa sauran rayuwarsa batare daya ajiye iyali ba.

mukarama ta cigaba da yin shiru sai dai wannan karon kanta na sunkuye ,murmushi yayi
saboda sanin halinta na kunya "haba zuciyar ishaq ki dan yi min magana ko naji dadi "tayi
dariya amman batace komai ba yace"kenan dai ana son ishaq ya hakura," mai yiwuwa ina da
wani abun da baza a soni dominsa ba?
sai a lokacin ta girgiza kanta, yace "ni kam muddin ba magana ki kai ba, gani nake ban canci
asoni ba ,shi yasa kika barni da kokon barana a hannu, ai sauran maneman ba hk ake musu

ba, ko kuma ko dan anga ni babban yaya ne kike ganin nayi miki tsufa?

maganarsa ta bata dariya har ta sa ta d'ago kanta da sauri suka dubi juna sannan tace "ko
kad'an ba haka bane, ni dai aguna baka da wani aibu da kowace irin mace zata kika ,sai dai
abunda nake son kagane ban taba yankewa kaina hukunci ba sai dai yayana ya yanke min.

"idan ta wannan bangare ne mugama magana da yayanki har ya amince har ma da sharadinsa
nason ki cigaba da karatunki byn aurenmu, na kuma ji na gani na amince da hakan ,saboda ina
matsanamcin sonki "duk da haka ni dai nayiwa kaina alkwarin komai zanyi sai da amincewarsa.
"da kyau kinga wannan biyayyar taki tana daga cikin abubuwan dayasa na kamu da sonki
tunda kin tabbatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login