Showing 63001 words to 66000 words out of 128821 words
Chapter 22 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf
kwanta gobe sammako zan yi zuwa seminar
din nan da na gaya makaâ€.
Daga haka ya bi matattakala ya haye upstairs da tafiyarsa mai nutsuwa, wadda babu garaje a
cikinta.
6/29/21, 9:00 AM - Buhainat: BEHIND
Aboulkhair ya damki hannayenta ya rike, ya ce, “Wuw! Thirty minutes cif ban kama Aalimah
ta ba, gaskiya na yi kokari. Lets go tun kokarina bai tashi a banza ba, ya yi mantuwa ya
dawoâ€.
Zame hannayenta ta yi, ta ce, “Da na sani ma kiss na yi maka a gabansaâ€. Ta yi gaba da
sauri. Ta ma manta da abin da Mu’azzam din ya ajiye mata, ya dauko ya biyo ta da shi yana
fadin, “Ka ji ta kamar gaske, alhalin ke kanki zama ki ka yi kamar wadda ta yi wa sarki karya
a gaban nasaâ€. Sai da ya tada motar ya dora mata katin da takardar a cinyarta. Credint card ne na bankin da
Mummy ke aiki JP MORGAN CHASE da pin numbers din ya rubuta a jikin takardar.
“Ba ki ya yi, yarinya kin zama Madame, ki yi ta zara ana karowa duk wata. Ga shi ko
shopping mall daya ba ki sani ba. In na koma hutu zan zagaya da ke ki ga gari, amma yanzu
lalalala, sai na gama honeymoon dinaâ€. Ya fada yana mai winking dinta. Murmushi ta yi, ta ce,
“Ka ajiye a wajenka, ni ba abin da zan saya, beside komai nake so zan iya gaya makaâ€. Haka suka yi ta musu, ta dage ba za ta karba a hannunta ba, ya dage nata ne shi ba zai mata
ajiyar kudi ba, in Mu’azzam ya gani a hannunsa ba zai ji dadi ba. In ba abin da za ta yi da
su din, ta kwashe ta tura wa Kawu Mansour ko mama Asi. Ta yarda da wannan shawarar.
Har suka zo gida Aalimah is very curious and questioning Aboulkhair a kan rayuwar
Mu’azzam saboda al’amuransa bakidaya sun kara rikitata. Sun kara daure mata kai,
mutum kamarsa mai cikar mutunci da kamala, ga rayuwar duniya Allah ya ba shi daidai misali,
amma babu iyali, babu ranar zancensu? Kallon da ta ke masa daga nesa-nesa da ta zo kusa da
shi ta ga ba haka ba ne. ba ta ga annoyance din a tare da shi ba banda ganewa da ta yi shi din
is a very serious person, mai matukar tsantseni da lokacinsa. Mai girmama bako, mai tarin
al’amuran yi fal a gabansa. Tambayoyin da ta ke yi wa Aboulkhair har ya rasa wanne zai
fara amsa mata.
Tambayarta ta karshe ita ce, “Wane magani yake cewa za mu cika masa gida da shi?
Maganin me yake cewa zai je ya sha ya kwanta?â€
Aboulkhair ya sanya hannayensa biyu ya toshe kunnuwansa bayan ya kashe motar a
ma’adaninta, ya ce, “Baby, ina da nawa matsalolin ki taimaka min in warware su.
Sannan in waiwayi naki matsalolin which is MU’AZZAM. Na daya, hundred kiss at mouth,
fifty at my nose, seventy at my tongue, eigthty at my eyes and two hundred at my neck. In kin
gama wannan ki zo na yi miki alkawarin warware miki rayuwar Mu’azzam bakidaya, tun
daga kuruciya har girma. Amma ko daya ki ka tsallake ina kirge da abuna, kin tsallake chapter
daya cikin labarin Mu’azzamâ€.
Aalimah ta dora hannayenta biyu a ka tana fadin, “Na shiga uku! Mon Amour ka yi min
sassauci, ba zan iya ba, and I really-really want to hear his story, amma haka zan ta binka ina
sumbata kamar zan cinye ka? A tarihin gidanmu babu mayeâ€.
Ya hadiye dariyar da ta ba shi, ya yi gaba yana fadin, “Za ki ga maita! Sai ki zaba ko maita
ko labarin Mu’azzamâ€.
Ta ciji yatsa ta bi shi da gudu, suka shige gidan nasu. Ta riko hannunsa zai shige dakinsa,
“Mon Amour ka saurare ni. Zan yi maka tausa dai kadai, Allah ba zan iya ba ina jin
kunyarkaâ€. Ta fada kamar za ta yi kuka.
Kwacewa ya yi ya shige yana fadin, “Ni fa na gama magana, ai it is an option, not a choice,
ban ce dole ba, ki rike tausarki, in ita ce ina da injin da zai yi min. I just want to confirm I’m
married to Aalimah Mansour, (kawai ina so in tabbatarwa kaina ina auren Aalimah Mansour)
saboda har gobe ji nake kamar a mafarki… kamar za ki kubuce min Aalimah… kamar har
gobe ban gama mallakarki ba. Kamar akwai wasu sauran gurabe cikin zuciyarki da ban kai ga
isa baâ€.
Intonation din da yake maganar da shi, da yanayin da ta gani cikin kwayar idanunsa su suka
taru suka sukurkutata, suka rikitata, suka sa ta jin wani irin tsoro na ratsa ta. Sanda ta kankame
shi ba ta sani ba… sanda ta soma rufe shi da sumbar a guraben da ya bukata da ma in da bai
bukata ba, ba ta yi shawara da zuciyarta ba. Ba ta tuna akwai wata aba wai ita kunya cikin
idanunta ba. Tun yana fadin, “Niceâ€. Ya koma, “Sweetâ€. Ya koma, “Splendidâ€.
Al’amarin da bai tuke a ko’ina ba sai a gadon barcinsu. Wata irin soyayya mai zafi da
tsanani wadda a yau ba ta Aboulkhair ba ce shi kadai, 80% ta Aalimah ce da hobbasarta.
Aboulkhair ya yaba, ya yi tukuici yadda ya kamata. Saida suka dawo hayyacinsu ya soma
kyalkyala mata dariya. Ya ce ba wuya za a sayar da kanta a Las vegas. Shi duk abin da ya fada
don ta yi masa abin da yake so ne, kuma ga shi ta yi.
“Ban da rashin wayo irin naki, wane gurbin ne ban kai ga isa ba? Yana ina? Nuna min shiâ€.
Hannayenta biyu ta kai ta rufe fuskarta, ya rungume ta tsantsan, ya ce, “Aalimah, Allah ya yi
miki albarka, ya albarkaci rayuwarmu da ‘ya’ya masu irin tarbiyyarki, ba wata kubucewa
da na yi tunanin za ki yi min banda ina so in koyar da ke yadda za ki tafiyar da ni. Kunyarki is
too much… Ni kuma… ni kuma…â€. Ya soma zagaye dan bakinta da yatsansa ibham,
“…Ina so kullum in ji sulbinshi da sanyinshi da taushinshi kan fatar jikina. In ki ka yi min
wannan kin gama min komai, kin kauda hankalina daga kowacce diya mace. Kin zama ni na
zama ke, mun zama sirrin juna. Bude kunnuwanki in gaya miki ko wane ne MU’AZZAM???
LABARIN MU’AZZAM.
Wato tunda muka taso daga shekaru biyar a duniya zuwa sama, mahaifiyarmu ta dora mu a kan
turbar duk abin da muke so sai mun same shi, kuma za ta iya samar da shi gare mu ta kowacce
hanya in har hakan zai sa mu farin ciki. Tun muna kanana Mummy ta lalata mu da kashe kudi, a
kullum tana gaya mana don mu ta ke aiki, burinta mu samu duk abin da muke so a rayuwa mu ji
dadi a kasar da muke zaune, mu zama daya da ‘ya’yan turawa, mu manta da ‘yan
kauyen dangin Daddy don ba kaunarmu suke yi ba. A cewar ta da ba su bar Nijar ba, da tuni
sun raba ta da Daddy, saboda rashin son da suke mata. In za mu tafi makaranta haka ta ke
damtso kudi ta ba mu, ta ce mu kashe duk da ga lafiyayyen abinci da abin sha ta cika mana
lunch box da shi. Mu kuwa mu yi ta bushasha da abokanmu.
Duk kokarinta na hana mu yin abokai tana cewa, mu zama abokan junanmu kadai, abokai suna
cutar da yaro ne kawai su canza masa tarbiyya. Wannan tsoratarwa ta Mummy ba ta yi wani
tasiri sosai a kanmu ba, saboda muna neman wadanda za su taya mu cinye tulin kudin da ta ke
ba mu ne, ba mu kuma san ya za mu yi da su ba. Abinki da makarantu na nasara masu
tsananin kula da sanya ido, ba a dade ba school authority ta fahimci irin kashe kudin da muke yi
a sayi banza sayi wofi, da irin abubuwan almubazzarancin da muke zuwa da su, ta yi wa Daddy
magana. Ya kuma bincike mu kan inda muke samun kudi, inda ba tare da bata lokaci ba muka
gaya masa Mummy ce ta ke ba mu. Don haka ya yi mata magana, ya kuma gaya mata
tsawatarwar hukumar makaranta. Sabida haka Mummy sai ta koma sanya mana a jaka ba tare
da sanin Daddy ba, ta kuma ce mu daina kashewa a makaranta sai mun dawo gida kafin ta
dawo daga aiki.
Zancen nan da nake miki, lokacin mahaifinmu na aiki da consulate of Niger ne, ainahin aikin da
ya kawo mahaifinmu kasar Amurka. Muna zaune a Washington D.C. Daddy ba wani babba ba
ne a consulate din (diplomat officer) ne kawai, amma albashinsa dai mai tsoka ne, don a haka
ya yi sponsoring karatun Mummy, har ta gama ba ta jima ba kuma ta samu aiki da daya daga
cikin manyan bankunan kasar, wato JP Morgan Chase, matsayin akawu (Accountant) domin ta
fito da digiri mai daraja ta farko, kuma a wannan zamanin samun aiki ga bakin haure bai yi
wuyar da yake da ita a yanzu ba. Namu karatun kuwa ni da Mu’az ba shi yake daukar
nauyinsa ba, ofishinsu ne. Don haka rayuwa muke cikin rufin asiri, ba mu nemi komai mun rasa
ba. Da Mummy ta soma aiki sai muka koma cikin wadata fiye da baya, saboda duk albashin
nata a kanmu yake karewa ni da Mu’az, suttura, kekuna, ciye-ciye da duk wani abu da yara
maza masu shekaru irin namu za su bukata. Mummy ta sakar mana dukkan bakin aljihunta. Sai
dai kuma aiki ya sa mun nesanta da juna, ita dai za ta ba mu kudi, ba ta damu da duk abin da
muke ciki ba, ba ta san wace irin rayuwa muke yi ni da Mu’az ba idan ba ta nan tunda ta
daukar mana house maid mai dafa mana abinci da kula da tsaftar jikinmu.
Kusa da gidanmu wani flat house ne, mallakin wani baturen Portugal da matarsa da dansa
Clarson. Wannan yaron Clarson ya girmi Mu’azzam da shekaru biyar, amma haka ya shige
jikin Mu’az suka zama abokai, ba komai ya sanya wa Clarson like wa Mu’az ba sai
ganin gatan da yake ciki, da irin kudin da yake kashewa kullum, kekunan da yake hawa ma
masu matukar tsada ne, ban da sitturunsa. Yayin da shi kuma Babansa giya yake sayarwa a
wani Bar a nan cikin Washington. Lokacin da Mummy ta samu labarin alakar Mu’az da
Clarson daga bakin mai aikinmu ta yi kokarin raba su, amma ta kasa saboda Clarson ya fi
Mu’azzam wayo da budadden ido, don haka ya shiga jikinsa ba da wasa ba. Clarson shi ya
koya wa Mu’az yadda zai dinga shan alcohol wadda babansa ke sayarwa, ya gaya masa ta
fi komai dadi, kuma sai kana shanta ne ka ke zama babban yaro, wanda ya wuce kowa ya taka
ka ko a raina ka.
A lokacin ni karami ne, ba su da mu da ni ba, ni ma kuma ban damu da abin da suke yi ba,
shekaru biyar ne tsakanina da Mu’az, wadanda ya girme ni da su. Sannan Allah bai yi ni da
daukar magana ba, ko iyayenmu in ba su tambaye ni abu ba, haka kawai ba za ka ji ina fade
ba. I’m very quite tun ina karami, mara son kwaramniya da rashin hayaniya. A gidan su
Clarson kuma a dakinsa suke consumption dinsu, wadda Clarson ke sayo musu wajen
Babanshi da kudin Mu’az, da sunan aiko shi aka yi, kuma da yake yana taya uban kan
sana’ar tashi wani lokacin ma shi yake zamar masa a bar din in zai je wani waje.
Clarson ko makaranta ba ya zuwa, neman kudi kawai ya kawo su Washington. Daddy bai samu
gida a cikin Niger consulateba, amma consulatedin ke biyan hayar gidan da muke ciki. Kananan
ma’aikatansu irin su Daddy kan zauna a cikin gari. Tun suna da shekaru kasa da sha biyar
suke shan giya, sha na fitar hankali har Mu’azzam ya zama addicted.Daddy ba mazauni ba
ne, haka Mummy, we spend 70% of our lives with a maid wata tsohuwar banasariya wadda abin
da aka sanya ta kawai shi ta sa a gaba, wato kula da cikinmu da tsaftar jikinmu. Ta gaya wa
Mummy yawan zuwan Mu’az gidan su Clearson tunda ta ja masa kunne ba ta dauki wani
kwakkwaran mataki a kai ba. Ita ba ma rashin tarbiyyar Clearson ne damuwarta ba, kawai
talaucin iyayensa ne, kuma dai ba ta son mu da abokai tun ba mu kawo lokacin ba. don haka
Mu’az ya dade yana shan giya kafin Daddy ya ankara.
Watarana ne ya dawo gida ba lokacin dawowarsa ba. Mu muna hutun rabin zango a makaranta,
shi da Mummy suna office. Ni kadai ya samu a gidan, Angela ta je cefane. Holiday assignment
nake yi a falonmu. Ya tambaye ni ina Mu’az? Ba tare da na dago ba daga abin da nake yi,
na ce da shi yana dakin Clearson. Cikin mamaki ya ce, “Clearson yaron Mr. Ben?â€
Na ce, “Eh, ai abokinsa neâ€.
Firgicin Daddy ya kasa boyuwa, ya ce in tashi in raka shi har dakin Clearson din.
Ni ne a gaba, Daddy na biye da ni. Gidan a bude yake, kuma kamar kullum Mrs. Ben, wato
mahaifiyar Clearson ba ta nan, ta tafi neman kudinta. Har dakin na raka Daddy inda ya gani,
ganin idonsa Mu’az na kwankwadar beer. Ga kwalabe birjik mai nuna shan giyar ma na
hauka suke yi. Mu’az ba ya ko iya bude idanunsa balle ya san waye a kansa. Haka Daddy
ya sanya hannuwa ya dauko shi, ya saba shi a kafada yana hawaye muka dawo gida, ko kallo
kwakkwara bai iya yi wa Clearson ba.
A wannan rana da Mu’az ya farfado ya ci duka a wurin Daddy, kamar ba zai barshi da rai
ba. ya kuma yi threatening dinshi da maida shi Nijar, Nijar din ma Tessoua in bai daina ba.
Amma Mu’azzam ya kasa dainawa, suka samu maboya shi da Clearson inda suke zuwa su
sha, shan giya wanda ya wuce ka’ida da tunanin mai tunani. Giya kala-kala zafafa wadda
ko manya ba sa ta’ammali da ita. Mummy kuma na ba shi kudin saye, mai tsada ta
‘ya’yan gata. Bayan lokaci mai tsawo Mu’azzam ya fara wata irin rashin lafiya kamar
ba zai yi rai ba, wanda a binciken likitoci suka gano alcahol ta soma lahanta hantarsa da
kwakwalwarsa.
Ita kanta Mummy hankalinta ya tashi, ta fara nadamar yadda ta ke ba shi kudin sayen giyar, ta
san Mu’az yana shan giya, amma hakan bai taba damunta ba domin kuwa a can ba wani
abu ba ne shan giyar, sai dai tana da masaniyar cewa it is wrong as well as prohibited a
addininmu, kuma Mu’azzam ya yi kankanta da ya sha giya. Har a lokacin he is under
eighteen. Al’adun nasara sun yi tasiri mai yawa a tare da Mummynmu a lokacin. Daga ita
har Daddy babu wanda ya taba tunanin sanya mu a islamic school, duk da cewa ga su nan
birjik a ko’ina na kasar nan. They only show us yadda za mu yi sallah, in Daddy yana gida
yana sa mu a gaba mu yi tare, maghriba da isha. Da asubah ma yana tashinmu mu yi tare,
amma kin ga azhar da la’asar ba kullum muke tunawa mu yi ba, musamman bayan
haduwar Mu’az da Clearson. A wannan lokacin Daddy ya soma neman aiki wuri-wuri don
dai ya raba Mu’azzam da Washington ya samar masa sabuwar rayuwa, bayan shafe
shekaru goma a Niger Consulate of America, ya samu residence permit. Wannan ne dalilin
barinmu Washington zuwa nan Boston (Massachusetts). Daddy ya samu aikin gwamnati (permanent) a jihar Massachusetts, muka tattaro muka dawo,
wannan ne ya raba Mu’az da Clearson. Sosai Daddy yake jan Mu’az a jiki bayan
samun saukinsa, yana nuna masa illar giya da haramcinta a addininmu. Aka yi nasara
Mu’azzam ya bar shan giya, amma sai ya fara wasu bakin halaye. Abu kadan sai ya fusata shi, in ya yi fushin kuma he will destroy everything behind him, no one
in the house can control his temper, not even me da yake matukar so. Komawa yake tamkar bai
san kowa a cikinmu ba, burinsa ya lahanta komai da hannunsa zai iya kai wa. In yana cikin
wannan halin Mummy ba ta iya komai, sai kuka. Daddy kan kama shi ya matse ya rungyme shi
ta karfi yana gaya masa kalamai na kwantar da hankali, yana tofa masa addu’a. Da abin ya
fi karfin Daddy, sai ya kai shi asibiti, inda da gaggawa suka yi referring dinshi zuwa Psychiatric.
A can ne bincike da gwaje-gwaje suka nuna yana da aggressive tendencies, wanda shan giya
ya haifar cikin neuron dinsa. Ya soma karbar treatment yadda ya kamata. Sosai ya nutsu, ya
koma yadda yake tun kafin ya san mene ne giya.
A Massachusetts Mu’az ya maida hankali ya gama karatun sakandirensa da takardu masu
kyau, ya kuma zabi jami’ar Nevada ta garin Las Vegas ya fara karantar Petroleum Geology.
Ya kama karatunshi sosai don a lokacin yana da shekaru ashirin da biyu, ya yi hankalin sanin
abin da zai amfane shi, da abin da ba zai amfane shi ba. Yana shekararshi ta karshe a
jami’a ya hadu da wata kaddarar bayan Clearson wato JUWAIRA.
Ni kuma a lokacin ne na fara jami’a a Louisiana, ba don komai ba na ki bin Mu’az
Vegas ba, sai don ba abin da na tsana irin ganin Mu’az cikin black opisodes dinsa na
aggressive temper. Abu ne da ke tayar da hankalina matuka, ya sa ni takurewa a gefe ina kuka.
Yana gama degree Daddy ya shiga nema masa aure ba da saninsa ba, daga dangin Mummy
don ta ce ba ta yarda ya nemo a nasa dangin da ba kaunarta suke ba.
A ganin daddy, aure zai sassauta masa wannan ciwon fushin, bayan magani. Ashe shi
Mu’az yana da wadda yake so, wato Juwaira. Iyayenta haifaffun kasar Ethiopia ne, zama ne
ya kawo su America. Mu’azzam ya