Showing 9001 words to 12000 words out of 128821 words

Chapter 4 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

bag, har ta gama cefanen kayan abinci kala-kala
nau’i-nau’i suka sa a bayan mota. Daga nan sai suka wuce Burlington Mall din ta yi ta
sayayyar kayan gayunta, su ma ba a barsu a baya ba duk wani abin amfani na mata na tsaftar
jiki da kayan shafa da kamshi sun saya, Daddy na ta biya, sannan suka taho gida.
Kafin su iso gida Mummy ta saki rai sosai tana ta jan mijinta da hira, su ma yaran tana kula su
har Aalimah. Shi dai kallonta yake yana mamakinta. Ta zame masa kamar wata mai ‘Multi
personality disorder’ yanzu ta ke daidai anjima za ta koma wata majanuniya. He loves his
wife as such! Wato yana son matarsa a duk yadda ta ke. Take-away suka yi na KFC kafin su
shiga gida don already dare ya yi, kuma duk yunwa suke ji mai girkawar ma Mummy ta gaji tibis.
Tun a lokacin ta soma regrettingkorar Easther da yanzu kafin su dawo sun tadda komai yana
jiransu a kan dining. To wai ma da ta yi gaggawar korar Easther how sure is she (wane tabbaci
ta ke da shi na cewa) Aalimah ta iya girkin da za su iya ci har mijinta? Damuwa karara ta
bayyana a kan fuskarta har suka shiga gida.
Kafin su kwanta, suna zaune a falo tare da yaran, Daddy ya ce, “Zulaiha ina tunanin daukar
wa yaran nan driver, Basma ba ta kai shekaru sha takwas baballe ta dinga tuka su. Duk da
Aboulkhair is coming for his holiday next month bana jin zai juri jigilar kai su da dauko su da

wannan baccin safen nasa. Hanya ta da tasu are parallel (sun baude) ina makara most often
(sau-tari)â€.
Da sauri Mummy ta ce, “Ka san bana son strangers Daddy, ka bar zancen daukar driver din
nan don Allah. Ni zan dauki nauyin kai su da dauko su dukkaninsu. Na gama course din da
office suka sanya ni yi a Worcesterkarfe hudu zan dinga dawowa, kuma zan zauna wata guda a
gida kafin na koma office so I will take care of their transportationâ€. Cike da gamsuwa ya gyada kai sannan ya dago ya dube ta yana murmushi.
“Promotion in progress… Ummu Mu’az, wannan karon ya kamata a cire min
parcentage, kudi sun yi miki yawa matar nan kuma ba mai ci, ke kanki ban ga kina ci baâ€.
Dariya ta yi cikin nishadi ta kada masa kyawawan idanunta,
“Kai ma ka san wa nake tarawa.
I want him to own a lodge in one of the America’s most expensive luxury condos. Be it in
San Francisco, Miami, Los Angels, Dallas, Seattle, New York, Oahu, Ohio, Chicago, nan
Massachusetts, or wherever he like. A penthouse; irin wanda ko a garuruwan nan dana ambata
sai dan gata zai iya mallaka. Ka san Allah Daddy ba don kaina nake wahalar aikin nan ba.
I’m doing it for “MU’AZZAM†da lafiyarsa, tunda na lura shi in don ta shi bai damu
ya tara komai ba.
Abin da ya sani kawai shi ne, ya yi ta bautawa wannan aikin nasa, yana karar da kudin a gidan
haya, bayan wannan ban san me Mu’azzam ke yi da kudin da yake samu ba. I’m
sometimes wondering he belongs to CHEVRON (wani lokacin ina tababar kasancewarsa
ma’aikacin CHEVRON)â€. Murmushi sosai Daddy yake yi yana sauraronta da mamaki. Ba tun yau ba ya sani,
Mu’azzam is her favourite childcikin ‘ya’yanta, amma bai taba sanin abin ya kai haka
ba. Ta ci buri mai girma a kansa.
Wato duk tsayin shekaru goman nan da ta dauka tana aiki da JP Morgan Chase yana mamakin
me ta ke yi da kudinta, tunda duk bukatunta babu wanda ta taba dauke mishi, sannan ya san ba
iyayenta ta ke kaiwa ba, don shi ne ya gaji da ganinsu cikin tsohon gidan da suke ciki ya sauya
musu, hatta petir din da za ta zuba a mota yana wuyansa, ashe this is her dream! Gyara zama
ya yi sosai ya fuskance ta, ya kira ta da sunanta na yanka,
“Zulaihatu!â€
Wannan ya tabbatar mata maganar da zai yin is highly sensitive. Bai damu da amsawarta ba,
ya ce, “Ki fidda ZAKKAH, ki yi sadaka, ki kai iyayenki Hajj da duk wanda ya kamata cikin
‘yan uwanki. Sannan ki ninka kyautatawarki gare su.
Ba’a san gawar fari ba, amma use your opportunity when it is in your hands (wani lokaci na
zuwa da za ki so ganinsu ko sau daya, amma zai zamo ba sa raye, ki yi amfani da damarki a
lokacin da ta ke hannunki). Mu’azzam baya neman agajin ki a halin yanzu, domin ya riga ya
tsaya a kan duga-dugansa. Abinda yake bukata daga gareki shine kawai ADDU’A da sanya
albarka. And thank Allah the exalted for making you two alive together,which is his foremost
success in life(kuma ki godewa Ubangiji Mabuwayi da ya raya ku tare, wannan shine babbar
nasarar sa a rayuwa). Wannanita ce shawara ta gare ki a matsayina na mijinki, uban
‘ya’yanki,wanda ya fi kowa kaunarki in an cire iyayenki. Besides, this boy is making a lot
of money beyond your expection (ta wani gefen, wannan yaron yana samun kudi fiye da
tsammaninki). Yarage naki ki dauka ko kada ki dauka. Ina kara maimaita miki

cewa(Mu’azzam ba ya bukatar kudinki don ya tsaya da kafafunsa, abin da yake bukata shi
ne, KE din kanki a raye, da addu’o’inki.
Yana gama fadin hakan ya tashi ya hau sama ya barta a nan tana ta karanta wasikar jiki. Tana
analysing kalamansa filla-filla.
*****


Kamar kullum washegari suka yi wanka suka shisshirya. Mummy Zulaiha ta zo har dakinsu ta yi
kiran Aalimah. Tare suka fita ta nuna mata duk yadda ake amfani da injinan cleaning din gidan,
da yadda ake tsaftace shi. Sannan ta tambaye ta ko ta iya girki? Ta ce ba abin da ba ta iya
girkawa ba. Sai ta ce, har English meals? Ta ce, ta iya wasu a wurin Mamanta. Sai ta ce, to shi
kenan daga yau ita za ta dinga girki da cleaning, mai aikinta ta yi tafiya. Tana kuma son kullum
ta gama abincin dare kafin dawowar Daddy. Tana kuma son wannan zancen ya tsaya a
tsakaninsu. Incase su Basma za su tambaye ta wani abu a kan hakan, ta ce, ita ta sa kanta.
Aalimah ta yi motsi da bakinta tana so ta tambaye ta makarantarta kuma fa? Amma ganin ba
fuska dole ta hadiye. Tun a lokacin ta fara girkin rana bayan MummyZulaiha din ta nuna mata
yadda ake amfani da komai.
Ta yi cleaning, ta yi girkin rana, ta yi na dare. Ko na minti biyu ba ta huta ba. Da suka tambaye
ta ko me ta ke yi haka tun safe? Ta gaya musu yadda uwarsu ta gaya mata. Ta kara da cewa,
Easther ta yi tafiya shi ya sa ta ke taimaka wa Mummyn. Allah ya so tun farko Mamansu ta hore
su da komai, ba ta da son jiki ko kankani. Ranar litinin, wato washegarin ranar,Mummy Zulaiha ta kwashe ‘ya’yanta ta kai
makaranta, ta bar Aalimah a kitchen. Mamaki ya kama su har hada baki suke wajen
tambayarta,
“Aal, will not go to school Mum?â€
Ta lailayo ashariyar da ba su san ta iya ba ta antaya musu, ta kuma ce duk wanda ya kara yi
mata zancen wata “Aal†ubansa za ta ci ciki da waje. Ta cire ta daga makarantar don
ubansu, su je su gaya wa ubansu su ga yadda za ta ci mutuncinsu. Duk suka yi lakwas. Zaginta
da balbalin bala’inta ya fi karfi a kan Basma, ta ce ta san ta fi kowa firirita a kan wata Aal, to
in ta isa ta je ta gaya wa ubanta RAAZEE ISHAQ ta cire Aalimah daga makaranta.
Hatta abokan karatun Basma sun fahimci yau ba ta cikin walwala. Wadanda suka damu har
tambayarta suke yi, me ke damunta? A gajarce ta ke cewa, “Headacheâ€.
Da yamma motar makaranta ta bi ta koma gida, Mummy ta ce su Khaleesat kawai za ta dinga
maidawa gida, she’s old enough ta kula da kanta (Basman).
Ko da suka dawo a kitchen suka tadda Aalimah ko wanka ba ta samu ta yi ba saboda aiki. Har
wanki Mummy ta jibga mata don ma dai da inji ne. A ranta ta ce, in kin ji wuya za ki koma inda ki
ka fito.
Idanu narai-narai da hawaye Basma da ke tsaye a bakin kofa ta ke kallon Aalimah, wadda duk
ta yi gumi ta yi maiko, ta takarkare sai kankarar tukunya ta ke da cokali tana ci, abinci cokali
daya wannan Mummy ba ta bata ba, duk da ita ta yi girkin. Tazo ta kwashe shi tsaf ta kai
‘dining’ kuma ta kasa-ta-tsare a falon tana ta ayyukan ta cikin system dinta, bata bari
Aalimah ta ganta ba ta bar wurin da sauri ta yi sama da gudu, ta fada gadonta tana hawaye. Me
za ta iya a kai banda fada wa Daddy? Babu!

Haka suka wuni dukkansu sukuku da su cikin damuwa da mamakin Mummy. Su dai sun san ko
a cikin iyaye tasu uwar is exceptional wajen kyautata wa ‘ya’yanta. Yaushe ta canzazuwa
maketaciya?
Rayuwar da suka yi ta yi kenan har tsayin wata guda, sai Daddy zai dawo ta ke cewa ta je ta yi
wanka, sai za a zauna cin abincin dare za ta samu ta ci. Amma ba ta da breakfast ba ta da
lunch. Sai karshen mako kuma, shi ma don Daddy na gida tana da freedom duk da haka komai
ita ta ke yi, bai taba lura ba. Yanayin abincin gidan ne kawai ya lura ya canza, kuma ya fi jin
dadinshi a kan na baya. Kuma da yake Allah ya yi shi mutum mara sa ido ko bin kwakkwafi, bai
taba tankawa ba. Sakin ciki yake ya ci iyakar cinsa.

Karatu fal! Ya yi wa Aalimah fintinkau, ya wuce ta, an bada assingments har ba adadi ba ta yi ko
daya ba. Absentness dinta da ya yi yawa shi ya sa coordinator dinsu da wasu daga cikin course
tutors suka ankara. Makarantar ta yi tracingguardian phone number dinta a file dinta suka yi
mishi phone call officially.
Ina kwalin digiri da masters din Mummy Zulaiha ya je ta manta da hakan zai faru? Oho!
She’s blindly chasing a way to push poor Aalimah from her house. Ta manta an ce rana
dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya.
Karfe biyu na rana Aalimah tana kwashe abincin da ta gama girkawa a warmers, Mummy
Zulaiha tana sama bedroom dinta tana barci abinta hankali a kwance. Kuka ta ke yi mara sauti
tana share hawaye da hanci da gefen mayafin da ke kanta. Ba tana kuka ne don aikin da
Mummy ke jibga mata ba wanda ko makaho ya shafa ya san ya fi karfinta ita kadai, ko kukan
yadda ta kasa treating dinta kamar ‘ya’yan da ta haifa ba, tana kuka ne na tausayin
kanta da iyayenta. Sun hana idonsu barci, sun yi fafutuka sun kawo ta don ta yi karatu an raba
ta da shi a banza a daidai lokacin da ta fara fahimtarsa, kwakwalwarta ta bude ya soma shiga
kanta, an maida ta boyi-boyin gida on no reason. Ba ta son zama sanadin kawo commution
tsakanin ma’auratan, amma da ta ce da kawunta ya maida ita hostel tunda ita ta fahimci
Mummy Zulaiha zamanta a gidan ne kawai ba ta so.
Ba zato ba tsammani sai ganin Daddy ta yi a tsaye a bakin kofa, ya dogara hannunsa na dama
da kofar kicin din. Ta yi nisa a kukanta, shi ya sa ko motsin motarsa ba ta ji ba.
Daddy ya jima a tsaye a bakin kofa yana kallon Aalimah ba tare da saninta ba, ba kuma tare da
sanin shi kansa mintuna nawa ya ba ta a wurin yana nazarin abubuwan ba. An ce four weeks
rabonta da school, ya zo ya same ta tana girki a kitchen. Wannan na nufin duk abincin da suke
ci tsawon sati hudun da ya fahimci canzawarsa ita ce ke girka shi? Wannan ne dalilin Zulaiha na
korar mai aikinta, ta kuma hana shi daukar driver da ya ce zai daukar musu? Ba ya so ya yardar
wa zuciyarsa Zulaiha ta aikata hakan da gan-gan, kuma za ta iya cin amanarsa har haka.
Ba zai yi saurin yanke hukunci ba sai ya ji daga bakin kowaccensu. Shigowa kicin din ya yi ya
kama hannunta ya ja ta suka fice daga gidan, kafarta ko takalmi babu. Da fari ta tsorata, amma
da ta ga Daddy ne sai ta yi shiru. Kukan ma bakidaya ya dauke. Ta san yau dubun Mummy ce
ta cika tunda yanzun ba lokacin dawowarsa ba ne. Za ta yi amfani da wannan damar ta roke shi
ya maida ita hostelno matter what. Yau da a ce zama ne ya kawo ta gidan ba karatu ba,
she’s willing to do beyond what Mummy wants from her… ita ma uwa ce a gare ta kuma
uwarta ma tana sa ta aiki, amma ba ta hora ta da yunwa. Daddy murfin chevrolet dinsa ya bude

ya sanya ta a gaban motar, ya zagayo ya shiga mazauninsa a nitse ya fita daga compound din
gidan nasa suka hau titi.
Sun yi tafiya mai nisa ba tare da ya ce komai ba, ita kuma ta yi kokari ta daina kukan da ta ke yi
ta tsane hawayen idanunta tsaf! Amma kallo daya za ka yi mata ka fahimci ta ci kuka ta koshi,
abinka da farar mace, fuskar nan ta yi jazur kamar jini zai fito. Sai daya yi nisa da unguwar su
‘Martha’s Vineyard Real Estate’ sosai sannan ya gangara ya sauka a gefen titi. Yadda fuskarta ta yi jajawur saboda kuka haka tashi ma ta yi, duk da shi ba kukan ya yi ba.
Tsananin bacin rai ne ya maida shi hakan. Ba Zulaiha kadai ya ji matukar haushi ba, har ita
Aalimahn. Cikin fada ya soma yi mata magana cikin harshen su Temachek. Ga abinda yake
cewa. “Me yasa baki gaya min ba ta kai ki makaranta ba?â€
Shiru ta yi, don ba ta san amsar da za ta ba shi ba. Mummy ba ta bata damar hakan ba,
‘ya’yanta ma sun kasa gaya masa balle ita? Idan ya dawo Mummy kasawa ta ke ta tsare
har sai ta tabbatar ya shiga dakin barcinsa ya kwanta. Ko ba don wannan ba baza ta iya hada
shi fada da matarshi da ta zo ta same su suna zaune happily da ‘ya’yansu, sannan tun
washegarin ranar da Mummy ta ce zata dinga driving dinsu ta karbe wayarta data bata daga
cewa za ta debi wasu muhimman contacts dinta da ke ciki, ba ta dawo mata da ita ba, and she
lacks the courage to ask her again (bata da karfin gwiwar sake tambayar ta) tunda ta san
wayarta ce.
Ko iyayenta da Yaya Aboubacar ba ta kira ba a tsayin kwanakin nan kusan talatin. He trust his
wifeso much(ya yarda da matarsa sosai) ta yadda har ya daura mata alhakin kai su da dauko
su.Howcould she told him that his wife is a green snake? (Ta yaya zata iya gaya masa cewa
matar tasa macijin sari-ka-noke ce?â€. Jin ta yi shiru,sai ajiyar zuciya kawai take yi, sai kuma ya sassauta daga fadan da ya ke yi mata.
“Gaya min kin ji ‘yata Aalimah, me ke faruwa a gidan da ban sani ba? Ya ya aka yi kowa
yana zuwa makaranta banda ke? Kada ki ji tsoro ki gaya min ba abin da zai same ki. Sai na ji
gaskiya daga bakinki ne zan san matakin da zan daukaâ€.
Sosai ya ke lallashinta, yadda Daddynta ke yi in yana so ya ji cikinta. Kuka ne ya kufce mata, ta
soma yinsa sosai.
“Na roke ka da Allah Daddy ka maida ni hostel, Daddy da Mama zuciyarsu za ta karye, in
na kasa yin karatun nan. I’m not here to stay at home. I’m here to study, don Allah
Daddy â€.
Shiru ya yi zuciyarsa har barbawa ta ke yi sabida bacin rai. Daga bisani ya ce,
“Ina wayarki? Me ya sa ko text ne ba ki yi min ba in kin kasa kira na?â€
Cike da fargabata ce,
“Ta karbi wayartaâ€.
Wuta ta dauke masa na dan lokaci, kafin ya ce cikin sanyin murya.

“I’m sorry my daughter, I failed to fulfill my responsibilities as a father. But that
doesn’t mean negligence, it’s because I trust my wife so much on everything, (ki yi
hakuri ‘ya ta, na gaza wajen cikasa hakkokina na Uba a gareki cikin gidana, saidai hakan
baya nufin ‘sakaci’, a’ah, na yi ne sabida na yarda da mata ta akan komai. Ban taba
zaton za ta iya yi min haka ba.

Na san ba ta son mutane, amma ban zaci har haka ba tunda ba yau muke tare ba. Kada ki kara
zancen hostel din nan while I’m alive, living in America. In mutane ba su zage ni ba, Allah
zai tambaye ni hakkin zumunci. Sai ka kyautata shi za ka shiga aljannah. Give me one last
chance...(ki bani dama ta karshe)zan gyara komaiâ€.

3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM - Buhainat: 🌹 *Aalimah* 🌹
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870*

FREE PAGES 5

Tsakaninsa da Aunty Zulaiha babu mu’amala mai dadi, duk wannan soyayyar da ake masa
an yi wurgi da ita. Yana tambayar kansa da ma haka ta ke? Ita shin meye matsalarta da zaman
‘yar dan uwansa ciki daya a gidan? Shi ya sha nono ya sakarwa ubanta! Inda hankali da
tunani Zulaiha ba za ta yi masa abin da ta ke yi ba don ya kawo ‘yar Mansour gidansa.
Wacce irin kulawa ce ba ya bawa nata dangin? Yana son Zulaiha matukar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login