Showing 33001 words to 36000 words out of 128821 words

Chapter 12 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf


bahaushe, wanda Mamansa ba ta sanshi ba. A gaban kowa, kiri-kiri ta ke nuna son
‘ya’yanta da nuna babu ya su a duniya. Su ne kadai ‘ya’ya. Sannan ya kira Yaya
Aboubacar.
Aboubacar sa’an Aboulkhair ne, bai fi watanni biyu Aboulkhair ya ba shi ba. Don haka hira
sosai suka yi, irin ta ‘yan uwa. Ya ce ya gaida Aalimah duk da ba a fi kwana biyu ba sun yi
magana shi da ita.
Yau dai Aboulkhair ya yi wa kamfanin wayarsa na VERIZON ciniki mai dumbin yawa, don bayan
gama wayarshi da ‘yan gidan su Aalimah ‘yan Nijar ya hau kira, duk wasu manya a dangin
ba wanda bai kira ya wanke kansa ba.
Inna Kasisi na yi masa tirjiya da hutsancinta, haka ya yi ta lallashinta har ta ware suka yi hira.
Ya yi mata alkawarin he will keep calling kuma zai zo Nijar next hutunsa. Albarka kuma ya sha
ta wajen malam da manyan Uncles dinsa. Ba su da riko ko kadan sai kaunar junansu. Ya kuma
yi mamakin matsayin da Mu’azzam ke da shi a family dinsu. Ya raina kansa, don ba wanda

zai yi magana da shi har ya kare bai tambayi Mu’az ba, bai fada mishi alherin da yake masa
ba. A karshe da ya gama wayar Mu’azzam din ya kira. Yana dagawa cikin sauri ya ce da
shi,
“At office, call laterâ€.
Murmushi ya yi yana jin kaunar Yayan nasa na kara ratsa shi.
A fili ya ce,
“Ni ma ba wani abu zan ce maka ba. I just want to hear your voice, (kawai ina son jin muryar
ka ne) kuma na jiâ€.
6/28/21, 7:32 AM - Buhainat: 185


Zuwa lokacin azahar ta yi, dakinsa ya koma ya yi sallah, ba ya bukatar abinci don haka ya je ya
yi sabgoginsa a cikin gari zuwa lokacin da Aalimah ta gaya masa tana da sarari. Yana yin
parking kuwa ya gansu suna fitowa, daga dakin laccar tana rungume da folder.
Tsura mata ido ya yi tana nufo motarshi. A zuciyarsa tambayar kansa yake yi, me ya fi so a
Aalimah? A gaggauce amsar ta halarto zuciyarsa… Yana son komai nata… komai ta yi abin
burgewa ne a idonsa. He loves her dearly.
Har ta shigo ta zauna a gefensa bai sani ba. Sai da ta hada yatsunta biyu suka yi kas! A
kunnensa. Kallonta ya yi, sannan ya dauko wayarta daga inda ya ajiye ta ya lalubo lamba ya
danna kira. Ba ta ankara ba ta ji muryar Mahmoud na amsawa da sallamarsa, yana tambayar
ina ta shiga kwana biyu? Kafin ta kwace wayar ya bada amsa, “Ba ita ba ce, mijinta ne, kuma Yayanta, wanda ya bada sadakinta ga iyayenta. This is for
your information not to call or text my wife againâ€. Ya datse kiran.
Aalimah ta ji ba dadi har fuskarta ta nuna.Mahmoud yana da mutunci a idonta ko don Yaya
Aboubacar. Ko rabuwa za ta yi da shi ba za ta so su yi irin wannan rabuwar ba.
Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta don ganin reaction dinta, amma ya kasa fahimtar komai
ban da rashin jin dadin da idanunta suka nuna. Magana ta yi a hankali cikin rarrashi don
fahimtar cewa so yake su yi rigima.
“Haba Yayan Basma? Abokin Yaya Aboubacar ne kuma…..†Ta yi shiru ta kasa ci gaba.
“…... Kuma saurayin kiâ€, yayi maza ya karasa mata. “Kawai ki fashe da kuka na raba
ki da saurayinki…â€.
Turo baki ta yi cikin shagwaba, “…Ni ba saurayina ba ne, cewa zan yi muna mutunci ni da
shi fa… Ni ba ni da saurayi…â€.
Ganin yadda yake kallon bakin nata admiringly ya sanya ta maida bakin nata ta kintse, ta kuma
sunkuyar da kanta. Murmushi ta shiga saki kasa-kasa a sanda ya sanyaya murya ya ce da ita,
“Har NI?â€
Tafukanta ta kai ta rufe fuskarta tana murmushi,
“Kai ma Yayana neâ€.
“Ko?†Ya tambaye ta.
Bai jira amsarta ba ya ci gaba, “Za mu bambance hakan ranar da aka daura mana aureâ€.
Ta kara tusa fuskar tata cikin tafukan nata, cikin matsananciyar jin kunya.
Wayarta ya jefa mata kan cinyarta ya tada motar, “Na bude miki Whatsapp, Daddy ya
amince min in dinga magana da ke ta waya, daga yau har zuwa ranar da zai karbi sadakinki.

Idan ki ka yi chatting da wannan mutumin Allah ya isaâ€.
Dariya ta soma yi tana fita daga motar. Ganin yadda yake maganar with confidence kamar ta
furta masa tana sonshi ita ma. Tana son mutum mai courage, wanda ya iya yarda da kansa.
Ko da ta koma class ta bude littafin da ta ke rubutu, samun hannunta ta yi da rubuta haruffan
guda tara, ‘A…B…U…L…K…H…A…I…R, ta zagaye su da zanen zuciya (heart).
Kafin ta ankara cewa a cikin littafin daukar laccarta ta ke yi. Hannu ta kai ta dafe goshinta tana
ambaton sunan Allah, me ke damuna ni Aalimah? Me ya shiga kaina? Me zuciyata ke nufi da ni
a kan Yayan Basma? Ina zan kai Mahmoud wanda ke can wata duniya yana jirana? To amma
me? The feelings are entirely not equal! Ko kusa da juna ba su zo ba, infact, abin da ta ke ji a
kan Aboulkhair ba ta taba jin irinsa a kan kowa a duniya ba.

******
Shi ya dawo ya dauke su. A kofar gida bayan su Basma sun fito daga mota ya dakatar da ita.
Tsare gida ya yi sosai, sannan ya jefo mata tambaya.
“Will you call him (Za ki kira shi)?â€
Da lumsassun idanunta masu gazar-gazar eye-lashes ta dago ta dube shi. Ita ma ta jefa masa
tambayar, “Who?â€
Don ita shaf! Ta manta sun yi zancen Mahmoud dazu.
Runtse idanunsa ya yi ya kasa budewa, shi kadai ya san kishin Mahmoud da ke cinsa a zuci.
Bai sani ba ko bayan lambarsa da ya goge daga cikin wayarta ko ta haddace lambar a cikin
kanta. He don’t know how intimate they are. Daga yadda Mahmoud ke magana da kuma
sakonninsa da ya karanta ya fahimci sun jima tare, kuma ta saba kiransa. Wannan tunanin ya
tsaye masa a zuciya ya hana shi sukuni. Wani zazzafan so yake wa Aalimah, wanda shi kanshi
yake ba shi tsoro.
Sai da fuskarsa ta yi jajawur sannan ya ce da ita,
“Saurayinki!â€
Murmushi ta yi ta dauke idonta a kansa, sannan ta ce, “Ba zan iya sanin cewa zan kira shi
ko ba zan kira shi ba, sai ka gaya min sunan budurwarkaâ€.
Bata fuska ya yi ya yamutse ta abin dariya kamar wanda aka nunawa kashi.
“But, I don’t have, I have only friendsâ€.
Murguda masa baki ta yi ta fice daga motar, sai kuma ta dawo ta zura kanta ta tagar murfin
motar a hankali ta ce,
“Ni ma Mahmoud abokina ne!â€.
Da gudu-gudu ta bi bayan su Basma ganin yadda yanayin fuskarsa ya canza bakidaya. Tana
tsoron ya kife ta da mari, duk da ta san ba zai yi hakan ba.
Ficewa ya yi da motar ya fasa shiga gidan. Yana fitowa mota kirar Rolls Royce ta sanyo
hancinta harabar gidan, wadda ke cike da korran shuke-shuken grass carpet. Tun daga nesa ya
gane ko motar waye, “Mummyâ€. Fasa zuwa inda ya yi niyya ya yi, ya yi reverseya dawo da
baya. A tare suka yi parking a harabar adana motocinsu, suka kuma fito a tare. Da sassarfa ya
karasa gare ta ita ma ta taho suka hade, ta rungume shi. Sun dade ba su ga juna ba, kewar mai
yawa ce. Duk da yana kallon mahaifiyarsa matsayin mai laifi ga rayuwar mahaifinsu, hakan ba
ya nufin matsayinta ya canza a zuciyarsa ko wani abu makamancin hakan. A mother is always
a mother!

Tana rike da hannunsa suka shiga gidan, su dai su Basma, Aalimah, Khaleesat da Yesmin sai
ganin Mummynsu suka yi a tsakiyar falonsu. Wani ihun murna da kowaccensu ta saka ta yo kan
Mummyn ta rungume ta, ba ka jin komai sai kalaman kewar juna da soyayyar junansu.
Aalimah ta koma gefe tana kallon soyayyar UWA da ‘ya’yanta, wata irin kewar iyayenta
ta kama ta. Ta koma gefe ta rakube kamar marainiya.
Sam ba ta ga tahowar Abulkhair gare ta ba. Hannunta ya kamo ya soma janyo ta har gaban
Mummy. Ta gintse farin cikin da ke kan fuskarta lokaci guda. Duk wata fara’a da ke kan
fuskarta sai ta dauke. Girgiza mata kai Abulkhair ya shiga yi, sannan cikin nutsuwa ya soma
magana. “Mummy, Aalimah is saying welcome back to youâ€.
Aalimah ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na son zubowa. Kamar Anty Zulaiha ba za ta yi
magana ba, sai kuma kwarjinin dan nata da ya kafe ta da kyawawan idanunshi ya cika mata
ido.
Ta sassauta grinning din fuskarta, ta ce, “Ita ba ta da baki? Ko kai ne bakinta?â€
Aalimah ta zube a kan gwiwoyinta a gaban Mummy Zulaiha cikin sanyin murya ta ce,
“Welcome Mummy. And I’m sorry if I hurt you. I’m very sorry!â€.
Aunty Zulaiha ta dan rufe idanunta, sannan ta bude ta dubi yarinyar. She’s innocent, tana
da innocence looks. She’s looking just like her husband kamar shi ya haife ta. Yanayin su
na sanyin hali iri daya ne. Wannan ya sa ta ke kama da su Basma. Tunda ta zo ba za ta ce ga
wani abu da ta yi da ya bata mata rai ba. Tana shaping tarbiyyar su Basma ne kawai, ba lalata
su ta ke yi ba. Sunkuyar da kanta ta yi kasa.
Basma ta ce, “PleaseMum talk to Aal, she’s our sisterâ€.
Khaleesat ta ce, “She is nice Mummy, she cooks for us, she’s taking care of us very
well in your absence (ki yi mata magana Mummy ‘yar uwarmu ce)â€. In ji Basma (tana da
kirki Mummy, tana dafa mana abinci, tana kula da mu da ba kya nan sosai)â€. In ji Khaleesat.
“And she bought for me sweets alsoâ€. In ji Yesmin.
Duk sun daure ta da jijiyoyinta. Ko ita ce tafi kowa rashin adalci a duniya. Sai ta mika hannu ta
kama hannun Aalimah. A hankali ta ce,
“Thank youâ€.
Dadi ya kama sudukkansu, kar dai Abulkhair ya ji labari. A haka Daddy ya shigo ya cimmasu.
Tsaye ya yi a tsakiyar falon ya kama kugu yana kare mata kallo. Ga hannunta cikin na Aalimah
shi ne abin da ya dan sanyaya zuciyarsa. Sama ya wuce rike da suitcase dinsa ba tare da ya ce
da kowa komai ba. Mikewa Mummy ta yi ta bi bayanshi, yaran kuma kowacce ta kama sabgar gabanta cike da farin
ciki. Aalimah ta mike za ta shiga kitchen suka hada ido da Abulkhair da ke zaune a kan daya
daga cikin kujerun dining table ya zuba mata ido. Wani irin sonshi da kaunarshi ya kara
mamaye ta. Murmushi ta hau yi masa ba ta san tana yi ba, ya wani dauke kai ya juya mata baya. Sai a
lokacin ta tuna ashe fa fushi yake yi da ita ta yi masa laifi. Karasawa ta yi kicin don yin abin da
ta nufa, amma sai ta ji duk ta damu, zuciyarta ta yi mata babu dadi da fushin nasa.
Da ta fito daga kicin din kuma ba ta same shi a falon ba ya fice ya bar gidan. Tana jiyo hucin
motarsa don ba za ta ce kara ba. Motocin Daddy are not making sounds wato (ba sa kara).
A can dakin iyayen suna can suna tafka ta a tsakaninsu, Daddy ya ce, don me ta dawo masa

gida bai neme ta ba? Ta ce, saboda gidan mijina ne, gidan ‘ya’yana, kuma mijina ba
sakina ya yi ba. Nan kuma ta kwantar da kai ta shiga ba shi haquri har da kukanta.
Mikewa ya yi zai bar mata dakin ta kamo shi ta kankame, ta shiga rantsuwa tana daukar masa
alkawarin wannan karon ta dau laifinta, za ta canza ya ba ta dama, she has no business ( ba
ruwanta) da kowa nasa da duk wanda zai kawo gidansa. Cewa ya yi I’m tired(na gaji) da
tuban muzurinki.You will never change Zulaihatu, (bazaki taba canzawa ba) mai hali ba ya fasa
halinsa, I’m tired of all these, ya kamata mu bai wa juna sarari, har kowannenmu ya je ya yi
kwas a kan halin dan uwansa. Na kasa saninki fully har gobe, in na ci gaba da biye miki halaka
ni za ki yi…!â€
Yadda ta rungume shi cikin jikinta da runguma mai tsananin karfi, jikinta yana rawa da karkarwa
da jin kalamansa, shi ya hana shi karasa magana. They missed each other to such an extent…
don haka duk wani mai korafi ma a tsakaninsu ya adana korafin nasa a gefe zuwa gaba. Amma
ko daga yanayin Zulaiha a yau da yanayin bugun numfashinta ya san ta yi nadama wannan
karon, wadda yake fatan Allah ya sa ta dore. In kuma hakan bai yiwu ba, duk son da yake mata
wannan karon zai ba ta mamaki ta inda ba ta zata ba. Al’amarin mace da miji sai Allah,
cikin daren suka shirya kansu.
A can dakin su Aalimah kuma, kowa ya yi barci ya barta. Wayarta ce a hannunta tana jira ko
Abulkhair zai kirata? Ta kasa barci ko kankani. Ganin har karfe sha daya na dare bai kiratan ba
bai kuma yi mata sako ba ya tabbatar mata fushin nasa na gaske ne. Ji ta yi duk ta tsani kanta,
don me zata batawa mutum mai kyakkyawar zuciya irin Abulkhair? Mai sonka shi yake KISHIN
KA, shi ya damu da al’amarinka. To amma don me zai damu kansa da zancen Mahmoud?
Ya sa pressure sosai a kan zancensa. Ita ba ta dauki al’amarin Mahmoud da zafi ba, ba ta
yi masa alkawarin za ta aure shi ba amma yafi karfin wulakanci a idanunta.
Abin da ta san ta ce da shi shi ne, “We can not runaway from our destinies but she is hoping
that destiny tied them together (ba za mu iya gujewa kaddarorinmu ba, amma tana fatan
kaddarar ta barsu tare). To kuma ga kaddarar ta yi gardama. Kamata yayi Aboulkhair ya dubi
present dinta ba past dinta ba. Damuwa ta yi damuwa a zuciyar Aalimah, ta jefa zuciyarta cikin
wani yanayi mara dadi. Ba ta san ta kamu da son Abulkhair har haka ba sai yanzu da ta ke
ganin yana kokarin barinta kan abin da bai kai ya kawo ba a ganinta.
Da gaske Mahmoud ya fi kama da aboki fiye da saurayi a zuciyarta. Akwai sabo a tsakaninsu,
duk da shi ba hakan ba ne a tashi zuciyar. Amma a halin yanzu ji ta ke zata iya komai don ta
samu Abulkhair, farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa ya fiye mata komai, hada da wannan
karatun da ta ke yi kuwa, za ta iya barinshi in har barin nasa na nufin mallakar Aboulkhair a
matsayin miji.
Ba ta da masaniyar cewar Abulkhair ya sanya lambar wayarsa a ciki ya adana, sai ganin wani
lafiyayyen french word ta yi yana yawo a fuskar wayarta, mai nuna shigowar kira; Ma cherie,
wato My love da harshen faransa. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki ta yunkura ta mike zaune.
Sannan ta hau juyawa damanta da hagunta kamar munafuka tana kallon su Basma don
tabbatar da barci suke ko idonsu biyu? Ta tabbatar sun yi nisa a barcinsu sai ta lallaba ta shige
toilet da wayar a hannunta.
Zuwa lokacin kiran ya katse wani ya kara shigowa. Zama ta yi a gefen bath tube, sannan ta yi
sliding wajen amsa kiran.
“Not asleep like me?â€

Ta ji muryarsa cikin damuwa tana tambayarta.
“Ta ya ya zan iya barci kana fushi da ni Yayan Basma?†Muryar da ta yi amfani da ita
wajen yin maganar ta nuna zahirin damuwar da ta ke ciki.
Tana jin yadda Abulkhair ya sauke ajiyar zuciya, “Ban san kin damu da ni har haka ba, da
ban sa kaina cikin damuwa haka ba. I thought you love him, since you cannot erase him from
your memories, you want your relationship to continue…†( na zaci kina sonsa, tunda bazaki
iya goge shi daga tunanin ki ba, kina son alaqarku ta cigaba). Dan runtse ido ta yi, tone din muryarsa na kassara duk wani sauran kwarin gwiwar da ta ke da
shi na yi masa bayanin da zai kwantar da hankalinsa. Da kyar ta iya yafito sauti daga
makogaronta.
“He is not in my memories, he is where he is (ba ya cikin tunanina, yana dai inda yake). I
feel nothing for him†(bana jin komai akansa).
Abulkhair ya kara nitsewa cikin duvet dinsa. Murmushi yake yi wannan karon, duk wata
damuwar da ya sanya kansa ya neme ta ya rasa. Murmushin da ake kira daga kunne zuwa
kunne don fadinsa.
“Ni kuma fa? A wane bangare aka sanya nawa feeling din? Tunda na shigo gidan nan na
rasa kaina, na zama ba ni ba Aal, duk bugun da zuciyata za ta yi ke ce a cikinsa. Aalimah, I
want to say it loud I love you… ba zan taba komawa yadda na zo ba sai na samu amsar
bakinki. Ki gaya min komai kankantar kalmar da zan amince ba ni kadai nake wahala ba. Amma
in kin fi son wancan mutumin don Allah kada ki gaya min, it will go away with my last breath (zai
tafi da numfashina na karshe)â€.
Tun da ya fara magana Aalimah ke jin wasu bululluka da suka danne zuciyarta na rugurguzowa
suna kara dasa shi a zuciyarta. Zuciyar ta zama ‘yar shafal babu sauran damuwa a cikinta.
Lumshe idonta ta yi ita kadai ta ke blushing tana rufe ido tana budewa. Ci gaba ya yi da gaya
mata duk abubuwan da yake fama da su cikin zuciyarsa a kanta yana kuma rokon mafi
kankantar kalma daga gareta mai nuna kauna ko yaya a gareshi. Kwalla ta ji ta taru a idonta, ta
so da kaunar Abulkhair da kuma tausayinsa duka a lokaci daya.
Ta samu kanta a mai tambayar kanta me ta ke da shi da har dan gata irin Abulkhair

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login