Showing 75001 words to 78000 words out of 128821 words

Chapter 26 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

ya-kamata. Amma a nasu gidan bayan plate guda ma da one spoon suke
amfani. Aboubacar ya riga gamawa ya tashi ya nufi wurin iyalinsa, wadanda suke a dakin
Aalimah na gidan. Kamar jira Aboulkhair yake ya tashi, ya ajiye cokalinsa ya mike. Ya juya kofar
dakin Mama da alama ta kulle ta ciki duk da dai ya san ba ta yi barci ba. Hannun Aalimah kawai
ya kama ya mikar da ita. Za ta yi magana ya dora yatsa a baki, “Zo mu je, sako zan ba ki,
yanzu za ki dawoâ€.
Aalimah ba ta gane Aboulkhair so yake su bar gidan ba, sai da ta ji ta a motar Aboubacar, ya
tada motar da gudu, suka harba kan titi.
Kasa magana ta yi har suka iso gidan Basma. Ya shigar da motar cikin gate maigadin ya rufe ya
wuce ciki ba tare da ya bari sun hada ido ba. To amma ai ita ta san kan kayanta, a kwayar
idanunsa ta ke gano komai nasa. Kuma a yadda ta san halittar mijinta ta san ya yi kokarin da
bai taba yi ba tun bayan aurensu. Sai ko komawar saJohn Hopkins yin part two exams dinsa da
suka jima ba sa tare. Ranar da suka hadun kuwa, har gobe ba za ta manta yadda ranar ta
gudana gare su ba, with a fondest thought!
Girgiza kai ta yi cike da tausayin mijinta, ta fito ta bi bayansa. Tun a falon Basma
al’amuransa suka soma ganar da ita kewar tata da ya yi ba ‘yar kadan ba ce. Ba ta hana
shi komai ba, karewa ma samun kanta ta yi da ba shi hadin kai da zuciya da gangar jikinta
bakidaya fiye da na kowacce rana cikin rayuwar aurensu. Da wani irin feeling a zuciyarta da
ruhinta da ba za ta iya kwatantawa ba.
Gare shi jin ranar yau yake kamar ranar da ya bare ta a ledarta, komai nata ya kara canzawa
fiye da baya, sakamakon matashin cikin jikinta. Aalimah, na cikin sahun matan da ba sa taba
gundurar mazajensu sabida baiwar ni’imar da Allah ya yi musu, wanda ita kanta ba ta sani
ba, shi kuma ba shi da bakin furta mata hakan sai dai ta gani practically daga yanayin da yake
kasancewa a kullum suke tare, wanda ke kara mata kaunarsa.
Dukkaninsu ba su san sanda wani irin barci ya sure su ba, wanda ba shakka na gajiya ne,

saboda dukkaninsu sun taimaki juna ne ta hanyoyi da dama da ba su taba samun kansu a ciki
ba.
Karar wayarsa ce ta tashe shi, ya janye Aalimah daga kafadunsa ya ga Aboubacar ke kiransa.
“Ban tambaye ka inda ku ka tafi ba, kawai ku yi zamanku da asubah mu biyo mu dauke ka,
ita kuma ta dawo da kanta, ai ta san gariâ€.
Dariya Aboulkhair ya yi, wadda ta tada Aalimah daga nata daddadan barcin, suka soma shirin
barin gidan.
6/30/21, 11:09 AM - Buhainat: *I'm writing this chapter with heartfelt TEARS*
😭😭😭😭😭😭😭😭














Sanda suka iso karfe goma sha biyu na dare Aboubacar na kofar gida. Kasa fitowa daga motar
suka yi dukkansu duk da sanin da suke da shi na cewa Aboubacar zai iya hango su ta glass.
Hannunsa ya dora a kan cikinta yana sauraron harbawar jaririn yana lumshe idanu ya ce,
“Kin san wani abu?†Girgiza kai ta yi, haka kawai ta ji ranta ba dadi, kamar su koma gidan Basman su kwana tare. In
ya tafi Niger ita da ganinsa sai nan da kwana goma in an gama bikin Khaleesat, sannan ne zai
zo su koma. Ba lokaci daya za su tashi da ‘yan Massachusetts ba, su sai nan da sati biyu. Ko
dai ta kyale Basma ne ta bi mijinta ga kyawawan ‘yammatan nan na zuri’arsu da ba ta
san iyaka wadanda za su kalle mata shi ba? Wani bala’e’en kishi ya turnuke ta irin
wanda ba ta taba sanin tana da shi ba. Sabida a inda suke rayuwa ba ruwansu da irin
wadannan abubuwan kowa da life-partner dinshi ba mai shiga gonar wani. Ta girgiza kai, ba
tare da ya fahimci tunanin da ta ke ba, ya ce, “In namiji ki ka haifa ‘MU’AZZAM zan
sa masa, in mace ce, ‘AALIMAH’ (mai ilmi) yadda zan ji dadin gaya mata how sweet and
loving her mum is, how helping and generous she is, how much I truly love her and the long
time I spend waiting to marry her. Duka zan gaya mata Aalimah, idan kuma namiji ne zan gaya
masa yadda na rayu cikin soyayyar dan uwana mai lalura, yadda nake sonsa da burin samun
lafiyarsa. Yadda ya kyautata wa rayuwata, ya tsaya min against all odds. Ya mayar da ni abin da
nake a yau; Aboulkhair mai rayuwa da tsayayyun kafafu mamallakin Aalimah. Har ga shi za ta
samar da Da a gare mu ni da Mu’azzam…â€
A lokacin ya ankara Aalimah kuka ta ke yi.

“Mon Amour na fasa zama, tare za mu tafiâ€.
Dan tsayawa ya yi yana nazarinta gabadaya ta birkice kamar ba ita ba. Nazarin maganganun
da ya furta yake yi, ko akwai na tashin hankali a ciki? Iyakar tunaninsa bai gani ba. Kuka ta ke yi
shabe-shabe da hawaye da majina. Janyo ta ya yi jikinsa, ya ce, “Aalimahâ€. Sunanta na
hakika. “Nda’amâ€. Ta amsa cikin rishin kuka, don rabon da ta ji ya kira ta tun zamanin
samartaka (‘yammatancinsu).
“me na fada wanda ya bata miki rai?â€
“Babu komaiâ€. Ta amsa da sauri.
“To me ya sa za ki canza shawara cewa sai kin je Niger? You are kidding. Kada ki dauka
ban san halin da ki ke ciki ba, ko daga kumburarrun kafafunki. Kina wasa ne ma da ki ke
tunanin zan barki ki shiga kujiba-kujibar bikin nan na Niger, ki je kina girkin roti da rawa a wajen
cocktail, ki jawo min asarar da ban taba shirya mata ba! Don haka ki saki ranki kawai mu yi
rabuwar arziki ko a yi ta tsiya-tsiyaâ€.
Ba ta san sanda murmushi ya kubuce mata ba, ga hawaye face-face a fuskarta. Ba ta yi aune
ba ta ji Aboulkhair ya rungume ta, sai saukar harshensa a fuskarta yana dauke hawayen
salla-salla daga kan fuskarta. Idanun kuwa har wani side su yake yi.
Aboubacar da ke gefe yana waya da Basma yana jiran Aboulkhair ya sallami Aalimah su tafi,
gefen idanunsa ya dan hasko masa abin da ke faruwa. Da sauri ya yi cikin gida yana bai wa
Basma labari, ta kai yatsunta ta rufe fuskarta wai tana ji masa kunyar abin da ya gano. Sai jinsa
ta yi a nata kumatun yana fadin, “Bari in nuna miki yadda suke yiâ€. Aboukhair da Aalimah ba su rabu ba sai karfe daya daidai na dare. Tana tafiya zuwa cikin gida
tana waiwayonsa da murmushi, yana tsaye jikin motar Aboubacar shi ma murmushin ya ke
mata. In ba ta yi kuskure ba ba ta taba ganin irin wannan kasaitaccen murmushin daga gare shi
ba.
*****
Daddyn Aalimah, Daddyn Aboulkhair, Aboubacar da Aboulkhair afilin jirgin saman Malam Aminu
Kano, fuskokinsu cike da takaici da bacin rai. Wai babu jirgi mai zuwa Niamey a yau sakamakon
lalacewar jirgin da suka yi booking din a safiyar yau, yana can Niamey ma bai taso ba ana
gyara shi. Aboubacar ya duba agogon hannunsa, ya ce, “Daddy, da wannan zaman cinye lokacin da
muke gara mu je mu bi mota. Tafiyar awanni goma sha biyu cif nan gaba za ta kai mu Niamey.
Yanzu karfe takwas na safe, in muka yi sauri muka dauki hanya zuwa tara na safe za mu isa
Niamey nan da karfe tara na dare. Za kuma mu samu daurin aure a kan lokaciâ€. Duk sun yi na’am da wannan shawarar, Daddyn Aboulkhair ya ce, “Aboulkhair is a very
good driver, na tabbata kafin lokacin ma mun isaâ€.
A gurguje suka dawo gida suka yi wa Mama bayanin canjin da aka samu. Ba su bata lokaci ba
suka dauki sabuwar motar Dr. Mansour kirar Jeep 2015 model, Aboulkhair ya tada ita suka
shisshigar da kayansu, sannan Aboubacar ya shiga gaba, iyayen suna baya su biyu. Ko su
Aalimah ba su san da wannan sauyin da aka samu ba, ba sa gidan dukkaninsu tun sassafe, ta
raka Basma asibiti, Hassana (Zulaiha) na fama da mura, Hussainar sunan mama aka sa mata
(Aseeya).

Sai da suka shiga gidan mai suka yi full tank, sannan suka dauki hanyar jamhuriyyar Niger.
******
Mummunan hadarin motar ya afku ne kafin a kai boarder din da ta raba iyakar kasar Najeriya da
jamhuriyyar Nijar, bayan sun tsallake garin Jibiya sun shiga boarder din kasar Nijar.
Wasu gungun fulani ne makiyaya suka koro shanu a kan titin za su tsallaka. Ga direban Jeep
din ya kwararo motar da gudu irin na neman biyan bukata. Burinsa su shiga Niger kawai kafin
azahar a kalla ya san suna cikin kasar ainahinta, inyaso su yi sallah su ci abinci su durfafi
Niamey ba tare da sun bata lokaci ba. Shanun sun taho fal da gudunsu, shi ma ya shararo motar, sai ya ga bari ya dauke kan motar
da azama tunda daya titin babu mota ko daya, ba tare da lura da cewa wata karamar mota ta
taho ita ma a guje ta bayansa ba, kawai ta ga motar a kan nata titin ba tare da ta tsammata ko
ta ankara ba. Kafin direban karamar motar ya yi tunanin abin yi, ya yi mugun taho-mu-gama da
bakar Jeep din wanda hakan ya sanya duka motocin biyu fara katantanwa a tsakiyar babban
titin kafin a karshe su duka biyun su hantsila wani katon rami a gefen titin. Ba ka jin komai sai
hailala da salatin mutanen da ke cikin motocin cikin mika wuya ga hukuncin mahaliccinsu.

******
Da asubahin ranar Hassana da Hussaina suka ci gaba da ruda gidan da kuka, wanda suka
kwana suna yi suna hutawa. Tun daren jiya sun ki karbar nono. Daga Basma har Aalimah babu
wacce ta runtsa, suna fama da yaran nan saboda mama na can dakinta kwance babu lafiya, ta
ce kuma takamaimai ba ta san inda ke mata ciwo ba, amma ko hannunta ta kasa motsawa balle
ta zo ta taimaka musu. Daga kwance ta ce su dinga yin addu’a suna tofa musu.
Basma gefe ta koma ta zuba tagumi, nonuwa sun mata suntum suna ta sukarta suna kuma
diga, duk sun jika gaban rigarta. Aalimah na so ta yi sallar asubah don har masallacin kusa da
su sun idar, yaran duka biyu suna hannunta tana jijjaga su, ta san in ta ajiye su Basma ko taba
su ba za ta yi ba. ta zama dumm! Kamar wadda ta samu ciwon kurumta na lokaci mai tsawo. Aalimah ta ajiye daya ta goya daya. Rabonta da goyo tun haihuwar Aunty Gumsu. Tunda aka
sallamo Basma Mama ke goya su, ta zura hijabi ta tada sallah zuciyarta na harbawa da kukan
da yarinyar ke zubawa a bayanta. Ga wadda ta ajiye ita ma ba ta fasa ba. Kawai ita ma sai ta
soma kukan tausayin Basma, ta san tsananin damuwa ne ya sa ta daina tabuka komai a kansu.
Allah-Allah ta ke ta idar su tafi asibiti, tukin motar da Aboulkhair ya nace ya koya mata duk da
ba ta so yau zai yi mata amfani. Da safe ma ita ta kai su asibiti aka duba yarinyar aka ce mura
ce kawai, suka sayo magani suka dawo.
Nan Mama ke gaya musu tafiyar su Daddy a mota sakamakon rashin jirgi. Duka addu’ar
sauka lafiya suka yi musu, suka ci gaba da hidimar yaran.
Tun bayan maghriba kuma suka bude makogaro suke zunduma kuka. Wanda shi ne har yanzu
suke fama. Tana idarwa ta fito goye da Husainar ta je dakin su Sabrina ta rufe su da duka suna
barci. A tsorace duk suka tashi suna tambayarta me ya faru? Kuka ta hau yi a gabansu tana
fadin, sai barcinsu na tsiya ya jawo musu masifa, uwarsu na kwance babu inda ta ke iya
motsawa tun dare suna nan suna barcin asara, duk kukan da ‘yan biyu ke yi ba su san ana yi
ba ko me? Rantsuwa suka hau yi mata suna dirgowa daga gado suna fadin, wallahi ba su sani
ba, kuma su ba su ji kuka ba. Ta ce su je su kula da Mama ita da Basma za su je asibiti a duba
yaran.

Wata na ture wata haka suka fita a gigice, ta bi su da harara da idanunta da suka yi jawur.
Lokaci-lokaci gabanta na tsinkewa ya fadi, har sai ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta ta
ambaci sunan Allah. Dan cikinta sai wani irin juyi yake kamar ya wuce watanninsa. Ta dawo
tana rarrashin Basma, ta canza riga su tafi asibiti, amma ta yi gumm! Kamar ba da ita ta ke ba,
gani kawai ta ke rasa yaran za ta yi, don haka ba ta ga amfanin su je wani asibiti ba. ga
Aboubacar tun kafin azahar rabonsa da kiranta, ita kuma in ta kira shi wayar ba ta shiga. Dalilin
damuwarta kenan.
Aalimah ta yi rarrashin duniyar nan, Basma ta ki tashi, kawai sai ta fashe da kuka mai karfi.
Ta ce, “Basma, ya ki ke so in yi da raina? Kina so na zauce? Ga Mama can ba ta san
wanda ke kanta ba, ni ma zuciyata tsinkewa ta ke yi, karfin hali kawai nake yi, su kuma da gani
akwai abin da ke damunsu. Jarirai su kwana ba su sha nono ba ki ce haka za mu ci gaba da
zama da su muna kallonsu?†Basma ko gezau! Sai ta rabu da ita ta sanya hijab din sallarta ta dauki mukullin motar
Aboubacar da ya bar musu don irin hakan, kamar ya san za su bukace ta. Ta nade Hassanar a
shawul mai kauri, ta dauki katinansu na asibiti ta tafi, Suhaima ta biyo ta da gudu ta karbi ta
hannunta tana fadin, “Muje na raka ki in ji Mamaâ€. Da suka je asibitin a sashen sababbin haihuwa aka karbi jariran (Day old), likitoci suka hau
bincikarsu. Suka samu wuri ita da Suhaima suka zauna. Sai a lokacin nutsuwa ta soma dawo
mata jin ta daina jiyo kukansu. Tunanin Aboulkhair ya fado mata. Ta kira shi bayan sun dawo
daga asibiti da safe ya ce mata suna Katsina, “in mun shiga Niger I will call you. Take care
of yourself and my baby for me MON AMOUR!â€.
Kiran da har yanzu ko kyallinsa ba ta gani ba. Tsabar jiran kiran wuni ta yi rike da wayar a
hannunta, in sallah za ta yi a cikinta ta ke soke ta. Da ta gaji da jiran ta yi ta gwadawa ita ya ki
shiga. Ta yi tunanin sun shiga sahara sun rasa network, amma har twins suka fara jiniyarsu
babu kiran Aboulkhair ko na Aboubacar. Mama ta ce, Daddy ma bai kira ba. A lokacin ya isa a
ce ma sun shiga Niamey. To balle yanzu da za a iya cewa sun kwana sun hantse, tunda har ga
shi alfijir ya keto.
Ba ta kawo wani mummunan tunani a ranta ba, duk da ta san Aboulkhair yana da layin Niger.
Ta sa a ranta bai samu sukunin kiran nata ba ne saboda gajiya duba da cewa, shi ya tuka motar
tun daga Nigeria har Niger, har kuma babban birni Niamey. Sai dai wannan tsinkewar na
zuciyarta shi yake damunta, saboda ba a son faduwar gaba ga mai ciki. A matsayinta na
medical personnel ta san hatsarin hakan, don haka ta koma hailala da salatin Annabi cikin
zuciyarta.
Daidai lokacin likitan da ya karbi yaran ya fito. Tambayarta ya yi, ina uwarsu? Ta ce tana gida.
Da mamaki ya dube ta, sai kuma ya basar ya
ce ta je ta zo da ita za a debi nonon a ba su ta hancinsu, masassara ce ta cika musu
makogaro.
Ta ce da Suhaima ta zauna ta je ta zo da Basma, ba za ta jima ba. Har Mama za ta dauko.
Tun daga nesa ta hangi bakar motar ‘yansanda fake a kofar gidansu. Tsinkewar da gabanta
ke yi ya fadi da ta samu ya lafa sabida karfin hailala ne ya sake faruwa da ita. ‘Yansanda biyu
na tsaye tare da maigadinsu Bilyaminu.
A hankali ta ke rage gudun motar ta wuce su ta nufi gate tana danna wa Bilyaminu horn da
nufin ya zo ya bude mata ta shige.

Bilyaminu ya karaso da sauri, maimakon ya bude mata sai ya tsaya yi mata bayanin wai
‘yansandan gidan suka zo. Wani babba a gidan suke son gani. Ba halinta ba ne raina babba
ko na kasa da ita, amma ba ta san sanda ta sakar wa Bilyaminu harara ba, “Amma dai ka
san daga Daddy har Yaya Aboubacar ba sa nan ko? Don me ba za ka gaya musu ba da za ka
tare ni kana gaya min? Ka san uzurin da ke gabana? Tunda ka ga na fita da asubah na dawo
yanzu ba sai ka bude min kofa ba ka san ya zaka yi da su ba, tunda ba sata na yi ba?â€
Daya daga cikin ‘yan sandan ya karaso ganin ta ki kula su, kuma ta rufe dattijon da fada,
“Excuse me Madam!†Ya fada da kyakkyawar siga.
Dole ta yi shiru ta bi shi da ido.
“Muna neman gidan Dr. Mansour Raazee, lecturer a jami’ar Bayero, tsangayar Mass
Communication, da gidan Aboubacar Raazee, accounter GTBank Hotoro Branchâ€. Ya fada
cikin harshen turanci.
A sanyaye ta ce, “Nan ne!â€.
“Ko za ki turo mana namiji ya bi mu ofishinmu? Akwai bayani a kansuâ€.
Girgiza kai ta yi, abin gwanin ban tausayi ta ce, “Ni ce babba a gidan, babu namiji bayan su,
uwata kuma ba ta da lafiyaâ€.
Tsayawa ya yi yana tunani, bai kamata ya tafi da ita ba ya gaya mata al’amarin da ke tafe
da shi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login