Showing 51001 words to 54000 words out of 128821 words

Chapter 18 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

yadda ta ke mu’amala da kowa ba, musamman dangin
mahaifinsa. Ya taba gaya mata, Inna Kasisi ta taba ce da shi; Ban san me na yi uwarka ta ke
gaba da niba. “Mummy why?â€
Wayarta ta janyo hannunta na rawa ta kira shi. Shigarsa ofishinsa kenan da sanyin safiyar
litinin. Kiran nasa a daidai wannan lokaci ba daidai bane. Don haka ya rufe kansa a tankareren
ofishin sa wanda ke cikin kamfanin man fetur na ChevronCorporationreshen jihar Las Vegas ya
amsa kiran mahaifiyarsa with utmost respect. “Mu’az, ina cikin wani hali. Ta kare min. Komai ya kare mini, ga kishiya ga mugun hali.
Ka yi hakuri na san ba ka da lafiya, amma kullum cikin kara maka damuwa nake da matsalolina
wadanda kullum ni nake janyo wa kaina su…â€. Ta saka kuka.
Zama ya yi a lallausar kujerarsa baka wuluk! Ya yi loosing tie din wuyansa. Fahimta yake
tattarowa ya sanya wa kalaman Mummy, don ya gane inda matsalar yau kuma ta sa gaba,she is
always in trouble with her husband, kuma in ya ba ta shawarar ba ta dauka. Wannan baya hana
gobe ta sake neman ya bata shawarar. Wannan ba ya hanawa gobe ta kwaso sabuwar
matsalarta ta kawo masa. Yana jin dadin yadda ta maida shi aminin ba ta kama gurbatattun
kawayen zamani ba.
Duk da in an dubi amintar tasu ta tsakanin Da da mahaifi ce, tana gaya masa ne don ta ji saukin
damuwarta ba don ta yi amfani da abin da zai shawarce ta ba. Amma yau ji ta ke ko me
Mu’azzam ya ce ta yi, za ta yi ko ba ta so, don ta zauna lafiya ta dawo da martabarta a
idanun mijinta. “Mummy me ya faru?â€
Ya tambaya da kwantacciyar murya cikin tattausan turanci, wanda ya kama harshensa fiye da
kowanne yare, sabida rashin abokin yin wani yaren bayan shi. In ka ji yana Hausa ko French, to
ya je Nijar ne, ko yana magana da Monsour Razee, kanin mahaifinsa mai matsayin uba da
aboki. Ta sassauta kukanta, ta gaya masa duk halin da ta ke ciki bayan sun dawo. Halayen Gumsu da
yadda Daddy yake martaba ta. Ta ce, ba wai ya sauya mata ba ne, amma ta lura ba ta da
martaba da tasiri mai sosai a zuciyarsa, yanzu ya fi muhimmanta ‘ya’yansa da Gumsu.
Ta gaya masa ta gane dukkan halayenta ba masu kyau ba ne a al’adar Malam Bahaushe. Tana so ta gyara ta rasa hanya. Ba ta so a alakanta canzawarta da wanzuwar Gumsu. Tana so

ta gyara tsakaninta da Inna Kasisi da Malam Raazee. Tana matukar nadamar watsar da su din
da ta yi da rashin daukarsu da daraja. Ko ba a fada mata ba ta san halinta ne ya sanya Inna
Kasisi tursasa wa Daddy yin aure. Ya ya za ta yi ta dawo da kyakkyawar alaka ta mutuntawa da
girmamawa a tsakaninsu???â€
Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee, komawa ya yi da bayansa ya jingina cikin kujerarsa yana
jero hamdala a zuciyarsa.. At last, ta dawo kan kyakkyawar turba irin wadda yake mata
addu’a kullum. Ta fahimci ita ce at fault ba kakanninsa ba. They hold nothing bad against
her(ba su da wani mummunan kudiri a kanta). “It’s o.k Mum, ki kwantar da hankalinki, na fahimce ki. Ba sai kin yi wani reaction da zai
sa su gane kina so ki canza din ba, zuciyarki kawai za ki canza ki warware duk wani kullaci da
ke cikinta, da tunanin ba sa kaunarki. Wadannan mutanen are very busy with their family life
babu kowa a gabansu sai yadda za su kula da ‘ya’ya da jikokinsu. Ki mu’amalanci
Daddy da kyakkyawar mu’amala irin wadda ki ka ga matar tasa na yi. Ki daina daukan
kanki sama da shi. Ki ba shi cikakken iko a gidansa irin wanda addininmu ya ba shi. Idan ya yi
umarni ki daina ketarewa, ki nuna masa ke abin ikonsa ce, sai yadda ya yi da ke. Ki saki
zuciyarki da matar idan ba mai fitina ba ce, ki dauke ta kanwarki.
Malam Raazee da Inna ki bar lamarinsu a hannuna, ba su dauke ki yadda ke ki ka dauke su
ba. Nan da sati biyu ma zan dauki annual leave zan je Nijar. Mummy zan gyara komai a
tsakaninkuâ€.
Mummy Zulaiha ta share hawayenta. Tambayar kanta ta shiga yi, me ta yi wa Ubangiji da ta
cancanci samun ‘ya’ya irin Mu’azzam da Abulkhairi? Ko sallar farillarta ba ta ba ta
hakkokinta yadda ya kamata sabida aikin banki, sai ta hada uku lokaci daya. Wani kukan ne ya
zo mata da ta tuno halin da Mu’azzam ke ciki duk a kan sakaci da addininta. Babu ranar
aure! Ba za ta dauki ‘ya’yansa ba? Kukanta ya karu har ya bai wa Mu’azzam tsoro.
Bai ga abin kuka ba cikin kalamansa.
“Mu’azzam, ka yafe min…†Kawai ta ke cewa, ta fada ya kai sau uku.
Ya ce, “Mummy, laifin da ki ka yi min tun kafin ki haife ni, da wanda ki ka yi min daga sanda
ki ka haife ni zuwa yau, da wanda za ki yi min shekaru dari masu zuwa in muna raye na yafe
miki. Rokona gareki ki sa min albarka!â€.
Mummy Zulaiha kasa ci gaba da rike wayar ta yi, ta sake ta a kasa ta rushe da kuka.
Ko dai irin auren baya za ta kara yi wa Mu’azzam, in ya so komai ta fanjama-fanjam???

******
Cikin sati guda kowa a gidan ya lura Mummy ta canza, ta zama saliha, ta aje izza, ta zama wata
irin nutsattsiya, kullum sallah za ka taddata tana yi, ko alkur’ani a hannunta tana tilawa. Da
ta dawo ofis ta ci abincin da Gumsu ce ke dafawa yanzu, za ta yi alwala ta shige daki. Ba ta son
hayaniya sam, in a weekend ne ita ta ke yin girki gabadaya, tun daga daren Friday har daren
Sunday. Ta daina kyarar Gumsu, ko kallon banza ba ta mata kamar farkon zuwanta.
Gane hakan da Gumsu ta yi sai ta kara zage damtse wajen girmamata. Ta ce ta bar mata
breakfast din ranar litinin da ta ke takura kanta ta yi, ganin tana makara. Girkin kwana uku-uku
suke yi. Canzawar Mummy Zulaiha ba ita kadai ya shafa ba, ya shafi walwalar gidan bakidaya,
yaran sun sake sosai maimakon da ko magana za su yi da Gumsu suna kauce wa idon

Mummy, yanzu kuwa ita da kanta tana kula Gumsun, har dakinta tana shiga, wanda Daddy ya yi
furnishing dinsa ya yi kyau sosai. Ita ma Mummyn ya ce zai canza mata ta ce ba ta bukata, ba
abin da dakinta ya yi. Shi da kansa ya lura Zulaiha ta canja, wata sabuwar Zulaiha ce wannan
ba wadda ya dade da sani ba. Ba karamin jin dadi da kwanciyar hankali hakan ya haifar masa ba. Har wata ‘yar kiba ya yi a
dan tsukin. Gidan Ishaq Raazee a garin Boston ya koma wani sansani na zaman lafiya da
fahimtar juna. A gefe soyayyar Aalimah da Abulkhair na kara gawurta. Duk da a waya kawai
suke tare da juna. A wannan satin su Aalimah suka samu hutun karshen shekara, maimakon yadda Daddy ya
tsara da farko, cewa ita da Gumsu za su zo, sai ya hado har da Basma. Za su yi sati biyu a Nijar
su wuce Nigeria gidan su Aalimah su karasa hutunsu.
Murnar zuwansu a wurin al’ummar gidan ba a magana, kada Inna Kasisi ta ji labari. A
dakinta Gumsu ta sauka maimakon na yayarta Bintou.
Inna Bintou na ta mata tsiya wai ta zabi suruka ta barta. Kan ka ce me ye wannan? Gidan ya
cika da ‘yammatan family din. Su Balkissa da Roumana mutanen Aalimah. Aka shiga yawo
gida-gida gaida dangi. Kwanansu uku a Niamey suka wayi gari cikin shirin tafiya Arlit, za su
raka Gumsu ganin gida. Wannan karon ma Hamoud ne ya kai su, sun kwana biyu a can suka
wuce birnin Agadez gidan su tsohon mijin Gumsu, ganin ‘ya’yanta, wadanda ke hannun
kakanninsu.
Aalimah sai da ta yi hawaye lokacin da ‘ya’yan Gumsu, Adizatou da Jamilatou suka
rungume mahaifiyarsu suna kukan ba za su kara yarda ta tafi ta barsu ba. Da ‘yar shekara
takwas da ‘yar shekara shidda. Duk kayan da ta sayo musu sun ce ba sa so ita suke so su
bi, Basma kasa jurewa ta yi sai da ta gaya wa Daddy a waya. A daren ranar ya kira Gumsu ya
ce, idan kakannin yaran za su yarda su taho tare da su, zai yi musu visa. Kememe dattijan sun
ki, sun ce su kadai gare su da za su dinga tuna musu dansu Jibreel suna yi masa addu’a,
Gumsu ta yi hakuri.
Yaran na kuka su Aalimah na yi suka bar Agadez a washegari. Gumsu ta yi dauriya sosai.
Soyayyar Gumsu da ‘ya’yanta ita ta sa Aalimah kasa cika sati biyu a Nijar. Kwanansu
goma hankalinta ya yi gun nata iyayen, da yau shekara daya da kwana goma rabonta da su.
Yayansu Hamoud ya sako su a jirgi mai tasowa daga Niamey zuwa Kano, Nigeria.
6/28/21, 7:33 AM - Buhainat: ADAMU DANKOLI





¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
£££££££££££££££££££

******
Garin Kanon-Dabo, bai canza wa Aalimah da komai ba. Sai karin tsayin gine-gine kawai. Sun
tadda Aboubacar ya zo daukansu don tun tasowarsu Hamoud ya gaya masa. karon farko wani
miracle ne ya afku tun a filin jirgin saman Malam Aminu Kano. Basma ta kalli Aboubacar Yayan
Aalimah, ma’aikacin bankin GT a halin yanzu, ta kara kallonsa ba ta iya kara yi masa kallo
na uku ba, sabida tsanantar bugun zuciya a gare ta.
Suna tafe a sabuwar motar Aboubacar kirar Honda Accord da bai fi watanni biyu da sayenta ba
a hanyarsu ta zuwa gida, Aalimah nata yi masa karadi, amma hankalinsa ba ya kanta. Basma
yake satar kallo ta madubi, wadda duk kaudi irin nata ta ji yau ta kama kanta. Maimakon
Aboubacar ya dauki hanyar B.U.K Road don isa ga gidansu wanda ke cikin rukunin gidajen
malamai na sabuwar jami’ar Bayero sai ta ga ya dauke kan motar ya yi Nassarawa, billa
can, billa nan sai ga su a kebantacciyar unguwar Sultan Road.
Aalimah ta ce, “Yaya Aboubacar ina za mu je ne?â€
Bai juyo ya kalle ta ba ya amsa, “Gidaâ€.
Daidai lokacin da ya sanya hancin motar a gate din wani kyakkyawan gida, wanda da ganinsa
ka san sabon gini ne. Ba ta gama wannan mamakin ba ta hango fitowar kannenta a guje.
Sultana a gaba, Suhaima biye da ita, Sabrina a bayansu. Mama ma ta kasa hakurin shigowar
Aalimah, fitowa ta yi kofar shiga falon sai murmushi ta ke yi. Kasa jiran Aboubacar ya gama
parking, Aalimah ta yi ta balle murfin motar ta fice saura kadan ta fadi. Tun daga nesa ta bude
dukkan hannuwanta su Sultana suka shiga bakidayansu ta rungume su. Daga bayan wuyansu
ta hango Mama sai kallonta ta ke tana murmushi. A kokarin mikewa ta kusa faduwa, sai da
Basma ta rike ta ta mikar da ita. Ta karasa da gudu ta rungume Mamanta. Maman ta rike ta
sosai a jikinta tana fadin, “Aalimah ta! Sannu da zuwaâ€.
Aboubacar ya karaso dauke da jakunkunansu, sai fada yake yi wa Aalimah, wai sai ka ce yau ta
taba ganinsu. Shi ai ba ta yi masa irin wannan tarbar ba. Ga bakuwa ta kyale kamar ta manta
da ita. Wannan karon ne Basma ta yi magana tana satar kallonsa komai da yake yi burge ta
yake, very gentle da shi. “Ni ba bakuwa ba ceâ€.
Ya juyo ya dan kalle ta ta saman idonsa, ya ce, “Ke da ki ka zo kasa ya kasa zuwa na farko
ya kamata a karrama ki, duk da gidanku neâ€.
Murmushi ta yi, Aboubacar ya yi saurin dauke kansa sabida wasu abu masu kama da electrical
shocking da suka fito daga cikin murmushinta zuwa idanunsa.
Mama ta saki Aalimah ta kamo hannun Basma ta ja ta suka shige har bedroom dinta su Sultana
suka shiga hidimar shirya abinci a dining. Aalimah sai bin gidan ta ke da kallon tsoro da
mamaki, don kuwa ta san mahaifinta malamin jami’a ne, bayan wannan ba shi da wata
sana’a. A cikinta suke ci suke sha, suke zaune cikin rufin asiri. Ko wata sana’ar ya
samu bayan barinta gida bai isa a ce ya tara abin da zai mallaki wannan gidan cikin shekara
daya ba. Mama sai ina-ta-ka-saka-ina-ta-ka-aje ta ke yi da Basma, ita kuma babu bakunta sai
zuba hira suke da su Sultana, kannen Aalimah sun ba ta sha’awa, ga su nan kusan kai
daya sabida bai fi shekaru bibbiyu ne a tsakaninsu ba. Sultana ce babba, shekarunta goma sha
biyu, Suhaima goma, Sabrina takwas.
Mama ta tambayi Basma abinci za ta fara ci ko wanka? Ta ce, “Wankan dai Mama. Jikina fa

har ya fara bashiâ€.
Aboubacar ya dago kansa daga kan wayarsa dariya ta kama shi. Ko a jikinta, ta ce, “Mama
kada ki so in matso kusa da ke, tun a Nijar ya fara bashiâ€.
Dariya Mama ta yi ta nuna mata Aboubacar da ya zuba mata ido zaune a kan stool din madubi
ta ce,
“Basma Yayanku yana jin ki fa!â€
Ta juya da sauri suka yi ido hudu, da gudu ta kwasa ta yi toilet. Ya girgiza kai ya fita yana
dariyarta.
A ransa ya ce, “Yar gayu da ke Basma! I’m sure in na matso kamshi zan jiâ€.
Mama ta kama hannun Aalimah cike da farin ciki, ta ce, “Come and seeâ€.
Gidan suka zagaye tana nuna mata ko’ina. Self content family house wanda da ma
mamakinsa ke damun Aalimah. A karshe suka dire a dakin da ke kallon na su Sabrina. Mama ta
sa mukulli ta bude, Aalimah ko Mama ba ta fada ba, ta gane dakinta ne. Chinese bed
madaidaici, wardrove din dakin ta jikin bango ce, sai madubin gadon da stool na kwalliya. An
shimfide dakin da carpet ruwan bula mai duhu, kalar labulen dakin. A gefe teburin karatu ne da
na’urar kan tebur (desktop), na’urar sanyaya daki na ta aiki gwanin dadi, kai ka ce
iyayen Aalimah ko kuma wanda ya shirya dakin bai da niyyar aurar da ita watarana.
RungumeMama ta yi don murna, sannan ta ce, “Shin don Allah Mama wa ya saya wa
Daddy gidan nan?â€
Mama ta ce, “Abin sirri ne Aalimah, kawai ki yi godiya ga Allah, ki kuma yi wa kowaye
addu’ar Allah ya ba shi duk abin da yake so duniya da lahiraâ€.
Basma ta shigo tana fadin, “Mama dakin Aalimah ai ya fi naki kyauâ€.
Dariya ta yi ta ce, “Kin santa da son blue shi ne Aboubacar ya sa komai blue ba mu dade da
dawowa gidan baâ€.
Ta ce, “Shi kenan in aka yi mata aure ni sai in dawo. I love the house da mutanen cikinsaâ€.
“Mutanen gidan ma bakidayansu suna sonki Basma, suna maraba da keâ€. In ji Mama.
Aalimah ta harare ta, “Ni ba auren da zan yi, ke dai za a yi wa sai a kawo ki gidan nan
dinâ€.
Mama ta fice ta barsu tana fadin, “Duk tare za mu aurar da ku mu huta. Kun zama wasu
gandama-gandaman ‘yammata in a nan ne ina za a bari ku kara shekara guda?â€
Dariya suka yi dukkansu don a wajen Mummy Zulaiha Basma har gobe ba ta wuce goyo ba, in
har za ta iya goya tan.
Sai dare Daddynsu ya dawo su Aalimah suka tadda shi a falonsa. Ya kasa boye jin dadinsa na
ganin yadda ‘yarsa Aalimah ta koma. Ya yi maraba da zuwan Basma har fiye da Aalimah.
Wannan ya nuna da gaske dan uwan nasa yake da ya ce zai gyara kuskurensa na baya. Nan
suka zauna hira bayan sun ci abincin dare tare har Yaya Aboubacar, Basma ce ta fara tashi ta
barsu sabida barci da ya soma dibanta.
Aalimah da iyayenta sun raba dare suna hira, labarin zamanta gidan kawunta a America ta ke
ba su, wanda duk ciki babu wanda ba alkhairi ba, ko da kuskure da tuntuben harshe ba ta ce
Mummy ta taba yi mata rashin kyautawa ba. Sai labarin yanayin karatunta da yadda ta tsinci
kanta a matsayin dalibar jami’ar Boston wanda har gobe ta ke gani kamar mafarki. A cikin
maganganunta tana ambaton Abulkhair da kyawawan halayensa da yawan kyautayinshi gare
ta. Idan ka kalli kwayar idanunta kauna ce zallah. Daddy bai gane komai ba, amma Mama ta

sanya wa maganganun Aalimah masu yawa a kan Abulkhair ayar tambaya.
Tambayar da Daddy ya yi wa Aalimah ta dan jefa ta a tunani.
“You praises Abulkhair so much,(kin yabi Aboulkhair da yawa) amma ko sau daya ban ji kin
ambaci Dana ba, bayan ya fi shi kirki, ya fi shi son zumunci. Shi Abulkhair bature ne irin
Babansaâ€.
“Wa kenan ka ke nufi Daddy?†Ta tambaya cikin dan yamutsa fuska na rashin fahimta.
“Dana MU’AZZAM!â€.
“A ina yake? Ni ban sanshi baâ€.
Cikin mamaki Mama da Daddy suka hada baki, “Mu’azzam fa Yayan su Basma, wanda
Abulkhair ke bi a haihuwaâ€.
Tunani Aalimah ta fada don son gano wanda suke nufi, amma iyaka tunaninta bai ba ta ba.
Girgiza kai ta yi, “I’ve never saw him (ban taba ganinsa ba)â€.
Daddy ya ce, “Mu’azzam din?†A cikin muryarsa akwai mamaki.
Aalimah ta ce, “Ni ko sunansa ban taba ji ba, ban da yanzu a bakinku. To ko shi ne wanda
su Basma ke yawan fadin yana wani gari Las Vegas?â€.
“An yi haka! A can yake. To amma ko a can yake aiki ya za ki ce ba ya zuwa gidansu?â€
“Wallahi Daddy bai taba zuwa ina nan ba, su Mummy din ne ke zuwa inda yake. Mummy
tana zuwa sosai. Shi ma Daddyn kwanaki na ji ya je duba shiâ€.
Da haka suka bar zancen, Mama na fadi cikin ranta,
“Wani abu sai bature. Iyaye ne ke zuwa gaida dansu ba dan ne ke zuwa gaida su ba!â€.
Sabanin Mama shi ‘yar hirar nan da ta fito daga bakin Aalimah a kan Mu’azzam a zurfin
tunani ta jefa shi. Ishaq ya dade yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login