Showing 114001 words to 117000 words out of 128821 words

Chapter 39 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

bai taba tsintar kansa a kwatankwacinsa ba. Aikin da yake yi mai
muhimmanci ne amma sai ya kasa gane me yake yi. Aalimah ta ci gaba da yin abin da ta ke yin
ba tare da tunanin komai a ranta ba, sai kawai ta ji muryar Mu’azzam ta soma canzawa har
bata fahimtar abinda yake fadi sosai, a lokacin da yake rokonta da ta bari. “....Stop it
Aalimah..... please stop it......!â€. Ya taso ya zauna ya jefar da system din gefe, kama
hannuwanta biyu yayi ya rirrike jikinsa yana wani irin kyarma. In ita ta shirya wa hakan a
tsakaninsu shi bai shirya ba, har gobe a matar ABOULKHAIR yake kallonta.
Ta ce, “Yaya Mu’azzam, nifa tausa kawai nake maka don na ga ka gaji ba da wata
manufa ba, sai ka barni ni kadai a daki alhalin bani da abin yi. Akalla mu dinga hira ni da kai, mu
abokanci juna ko ya ya ne, mu dinga jin damuwar junanmu, mu debe wa juna kewar iyaye da
‘yan uwa tunda ba mu da kowa a nan sai junanmu. In kai kana da aiki a system din da za ta taya ka hira, ni ba ni da shi. I just want us to be
friends, abin da ka ke tunanin ina bukata ba shi ba ne Yaya Mu’azzam, na dade da cire
wannan section din daga gangar jikina tun ranar da na rasa Aboulkhair, ban kara tunawa ni
mace ba ce, balle in yi tunanin neman wani abu daga garekaâ€.
Wai kuma sai ya ji kamar kalamanta sun masa tsauri da yawa. Kamar ta dan zuba masa ruwan
zafi….. Ta zo gabansa tana fadin tun ranar data rasa mijin ta kaza-kaza.......tsaki ya ja mai
sauti. Da kyar ya fizgo sauti daga makogaronsa. Ya ce.
“Did I ask you how you are feeling when lost your husband?†Ta wani murguda baki
ta juyo masa keya, yana hango lallusar gashin baki sidik data kalmashe a cikin bind. “Toh,
Na ga ka yi min wata fassara ne daga yi maka tausaâ€. Murmushi yayi cikin takaici.

“Friendship ki ke so?†Ya sake tambayar ta. Bayan ya kauda idonsa da sauri.
Ta ce, “Ehâ€.
Ya ce, “To na amince miki ki shiga makwabta ki cigita ki nemi sa’anninki watakila za ki
dace da samun abokinâ€.
Rausayar da kai ta yi abin tausayi.
“Yaya Mu’azzam ka manta a inda muke ne? Ai ba ruwan kowa da kowa, ta yaya zan
shiga gidan mutanen da basu sanni ba ban sansu ba, ba addini da yaren mu daya ba?â€.
A dan harzuke ya ce, “Na ji, zan miki komai ki ke so, but don’t touch me like this again,
pleaseâ€.
Ta ce, “ba wani abu ne mai yawa nake so ba, hira nake so mu dinga yi tare, zuwa yawon
cikin gari ni da kai da daddare, beaches, shopping malls da kasuwanni duk mu dinga zuwa tare
a duk lokacin da zanyi cefane ko sayayya, ka kuma daina bani sako ta hannun Harrison ba na
so, ka bani da kanka ba muharramina bane, duk wani sako tsakanina da shi daga yau ka yanke
shi, zan kuma din ga shigowa dakin nan duk sanda na ga dama..…Na daina tsayawa a bakin
kofa ina neman izni kamar wata almajira…..â€.
Da sauri ya katseta,
“….Ban yarda da wannan ba. Ki shigo min daki duk sanda kika ga dama in kuma ba a
shirye nake ba fa. You are just creating a problem, ….you and your problems…â€.
Dariya ya bata sosai, da ganin fuskarsa ka san ta hada masa zafi. Ta hadiye dariyar ta ta ce
“ba su kenan ba ai issues din nawa, sai kuma hada maka ruwan wanka kullum da aje maka
towel, sai kuma zabo maka kayan da zaka dinga sanyawa, I also want be choosing neck ties for
you. Tied it by your neck…. That’s all I want from youâ€. Ajiyar zuciya ya yi, ya kura mata ido kamar ya maketa, me yarinyar nan ta ke so ta zama ne? Ya
tambayi kansa.
“Close to your lifeâ€.
Abin da ta ke nufi kadai kenan, zuciyarshi ta bashi amsa, shi kuma wannan wani gurbi ne da ba
zai iya bai wa kowa ba. Intimacy din zai yi yawa. Aalimar da ya sani da kunya da kawaici a
lokacin Aboulkhair, wadda ko ido bata iya hadawa da shi, yau rana daya ta zo masa da wasu
bakin halaye tamkar mai multi personality disorder! Ba ya tantama zama da matar Daddy ne ya
maida ita haka. Tunda bata da kawar data fi ta.

“Ki yiwa Allah ki kyaleni Aalimah, kin ga inada ayyuka da yawa, in dai system ce zan saya
maki gobe ki dinga yin karatu da ita insha Allahuâ€.
Turo baki tayi kamar kankanuwar yarinya “Yaya Mu’azzam ni ban ce ka saya min
computer ba, inada ipad. I mean nothing, I only need a friend in you. Tunda an rabo ni da kowa
nawa an kawo ni nan, inda ba ni da kowa sai kaiâ€.
Ta soma jan hanci alamun kuka zata soma daga kowanne lokaci daga yanzu.
Mu’azzam ya shafo sumar kansa cikin damuwa, da sauri ya ce, “to shikenan na yarda,
amma kar ki sake taba ni, don Allahâ€.
Aalimah ta sake cuno baki, ta mike tana kunkuni har da bubbuga kafa a kasa.

“Ai Allah bai ce kada in taba ka ba!â€.

Abin ya ba shi dariya a karo na farko, amma ya gintse.
“To kuwa kada ki sake shigo min daki in ba ni na neme ki ba. Abincin a bar min a dining in
na bukata zan zo da kaina in ciâ€.
Juyowa tayi cikin far’a mai yawa tace masa.
“Nan fa daya! Mun riga mun wuce wurin nan, ka riga ka amsa. I will be in my husband’s
bedroom whenever I wish. Magana biyu ba taka bace Yaya Mu’azzamâ€.
Girgiza kai yayi ya bita da ido a sanda ta kama hanyar ficewa.
Har ta kai bakin kofa ta juyo ta marairaice. “To don Allah in zo ka kai ni shopping? Wallahi
ko man shafawa ba ni da shi, ni ko kayan lefe babu wanda ya yi min just because an fi son ka a
kainaâ€.

Bai san sanda ya ce “Je ki ki shirya†ba.

Har da dan tsallenta ta fice kamar wata kankanuwar yarinya.

Mu’azzam ya dafe kansa dake sarawa saboda rigimar Aalimah, ya dade bai yi magana mai
tsayi irin wannan ba, ta sa shi magana mai yawa. Ita a dole sai ta koyar da shi sakin jiki da ita.
Bayan da farko ta nuna masa ba ta da hayaniya, ashe shigo-shigo ba zurfi ta yi masa?
Murmushi ya yi tare da lumshe idanunsa. Ashe hayaniyar ga wanda ya iya ta nishadi take
sanyawa? Kwarai ya samu kansa cikin nishadi wanda rabonsa da irinsa har ya manta. Ya koma
ya jingina da jikin gadonsa, yana mai hasashen inda karshen wannan tafiya za ta kai su???.

Suna tafe cikin motar Mu’azzam (Acura) fara sol, Mu’azzam ne ke tukin motar. Tunda
suka taho kira’ar Sheikh Abdurrahman Sudaith ke tashi a motar cikin (Suratul
Ali’Imran). A fili Mu’azzam ke bin karatun wanda ya sanya wa Aalima nutsuwa sosai. Ta
nutsu, ta kwantar da kanta a masangalin kujerar da ta ke zaune tana sauraronsa. Ba ta yi
mamakin iya karatun Mu’azzam ba, kasancewar Aboulkhair ya gaya mata komai na
rayuwarsa har a Madinah.
Shagon da yake nasa shopping din ya kai ta, ya ce ta je ta yi siyayyarta zai jira ta a mota, idan
ta gama ta yi masa flashing ya je ya biya su tafi. Ta fahimci abin da yake nufi (ba zai jera da ita
ba) to ita kuturwa ce ko ko me yake nufi? Duk da haka ta gode, domin sauyuka ne da ba ta
tsammata a nan kusa ba daga gare shi. Ta shige cikin shagon kai tsaye wajen kayan kwalliya ta dosa. A sannu za ta canza komai da
yardar Allah. Ashe dai duk laifinta ne wannan mugun zaman da suka shekara cikin sa.
Mu’azzam yana da saukin kai matuka idan kayi hakuri da shi kuma a sannu zaka fahimce
shi. Yadda ka bayyana kanka da haka yake biyar da kai. Tana rokon Allah ya ba ta kwarin
gwiwar mayar da Mu’azzam ma’abocin walwala da farin ciki kamar sauran mutane
koda ba entirely ba.

Mu’azzam bai san me Aalimah ta sayo ba, sai da suka dawo gida, ta ware nata siyayyar a
dakinta ta dauki wata katuwar leda ta bi shi da ita. Yana kokarin canza kayan jikinsa zuwa
pajamas ta yi sallama tare da tura kofar ta shiga gaba-gadi tana mai kawar da kai daga gare shi
ba tare da ta bari yayi mata iznin shiga ba. Tsaki ya yi mai sauti ya juya mata baya, ya ci gaba

da zarga igiyar pajamas dinshi. Yarinyar nan tana son shiga rayuwarsa da yawa, abinda ba zai
dauka ba. A dan fusace ya juyo yana kallonta, ta ce shopping ya kai ta, an dawo kuma ba za ta
barshi ya huta ba? He want to be alone ko ya samu ya sha maganinsa ya kwanta.
“Oh please Aalimah mene ne kuma?â€
Ya tambaya, rabi a fusace, rabi cikin boye fushi.
Zama ta yi gefen gadonsa ta soma fiddo kayan da ke cikin ledar, shampoo ne na maza
(Arganavita), shavers da after shaves kala-kala turaren wanka (bath robbs), handkerchiefs,
vest, boxers da duk wasu tarkace na maza irin wadanda ta ga yana amfani da su. Ta marairaice
tare da karyar da kai, ta ce, “Da ma sayo maka na yiâ€.
“Na ce ina bukata?â€
Ta yi kasa da murya,
“Don na san kana bukatar neâ€.
Ta tattara su ta yi toilet din shi da su. Bin bayanta ya yi da kallo, ko’ina a jikinta rausaya
yake kamar mai yi da gangan. Bai dauke idonsa ba sai da ta kule cikin toilet din. Ya yi ajiyar
zuciya ya bar kallonta. Bai san me ta ke so da shi ba kuma, duk abinda take so yayi mata,
amma bazata barshi ya huta ba, ta fara takura masa. Ba ya son damu, gara zaman su Mummy
sau dubu da wannan Aalimar ta yau, ba sa gigin shigar masa daki. Amma Aalimah…
Aalimah… ta fara shigar masa hanci, in ta yi wasa zai bar mata gidan gaba daya.
Cikin kwanaki bakwai da suka biyo baya Aalimah tayi nasara mai yawa akan Mu’azzam, ko
baya son magana sai ta bashi dramar da zai yi dariya. Ta like masa ta nace masa kamar kaska.
In zai tafi ofis sai ta bata masa lokaci. Har stool din mudubin dakinta ta dauka ta mayar nasa
dakin saboda ta taka ta kamo tsahon Mu’azzam ta daura masa necktie, yana baya so ta
bari amma sai tayi, bata damuwa da gwasalensa ko kadan, ba dama ya zabi kayan sanyawa
sai tace ita basuyi mata ba, dole da wanda ta dauko zai yi amfani, undies dinsa ita ke wankewa
kal duk bayan kwana uku wadanda duk farare ne.
In tana son sa shi dariya to tace a baki zata bashi abinci. Rannan data dage sai ta bashi ta ciko
fork da dankalin turawa ta nufo bakinsa, abin yayi amusing dinsa sosai yace “Aalimah mai
yasa bakya ji ne wai? Ni kuma gotai-gotai dani zan tsaya ki bani abinci a baki? Ki jira ki haifi dan
ki tukunna sai ki yi ta bashiâ€. Sai ta rangwadar da kai tana masa wani irin kallo da ita kanta
bata san tayi ba tace.
“Allah zai bani ne!â€.

Mu’azzam sai ya samu kansa da amsa fatan Aalimah a cikin ransa na Allah ya bata Da. Sai
dai method din samun dan har gobe bai san ta ina zai zo ba. Amma kwarai shima yake fata da
addu’ar ganin dan kansa a duniya. Bai san irin soyayyar da wannan dan zai gani daga gare
shi ba.
Abin da ta sa a gaba yanzu shi ne, neman Dr. Nebrass, kwarai ta ke son ganawa da shi. Amma
ta rasa hanyar kai wa gare shi. Itama ta san wasa ta ke ta taba wayar Mu’azzam, yadda
yake kaffa-kaffa da abarsa kamar munafukin miji mai mata hudu. Dabara ta zo mata, tunda dai
ba ya shiga bayan gida da waya. A wani marece ta yi sallama ta shiga dakin, asabar ce ba ya zuwa aiki, kuma gab ake da shiga

lokacin sallar azahar.
Ko kallonta bai yi ba, yana bisa keken motsa jiki da ke can gefe a dakin. Waje ta samu ta zauna,
in ta ce ba ta jin ciwon shakulatin bangaron da Mu’azzam ke yi da ita a wasu lokutan ta yi
karya, sabida ba haka mijinta mai sonta ya sabar mata ba. Sai dai ta sa a ranta zamanta da
Mu’azzam zaman jihadi ta ke yi. Zaman son maida shi mutum kamar kowa, mai cikakkiyar
rayuwa kamar kowanne dan Adam. Albarkacin mahaifinsa da nata, wadanda ba su rage ta da
komai ba a rayuwa. Kuma alhamdulillah ta san cikin kashi arba’in cikin dari (40%) tayi
nasarar sauyawa Mu’azzam halayensa da dama.

Tunda an ce babu magani na farat daya a kan lalurorinsa, a ganinta dabarunta za su yi aiki
wajen ba shi ingantacciyar rayuwa. Sannan fisabilillahi ta fara shiga halin ha’u’la’i
mai tsanani da gangar jikinta, wanda har ya soma shafar lafiyar barcinta da sukuninta, bukata
irin ta kowanne dan Adam mai lafiya a cikin gangar jikinsa, musamman wanda ya san cewa
yana da aure. Kuma ga mijin yana tare da shi ko yaushe.
Dadin dadawa yawan shigewa Mu’azzam da ta ke yi duk da ya nuna ba ya so a yanzu yana
tasiri sosai a zuciya da gangagar jikinta. Ita kuma a wannan dan tsukin ta zama infatuated
akansa. In fact, bata taba jin son kusantar wani da namiji a duniya irin yadda take ji akan
Mu’azzam ba. Amma shi ko a jikinsa. Barin keken motsa jikin ya yi ba tare da ya ce da ita ci kanki ba don ya san wata matsalar ta zo
masa da ita, wadda yau hutawa yake son yi, bashi da lokacin sauraronta, “you…. and your
problems†(kamar yadda yake kiranta), ya shige toilet don dauro alwala. Aalimah ta yi wuf! Ta
dauki wayarsa, ta lalubo lambar Nebrass ta shigar cikin tata, ta ajiye masa. Fitowa ya yi daure da alwala, a lokacin da ita ta ke shirin barin dakin. Ciki-ciki ya ce da ita,
“Ki zo mu yi jam’iâ€.
Ba tare da ta juyo ba ta ce da shi,
“bani da tsarkiâ€.
Ta fice ta ja masa kofar.
7/9/21, 7:20 PM - Buhainat: RAAZEE'S



Bayan ya idar, ya zauna bisa darduma yana tunani. A tun sanin da ya yi wa Aalimah bayan
aurenta da Aboulkhair yarinya ce mai kunya da kawaici, ko kwayar idanun shi ba ta iya kallo,
wani irin respect ta ke ba shi irin wanda ta ga Aboulkhair na ba shi. Haka farkon zuwanta
gidansa wannan halin bai canza ba ko kadan. Me ya sa ta sauya halin ta rana daya? Ta ke so
shi ma sai ya sauya ko ta wanne hali? Haushinta da yake ji yau na wadannan sababbin halayen
ne da ta aro ta yafa rana daya, ta cika masa gida da su. Wanda ke nufin tana da mission a
kansa da ta ke son cikawa, amma ba halinta bane. Aalimah ba son shi ta ke yi ba in ya yi
la’akari da tsayin lokacin nan ba ta taba neman shi da ya ba ta hakkinta na aure ba. Wata
zuciyar ta yi saurin kare ta da cewa “ita za ta nema ko kai?
A al’adarta ta iyaye da kakanni, miji ke kai kansa ga matarsa ba matar ke kai kanta ga mijin
ba. Ko babu soyayya mata basa jurewa wannan. Kuma ta san kana da lalura, tsoron hakan ma
na iya cire mata sha’awar komaiâ€.

Yana wannan tunanin ya ji motsinta tana shigowa. Daga kai ya yi ya dube ta a hankali, doguwar
riga ce a jikinta (milk colour) samfurin Oman, yadin kamar na roba, don haka ya fiddo surar
jikinta shapely, ta daure kanta da dankwalin rigar, gashin kanta ya kwanto ta baya. Ya samu
kansa da kasa dauke ido a kanta. Wani magnet na jan idanunsa zuwa gareta. Ya kasa dauke
ido a kanta.
Ba tare da ta ankara da irin kallon da yake mata ba a yau take ce da shi.

“Nan zan kawo maka lunch, ko in bar shi a dining?â€
Zuba mata idanu ya yi kamar wani maganadisu na fizgar zuciyarsa zuwa gare ta. Kamar wanda
aka yi wa wahayi; ji ya yi duk wani nauyinta da shakkarta da yake ji, a yau ya kau daga
idanunsa. Hannunsa ya mika ya kamo nata a hankali, tare da ambaton sunanta da sassanyan
sauti daga can karshen makogaronsa. Sai jinta ta yi gaba daya a jikin Mu’azzam ba tare da
ta shiryawa hakan ba, ya soma wani irin sunsuna ta tun daga wuyanta har cikin jikinta. Turaren
da ya dade yana ji daga nesa nesa yana dimautar dashi yau ya samu completely a jikinsa.
Aalimar da ya dade yana kallo daga nesa nesa yana kintata laushin fatar jikinta da sulbin
bakinta, yau ya samu kwance a jikinsa.
And the skin is softer than he imagined.
Samun kansa yayi da rungumeta sosai tare da manna ta a kowacce kusurwa ta jikinsa.
Ajiyar zuciya yake saukewa a jejjere kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa. Is that the
feeling of being with a woman???
Idan kuwa shine it’s the most pleasurable, and most intoxicating feeling in the history of
man ever.
A hankali ya shiga kurdawa ta wuyanta har ya samu ya kai bakinsa zuwa ga nata.
It is a kind of gentle kiss wanda ya hautsinasu cikin dan lokaci bakidayansu.
Jikinta rawa ya soma yi tare da tasowar dadadden al’amarin da ta jima tana kokawa da shi
da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login