Showing 60001 words to 63000 words out of 128821 words

Chapter 21 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

stitches dinâ€.
Hannayenta biyu ta sa ta rufe fuskarta tare da yin baya da sauri za ta gudu. Da azama ya cafko
ta.
“Mun wuce wannan stage din Aalimah, ki kwanta in dubaâ€.
Yadda ya yi maganar cikin seriousness ya sa ta bi umarninsa.
Rungume ta ya yi sosai, yana fadin, “I’m sorry Aal, really sorry. Ba Aboulkhair ba ne ya
aikata wannan laifin sabon mijin Aalimah ne. Shi Aboulkhair ai kin san shi mai tausayi ne ko?â€.
Ya hau sumbatarta kusfa-kusfa yana rokonta ta yafe masa. Toshe masa baki ta yi da tausasan
yatsunta.
“Aalimahr is nothing but his wife wadda Allah ya yi masa izinin ya zo mata sanda ya so, duk
ta inda ya yi umarni, ita din gona ce a gare shi. In dai Aboulkhair ne yanzu ma ya maimaita
goman laifin nan a shirye Aalimah take da karbarsa cikin kowanne hali Monsieur Aboulkhair. Na
san ba rashin so ba ne, kauna ce. Kaunar ma ta Aboulkhair ga Aalimah, ‘yar asali, mai dogon
tarihi, wadda ta cancanci bugawa a littafi da na iya rubutuâ€.
Murmushi Aboulkhair yake ta yi, wanda ke fitowa kai tsaye daga zuciyarsa, a lokaci guda yana
mai cakuda yatsunsa cikin lallausar gashin kanta, ya ce,
“Gara da ba ki iya ba. haka kawai! Masu karantawar su ce… su ce…â€
Dariya Aalimah ta saki, ta ce, “Su ce me?â€
Karan hancinta ya kama ya ja da karfi, ya ce, “Na ki fada din, balle ki fara rubutun a kaina.
Ki dai fara a kan wannan Gumsun uwar taki mai budurwar zuciyaâ€.
Dukkansu dariya suka saki suna kewarta.
Ya ce, “A duniya ina son Aunty Gumsu, amma kwanan nan tana shigar min hanci,
she’sannoyingâ€.
Aalimah ta ce, “Ba ka ga abin da ta yi wa Basma ba, namu nafila ne. Har daga zanin gadon
ta ke tana shiga da shi daki-daki wai wadanda ba su gani ba su zo su ganiâ€.
Ya girgiza kai, ya ce, “Shi ya sa na zage na wanke abuna kada ta dauki hoto ta tura
Nigerâ€.

******
Kwanaki uku da suka biyo baya wata irin rayuwa ce mai cike da soyayyah, Aboulkhair da
Aalimah ke gudanarwa a gidansu. Su yi girki tare, su ci abinci tare, su yi wasa su yi dariya, su

sanya juna nishadi. Tarairayarta yake da jinya har ta warware. In ba wani abu da ya kama dole
zai sayo musu ba, ba ya fita. Sallah kuwa jam’inta suke su biyu sau biyar a rana. Nata
dakin sun kulle shi da nashi suke amfani. Sun yi wata irin shakuwa mai ban mamaki fiye da
shekaru biyar din baya. Yau suna zaune a dan karamin dining dinsu mai kujeru biyu kacal, wanda ke cikin kitchen dinsu
suna cin abincin rana. Wayarsa ta yi kara, ya kalle ta da gefen ido, bai yi niyyar amsawa ba don
a kwanakin nan ma amsa waya wahala yake masa, ta fi zama a kashe a yawancin lokuta kafin
ya karasa cinye kwanakin hutunsa da suka rage. Amma ganin mai kiran da sauri ya dauka. Aalimah na ganin yadda ya tattara bakidaya hankalinsa a kan wayar, ya kuma mike tsaye. Hatta
muryarsa canzawa ta yi, magana yake with utmost respect.
“Ban san ka shigo gari ba, da tuni na zo na kwance jaka. A yi min izini na kawo Aalimah ta
kwashi gaisuwa wajen babban Yaya, ba ta taba ganinka baâ€.
Ba ta ji amsar da Mu’azzam din ya bayar ba, ta dai ga Aboulkhair ya kara nutsuwa yana
rokonsa ya barsu su zo. Har yana fadin, ya fadi iya mintunan da zai iya ba su da bakinsa in
suka haura gobe kada ya barsu su sake zuwa. Takaici ya kashe Aalimah daga zaune, sarkin ina
ne wannan? Dole ne zuwa wajen nasa? Me yake rabawa da sai an roke shi za a je inda yake? Ba ta gama wannan tunanin ba ta ga Aboulkhair ya cillar da wayar tasa gefe ya rarume ta ya
mikar. Cike da zumudi ya ce, “kiyi girki, wanda ya fi kowanne dadi mu kai wa Mu’azzam,
ki hanzarta mintuna talatin kawai ya ba mu in mun je, yana da wata seminar gobe da
(Concophillips oil Gass) yana shiri, kada ki bata lokaciâ€. Aalimah ta rausayar da kai, ta ce,
“Me zan dafa? Ban san me yake so ba?â€
Ya koma ya zauna ya hau lissafi.
“Girkin da ya fi kowanne dadi with aroma and maggiâ€.
Ba ta san sanda ta saki dariya ba, ta tabbata Aboulkhair yana matukar son Yayansa, ba ta taba
ganin ya dau lamarin wani da muhimmanci irin haka ba.
“Kowanne girki ai dole a sa masa aroma da maggi, I mean irin abincin da yake soâ€.
“Tashin hankaliâ€. In ji Aboulkhair, “Ai wato menu ake ba shi daga WALDORF ASTORIA
(mafi shaharar restaurant a Las Vegas) ya zabi abin da yake so, ni kaina ban sani ba. amma ke
me ki ka ga ya dace?â€
Aalimah kamar ta yi kuka, a ranta ta ce, ‘Haka kawai ina zaman-zamana za ka taro min
aradu da ka, wannan basaraken naka ai sai kaiâ€. A fili kuma ta ce, “Burabisko da miyar
tausheâ€.
Ya zaro ido, ya ce, “You are not serious. Gero zaki dafa masa ya shaqe shi? Tukunna ma
kin san wai wajen wa nake magana ne?â€
“Ka ce sunansa Mu’azzamâ€.
Ya ce, “Ba ki san Yayanmu ba ne?â€
Ganin kamar ya soma harzuka ta shiga nutsuwarta sosai, ita haka kawai ranta bai son
Mu’azzam din nan tun daga lokacin da ta fahimci irin life style dinsa, da maganganun da
kannensa ke yi a kansa na irin rashin kirkinsa da ginshirarsa, sannan shekaru biyar ta kwashe a
gidan Ishaq Raazee daidai da rana daya ba ta taba ganin sawun wannan Mu’azzam din a
gidan ba, da sunan ya zo gaida iyayensa. Sai dai kullum ta ji Mummy a hanyar zuwa gidansa,
what a life! Sannan yanzu ta kara fahimtar wani abu, Aboulkhair ba ya hada lamarin

Mu’azzam da na kowa, ita kanta ba a bakin komai ta ke ba in dai a kan Mu’azzam ne.
She has to be careful don tsira da mutuncinta a idon mijinta-mai-kaunarta.
Da kyakkyawan sauti ta ce, “Ina ganin mu yi masa tuwo. Ka fahimce ni Mon Amour (my
love), ba abin da ya saba ci ya kamata mu kai masa ba, ba za mu burge shi ba. African cuisine
shi ya kamata. Idan Mu’azzam ya kasa cin tuwo na ka mare ni sau ukuâ€.
Bai san sanda ya yi murmushi ba, amma kwarai ta bata masa rai da farko, zancen
Mu’azzam fa yake mata, amma ta maida shi kamar wani marainin wayonta. Kodayake ya
mata uzuri, ba ta sanshi ba, ba ta taba ganinsa ba, ba ta san komai a kanshi ba.
Wanka ya shiga kafin ta gama, ita kuma ta dukufa sarrafa kyakkyawan farin tuwon shinkafa da
miyar danyar kubewa da ta markadata da blander. Ta yi masa kyakkyawan tuki, ta kwashe shi
kananan malmala a farar leda ta jera a food warmer madaidaiciya. Kafin ta saka kaza a miyar
sai da ta soya ta, sannan ta zuba su a miyar suka dahu tare. Kafin ta gama zobon da ta jika da
ruwan zafi ya jiku, ta tace ta yi masa hadin danyar abarba da danyar ginger (citta), ta sa sukari
da pineapple flavour. Ta juye a cooler irin ta zuwa picnick din nan. Ta jera komai a kwandon
abinci har farantai da cokullan da za su yi amfani da su ta dauka. Sannan ta fada wanka.
Dukkansu sun yi tsaf cikin Hausa Attire, sai kamshi suke yi. Suna tafe a hanya Aboulkhair ya
kunna musu kira’ar Abdurrahman Sudaith cikin suratul Ma’idah, wadda ta kara sanya
nutsuwa da kwanciyar hankali a zukatansu. Aalimah cikin ranta cewa ta ke yi, yau dai za ta ga
Mu’azzam din nan, ta ga shin me ya taka a rayuwarsa? Wane ne shi? Wane irin mutum ne
shi? Zaman me yake yi shi kadai a gida babu iyali? Ba mamaki ma matan banza yake kai wa
gidan, wanda ko gaida iyayensa ba ya yi, ba ta zaton masa wata rayuwa mai albarka. Sosai ta
ke jin rashin kaunarsa a zuciyarta. Ta tuno kannensa da yadda suka tsane shi, da kuma yadda
kullum zancensa ya ratso cikin hirarrakinsu suke kiransa ANNOYING son of Mum. Kalmar da ke
da tarin ma’anoni masu yawa daidai da fahimtarsu. A saninta kalmar annoying na nufin
irritating, infuriating, tiresome kuma troublesome. Da ta tattara ma’anonin wadannan
kalmomi, hadida tattara su wuri guda in a nutshell suna nufin Yayansu Mu’azzam mai
yawan fusata ne, mai tayar musu da hankali (ta hanyar yi musu fada), mai tilasta su su yi abu
ko da ba sa so, mai yawan damuwa a karan-kansa, kuma mai tarin matsalolin rayuwa.
Idan ta jimlace wannan fassara a ma’auni na hankali da tunani da zurfin iliminta, za ta iya
fahimtar lamarin ba komai ba ne; is simply a subject matter that others around him are not
understanding what he is going through. Ita ce makalar da ke tattare da rayuwar Yayansu
Mu’azzam, har ta kai ta kawo cewa, he lack positive emotions like happiness and
laughter… wanda kannensa suka fassara shi yadda suka ga dama, ba tare da bin ba’asin
dalilan da suka mayar da rayuwar tasa hakan ba, ko abin da ya janyo masa wannan rayuwar da
yake ciki. everything has CAUSE! Wato komai yana da tushe.
Haka kawai ta ji jikinta ya yi sanyi, zuciyarta ta dugunzumarta da son sanin WANE NE
MU’AZZAM??? Za ta bi kwakkwafi ta ji mene ne cikin rayuwarshi haka da ya maida shi
hakan ta hanyar mijinta, mafi kusanci da shi ko da hakan na nufin canzawarta daga mai
harhada magunguna zuwa ethnographer ne. Shebecame extremely intrigued. Ta yi nisa cikin wasikar jakinta ta ji yatsun Aboulkhair saman fuskarta yana shafa kuncinta a
hankali, ashe ya jima da kashe motar a kofar gidan Mu’azzam.
“Mrs. Thinker tunanin me ki ke yi? Ga mu gidan Mr. Mu’azzam Raazi, taho mu jeâ€.
Sai kuma ya dakata alamar ya yi mantuwa, “In mun shiga kada ki zauna a kusa da ni,

kunyarsa nake ji sosai, har fiye da Daddy. Ko hannunki ba zan kama baâ€.
Dariya ta kama Aalimah matuka, da ma akwai wanda Aboulkhair ke jin kunya a duniya? Ta ga
dai a gaban Mummy ya ce da Gumsu ta dawo dakinsa su kwana, ita ya bari da ji masa kunyar.
Girgiza kai ta yi, ta murguda baki, ta ce, “In ka ce masa ma ba sona ka ke ba sadaka ta aka
ba ka, duk daidai neâ€. Hannu biyu ya dora a ka yana leken idanunta, amma ta ki yarda ta kalle shi, ya ce,
“Ya fi ki sanin yadda nake son naki, da wahalar da na sha kafin in same ki. Ba don shi ba da
ba’a kawo yau ba, da tuni na watsar da karatu na rungumi Aalimah a cikin gida. Da ma
karatun don shi nake yinsa, kuma with his support and encouragement, yau na tsira da ku
bakidaya (ita da karatun)â€. Murmushi ta yi tana kici-kicin fiddo kwandon abinci daga bayan motar. Ya karbe ta yana fadin,
“Idan ina kusa, ko Babyn mu ba za ki dauka ba balle wasu kayaâ€.
Wata harara ta sake masa, “Wai baby, har yaushe akai daren da garin zai waye?†Ta fada
a karkashin zuciyarta, tana dubansa ta kasan ido cike da so da kauna.
Aalimah ta daga ido a hankali tana kallon kyakkyawan gidan da aka kira mallakin Mu’azzam
Raazee ta hanyar rubutawa a jikin kofar shiga gidan, wanda ke cikin kebantacciyar unguwar
HillsboroughEstate, mai hawan sama da kasa. Irin gidajen da suka kira ‘Fairfield Terrace’
wadanda sai dai mallaka ba dai haya ba (rent). Wani mutum yana goge motoci da ya juyo, sai ta
gane shi, shi ne direban da ya debo su daga airport ya kuma kai su Mummy gida. Da fara’a
ya gaishe su, ya karbi kwandon hannun Aboulkhair ya bi bayansu.
A falon da suka fara tararwa Aboulkhair ya ce ta zauna ya hau sama ya kira shi. Da
gudu-gudunsa yake hade steps biyu-uku yana kiran, “Mu’azâ€. Har ta daina ganinsa.
Ta shiga wurga ido tana kallon wani irin English parlour da ko a talabijin ba ta taba ganin mai
tsari da kayatuwarsa ba. Ta fahimci gidan ba mai girma ba ne da yawa, amma a yalwace yake.
Komai fari tas a cikin falon, hatta curtains da kujerun leather duka farare ne kal-kal! Tana nan
tana baza ido ta jiyo takun Aboulkhair yana saukowa, amma ba ta ji taku na bayan nasa ba, duk
da cewa su biyu suke saukowa. His own steps ba ya making sound sabida babu takalmi a
kafarsa. Kuma ma dai hatta tafiyarsu ta bambanta, taku yake kamar basarake.
Kallo daya ta yi masa ta ji ba za ta iya ci gaba ba, kada idanunta su samu rauni, ko nakasu.
Domin kwarai kwarjininsa da cikar zatinsa ya dusashe ‘yan idanunta. Ga wata irin kamala da
charismatic personality. Da ganinsa ka ga ruwa biyu (Nigeria da Niger). Cikin iyayensa bai
dauko mutum daya ba, mixed appearances dinsu ya debo sabanin Aboulkhair fari tas! Kalar
abzinawa masu tarin sumar kai, Ishaq Raazee bakidaya. Shi Mu’azzam kansa babu tarin suma, wani irin saisaye ne mai aji. Kananan kaya ne a
jikinsa (farfetch) army green colour daga T/shirt har wandonta. Wani irin agogo daure a damtsen
hannunsa mara walkiya, sai daukar hankali samfurin ‘Blooming Dale’s’ ruwan azurfa.
Ya fi Aboulkhair tsayi, ya fi shi kauri. Alamu duk sun gama nuna mata he is living in an affluent
life of the western world wanda a duniyarta ba ta san da irin rayuwarshi ba, ko mutane masu irin
personality dinsa.
Duka wannan observations Aalimah ta yi su ne a kallon farko da ta yi masa, daga haka ba ta
kara ba. Fargaba ma ta shiga ta yadda za ta bai wa wannan handsome GENTLE din tuwo,
Aboulkhair ya fi ta gaskiya. Ji ta yi duk ta muzanta, ta soma Allah-Allah su bar gidan don ko a
fuskarsa ba ta hango wani maraba da zuwanta gidansa ba.

Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta. Tana jin maganganun da suke yi shi da
Aboulkhair sai Aboulkhair ya fadi biyar bai ba shi amsar biyu ba, kamar mai ciwon baki. A
karshe ta ji zaman mutum a gefe ya ja kujera karama ya zauna yana fuskantarta. Kamar daga
sama ta ji yana mata sannu da zuwa cikin harshen Hausa, sannan ya tambaye ta ya ya
bakunta, kuma ya ta samu kanta a Las Vegas?
Zamowa ta yi daga kujera tana amsawa, sannan ta gaishe shi cikin nutsuwa.
Ya ce, “Koma kujera ki zauna, ni ba surukinki ba ne, dan uwanki ne. Ya ya Kawu Mansour,
Mama Asi da Aboubacar?â€
Mamaki kamar ya zauta Aalimah, sai kuma ta tuna su ma mutanen gidan nasu ai sun sanshi,
har mamaki suke da ta ce ita ba ta sanshi ba. Kafin ta samu zarafin amsawa ya mike ya bi wata
kofa. Sai ga shi da lemon Sangria Mocktail cikin kofin gilashi biyu, ya mika mata daya ya zauna
da daya a hannunsa yana sha a hankali. Aboulkhair ya yi narai-narai da fuska, wai shi ba a ba
shi ba.
Murmushi ya yi, ya ce, “Na dade da yayeka, ka bar ni in yi wa bakuwata barka da zuwaâ€.
Ita dai har zuwa lokacin duk da ya saki fuska yana kuma kulata ta kasa sakin jikinta. Ta rike
kofin mai cike da kananan fruits kamar fruit-salad cikin ruwan grape juice, sanyinsa na ta ratsa
tsokar hannunta. Sosai ta ke so ta sha ko don ta ji ya dandanonsa yake, amma ba za ta iya sha
a gabansa ba. Ya tambaye ta abin da ta karanta, ta gaya masa. Sai ya juya ya dubi Aboulkhair yana masa
hararar wasa,
“Da ma kun zo garina ne don ku cika min gida da magani ko?â€
Dariya Aboulkhair ya yi, itama tayi dan murushin abinda yace din, ya ce, “Da na rubuta zan
bata ta hado in kawo. In har ita ma za ka nema mata ko cikin pharmacies din asibitinmu neâ€.
Ya ce, “Wannan abu mai sauki? Ka ba wa Dr. Kennieth takardunta. Aalimah could you work
at Las Vegas?â€
Murmushi ta yi, ta ce, “In ya amince(tana nufin Aboulkhair)â€.
Ya ce, “Karewar amincewa, ba ni na ce a nema miki ba? Youonly have to eradicate all kind
of smiles from your lips, daga sanda kika fita har ki dawo aikinâ€.
Murmushi Mu’azzam ya yi kamar bai ji ba, ya soma duba agogo (kada su shiga lokacinsa).
Aboulkhair ya janyo basket din nan gabansa, “Girkin dare ne amarya ta yi maka na neman
albarka, ta ce in ka kasa ci in mare ta sau ukuâ€.
Sunkuyawa ya yi ya bude yana murmushi, ya ce, “To zuba min in gani, ko Allah zai sa a yi
marin amarya a gabanaâ€.
Murmushi ta yi ta nade mayafi ta hau serving din, amma maimakon ta fara zuba masa, sai ta
fara zuba wa mijinta, tukunna ta zuba masa. Mu’azzam ya lura da abin da ta yi, ya kuma
yaba da hankalinta a ransa, “Miji first! Before anybodyelseâ€.
“Tastes goodâ€. In ji Mu’azzam.
Daga haka bai kara magana ba sai empty plate ya ajiye wa Aboulkhair a kan cinyarsa,
“Ina ya kamata a mara kenan?â€
Dariyar jin dadi Aboulkhair ke yi. Ya saci kallon Aalimah ita ma murmushin ta ke yi. Ya ce,
“Ban taba ganinka kana cin tuwo ba ne shi ya sa na yi mata musu. Ko Mummy ce ta yi sai in
ga ta maka wani girkin dabanâ€.
Mu’azzam ya mike yana fadin, “Na gode da ziyara da girki mai dadi amarya Aalimah.

Indeed bana son tuwo, amma na ji dadin naki, saboda kin yi shi da nutsuwa ga dukkan alamu.
Kamar yadda na fahimci ke ma kanki mai nutsuwa ce. I wish you the best. Have a good stay in
Vegasâ€.
Ya ciro biro ya yi rubutu a ‘yar takarda ya ajiye mata tare da wani dan kati, ya juya yana ce da
Aboulkhair, “Na sallame ku, zan sha magani in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login