Showing 24001 words to 27000 words out of 128821 words

Chapter 9 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

emotions and feelings din da ta kwana da su a kansa.
A karshe kuma ta yi wa kanta fada, ta gaya wa zuciyarta wannan al’amarin da a yanzu ta
gama fahimtar ‘soyayyah’ ne irin wanda ke kasancewa tsakanin mace da namijin da
suka kai munzalin balaga comes at a very wrong time for her! ( ya zo a lokacin da bai dace ba).
Sannan it could destory her parents dream on her… it can also destroy her future ( zai lalata

mafarkin iyayenta akanta, sannan ya rusa future dinta) idan ba ta sanya taka-tsan-tsan ba da
jajircewa a cikinsa. Ta sha jin yadda maza suke yaudarar ‘yammata su hana su karatu, su yi
musu cikin shege, iyayensu kuma su tsine musu su shiga karuwanci ko su haife shege.
Zuciyarta ba ta taba kawo mata tunanin aure nan kusa ba. Da wannan dalilin dama wasu da dama ya sanya tun safe ta ke yaki da zuciyarta a kan
Aboulkhair duk da cewa dan uwanta ne, ta san ba zai cutar da ita ba. Amma ba a shaidar maza
a wannan fannin, Mahmoud kadai zata iya shaida a cikin maza. Sannan shi da kansa
(Aboulkhair ) ya tilastawa zuciyarta ta ji tsoronsa daga yadda yake behaving ga kannensa tun
jiya. Sosai ta himmatu wajen yakice shi daga zuciyarta ta ke ta karatu tun safe. Sun yi lacca
biyu suna da hutun awa daya kafin su koma wata, shi ne ta roki Alex ya yi highlighting dinta
abin da ya shige mata duhu.
6/28/21, 7:32 AM - Buhainat: Aalimah

SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
07030137870

“…You goddam talkatives!Kuna duba agogo kuwa? Har downstairs nake jiyo karadinku tun
asuba. Kun hana ni barci, kun hana kunnena zaman lafiya. Kun san cewa doguwar tafiya na yi,
ina bukatar hutu, kuma ba abin da na tsana irin a hana ni barci da safe… za ku wuce ku karya
ku tafi, ko shi ma Daddyn sai kun makarar da shi ya hana ni barci saboda ku?†Turanci yake zubawa kamar Charles Dickens ya sauka a Massachusetts. Tuni jikin Aalimah ya
hau bari an fara abin da ta ki jini, wato (fada). Sum-sum-sum suka shiga wucewa, Allah ya so
duk sun gama shiryawa. Basma har da zumburo baki, Aalimah ce karshen wucewa ta gabansa
duk ta gigice. Babban abin da ke maida ita upset shi ne hargagi. Ai kuwa ta ci uban tuntube da
kafarsa ta dama, ta tafi za ta ci da baka. Da wani irin zafin nama ya taro ta da dukkan
hannayensa. Ido ya bude yana kallon cikin idanunta sosai da dukkan nasa idanun, kamar mai
son karanto al’amarin da ke cikinsu. Ba ya so ya yarda da abin da kyawawan idanun ke
gaya masa, cewa al’amarin da ke cikinsu, daya yake da wanda ya hana shi runtsawa a
tsayin daren bakidayansa.
Yadda nasa idon ya tasa ya yi jajawur yayi luhu - luhu haka idanun nan da ke kallonsa suke.
Sai dai kuma a nassi mai kyau na zuciyarsa na gaya masa, kada ya bari ta gane, dukkaninsu
are too young da soyayya! Yanzu ne suke kokarin gina future dinsu. Kafin haka, soyayya da duk
abin da ya shafe ta ba nasa ba ne. Infact, it’s out of his vocab bank (vocabulary bank). Zuciya ce dai da ba ka da iko da linzaminta. He has a mission that he want to fulfill(yanada uzrin
da yake son gabatarwa) kafin soyayyah. Yanzu ne yake shekara ta uku a jami’a, sannan
yana da mashahuriyar damuwa da ke danne duk wani situation da ka iya samun zuciyarsa, na
farin ciki ko na bakin ciki. He will help his sister to concentrate on what she’s here for (zai taimakawa ‘yar uwarsa
ta maida hankali kan abindaya kawota) ta manta da shi da duk abin da ya shafe shi.
A hankali ya lumshe idonsa na tsawon lokaci ba tareda ya san lokacin da yayi hakan ba,
sannan ya bude su a kan Aalimah, wadda ta yi suman wucin-gadi a hannunsa. Dago ta ya yi ta
tsaya da kafafunta, sannan ya sake ta, amma bai iya ci gaba da fadan ba, kamar wanda aka
daurewa bakin. Ita ce karshen fita, da sassarfa ya biyo stairs ya sauko daga benen. Bai kalle su

a dining ba ya wuce dakinsa.
Cikin quilt dinsa ya shige da sauri ya dukunkune kansa, zuciyarsa na racing wajen bugawa.
Numfashin da yake shaka ya ji yana sauyawa da wani irin mayataccen kamshi, kuma kamshin
(is feminine) wato na mace ne mai tada hankalin duk wani lafiyayyen Da namiji. Ya fahimci ma
kamshin daga jikinsa yake, in fact shi yake kamshin sexy perfume din (‘Nude’ by
Rihanna) wanda babu tantama a jikin Aalimah ya kwaso. Abulkhair ya ji komai nasa yana
canzawa har numfashinsa. Wani situation ne da bai taba tsintar kansa a ciki ba.
Ya dauki lokaci cikin yanayin da yake ciki din yana kuma neman hanyar samun sauki. First, he
have to get rid out of these clothes.(Gara ya cire kayan nan). Mikewa ya yi zaune ya soma
zare su daya bayan daya, sannan ya shige toilet ya sakar wa kanshi shower.
Saukar ruwan a tsakar kansa zuwa jikinsa na tafiya tare da kawo sassauci a bugun zuciyarsa.
Duka wannan ya faru cikin mintunan da ba su wuce goma sha biyar ba. Al’amarin ya zamo
tamkar wani majigi da ya gifta a idanunsa. Har mamakin kansa yake yi, tunda dai ba yau ya fara
ganin mata da yin alaqa da su ba. Matan ma ajin farko da suka amsa sunan mata a duk inda ya
yi rayuwarsa cikin kasar America, daga sakandire har jami’a.
Sunyi dukkan rayuwarsu a Washington D.C ainahinaikin da ya yi sanadin kawo mahaifinsu
kasar Amurka(consulate officer ne a baya). A Washington din duk suka yi sakandire shi da
Yayansa MU’AZZAM, shi Aboulkhair bai ma karasa a can din ba.Abubuwa da yawa suka
raba Daddynsu da Niger consulate America.Amma ba don dukkaninsu suna so ba. Na farko rashin lafiyar Mu’azzam, wanda likitoci suka bada shawarar inda hali a sauya
masa inda yake rayuwa zai fi jin dadin canza rayuwarsa, kuma a barshi a inda ya fi so. Sannan
kuma Daddyn ya samu hanyoyin budi daban-daban wadanda samunsu ya fi na consulatedin
kasarshi nesa ba kusa ba. Sannan lafiyar Mu’az tafi musu komai. Wannan ne mafarin
komawarsu Massachusetts ba don suna son garin ba.
Kamar wanda ya saba zama a Abuja ne a ce ya koma Adamawa ko Yobe. Sai dai Alhamdu
lillahi lafiyar Mu’az ta inganta.
Ya zabi Jami’ar Louisiana don ya yi nisa da Mu’azzam, saboda wasu dalilai da dama,
muhimmi shi ne; ba ya iya jure ganin Mu’azzam cikin halin da ya kan samu kansa.
Bai taba sanya al’amarin mata a gabansa ba balle ya dame shi. Burinsa kadai ya zama
‘psychiatric doctor’ don ya san mene ne matsalar Mu’azzam ciki da bai dinta, ya yi
masa maganinta. In haka ne, kenan abin da zuciyarsa ke darsa masa daga jiya zuwa yau
akan... Aalimah ba nasa ba ne! He has to be cautious in his relationship with her(dole ya zama
mai taka-tsan—tsan a mu’amalar shi da ita). Daga shi har ita, sunadafocus fiye da wannan
da zuciyarsu ke son kai su.
Kwankwasa kofar dakinsa ake yi, tun ana yi a hankali har aka soma yi da dan karfi.
‘shower’ din ya kashe ya janyo tawul ya goge kansa da jikinsa a gaggauce. A gurguje ya
saka kaya yana jiyo muryar Basma a kofar dakin nasa tana ambaton sunansa a
tausashe“Monsieur Aboulkhairâ€. (Kalmar‘Monsieur’ da suke kiran shi da ita is a
French-speaking word da ake amfani da ita don nuna girmamawa ga namiji kamar a ce Mr, ko
makamancin haka)â€.
Bude kofar ya yi kafin ya ce komai ta mika masa mukullin mota, “Daddy latti, ya ce ka yi
ajiye mu, in mun tashi ka dauko mu. Ya fasa neman direban tunda ga kaâ€. Ta fada tana dan ja
da baya koda zai kawo mata mari.

Harararta ya yi, sannan ya karbi mukullin. Ya san daddy ya yi haka ne don ya hana shi barcin
safensa. Ai shikenan, shi ma dama ya fara tunanin guduwa ya bar musu gidansu zuwa inda zai
samu hutun jiki da na zuciya sosai, ya yi huta daga tunanin bakuwar gidan su Aalimah mai
kokarin raba shi da numfashinsa da burikansa. Haka ya sanya su a mota ya kai su makaranta daya bayan daya, Aalimah na jin Khaleesat da
Basma suna rada a kunnen junansu,
“What’s wrong with this man ne?†(Me ke damun wannan mutumin ne?) In ji
Khaleesat.
“He come with strange behaviours, I’m praying not he becomes ANNOYING like the
other person†(ya zo da sababbin dabi’u, ina addu’ar Allah yasa kada ya zamo mai
ban haushi kamar daya mutumin)â€. Ta fada cike da damuwa.

Abulkhair na da kyakkyawan ji at times, sosai ya ji abin da suka ce. Ya dafe sitiyarinsa ya ci
gaba da sarrafa shi cikin gwaninta yana murmushi. Can kasan zuciyarshi kuma ya ji ba dadi for
calling Mu’azzam da ANNOYING da suke yi tunda suka fara wayo. Wane bayani zai yi
musu su fahimci. Yayansu is not annoying, but rather; he’s fighting with his destiny?(Yayan
su ba mai ban haushi bane, a’ah, yana gwagwarmaya ne da kaddarorinsa). Shekarunsu da
iliminsu sun yi kadan su san mece ce matsalar Yayan nasu?
Ya fara sauke Yesmin da Khaleesat, sannan ya kawo Basma da Aalimah har gaban block din
da za su shiga lacca, ya sauke Basma, ya kara gaba kadan zai sauke Aalimah ba tare da ya ce
da su komai ba. Da ta zo fita kasa jurewa ta yi sai da ta saci kallonsa, shi ma satar kallon nata
yake yi ta gefen idanunsa, har ta fice rungume da folder dinta a kirjinta. Tafiya ta ke yi cikin
nutsuwa babu waiwaye. Wani numfashi ya ja ya kuma sauke shi sharply, sannan ya ja motar.
Daga university of Boston kai tsaye ma’aikatar su Daddy ya nufa. Akwai abubuwa da yawa
da yake so su tattauna, wadanda suke bukatar nutsuwa, kuma wadannan yaran da hayaniyarsu
ba za su barsu su tattauna su a gida ba, sannan ba zai iya komawa gida ya yi ta jira har sai
Daddyn ya dawo ba, hypertension sai ya kama shi in tunanin Aalimah bai zauta shi ba. Yana nukatar karin bayani akan ta daga bakin Babansa. Yana kuma son jin me ya hada
iyayensa fada duk da ba yau suka soma ba, kuma kullum Mummy ce da laifi sabida anti-social
nature dinta. Ya kira ta jiya ya gaya mata ya zo gida zai yi four weeks winter holiday dinsa bai
ganta ba, ya kuma tambayi Daddy tana ina? Ya ce masa tana Las Vegas, ba tareda wani karin
bayani ba, ya tambaye ta yaushe za ta dawo?
Ce masa ta yi Daddyn ya kore ta, kuma ita ba za ta dawo ba sai Aalimah ta koma
Nigeria. Ya tambaye ta abin da ya faru ta ce ya tambayi wanda ya kore ta. Ko kadan bai sa
damuwar komai a ransa ba ya ci gaba da sabgoginsa don ya riga ya fahimci abin da ya faru.
Mummy and her anti-social nature and the existence of stranger. Maybe this time around
Daddyya motsa kwanjinsa, ita kuma tunda tun farko ba haka ya sabar mata ba ta kasa dauka.
Haka ya yi ta kiyasce-kiyasce har ya iso ofishin Daddy.

Sai da sakatariyar Daddy ta yi masa iso, ya kuma bi layin mutum uku da ke kan layin ganin
Daddyn, daga bisani ya samu ya shiga. Fridge ya fara budewa ya sha ruwa sosai. Kansa ya
dau zafi da yawa, Daddyn na kallonsa yana ci gaba da aiki cikin na’ura mai kwakwalwa.
Sannan ya zo ya zauna a kan kujerar da ke fuskantar makeken tebirin Ishaq Raazee. Dan Nijar

din da ya rikide ya zama gawurtaccen Ba’amurke cikin shekaru ashirin da bakwai tsayin
zamansa a Amurka. Ishaq Raazee ya raini ‘ya’yansa da rainon Bature ta hanyar maida
su manyan abokansa, daga matan har mazan. Ba sa iya boye masa komai na rayuwarsu. Shi
ya sansu fiye da sanin da mahaifiyarsu ta yi musu. Shi tashi soyayyar ba ta hana shi ba su
tarbiyyah ba, amma ita ba ta san komai ba sai son ‘ya’ya da kokarin ganin sun fi
‘ya’yan kowa gata da jin dadi.
Duk amincin Abulkhair da Babansa yau ya samu kansa da kasa bude mishi cikinsa da amayar
masa da damuwarsa. Sabon al’amarin da ya hana shi bacci daren jiya bakidayansa, ya
hana shi nutsuwa tun wayewar gari.
Ya zo gaban mahaifinsa don ya gaya masa ko ya samu sassauci, amma ga shi ya kasa.
Kallonsa Daddy ya ci gaba da yi yana murmushi, bai ce komai ba shi kadai ya san me ya
fahimta tun jiya a tare da Dan nasa. Amma tunda bai furta ba bari ya bi shi da yadda ya zo
masa. “Mummy, na yi magana da ita ta ce kai ne ka kore taâ€.
Aboulkhair ya katse shirun nasu ganin Daddy bai da niyyar tankawa.
“Ni ban kore ta ba, zabi na bataâ€.
Ya fada ba tare da ya dauke kai daga aikin da yake yi cikin na’ura mai kwakwalwa ba.
Abulkhair ya yi dan jim! Kafin ya ce,
“Is that related to Aal… I mean Aalimah?â€. Ya fada kansa a kasa, muryarsa na sarkewa
da ya zo furta sunan. Tun jiya in zai furta sunan sai harshensa ya sarke ya rasa dalili.
Murmushi Daddy ya yi, ya kashe system din gabadaya ya juya kujerarsa mai tayoyi baya ya
fuskance shi da murmushi bisa lebbansa, “Pronounce the name properly (furta sunan yadda
yake daidai)â€.
Kunya ta rufe Abulkhair, ya kasa dago ido ya kalli Babansa.
Ji yake yana dagowa Daddy zai karance abin da ke cikin idanunsa tsaf! Tunda ga shi yana
kokarin karanto rudanin da ke tattare da muryarsa akan furta sunanta. Shi kuma ba zai so
hakan ba, saboda shi kansa bai yarda da kansa ba. Bai yarda da feelings dinsa are morethan
emotion ba. Bai yarda zuciyarsa ta kamu da son Aalimah ba, don a ganinsa babu dalilin hakan. Abin da ya yarda da shi shine there are certain characteristics about her da za su rikita
kowanne Da namiji mai cikakken hankali ba shi kadai ba. Her well-structured body, her pointed
nose… these thick eye-lashes… this red soft lips are all breadth taking! (Wannan ginannen
jikin nata, wannan tsayayyen hancin nata, wadannan jajayen tausasan lebban, wannan
cikakken gashin idon da gashin girar, duka masudauke numfashin mutum ne!) Kowanne namiji
zai yi mafarkin samunta matsayin matar aurensa!!!
Shirun Abulkhair ya yi yawa, sannan ya ki dago kansa. Daddy ya ba shi mintoci masu kyau don
ya gama duk tunanin da zai yi, amma ganin ba shi da niyyar magana kuma ya kasa dubansa,
sannan yana cinye masa lokaci, sai ya kira sunansa cikin nutsuar murya. For all he know,
Abulkhair dinsa ba miskili ba ne, Allah ya sa kada Aalimah ta sauya shi. In hakan ta faru ya ya
zai yi da miskilai biyu? A Aboulkhair yake samun duk abin da yake so daga aboki, he is cheerful
as well as passionate. Dayan, da shi da babu, duk daya. Ba rashin lafiya kadai ke aiki a jikinsa
ba, har da hali. Tunda yana samun sound-medical treatment.
A wannan din yake jin dadi, yake samun duk abin da yake so daga aboki, ba zai so abin da zai
yi spoiling farin cikin Aboulkhair ba, zai yi duk wani kokari ya samar da shi gare shi, ko da hakan

na nufin… hadiye sauran tunanin ya yi, don yana ganin nan din ba filin yinsa ba ne ba.
Dago kansa ya yi ya dubi mahaifinsabut he is still lowering his gaze (har yanzu yana yin kasa
da ganinsa) duk a kokarinsa na kada mahaifin nasa ya karanto idanunsa.
“Wouldn’t you speak out abin da ya kawo ka? Kana ganin ayyukan da ke gabana,
sannan dube ka ko wanka ba ka yi ba, dubi kayan jikinka, dubi gashin kanka. Dubi idanunka,
bana jin duk son ka da barci yau ka yi shi yadda ya kamata, ka koma gida za mu yi maganar
Mummyn in na dawo, amma nan office neâ€. Yana so ya gaya masa ba maganar Mummy ce kadai ta kawo shi ba, in da sabo ai sun saba da
cases din Mummy da yin yajinta zuwa wajen Danta. Gara ya yi ta zama a gaban Daddyn har ya
gama aikin su koma gidan tare, a kan ya koma ya zauna shi kadai a gidan. Bai san me zai faru
da shi ba, he’s afraid of going back to Boston University. Tunda can din ma in ya je bai san me zai aikata ba. Gara nan din sau dubu a kan ya koma gida.
“Zan jira ka Daddy har ka gama, sai mu koma tareâ€.
Ya samu kansa da furta kalaman daki-daki ko Daddyn ya fi fahimtarsa. Amma Daddyn ya nuna
shi bai fahimci komai ba.
“Ni kuma bazan iya ci gaba da aiki na kazo ka sani a gaba ba sai ka ce wani uwata. In dai
uwarka ce na ce ban kore ta ba zabi na bata. In za ta iya sona da duk wanda ya shafe ni ta
zauna, in ba za ta iya ba she could go to someone who has no relatives, but Ishaq Raazee is a
family Man. Wannan shi ne kawai sakona gare ta. Abin da ta zaba determines ci gaba da
zamanta gaban ‘ya’yanta or notâ€.
Sosai ya fahimci Daddyn, amma har yanzu bai yi magana a kan gabar da yake son ji ba. Kuma
da alama ba shi da niyya. Ya ci gaba da zama, ya ci gaba da yin shirun.
Daddy dai kallonsa yake yana cewa a ransa, ‘I wouldn’t, untill you did (ba zan yi ba har
sai ka yi)’.
Mikewa ya yi ya dauki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login