Showing 96001 words to 99000 words out of 128821 words
Chapter 33 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf
mai gaskiya tsakanin Mummy da Daddy?
Shi yana so ya yiwa mahaifinsa biyayya don ya gama da shi lafiya ita kuma Uwa ce mai jin qan
abinda ta haifa mara cikakkar lafiya!
7/5/21, 8:20 AM - Buhainat: HABUBAKAR ADO
#######################################################
Cikin satin suka biyo jirgi da komai nasu suka baro kasar Amurka. Bari na din-din-din. Ishak
Raazee na mai jin wata irin kewa wadda sabo ke haddasawa na mamayar zuciyarsa. Mummy
na mai jin kamar ita daya ta rage a fadin duniya sabida kewar mijinta da ‘ya’yanta. Saidai
ko kadan bata yi nadamar hukuncin da ta zartas ba. Yesmin na kuka kamar ranta zai fita a kan
rabuwar iyayenta, suka taho shi da Moiram da diyarta Nurat, ya baro mata Yesmin ne don rage
mata bacin rai.
Haka Mummy ta yi kokarin shanye damuwarta wannan karon ba tare da ta raba ta tare da
Mu’azzam ba, ganin cewa bai jima da barin gadon asibiti ba. Kuma in ba za ta manta ba
Aboulkhair ya hane ta dora wa Mu’azzam damuwa, ko dai ta shanye kayar ta ita kadai, ko
ta raba ta tare da shi (Aboulkhair) din, amma sharing dinta da Mu’azzam babbar illa ce ga
kyakkyawan treatment din da yake samu.
Ko da ta koma office a washegari da niyyar bada hakuri a maida ita bakin aikinta wani ta tarar a
mazauninta (JP MORGAN CHASE) ba su daukar wasa da aiki, ko da kuwa da excuse. Balle ita
nata babu excuse din ma. Rana daya aka nemeta a kasar aka rasa. Tsabar rudanin rayuwar
data samu kanta ya mantar da ita cewa ita din ma’aikaciya ce, ma’aikaciyar ma ta
babban bankin Amurka irin JP Morgan. Haka ta dawo kafafu a sage, ta soma neman wani aikin
ta yanar gizo, amma har watanni uku suka shafe bata dace ba. Sakamakon matsin lambar da
musulmin kasar ke fuskanta a lokacin daga sabuwar gwamnatin Amurka karkashin mulkin
sabon shugaban kasa Donald Trump. Da yawa sai komawa suke kasashen su na asali. Ba don
Yesmin da ke zuwa makaranta ba Las Vegas za ta tattara ta koma bakidaya, in Mu’azzam
ba zai rike ta ba ita da autarta, ya san yadda zai yi da su. Shine kadai dolenta a yanzu.
******
FLASHBACK
An sallami Mu’azzam ranar wata lahadi, sati guda kacal ya kara a gida, sannan ya koma
aikinsa. Ya hada wayoyinsa, ya kira duk wanda ya dace ya gaisar. Ciki har da Mummy, ta gaya
masa tana Boston amma ba ta gaya masa cewa Daddy ya sake ta a kansa ba. Sosai ta koyi
hadiye damuwa, in ta tuna da Aboulkhair. Ta san da yana raye ransa zai yi matukar baci, za ta kiyaye abin da ba ya so a bayan ransa. Ta
kasance mai bata masa rai da hakan a sanda yake raye. Zata kasance mai kiyayewa a sanda
babu shi. Ta ce masa Daddy yana Niamey, kuma ta turo masa kudi cikin account dinsa kafin ya
samu albashi ya soma shigo masa ta san zai bukace su sosai. Sosai ya yi godiya, yana mai jinjina soyayyar uwa ga abin da ta haifa, ta Mummy is special. Ita
dai ‘ya’yan ta kawai. Su samu jin dadi shine burin ta. Kada su nemi wani abu su rasa a
rayuwar su. Bazata taba canzawa daga hakan ba.
Ya kira Daddy suka yi hira sosai, inda ya gaya masa ya koma Yamai, ya samu aiki a can da
hukumar hulda da kasashen wajen su, yanzu kuma ya samu wani makeken fili kusa da gida ya
saya ya fara gini. Gini yake so ya yi one in town wanda dukkansu zasu sake a cikin sa.
Ya cigaba da gaya masa amon muryarsa dauke da kauna irin ta uba ga dansa, irin tsarin
duplex din da yake so a yi masa. Yace sai yafi gidansu na Boston kyau nesa ba kusa ba, zai
masa part din sa guda wanda zasu ke sauka in sun zo shi da iyalinsa. Sosai ya baiwa
Mu’azzam dariya. Ya canza position din rikon wayar daga dama zuwa hagu ya cigaba da
sauraron almarar Daddy. Koko ya ce mafarkin Daddy. Ba tare da Daddyn ya kula da karbar da
yake yiwa zancen nasa ba ya cigaba da labarta masa cewa har dakin yaran su za’ayi a
cikin bangaren nasu, a zuba duk wani nau’I na kayan wasan yara. Mu’azzam tausayin
mahaifin nasa yayi matukar kama shi, su iyaye wato har kullum fatan su nagari ne ga
‘ya’yan su ba ruwansu da reality din da rayuwar ‘ya’yan ke fuskanta.
Ji yayi idanunsa na son kawo ruwa, don haka ya matsu su yi sallama da Daddy. Ko kusa bai yi
masa zancen mahaifiyarsa ba har suka yi sallama, hausawa suka ce wai ido da kunya. Ba zai
iya kallon tsabar idanun sa ya gaya masa ya saki uwarsa ba sabida ta zabi zama a kusa da shi
ta bashi kulawa. Sai Mu’azzam ya dauka za ta bi su ne daga baya in ta gama kintsawa,
tunda ita ma’aikaciya ce. Bincike-bincike da zakule-zakulen halin da wani ke ciki da ma tun
fil azal ba halinsa ba ne shi.
Cikin dan lokaci Daddy Ishaq ya gama ginin kyakkyawan duplex dinsa a nan unguwarsu
plateaux suka koma shi da Gumsu. Wannan ya kawo tabbataccen kwanciyar hankali a zukatan
iyaye da ‘yan uwansa. Ranar litinin ya soma shiga sabon ofishinsa a Ministère des affaires
ètrangères na kasar Niger. Duk da ko kusa ba za’a hada sauki da sukunin rayuwar yanzu da wadda ya yi a baya ba,
yafi jin dadin rayuwar yanzu, akan ta baya. Cike yake da godiyar Allah da ikhlasi a zuciyarsa, da
albarkar iyaye baibaye da shi. Kullum sallolin su biyar cikin jam’i suke yin su shi da ‘yan
uwansa da mahaifin su a masallacin dake like da (main house) dinsu. Babu wanda ya san ya
saki Mummy, sai Malam da Inna.
Mummy ta dukufa neman aiki a yanar gizo don saving dinta ya fara yin kasa sosai. Kason data
ke karba duk wata na shares dinta duk a cikin su da lalurorin yau da kullum yake tafiya.
Rayuwar mai tsada ce sosai. Ta dukufa neman aiki ba ji ba gani amma kamar wadda uwa ta
cewa jeki kya gani ko aptitude babu wanda ya kira ta duk da experience dinta. Ita ke dauke da
nauyin karatun Yesmin, cinsu da shansu da maintenance din gidan, ga wanda ta ke turawa
Mu’azzam duk da ba shi ya tambaya ba kuma ya hana ta amma ta ki ji, kullum gani take
kamar albashinsa baya isar sa sabida tsadar magungunansa da rayuwar da yake yi mai tsada.
Tana cikin wannan halin aka zo aka ce ta tashi daga cikin gidan masu shi za su shiga, aka nuna
mata shaidar mallakar takardu da komai.
Ba da saninta ba Daddy ya dade da sayar da gidan ya karbe kudinsa ya tafi da su kasar
haihuwarsa don ya gina gida acan, da kuma niyyar sa ta fara kasuwanci da su irin wanda ya
taso ya ga Malam da manyan yayyunsa na yi, wato na shigo da kayan abinci daga kasar
Faransa zuwa jihohin kasar Niger. Bala’i goma da ashirin ga Mummy, Ishaq ya shammace ta, bata taba tsammanin zai sayar
da gidan nan ba, daga karshe kan ba yadda zata yi ta tattara ta taho Las Vegas ita da Yesmin
gidan Mu’azzam.
Mu’azzam sai dawowa office yayi ya gansu da iyayen kayansu tirim! Sun gyare dakin da
Mummy ke sauka in tazo sun baje suna barcin gajiya. Ya tura Harrison yayo musu takeaway din
abinci. Kwanansu uku kacal hayaniyar Yesmin ta fara hana Mu’azzam sakat, duk da
kokarinsa na bin shawarar kawunsa Mansour na ya bude zuciyar sa ya kaunaci ‘yan uwansa,
ya ba su kauna da kulawar da Aboulkhair ke ba su, yayi acting na mutum biyu a gare su, ya ga
cewa abun kamar da wuya ba zai iya ba! Ya yi duk iya kokarin sa amma ya kasa. Mummy ta
riga ta gama shagwaba Yesmin ta yadda bai isa ya tsawata mata ba yanzu zai ga bacin ran
Mummy, kullum Yesmin sanyata take a gaba tana kuka wiwi kamar ‘yar goye kan wai su
koma Boston bazata iya barin makarantun ta na can ba ko a maida ita cikin ‘yan uwanta. Ita
bazata iya karatu a ko’ina ba sai a Boston. Mummyn kuma tayi ta aikin lallashi amma
Yesmin ba ta fasa komai cikin shagwabar ta. Wannan ba karamin kular da Mu’az yake ba,
yayi mata tsawa kuma cibi ya zama kari daga Mummy.
Zaman Mummy da Yesmin a gidan, su ba zuwan bakunta ba kamar yadda suka saba, a’ah,
wannan karon zama suke nufin yi na har illa masha Allahu. Ba abunda yake so a rayuwarsa irin
(kadaici) yadda zai samu damar ayyukan sa na office a nutse da zurfafa bincike akan aikin
nasa. Amma shikenan yanzu bashi da hutu da nutsuwa a gidansa? Kullum cikin ciwon kai yake kwana, muddin yana cikin gidan. Ga shi Mummy ta ce Daddy ya
sayar da gidansu ne. Wato babu ranar da zasu bar shi ya sarara. Shi ba abun ya ce su tafi ba,
ina za su je? Su dafa wannan su dafa wancan, duk gidansa ya dume da kamshin abinci kamar
wani restaurant abin da shi kuma ba ya so tunda ba iyali ya aje ba. Mummy enjoys cooking in
her life. Dabara ta fado masa, ba don ya gaji da mahaifiyarsa da kanwarsa ba sai don ya samu
nutsuwa yadda ya saba. Ya kira Daddy ya hau rokonsa don Allah ya zo ya tafi da Mummy, ya
gaya masa zamansu ya takura masa, basa barinsa yayi bacci da aiki a nutse. They are giving
him headache. Yesmin is very noisy. Kuma Mummy bata son laifinta. Daddy ya yi ta dariya har
da kyakyatawa har ya godewa Allah, a karshe ya ce da Mu’azzam.
“Shin mutum ya taba gajiya da uwarsa da kanwar sa?â€
Mu’azzam kamar zai yi kuka, ya ce, “Daddy ka fahimce ni, ni ba gajiya na yi da su ba, I
love quietness, tunda suka zo na rasa samun sa, sannan suna mayar min da gida kamar gidan
mata, alhalin ni ba aure ba. I want my house to be calm, cool, like before. Don Allah Daddy ka
zo ka tafi da suâ€. Damuwarsa ta bayyana karara cikin magiyarsa. Ga mamakinsa ko a jikin Daddyn sai cewa ya
yi,
“Ku je ku yi ta cakudawa a haka, sonka ta ke, tunda har ta zabe ka a kaina. In ka ji ciwon
kan ka sha paracetamol, in ka kasa zama da ita waye zai iya?
Gara ma ka sauya hali, ka fadada zuciyarka ka kaunaci kowa naka ka kuma koyi zama cikin
mutanen da suka zame maka dole, don sauya maka akalar rayuwa zan yi bakidaya nan ba da
jimawa ba, insha Allahuâ€.
******
Malam Raazee na cin tuwon dare Daddy Ishaq ya yi sallama, amsawa ya yi yana wanke
hannunsa cikin bowl na silver. Daddy ya dauke kwanukan bayan ya gama wankewa ya yi gefe
da su, ya zauna a muhallinsu.
Sake gaisawa suka yi irin gaisuwar su ta buzaye. Malam ya dube shi cike da kulawa yana tsane
hannunsa da tawul. Ya ce,
“Ya ya Mu’azzam? Ya jikin nasa? Mun kwana biyu, ba mu yi waya baâ€.
“Mu’azzam yana lafiya, ko dazu ya kira ni…â€.
Nan ya ba shi labarin yadda suka yi dazu, suka yi ta dariya. Malam ya ce, “Ina ruwan
Zulaiha, kaza uwar son ‘ya’ya, shi kuma dan gashi yana gudunta kamar kyanwa da
beraâ€.
Daddy ya ce, “Abin da ta kasa ganewa kenan, shi Mu’azzam duk wata mu’amala in
dai da shi za a yi ta, to a yi ta daga nesa-nesa, ko ya ya za ka zauna mai a gida, to fa zai ce ka
takura masa. Zulaiha ta kasa ganewa, kodayake tausayinshi ta ke ji, shi kuma ba ya tausayin
kanshiâ€. Haka suka yi ta hirar Mu’azzam da Zulaiha suna cin dariya, Daddy Ishaq na fadin “Da
kafarta za ka ganta ta dawo tunda masu gidan Boston suka bukaci abinsu, idan ita ba ta bar
masa gidan ba na rantse shi zai bar mataâ€.
Aalimah ta yi sallama a dakin a hannunta karamar kwarya ce mai cike da nonon Rakumi mai
dumi sabon tatsa, kai tsaye Malam ta nufa. Da murmushi a fuskarta ta russuna har kasa ta ce,
“Malam ga shi Inna Bintou ta ce a kawoâ€.
Hannu biyu ya sa ya karba ya ce, “Madalla da Bintou da jikanyar ta, an gaishe ku,
madallahâ€.
Ta juya za ta fita, sai kuma ta dawo ta tsuguna.
“Malam Aunty Gumsu-Moiram ta yi min waya dazu tace in je in mata kwana biyu, na ce
mata sai na tambaye ka tukunnaâ€.
Ya ce, “Ba yanzu ba Moiram ta yi hakkuri, bana so ki je ko’ina sai kin warware dukkanki,
har yanzu ban ganki kamar yadda nasan ki ba, a bai wa Gumsu hakkuri inji niâ€.
Fuska a sake ta ce, “toh Malamâ€.
Ta juya ga Daddy ta gaishe shi cikin nutsuwa da sanyin muryarta.
Ya ce, “Anya Aalimah? Haka dan Adam zai rayu da damuwa bayan ba abin da za ta sa, ba
abin da za ta hana? Dubi kasusuwan wuyanki, dubi idanunki yadda suka zuzzurma ciki. Don
Allah don Annabi Aalimah ni Baban ABOULKHAIR ina mai cewa a karo na sau ba adadi, ki yi
hakuri. Ki yi hakuri! Ki yi hakuri…â€. Ko kafin ya kai karshe ya fahimci hawaye sun gangaro daga idanunta. Muryarta ba ta fita sosai.
A sanda take cewa.
“Na yi hakuri Daddy, na dade da yin hakuri. Zuciyata ce ta ki daukar reality, ce min ta ke ba
shi ne ya mutu ba, zai dawo. Don Allah Daddy da gaske ne??â€
Malam Raazee da Daddy Ishaq suka juyar da kai don share nasu hawayen.
Daddy ya ce, “Aalimah, wanda ya mutu ba ya dawowa. Ki yarda da ayar Ubangiji
subhanahu wata’ala, kullu nafsin za’ikatul maut. Aboulkhair ba zai taba dawowa ba har
abada. Ki bai wa rayuwarki da ke gaba kofa ko ya ya ne ta samu farin ciki kin ji Aalimah?â€
Daga kai kawai ta yi, don ba ta da abin da za ta yi bayan daga kan, ko ta yarda ko ba ta yarda
ba, ya ce,
“Tashi je ki cikin ‘yan uwanki, Allah ya yi miki albarkaâ€.
Jiki babu lakka ta mike ta wuce cikin gida.
Bayan wucewarta da minti biyar daga Malam har dansa Ishaq babu wanda ya kara yin magana.
Daga bisani Malam din yayi gyaran murya ya ce,
“Ni sai inyi ta wani tunani, a duk sanda Aalimah ta zo gabanaâ€.
Daddy ya ce,
“Tunanin mene ne Malam?â€
Malam ya girgiza kai, har da daga hannaye sama ya ce, “Uhum-um-umh-uhm, a bar kazar
‘yan boko cikin gashinta, yanzu in aka yi kokarin fige ta sai kun dawo da George Bush da
Mungo Park gidan nan sabida kawo nassi na bijirewa da nuna kin amincewaâ€.
Murmushi Daddy ya yi, shi ma zuciyarsa ta yi nauyi. Babu mamaki idan ba irin tunaninsa Malam
Raazee ke yi ba. Bai ja zancen da nisa ba ya yi wa Malam din sallama ya mike ya kwashi
takalmansa ya fice don tafiya gidansa, wanda ba shi da nisa da gidan iyayensa trackable
distance ne. 7/5/21, 11:40 AM - Buhainat: HAULATU66
Aalimah ta yi sallama a shigifar kakansu. Daga shi sai Daddy 2 ta tarar a dakin, babu kowa. Ta
samu gefen Malam ta zauna. Malam ya dube ta cikin kulawa, ya ce,
“Uwata me ya faru ne?â€
Ta saci kallon Daddy 2 wanda kallon fuskarsa kawai ta yi ta ji ya ba ta tausayi, da alama cikin
damuwa mai tsanani yake. Ta ce, “Malam wai Daddy ne ya ce zai min aureâ€.
Yayi murmushi.
“Ke kuma ba kya so ko?â€
Ta ce, “Malam ba zan iya mantawa da Aboulkhair ba, balle in hada rayuwa da wani a
bayansa, kullum ji nake a jikina zai dawo. Idan ya dawo ya same ni da aure, na ci amanarsaâ€.
Murmushi Malam ya yi kafin ya ce, “Ko da a ce MU’AZZAM ki ka aura ba za ki manta da
shi ba?â€
Idanunta suka kara girma, at the same time suka kankance suka firfito waje, cikin sanyin murya
tace.
“Malam, wanne Mu’azzam din?â€
“Mu’azzam Raazee Yayan Aboulkhairâ€.
Wannan karon Daddynta ne ya ba ta amsa, with every affirmation a cikin muryarsa.
Sai Aalimah ta gurfana a gaban mahaifinta a kan gwiwoyinta. Rokonsa ta ke idan wasa yake yi
tana mai rokonsa da girman Allah da darajar zatinsa da ya bari, Mu’azzam tamkar uba yake
a gare su daga ita har Aboulkhair. Gara ya aura mata mazan duniya bakidaya ta amince, a kan
ya aikata wannan babban zunubin a gare ta. Kamata ya yi ya tasar da ita daga durkuson da ta yi a gabansa kamar mai neman gafara.
Idanunsa sun kada sun yi jajir da tausayin ta. Sai dai ko sama da kasa za ta hade ba ya jin
akwai abin da zai sa shi fasa hada wannan aure, muddin yana raye ita ma Aalimah tana
numfashi. Ya ce, “Ki nutsu Aalimah ki fuskance ni, Mu’azzam shi na so tun farko ki aura Allah bai
cika min wannan burin ba. Idan har da gaske kina kaunar Aboulkhair ba abin da za ki yi ki nuna
masa wannan kaunar a lokacin da kasa ta rufe masa ido, banda tallafar rayuwar Mu’azzam.
Kin sani Aboulkhair ba shi da wani buri da ya wuce Mu’azzam da lafiyarsa. Aalimah ba kya
tausayin Yaya Ishaq? Mutumin da ya dauke ki babu bambanci da ‘ya’yan cikinsa ya
karrama rayuwarki? Kina sane da cewa ba shi da buri a yanzu da ya wuce