Showing 12001 words to 15000 words out of 128821 words

Chapter 5 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

so ta yadda har ake
ganin ta fi karfinsa. Amma wannan karon ya sha alwashin motsa kwanjinsa ba zai bari ta juya
shi ba when it comes to Mansour. A kan komai ta yi ta yi, amma ban da wannan dan uwan.
Ita da kanta Aunty Zulaiha ta fara gajiya da irin zaman da ta ke yi da mijinta da ‘ya’yanta
a kan wata banza Aalimah. Walwalar gidan completely reduced. Ga shi duk yadda ta so ya
kwantar da kai ya lallashe ta ya soma ba ta excuses a kan zaman yarinyar tare da su ya ki yin
hakan. Ta fahimci ma makarantar da zai kai Basma tare ya kai su wanda ke nuna babu ranar
barin ‘yar Mansour gidan.
Dole ta sauke makaman yakinta ta nemi sulhu da shi, maimakon ya ba ta excuses ita ce ta
dawo tana bayarwa. Tana gaya masa ita ba danginsa ne ba ta so ba, she don’t want the
house to be bulky (bata so gidan ya cika) sannan yaranta za su matsu, dakin ya yi musu
kadan, sannan a budget dinsu na abin da suke spendingmonthly babu karin komai, in karatu ta
zo yi America ya maida ta hostel za ta fi maida hankali ta yi karatu sosai.
Wannan karon ma banza ya baiwa ajiyarta, yana tauna silly(wawayen) maganganunta a ransa,
ko daya babu gamsasshe. Halinta ne dai da ya sani na rashin son mutane ba danginshi kadai
ba har nata ma ba su ishe ta kallo ba, yadda shi yake zumunci da ‘yan gidansu da iyayenta
ita ba ta yi. Aunty Zulaiha dai ta ga babu mafita, wankin hula zai kai ta dare dole ta dawo ta lallaba abinta,
ta ce ta yarda Aalimah ta zauna, amma a bude mata rufaffen dakin Mu’azzam da ke kasa ta
koma, akalla dai su Basma ba su matsu ba.

Wannan karon ne ya dago manyan idanunsa na IYALAN RAAZEE da suka gigitata, ya dube ta
da su da kakkausan kallo. Sun kada sun yi jazir. Sosai ta razana, don bai taba yi mata irin

wannan kallon ba, in ba ta yi kuskure ba sai ta ce har tsana-tsana (hatred) ta hango a cikin
kyawawan idanun da suka rudeta ta fada a makauniyar soyayyarsa.
Ya dade yana mata kallon har sai da ta ja baya don tsoron kada ya kai hannunsa gare ta.
“Da abin da na haifa, da wanda Mansour ya haifa daya ne a wajena, babu bambanci. You
can book an apartment for rent in wannan ya muku kadan ke da ‘ya’yan nakiâ€.
Duk inda Aunty Zulaiha ta ke tsammanin Ishaq Razee a kan zaman Aalimah a gidansa, sai ta
same shi ya wuce nan. He’s no longer the Ishaq she know, father of her children, apple of
her eyes…! Mene ne abin yi a gare ta? Surrender! Zuciyarta ta ba ta amsa, wato sallamawa ga
zaman ‘yar Mansour a tare da su. Ta yi amfani da wata hikimar daban ban da tursasawa. A sati na biyu, kwana goma sha hudu da zuwan Aalimah America ta fahimci wani abu, Aunty
Zulaiha ta canza mata sosai, tana janta a jiki in har Daddy na gida ko yana zaune a waje. In ba
ya nan kuwa kashi ma ya fi ta daraja.
Maganar da ya gaya mata ta cewa;she can book a rent with her children (zata iya kama haya
itada ‘ya’yanta idan gidan ya musu kadan) a kan Aalimah ta tsaya mata a zuciya, ta
kuma sanya mata TSANARTA. A da, ba tsanarta ta yi ba, apparentlybako ne ba ta so a cikin
gidanta. Amma reactions dinsa da amsoshinsa gare ta sun nuna yana son ‘yar dan uwansa
kamar, ko ma fiye da yadda yake son ‘ya’yansa. Wani abu da zuciyarta ta gaza dauka,
ba kuma za ta iya dauka din ba.
Duk kokarin Aalimah na kin sanya damuwa a rai don tana da masaniyar yadda ta illata
kwakwalwar mahaifiyarta dole ta fara damuwa da halayen Mummy Zulaiha. Tana riga kowa fita
a gidan saboda banki, amma duk suna riga ta dawowa. Duk walwalar da ta ke ciki da ta jiyo
horn din motar Mummy, gabanta zai yanke ya fadi, ta soma neman inda za ta adana kanta. Basma da Khaleesat suna da hankali, kuma zuwa yanzu sun lura Mummy is not happy any
more da zaman Aalimah tare da su. Musamman suka same ta a daki suna lallashinta kan ta
karbi Aalimah, she’s nice, she’ll come to like her too(tana da kirki, itama zata so ta) idan
ta saki zuciyarta da ita. Ba tare da sanin Aalimah ba. Ce musu ta yi su tashi su ba ta wuri, ita ina ruwanta da wata sister dinsu? Ko a kanta ta ke
zaune?
Sosai ta saki rai da Aalimah, har da tsokana in Daddy na zaune. Rannan ta ce masa ma ya ba
ta kudi za ta yo mata shopping ta lura akwai abubuwan da Aalimah bata da su. Dadi ya ji har
ransa ganin ta fara son farin cikinsa.
A hankali yake nuna mata Aalimah yarinyar kirki ce ta ba ta dama ta fahimce ta, ba zai kawo
wadda za ta cutar da su ba, above all jini ba wasa ba ne, jinin da ke yawo a jikin Aalimah, shi
yake yawo a jikin ‘ya’yanta. Ta bude zuciyarta ta so mutane, mutum rahma ne, kuma
falala gare shi. Duk da cewa zama da shi da wuya. Amma in kayi katari dana kirki rahma ne a
gareka. Ya gaya mata irin canjin da yaransu ke samu tun zuwan Aalimah, yanzu har Yesmin ba
ta bari sallah ta wuce ta.

Maimakon zuciyarta ta yi sanyi, sai ta kara zafafa ta fusata fiye da kima. Is she here to study, or
to distort her children? (Ta zo karatu ne ko ta zo canza rayuwar ‘ya’yanta?) Amma ta
hadiye ta kuma ba shi hakurin rashin fahimtar ta. Credit card dinsa ya bata ma gabadaya na
bankin (Well Fargo) ya ce ta ciri duk abin da zai isa ta yi musu siyayyar dukkaninsu har ita.

A daren ranar bayan an yi dinner suka koma kan kujerun falon suka zazzauna. Mummyn aiki ta
fara yi cikin system dinta ba ta kallonsu. Daddy news yake kallo a tashar Aljazeerah, ya canza
ya mayar CNN. Basma na danne-danne cikin Ipad dinta, Khaleesat alqur’ani ne a hannunta
tana manne da Aalimah wadda ita kuma text book ne a hannunta tana duba course din da suka
yi yau, littafin introductory ne ga fanninta na harhada magunguna, in Khaleesat ta karanto aya
cikin suratul Yasin, sai ta ci gyaranta ba tare da ta duba Qur’anin ba ita. Idonta na kan
littafin hannunta.
Yesmin ta ce, “Aunty Aalimah, yaya ma ki ka ce addu’ar shiga toilet? Zanje nayi
fitsariâ€.
Ta ce, “Allahumma inni a’uzu bika minal khubsi wal khaba’is. In an fito kuma a fito
da kafar dama a ce, Gufranakallahummallazee azhab anniyal azaaâ€.
Yesmin ta maimaita, sannan ta nufi bandaki da gudu. Bayan ta dawo kowa ya ci gaba da abin
da yake yi, kamar daga sama Yesmin ta sake cewa,
“Mummy ina dankwalinki? Ba kyau zama ba dankwali. Dubi yadda Shaitaan duk ya bi ya yi
miki fitsari a kaâ€.
Ai kuwa kowa ya cira ido ya dubi Mummyn, har Daddy, sai a lokacin ya lura duk cikinsu babu
wadda ba ta daure kanta ba sai Mummyn, kuma ya san da ba haka suke ba. Dariya ce ta kama
shi, yadda Mummy ta yi wani kicin-kicin da fuska tana kallon Yesmin kamar ta kai mata
mangara. Wai ita ce kanta da fitsarin Shaitaan? Tabbas a bakin Aalimah ta ji wannan nassin.
This is not her words, beside(wadannan ba kalaman ta bane, tukunnama) yaushe ma
dukkaninsu suka koyi daura kallabi? Oho! Ko silin gashinsu daya babu a waje, sun bi sun
dukunkune abinsu cikin hula. Ba ta ce mata komai ba ta ci gaba da abin da ta ke yi, zuciyarta a
cunkushe. So she want to change her chindren to total ‘yan kauye as she is ko me? Ba ta
son shisshigi da katsalandan cikin al’amarin ‘ya’yanta, ina dalili? Aalimah must go!
She cannot take it.
Tun zuwanta sau daya ta yi magana da gida, shi din ma da wayar Daddy. Ta nemi wayarta ta
rasa sama ko kasa, ba ta sani ba can wani loko a cikin kayanta ta shige. Cike da kauna Daddy
ke dubansu tana ma Khaleesat kari da ka, ba tare da ta duba Qur’an ba har suka gama.
Khaleesat ta karanta Fatiha suka shafa. Cewa ta ke gobe za ta bai wa Shaikh (Malaminsu na
islamiyya) mamaki, ta iya inda zai dora musu tun kafin kowa a ajin ya iya. Wata islamiyya Daddy
ya kai su ta mutanen Libya in sun taso daga boko. Khaleesat ta haye sama tana fadin bacci ta
ke ji, bayan ta sumbaci iyayen daya bayan daya.
Ya ce, “Aalimah kina kiran su Aboubacar kuwa kuna gaisawa? Dazu Mansour ya kira ni ina
office ya ce in ba ki, ni kuma lokacin bana gida, na ce masa in na dawo I will check on you, me
ya sa ba kya kiransu?â€
An tabo mata babbar damuwarta a dan tsukin. Ta sunkuyar da kanta, ta ce, “Daddy, tunda
na zo ban ga waya ta baâ€.
Fada ya hau ta da shi, ya ce, he’s no longer her Dad kenan, tunda har ba ta da waya tsayin
wannan lokacin ba ta bude baki ta gaya masa ba. Hakuri ta shiga ba shi tana fada masa ta san
wayar ba bata ta yi ba, wani wajen ta jefa ta ta manta.
Ya dubi Aunty Zulaiha ya ce, “Yaushe za ku je shopping din ki sama mata waya?â€
Ta ce, babu damuwa za ta ba ta daya daga cikin nata kafin su je, sai weekend za su fita.
A gaban Daddy ta cire layin daya daga cikin kan wayoyinta guda uku, ta bai wa Aalimah. Hannu

bibbiyu ta karba ta yi godiya.
Ya ce da Basma gobe kafin su fita ta kunna mata WiFi dinsu, ta kuma saya mata credit in sun
fita gobe.
Sallama suka yi wa iyayen suka wuce dakinsu har Yesmin don su kwanta. Babu mai yin latti a
cikinsu. Ta lura duk al’ummar kasar ma babu lateness cikin dictionary dinsu.
A washegari Basma ta sayi layin ta sanya mata, ta loda mata kudi. Yau ba su yi lecture da yawa
ba suka koma gida. Ko abinci ba ta ci ba sai da ta kira kowa nata da sabon layinta. Duk ta
haddace lambobinsu a kanta. A karshe ta kira Mahmoud, yana zaune a office dinsa cikin
ma’aikatar hukumar zabe ta Katsina a lokacin, aiki ya dan ragu masa, ya dafe kai a kan
tebirinsa. Ba tunanin komai yake ba sai na Aalimah. Tunda ta tsallaka Amurka bai kara jin
duriyarta ba, she didn’t give him a call as she promised (bata kira shi ba kamar yadda tayi
alkawari). Ko ta samu dadin duniya ne ta manta da shi? Ya sani tun tafiyar Aalimah, wata
zuciyar na gaya masa ya yi wauta, babbar wauta kuwa da ya bari ta tafi ba tare da
gamsasshiyar magana a tsakanin iyayensu ba.
Aalimah a Nigeria ma zubinta na ‘ya’yan manya ne, balle ta haura Amurka. Ko kadan
ransa bai son wannan tafiyar, don dai ba yadda zai yi ne, tunda bai isa ya hana iyayenta iko da
ita ba, tunda ba aurenta yake ba. Sai dai wani saqo can na zuciyarsa na gaya masa… this is
the deadly mistake(kuskure mafi muni) da ya taba yi a rayuwarsa, babu wanda ya san da
zancensa da Aalimah daga nasa iyayen har nata. A hakan kuma wai yana jira ta dawo ya aure
ta. Yaushe? Ta wacce hanya?Kuma a ina? Sanda zata dawo ta kara shekaru da sanin ciwon
kanta. Za ta iya haduwa da wani ya karkatar da zuciyarta daga gare shi… ‘NO!!!†Ya fada
da karfi, tare da naushin tebirin da ke gabansa. Yana da kyakkyawan zato a kan, Aalimah,
duniya ba ta gabanta. Za ta rike soyayyarsu da amana no matter what ya yarda da wannan!

Wayar da ke gefensa ce ta hau ruri, ta yi har ta katse, ta sake ci gaba kafin ya dauka. Lambobi
ne rututu irin na kasar waje. Wani sanyi ne ya tsirga a zuciyarsa, ya amsa da sauri.
“Aalimah!â€
Ya fada in exclamation.
Bai ba ta damar cewa komai ba ya dora, “You keep me anxiously waiting(kin barni inata jira
cike da taraddadi) kwana ashirin da daya, Na dauka ma kin manta da niâ€. Ya fada da karyewar
sauti.
Sosai ta ji tausayinsa ya kama ta, ta san yadda Mahmoud ya damu da ita, yake kuma sonta ita
ko rabin hakan ba ta masa. Tunda ta zo ba za ta ce ga lokacin da ta ware ta zauna don ta yi
tunaninsa ba. She justadmires him, she likes him,because he has brain.(Kawai tana son shi
sabida hazakarshi). Haka nan tana jinsa a ranta sakamakon shakuwar da suka yi da shi na
shekara guda a gidansu. He is good and well-mannered (yanada kyawawan dabi’u).
Sanda za ta taho a waya suka yi sallama, ya tada hankalinsa sosai, kiris ya rage ya yi mata
kuka. Ya ce, tsoro yake ji, tsoron rasa ta. He’s afraid, and he don’t know WHY?.
Murmushi ta yi, murmushin nan nata mai nutsar da zuciya, duk da Mahmoud ba ya ganinta ya ji
sautin murmushinta. Shekarunta goma sha shidda, amma ma’abociyar tsinkaye ce, amma
tsinkayenta bai taba tsinkayo mata akwai abin da zai sa ta ki Mahmoud ba, ko ta juya masa
baya. Cewa ta yi da shi, “We cannot run-away from our destinies, but I’m hoping that destiny tied us togetherâ€.

(Bazamu iya gujewa kaddarorin mu ba, amma ina fatan kaddarar ta bar mu tare).

Wadannan sune kalaman Aalimah da yake kwana ya tashi da su tun tafiyarta, zuciyarsa na yi
musu fassara kala daban-daban, mai dadi da mara dadi. Wannan ne yanayin da yake ciki har
zuwa yau da ya samu kiran Aalimah. Ya lumshe ido ita kuma ta yi ajiyar zuciya. A hankali ta
shiga warware masa dalilin da ya sa ba ta kira shi ba tun zuwanta, she lost her phone, she has
been busy with school, (ta rasa wayar ta, tana cikin hidimar makaranta) ko su Mama ba ta kira
ba sai yau.
Ajiyar zuciya ya yi, ransa ya yi masa dadi. At least Aalimah ba ta manta shi ba bayan shigarta
USA. Suka shiga hira ya gaya mata har Aboubacar ya kira don ya samu lambarta ya gaya masa
su ma da lambar kawunta suke magana da ita, ya san in ta nutsu za ta kira shi. Ya kara da yi
mata nasiha kan ta kama kanta a kan wanda ya santa da shi, shi in son samu ne ma ta dinga
sa hijabi da niqabi he’s always afraid bai san dalili ba.
Dariya Aalimah ta yi a ranta tana tunanin ta ya ya wani zai ce yana sonta a nan? Duk abin da
yake hange ba haka yake ba, ga ‘yammata nan birjik masu mugun kyau da ya dame nata ya
shanye, abin da ta lura ma kowa is busy with himself a nan ba ruwan wani da harkar wani in ba
wani naka ba. Hijab kuma ai ba sai ya sa ta ba tana sa abinta (a lokuta da dama) duk da
kanana ne, amma ta san shigarta is fully Islamic.
Sai da Khaleesat ta shigo tana kiranta, sannan suka yi sallama da Mahmoud ta kashe wayar
gabadaya. Ba ta da ra’ayin shiga kowanne‘social media’ don yanayin karatunta,
sannan kuma, ba ta son hayaniya, ba ta da ra’ayinta.
Ranar asabar da safe Aunty zulaiha ta gaya musu su shirya za su je shopping da yamma kuma
za su shiga kasuwa. Daddy na gefe yana ta ‘making calls’, amma ya ji ta. Bayan ya
gama ya dube ta da murmushi ya ce,
“Umm Mu’az, ki kai su inda za a samu ready-madeAfrican wears ki saya wa kowa
yadda ta ke so, sun gaya min sun daina saka wando, sai ki hada musu da Arabian gownsâ€.
Cikin mamaki Mummy Zulaiha ta dago ta dubi Khaleesat, sannan Basma da Yesmin ta ce,
“Dalili? Are we in Africa or what?â€
Duk suka yi shiru suka sunkuyar da kai ganin yadda ta fusata ainun. Gab ta ke da ta kai musu
duka. A nitse Daddy ya bi ta da ido yana son karanto matsalar matarsa a dan tsukin nan,she
becomes pepper-tempared. Shin ita wace irin uwa ce da ba za ta iya bambance abu mai kyau
da mara kyau ga ‘ya’yanta ba? Al’amarin Mu’azzam bai isa ya zama iznah a
gareta ba? Me suka yi abin bacin rai a nan?She’sgetting angry easily a dan tsukin nan duk
da yadda yake kokarin kyautata mata don ta kara sakin ranta da Aalimah.
A nutse ya ce da ita“I think you are supposed to be happy, they are trying to adopt their
native culture (Na yi tsammanin farin ciki zakiyi, suna kokarin daukar al’adun su na gado)
su ajiye wannan mara tushen?â€
Tashi ta yi fuuu! Ta bar falon ba tare da ta ce da shi komai ba ganin yadda yaran gabadaya suka
zuba mata ido har Aalimah.
Safah da marwah Mummy ta shiga yi a dakinta. Tunanin hanyoyin da za ta bi ta kori Aalimah
daga gidanta ta ke yi from every direction ta rasa. A karshe ta samu guda daya, duk da ba ta da
tabbacin dorewarta da sahihancinta..
Kafin yamma ta yi kokari ta saki ranta. Yau ita da kanta ta shirya musu abincin rana. Aalimah ta

zo tana so ta taimaka mata don ta aiki Easther ta ce ta wuce ta ba ta guri, ba ta son karambani.
Su Basma da ma ba abin da suka tsana irin aiki, don haka ko kusa ba sa dosar kichin in ba
wani abu za su dauka ba.
Easther na dawowa ta kira ta gefe, ta sallame ta da kudi masu yawa, ta ce da ita daga yau ba ta
bukatarta, ta je ta nemi wani aikin, amma duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login