Showing 30001 words to 33000 words out of 128821 words

Chapter 11 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf


or twice in a week. And it shouldn’t contain deep emotional talks that would inturn arouse
his fantasies. It ought to stick on “how are you†and “how is studies?â€
Dariya Aboulkhair ya shiga kyalkyalawa kamar babu gobe. Shi kansa Daddyn dariya yake yi,
zukatansu suka yi dadi tamkar babu sauran damuwa a cikinsu.

Yana komawa dakinsa ya rufe kofa ya dauki wayarsa da niyyar ya kira Yayansa, amma sai ya
duba lokaci, lokacin shan magungunan Mu’az ne yanzu, yana sha kuma zai yi bacci. Kamar
ya kyale shi, amma sai ya ga ba zai iya ba, ya kamata yasan komai da ke faruwa tsakanin
Mummy da Daddy daga bangaren kowannensu don yayi sulhu. Ya manta da situation din
Mu’az da tunanin zai shiga lokacin barcin sa ya danna masa kira. Sai da ta kusa katsewa
kafin ya daga.

“I’ve been expecting your call since yesterday, where have you been?†(nayi ta
tsammanin kiranka tun jiya, ina ka shiga?â€

A cikin muryar akwai maturity, akwai nutsuwa da haiba, akwai gentleness, akwai kwarjini da
kamala, akwai wani abu wai shi ‘class’ da sanin ciwon kai. Sannan it is so caring as well
as affectionate ga wanda ake magana da shi. Shi ma wanda ya yi kiran respect ne da affection
zallah a tashi muryar. Ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya daidaita tone din muryarsa yadda ba zai
zama boring ga mai saurare ba, sannan ya zauna a gefen gadonsa ya yi wa wayar rikon aminci,
yadda ba za ta zame ba.
“Is Mummy beside you? Mummy na kusa da kai?â€
“No, ta shiga barci tun dazu. Ni ma I’m about to take medicines(gab nake da shan
maganina) in kwanta, wani aiki ne ya dan tsare ni da ba za ka same ni ido biyu baâ€.
“Kayi hakuri da rashin kiranka tunda na iso, bana cikin nutsuwa, I metatedious threshold
inthe house…†Ya warware masa komai; tun daga farko har karshe da nasa observation din
na halin Momy tun suna kanana. Da irin kukan da suka yi dazu shi da mahaifinsu. Amma bai
gaya masa he is in love da Aalimah ba, komai da lokacinsa. Shiru Mu’azzam din ya yi, kamar ruwa ya cinye shi. He didn’t cry. Ba abu kankani ke sa
Mu’azzam kuka ba, sannan ba ya jan magana da nisa, his words are specified, he is very
selective and picky before he utter a word. Amma duk sanda ya furta magana zata kasance ta
kunshi ma’anoni masu yawa a dunkule. Aboulkhair ya yi zaton sam ba zai yi magana ba har
sai shi din ya gaji ya ajiye wayar, bai damu ba, sabida ya san dan uwansa fiyeda kowa a duniya.
Ya san bynowzuwa yanzu ya gama tunanin yadda zai shawo kan matsalar iyayen nasu gaba
daya cikin dan wannan lokacin da ya dauka shiru.
Daga baya Mu’azzam din ya kira shi.
“This is totally opposite with what she told me…â€. (Abinda ka fadamin kwatakwata bai yi
dai-dai da wanda ta fada min ba). Mu’azzam ya fada cike da tausayin mahaifinsa.
Suka yi maganganu na maza masu hankali na dan gajeran lokaci, kafin Mu’azzam ya ce,
“Is the girl still in the house? (Har yanzu yarinyar na gidan?)â€
“Yes, she is, the nicest sister I ever met (eh tana nan, ‘yar uwa mafi dadin mu’amala
dana taba haduwa da ita a rayuwaâ€.

“Greet her for meâ€.
(Ka gaishe min da ita)

“Za ta ji insha Allahâ€.
“As for Mummy (Game da Mummy, ofishin su sun kirata jiya, kyale ta kada ka kirata don ka
rarrasheta, da kanta zaka ga ta dawo. Ka yi kokari ka gina kyakkyawar mu’amala a
tsakaninta da yarinyar kafin ka koma makaranta. Ka nunawa yarinyar yadda zata yi hakuri da
ita.Sukuma ka rabu da su za su shirya kansu a junansuâ€. (Yana nufin ita da Daddy) Da haka suka yi sallama.

******
ABOULKHAIR DA WAYAR AALIMAH!
Sai da ya gama komai da ya saba yi kafin ya kwanta, kama daga wanka, brush, shan black tea,
ya daura pajamas sannan ya shige cikin quiltdinsa da wayar Aalimah a hannunsa. ‘Yar

kankanuwar waya Daddy ya saya mata kirar Iphone. Contact list shi ne abin da ya fara shiga,
contacts din ba su da yawa, ba su fi ashirin ba. Ya ci gaba da scrolling contactsdin, akwai
mamere, watau Mamanta kenan, mon pere (Babanta), sai Bhaiyya, wato Yayanta Aboubacar da
harshen India. Sai ta Daddy, ta Basma, ta Khaleesat, Malam Raazii, Kawu Oussama, Kawu
Edrissa, Balkissa Eedrissa, Grandma Kasisi, Grandma Bintou. Sai lambobin maza guda biyar
wadanda ya ga ba zai jurewa zamansu ba.
Alex ya fara gogewa, ya goge Harrison, ya goge Mr. Edward Proffessor. Bai san cewa
course tutor dinsu ne ba ma. Harrison kuma course mate dinta ne. Lambar da ta rage guda
daya ce ta tsaya masa a makoshi, kuma ya kasa goge ta. Akwai bukatar ya dauke ta a tasa
wayar, sannan ya goge. ‘MAHMOUD’. Ba don komai ba sai don ya kawo karshen
alakarsu ko ma wane ne. Har wani heart ta makala masa bayan ta rubuta sunansa. Bai yi
mamaki ba, don yarinya kamar Aalimah ba yadda za a yi a ce ba ta da mashinshini har zuwa
wannan lokacin. But he’s jealous, in ya ce jealous to guda daya kenan. He is very-very
jealous! Don ya lura ko ma wane ne wannan Mahmoud din ba yau ya fara son Aalimah ba,
kuma bai fara don watarana ya daina ba.
Zuciyarsa ba ta gama tsinkewa ba sai da ya shiga message inbox. Sakonnin Mahmoud
din ne rututu masu barazanar tarwatsa kwanyarsa. Bai iya ci gaba da karantawa ba ya hada su
duka ya goge su daga doron kasa. Abu daya ya dan kwantar da hankalinsa, ba reply mai zafi
daga Aalimah, ga dukkan alamu ba ta damu da yin rubutu cikin waya ba, babu wani social
media da ta bude, she only text Mahmoud twice, saying that she saw his messages, she’s
doing morethan fine. She will call him when she is opportune, he know how tedious her studies
is. (Sau biyu ta yi ma Mahmoud sako, inda tace ta ga sakonsa, tana nan lafiya, zata kira shi in
ta samu dama, ya san yadda karatunta yake da tsauri). Wannan ne kadai ya dan sanyaya
ransa. Amma ya rantse gobe sai ya raba Aalimah da Mahmoud yadda zuciyarsa za ta buga ya
mutu ya huta.
Ya dauki lambar Daddynta, mamanta da ta Yaya Aboubacar. Lambobinsa ya zuba cikin wayar
tata, ya yi saving da Mon Amour (MY LOVE da harshen faransa), sannan ya yi mata
downloading din whatsapp application. Da niyyar cewa shi kadai zai dinga mata magana ta
cikinsa, not even Daddy karshenta kenan. Sannan ya koma cikin gallery na wayar, duka
yawanci selfie ne ita da Basma a makaranta, wani a mota, he can guess that she adores
Basma a lot (tasu ta fi zuwa daya).
Murmushi ya yi da ya tuna Khaleesat ko Daddy bai cika shiri da ita ba sabida I don’t care
attitude dinta. Tafi shiri da Mummy. Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskar da ta zame masa
madubin zuciya daga jiya zuwa yau. Ta rusa duk wasu plans da ya yi wa rayuwarsa, ta kuma
zamo babban kalubalensa na rayuwa a yanzu. Mallakarta is the greatest challenge of his life
now. Ban da barci ya fi kowa iya sata da Aboulkhair yau ma bai runtsa ba kamar yadda ya ga
dare da rana jiya.
Amma yau ya yi barci yadda ya kamata da wata irin nutsuwa da ya dade bai samu ba a
rayuwarsa.
Washegari, Aboulkhair ya yi wanka ya shirya cikin shirt da wando ‘yan gidan Nordstrom, rigar
orange ce da ratsin baki, wandon fari tas. Sumar nan ta sha taza ta kwanta luf a kansa. Samun
kansa ya yi da zakulo turaren da ya fi kowanne kamshi mai sanyi cikin tarin turarukansa masu
ban sha’awa, sannan ya fesa. Ya fi son shi fiye da dukkan turarukansa, saboda Mu’az

ke ba shi (SAUVAGE Dior). Duk wani abu kuma da ya fito hannun Mu’azzam is preciousa
gun Aboulkhair. Ya san dai ba yau ya fara fesa turare ba, amma shi kansa ya san wanda ya
fesa yau bai fesa shi don radin kansa ba.Is meant for AALIMAH ta ji yana kamshi.
Wani murmushi yake saki shi kadai yana yi wa kansa dariya. Sanda ya fito su ma duk sun yi
shirin makaranta suna dining suna karyawa har Daddy, sai Aalimah da ke ta shige da fice daga
kitchen zuwa dinning area din tana miqo musu abubuwan da suke bukata.
Sosai ya ji haushi, amma bai ce komai ba har ya zauna. Shi ma ita ta yi serving dinshi ba tare
da ta yarda sun hada ido ba.
Ya dubi Basma, “Ina mai aikin Mummy?â€
“Aal, ta hana ta zuwa by 6am ta ce ita za ta dinga yin breakfast, Easther ta yi lunch and
dinnerâ€.
Ya dubi Daddy ko zai ce wani abu? Ya ga bai ce komai ba, sai shi ma ya yi shiru. After all ita
mace ce kuma rainon Nigeria, she might be willing to do so. Shi kansa ya fi son cin nata abincin
a kan na Easther, tunda ya ci pounded yam sau daya. Amma anya hakan ba zai zamo takura a
gare ta ba? Muryar Daddy ya ji yana yi wa su Basma fada kan su dinga shiga kitchen din da safe tare da ita
za su fi sauri, kuma su ma su koya. Ajiyar zuciya ya yi cikin jin dadi.
Fara cin abincin ya yi, su kuma suka koma sama don dauko jakunkunansu da mayafansu.
Khaleesat da Yesmin da ma uniform ne a jikinsu. Daddy ya riga su ficewa, su ma mota suka
wuce don su jira shi, bai dade ba ya gama ya fito. Kofar direba ya shiga ya rufe, sannan ya mika
hannu ya bude kujerar gefensa. Basma za ta shiga, ya ce, “No, koma baya, daga yau seat
dinta neâ€.
Ta ce, “Who?â€
Harara ya galla mata ba shiri ta shige bayan don ta lura daga zuwansa zuwa yau he’s a
changed person. Aalimah ba da son ranta ba ta zauna a gaban, ba ta so ko kadan su Basma
su fahimci tsakaninta da Yayansu akwai wani abu, kunya ta ke ji sosai balle ta san Basma da
digimi da maida allura garma. Sai da suka hau titi sosai ya dan juyo ya dube ta. Ta yi masa kyau
sosai cikin doguwar riga ruwan kasa da veil dinta sakar kasar Kuwait. Takardun hannunta ta ke
dubawa tana da gwaji yau (test). A duk lokacin da ya dube ta his feelings for her heightened bai
san dalili ba. Cikin tattausar murya ya ce, “Babu gaisuwa Aalimah?â€
Ko su Basma da ke baya ba su ji abin da ya ce ba, sabida raunin muryarsa. Ba tare da ta dago
ba ta ce,
“Bonjour?â€
Ya amsa, sannan ya ce, “What time is your interval (lokaci na hutu tsakanin wata lakcar da
wata). Ta gaya masa.
Daidai lokacin da suka shigo Boston campus ya ajiye su ya juya. Ko da ya koma gida kasa
hassala komai ya yi, sai tunanin Aalimah. Tashi zaune ya yi daga kan resting chair ta falon da
yake kwance a kai, ya hau saman gidansu. Akwai wani balcony da galiban daddy ke zama da
yamma ya yi karatun jarida a weekends can ya je ya zauna. Wayarsa ya lalubo ya nemo
lambobin da ya yi saving jiya daga wayar Aalimah ya kira ‘UNCLE MONSOUR’. Gara ya
fara yi wa kansa yakin neman auren Aalimah kafin Daddy ya gama yangarsa ya fara nasa.

Dr. Monsour Raazee, na zaune cikin ofishinsa da ke cikin sabuwar jami’ar Bayero yana

marking takardun dalibai ya ga shigowar kiran mai dauke da lambobin kasar Amurka cikin
wayarsa. Amma kuma ba Aalimah ba ce ba, kuma ba yayansa Ishaq ba, sannan it is not his
darling son MU’AZZAM ISHAQ RAAZII, wanda sati ba ya shigowa ya shude ba tare da ya
kira shi ya gaishe shi ba, musamman a ranakun karshen mako. To ko Aalimah ce ta canza layi?
Haka ya mika hannu ya sanya ta a handsfree yana ci gaba da marking din da yake yi saboda
tsabar kwarewa da aikinsa.
“Assalamu alaikum Uncleâ€. Ya jiyo muryar saurayin mai wani irin accent shi ba bature ba,
shi ba balarabe ba, ba ma kuma za ka sanya accent dinsa a jerin na Hausawa ba duk da
uwarsa cikakkiyar bakanuwa ce.
“Ameenwa’alaikumus-salam warahmatullah, da wa nake magana?â€
Kunya da jin nauyi da nadama baki daya sukayi rubdugu a kan Aboulkhair, a girmansa ba zai
iya tuna rana ta karshe da ya kira wani cikin dangin mahaifinsa ya gaishe shi ba, tun suna yara
Mummy ke gaya musu they don’t love them, they are always saying ‘baku da
tarbiyyah’ don kawai ba sa sona!’ Ya runtse idonsa yana jin wata irin nadama tana ratsa shi. A shekarun girmansa kuma he is
very busy with schools musamman da ya fara karatun jami’a ya bar iyayensa ma bakidaya
ya tare a jami’a, sannan ga yanayin karatunsa, he hardly find time for himself ma balle ya
tuna mutanen da suka shafe shi. Ko askin kansa ba ya samun damar yi sai gashin na neman
rufe masa ido. Ko kadan bai dauko Mummy ba, sai idanunta da duhun fatarta, he is a perfect
photocopy of his father. Mu’azzam ne mai kama da ita, sai dai shi kuma ya yi hasken fatar
Daddy, bai yo yawan sumar kai ba, sannan he shaves regularly (yana yawan yin aski).
Ya yi nisa a tunani, wanda ya mantar da shi cewa ya kira waya har kawun ya amsa. Muryar
Kawun nasa ya ji yana tambaya cikin sanyin murya,
“Ko ABOULKHAIR ne?â€
Ya cije labbansa cikin mamaki mai cakude da jin kunya da jin dadi duk a lokaci daya, ya ce,
“Ni ne Uncleâ€.
“I guessedâ€. Inji Dr. Mansour, “Ya ya ku ke, ya Babanka da ‘yan uwanka da
mahaifiyarku?â€
“Suna lafiya Uncle, I’m sorry for not calling you. Nayi nadama uncle.Uncle na ji
kunyarka, amma ka yarda da niban taba mantawa da ku ba. Bana tare da iyaye na, ina karatu a
Louisiana shekaru hudu kenan. Yanzu ma hutu na zo, kuma nanda sati hudu zan koma.I need
your blessing!â€. Hausa yake iyakar iyawarsa tana subuce masa yana cakudo ta da turanci.
Dr. Monsour ya yi murmushi kamar yaron na kallonsa. Hamdala yake yi cikin zuciyarsa,
addu’ar mahaifinsu da kalaman mahaifiyarsu ba su fadi a banza ba. Inna Kasisi ta sha
cewa kowa ya daina damuwa da rayuwar Ishaq da ‘ya’yansa, idan ‘ya’yan na
halal ne da kansu za su neme su. Malam kuwa ya sha cewa, “Da izinin Allah kan
‘ya’yansa da jikokinsa ba zai rabu ba ko bayan ransa. Ishaq da ‘ya’yansa da suka
zama saniyar ware, yana rokon Allah ya karkato da hankalinsu gida, su rungumi ‘yan uwansu
da iyayensu.
Kiran sunan yaron ya yi wanda ya fada cikin damuwa da shirun Kawun nasa.
Ya ce, “Aboulkhair, Aboulkhair! Kana jina?â€
“Eh Uncle, I’m still onlineâ€.

Ya ce, “Ka daina damuwa, I’m your father, an halicci iyaye da dabi’ar zama masu
karbar uzurin ‘ya’yansu. Na ji uzurinka, kuma in gaya maka ban taba damuwa da hakan
ba, tunda na san lafiya ku ke. Amma ka dinga koyi da dan uwanka wajen kula da zumunci. Ya fi
ka yawan hidimomi tunda shi babban ma’aikaci ne, still ya rike danginsa kam-kam. He is
not with us, but we are feeling him beside us. (Baya tareda mu, amma jinsa muke kamar a
gefen mu). Sallar bara da ta wuce tare da shi muka yi sallar idi a Nijar, ya je Zinder (garin su
Inna Kasisi), ya je Tessaoua (garin su Malam Ibrahim Razee), har Arlit (garin su Inna Bintou) ba
inda bai je ya ga dangi su ma sun ganshi ba. Ga albarkar kakanninsa da iyayensa yana sha ta
ko’ina, ba ka yi wa kanka kwadayin hakan?â€
Ya ci gaba da kawo masa ayoyi da hadisai da Allah ya yi umarni da zumunci, da kyautata shi,
musamman ga maza kuma manyan jikoki a family. A karshe ya saka masa albarka, shi kuma ya
yi alkawarin zai ci gaba da kiran kowa. Ya ce yana son kiran Maman Aalimah da yaya
Aboubacar, amma bai sani ba ko sun manta shi? Dr. Mansur ya ce, “You are welcome to call everybody within your family, babu wanda ya
manta da ku ko don Mu’azzam. Allah ya yi muku albarka bakidayaâ€.
Bayan sun gama waya da Daddyn Aalimah ya dade a wurin, ya jingina da karfen balcony din
zuciyarsa ta yi masa dadi. Sai kuma ya fada wani tunanin. Wato duk yadda yake da tabbacin ya
fi kowa sanin Yayansa Mu’az har gobe bai zo rabi a sanin nasa ba! Abubuwan mamakinsa
yawa gare su, kuma ba wanda ya isa ya san cikinsa hatta da iyayensu idan aka zo maganar
abin alkhairin da yake yi a rayuwa. Sai dai ya tsinta nan da can kuma bai isa ya yi masa zancen
ba, yanzu zai ce bai san maganar ba, ko ya ce ya kyale shi da unnecessary magana, ba ya son
yin magana mai tsawo.
Ajiye tunanin Mu’azzam ya yi a gefe, don abubuwan mamakinsa ba masu karewa ba ne.
He is just far beyond everyone’s assumption (ya wuce da sanin kowa). He is a patient,
amma abubuwan da yake yi da yadda yake gudanar da rayuwarsa masu lafiya dari bisa dari ba
za su iya ba. Maman Aalimah Hajiya Aseeyaita ce mutum ta biyu da ya kira. Ita kam ba ta gane shi ba, sai da
ya kara da bayanin kansa sannan ta gane. Sosai ta shiga janshi da hira, tana tambayar
kannensa da mamanshi. Abin da ya ba shi mamaki, ba ta tambayi Aalimah ba, sai su Basma.
Abin ya burge shi kwarai da gaske. Kawaici wani abu ne mai kyau cikin al’adun malam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login