Showing 69001 words to 72000 words out of 128821 words

Chapter 24 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

ki ke samu? Aalimah kada ki kasance cikin masu dora wa
mazansu hidimar da ta fi karfinsu don ki wadata iyayenki. Mu din we’re contented with our
life ba mu nemi komai mun rasa ba, Aboulkhair me ya tara, yaushe ya fara aikin da ki ke
kwakularsa wadannan makudan kudaden?â€
Dariya Aalimah ta yi, sannan ta soma yi masa bayani, cewa kudin farko, na biyu da na uku duk
Mu’azzam ke saka mata cikin ATM don ta yi lalurorin gabanta ba tare da ta roke shi ba. Ita
kuma ba ta da bukata shi ya sa ta tura musu. Na yau din kuwa halak dinta ne, guminta ne,
albashinta ne na aikin da Mu’azzam ya samo mata daDesert Parkway Health Center. Dr. Mansour kasa magana ya yi, akwai matashi mai zuciyar riko da zumunci a duniya irin
MU’AZZAM ???
“Yaa Allah ka dubi wannan bawa naKa da tarin alherinsa da jin kansa ga ‘yan uwa da
sauran al’umma, Ka ba shi lafiyar da ka ke jarrabtarsa a kanta, ya yi rayuwa mai dadi kamar
kowanne dan Adamâ€. Addu’ar da Dr. Mansour ya shiga yi wa dansa Mu’azzam kenan,
wani Da mafi soyuwa a zuciyarsa cikin dukkan ahalin Raazee, manyan su da yaransu.
*****

Shekaru guda biyu kwarara kenan da wannan aure mai dumbin albarka, wanda ya zamo wani
tubali na hadin kan iyalin Malam Ibrahim Raazee bakidaya. Ya kawo alheri mai yawa ga
kowannensu. Duk weekend Aalimah da Basma na rike da juna a kan waya, sabida a weekend
din kadai ta ke samun lokacin gaisawa da ‘yan uwa da iyayenta, saboda yanayin aikinta da
hidimar Aboulkhair da ba ta karewa. Shagwababbe, cingam, super glue din Aalimah, dan gatan
Engnr. Mu’azzam Raazee. A karshen shekarar Aboulkhair ya koma John Hopkins
University ya zana jarrabawar part 2 dinsa. Ba da jimawa ba sakamako ya fito, ya cinye komai
da wata irin madaukakiyar nasara, ya dawo asibitinsu inda aka canza masa ofis a matsayinsa
na cikakken consultant (Neuro-Psychiatrist) a halin yanzu.
A wannan lokacin ne Dr. Nebrass likitan Mu’azzam na shekaru masu yawa da suka gabata
ya danka wa Dr. Aboulkhair Raazee kulawar dan uwansa Mu’azzam bakidaya, ta hanyar
damka masa file dinsa sabida shi kansa jinjinawa kwarewa da fasahar Aboulkhair yake yi,
kamar wanda ya shekara goma yana practicing. Bai sani ba, hakan na da alaka ne da zuciyar
‘yan uwantaka da shakuwa wadda aka gina karatun kacokam a kanta, sannan shi din
shekarunsa na komawa gida ya huta (retire) sun cika.
Zuwa wannan lokacin Daddy Ishaq ya gama komai na shirin komawarsa gida Niger da iyalinsa
mata bakidaya. Abu daya yake jira su ajiye ayyukansu su koma (takardar daukarsa aiki da
ministere des affaires etrangeres), wato ministry of foreign affairs, hukumar hulda da kasashen
waje ta kasar Niger mai location a babban birni Niamey, wadda wani tsohon abokinsa
ma’aikaci a wurin da suka yi aiki tare tun a Niger Consulate America yake ta kokarin nema
masa.
Sun hadu ita da su Mummy a Massachusetts sun je wa Aboulkhair jami’ar John Hopkins
har can garin Baltimore (Maryland) ranar da ya karbi shaidarsa ta zama consultant, tare da shi
suka taho Boston. Kwanansu biyu da iyayen nasu da kannensu su Khaleesat wadda ta gama
karatunta ita ma a wannan shekarar, suka koma gidansu. Kafin su shiga gida ya ce, lallai wannan karon sai sun je ta gaida Mu’azzam. Zuwanta daya
a kulliyar zamanta cikin garin da yake, sai dai in suna waya da Aboulkhair yakan ba ta su gaisa
a gajarce. Ita girmansa da respect dinta gare shi ke hana ta sakewa da shi, a wani bangaren
kuma tausayinsa bakidaya. Yayin da shi kuma a nasa bangaren da ma ba ya sakewa da kowa
sai Aboulkhair, sai kuma Daddy da kaninsa Mansour Raazee, da kuma kakansa mai ran karfe.
Ko Mummy ba ruwanta da rayuwarsa. In ka ji suna magana mai tsawo, to nata matsalolin ne da
ta ke neman ya taimaka mata ta fita daga cikinsu. Da shawarwarin Mu’azzam ne ta
tabbatar a yanzu ta zauna lafiya cikin sukunin zuciya da kyakkyawar mu’amala da kishiya
da dangin mijinta, mutuncinta ya dawo cikin idanunsu.
A halin yanzu ma ta neme shi kan babban kalubalenta na yanzu (barin aiki da Daddy ke so ta yi
su koma gida). Tana cikin damuwa da hakan matuka. Abin da Mu’azzam ya ce da ita shi
ne, “Mummy me kuma ki ke nema a rayuwa? Kin aurar da duka manyan ‘ya’yanki
bayan kin ba su wadataccen ilmi, nan da shekara daya za ki aurar da wadda ta saura. Kudin da
ki ka tara shekaru masu yawa ki ka ba ni, ki ka ce in sayi gida in bar rent, gaya miki ne ban yi
ba, hannayen jari na siya miki da su a manyan bankunan Nigeria da Niger. A yanzu haka gidan
nan da nake ciki mallakina ne, na dade ina biya da kadan da kadan na kuma hada da wani kaso
kadan daga wanda ki ka ba ni. Don haka don Allah Mummy ki yi wa mijinki biyayya kamar
yadda ki ka saba, ke ma ki zauna waje daya ki huta kamar kowacce matar aure ki fara rainon

jikoki da tarbiyyarsu. Aboulkhair ya gaya min Basma ta kusa haihuwa, shi ma tashi matar ta
samu yanzu, ga Khaleesat za ta shiga daga ciki ita ma. Mummy you are blessed ki kara gode
wa Allah, ki koma neman lahira. Na yi miki alkawarin 40% na albashina duk wataâ€.
Kuka Mummy Zulaiha ta saka, abin da Mu’azzam ba ya so daga gare ta.
“Mu’azzam ban san da wane harshe zan daina cewa ni na jawo rushewar farin ciki da
cikar rayuwarka ba. Ba zan iya daina cewa ka yafe min ba! Ka ambaci kowa zai haihu ban da
kai, Mu’azzam naka na fi son gani. Mu’azzam ka taimaka min in sake yi maka aure ko
me zai faru. Ni ban yarda da kafiran nan ba, namu addinin ya ce kowacce cuta tana da magani,
Malam Raazee da kawunka Edrissa sun ce za su nemo magani…â€
Ta ci gaba da kuka sadidan fiye da wanda ta ke yi a baya.
Mu’azzam ya dafe kansa da hannun damansa, jijiyoyin kansa na sarawa. Da kyar ya ce,
“Mummy ki daina maganar nan don Allah. Na riga na karbi kaddarata da hannu bibbiyu.
Mummy I don’t have a feeling to give to a woman. Mummy aure is not about having sex and
children only, there’s a matter of LOVE and AFFECTION. And Mu’azzam don’t
have any, not even a remnant. Ki sa a ranki ‘ya’yan Aboulkhair da Basma ‘ya’yana
ne da na haifa tunda in an tsaga jikinsu za a ga jinina. Mummy please..... ki daina kukan nan,
kina tayar min da hankali. In Aboulkhair ya san abin da ki ke gaya min zai hana ni yin waya da
ke…â€.
Alamun zaman mutum ya ji a kusa da shi, ya daga idanunsa da suka rine da sauri ya dube shi,
Aboulkhair ne.
Gabadaya yanayinsa ya canza, bacin rai da tashin hankali sun bayyana karara a kyakkyawar
fuskarsa. Idanunsa sun kada sun yi jazir. Mummy ba ta kyauta masa ba. Yana tufka tana
warwara, maimakon ta shanye damuwarta ita kadai, ko shi ta kira shi ta yi masa. Me
Mu’azzam zai maganta mata ban da ta kara masa damuwa, yana fama da jinyar tashi
zuciyar da kwakwalwar? Mu’azzam din ya kamata ta gaya wa halin da ta ke ciki a kansa?
Mikewa ya yi zai fita, Mu’azzam ya rike shi yana daga zaune. Bai iya ya juyo sun hada ido
ba saboda idanunsa da suka cicciko da hawaye. Murmushi Mu’azzam din ya yi duk da
idanunsa sun kada, ya ce, “Ina ruwanka da hirata da uwata? Wato labe ka koma? Kuma
meye laifi don ta yi sharing damuwar zuciyarta da ni?†Ba tare da ya juyo ba ya ce, “I’m your doctor. Not a brother. I’m responsible for all
the progress and the downfall of your health. Da ni ya kamata ta tattauna abin da ta ke
tattaunawa da kai. Mummy ba ta kyauta min ba! Damuwa da tunani suna hana mood stabilizers
aiki yadda ya kamata. Kuma na san abin da zan yiâ€. Ya kwace hannunsa zai fita. Mu’azzam ya daga murya ya ce, “Aboulkhair uwata ce fa!
Za ka hana ni magana da ita ne? Ka shiga hankalinka kai da likitancin naka. Rayuwa da ciwo
duka a hannun Allah suke. Idan Allah ya ce ma mutuwa zan yi dukkaninku ba abin da za ku iya.
Ni gara ma in mutu in huta da wannan rayuwar…!†Da gudu Aboulkhair ya dawo ya rungume shi. Hawaye ya soma yana fadin, “Insha Allahu
kai za ka binne ni, ba dai ni in ga kabarinka ba Mu’az, ba zan iya jura ba. Zan yi abin da ya
fi hauka, ba zan iya rayuwa ba, na roke ka kada ka kara yi min wannan fatanâ€.
Ya dago shi ya zaunar kusa da shi, yana bubbuga bayansa.
“Na ji ba zan kara ba. Amma kada ka kara fadin in ba ni ba za ka iya rayuwa ba. kowanne
rai sai ya dandani mutuwa Aboulkhair. Abin fatan shi ne mu cika da kyau da imani. Ka yi wa

Mummy uzuri kada ka ce mata komai a kaina.
Ta hanyar expressing griefs and sorrows dinta (bakin cikinta) a kaina ne kadai za ta samu
sassaucin tata zuciyar. Ni ne mai ciwo Aboulkhair, amma UWA ta fi ni ji a jikinta. Yanzu tashi mu
je kasa in ba ka Sangria Mocktail (Non-Alcoholic fruit drink) ka sha, ka kai wa matarka ita ma.
Dazu na yi order dinsaâ€. Murmushi Aboulkhair ya yi, kaunar Yayan nasa na kara keta zuciyarsa. Ya san so yake ya gusar
masa da bacin ransa. Sai a lokacin ya tuna tare da Aalimah yake ya barta a falon kasa.
“Tare ma muke da ita, mu je ka bata da kankaâ€.
Suka sauko tare.
Tun daga nesa ta hango su don haka ta kara nutsuwa ta ajiye littafin da ta dauka na
Mu’azzam, wanda ta fahimci dubawa yake yi ya ajiye ya tashi, ‘The Danger Of
Hypersexual Disorder (By Dr. Martin Kafka, 4thEdition)’.
Da sauri ta ajiye ba tare da kowannensu ya lura ba. Aboulkhair ya zauna a kusa da ita,
Mu’azzam ya wuce firjinsa ya zuba mocktail din a manyan kofunan glass guda biyu, ya
sanya straw a kowanne ya iso gare su. Aalimah ta sa hannu tana ture Aboulkhair daga kusa da
ita, shi kuma ya ki turuwa har Mu’azzam ya iso. Karshe ita ta tashi ta matsa gefe,
Aboulkhair ya bi ta da harara.
“Koma wajenki ki zaunaâ€. In ji Mu’azzam da muryar manyantaka irin tashi in yana
magana da ita, wadda ta dade da lura ba da irinta yake yi wa Aboulkhair magana ba.
Aalimah ta sunkuyar da kai tana murmushi, a kunyace ta ce, “Shi ya ce in mun zo gidan nan
kada in zauna kusa da shiâ€.
Aboulkhair ya hangame baki, ya ce,
“Yaushe aka yi haka???â€
Mu’azzam ya mika mata kofin, hannu biyu tasa ta karba ta yi godiya ya samu kujera mai
fuskantarsu ya zauna. Ya dubi Aalimah ya ce,
“Kin ga kuma ni din, sanda ya fara sonki sai da na yi da gaske ya tsaya ya yi karatu. Sai da
na ce zan aura masa mata hudu in ya dage ya zama Psychiatric dina. Yanzu haka yana min
tunin ukun da suka yi saura ne a sama kafin mu saukoâ€.
Aboulkhair ya sake kwalalo idanu ya sake hangame baki, ya ce, “Yaushe aka yi haka???â€
“To mu duka ka mana tambaya iri daya, wadda ke nufin dukkanmu kana nufin mun yi maka
karyaâ€.
Mutsu-mutsu ya hau yi da baki yana rokon Mu’azzam da ido ya warware masa gadar zaren
da ya kulla masa ba tare da ya ce da ita ya yi karya ba.
Aalimah ta fahimci halin da Mu’azzam ya jefa mijinta, har gumi yake yi, duk da sanyin garin
Las Vegas, ta ce, “Yaya Mu’azzam ai addini ya bashi damaâ€.
Mu’azzam ya zuba mata ido na ‘yan dakiku, ba tun yau ba ya fahimci yarinyar tana da
hankali, ga nutsuwa da girmama na gaba. Ya ce,
“Haka ne Aalimah! To amma me ya sa ya ce kada ki zauna a kusa da shi a gidana?â€
Da sauri Aboulkhair ya ce, “Ni fa ban san an yi ba Aalimah, ban sanki da karya ba!â€.
Dariya ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, ta ce, “Yaya Mu’azzam ka san ko zan
yi karya kai ba zan yi maka ba. Wai kunyarka yake jiâ€.
Murmushi Mu’azzam ya yi, murmushin nan nasa ingentleness,ya juya yana kallon
Aboulkhair da kyawawan idanunsa cike da kauna, bai ce komai ba. Duba agogo ya hau yi,

Aalimah ta ce a ranta, “Mun shiga lokacinsaâ€.
Tun kafin ya ce, “Ku je na sallame kuâ€. Dinsa tayi buzut ta mike ta ce,
“Mun tafi Yaya Mu’azzam, sai mun sake shigowaâ€.
Yana mai kara yaba hankalinta ya ce, “Tun ban sallame ku ba? To na gode, kuma ki je
ATM.I’ve nothing to give youâ€.
Murmushi ta yi ta ce, “Muna godiya ni da wadanda nake aikawa kudin. Allah Ya kara budiâ€.
Juyawa ya yi ya haye upstairs dinsa.
6/30/21, 11:09 AM - Buhainat:
💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔ğŸ’
”💔
€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€
€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€




@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@


Suna tafe a hanyarsu ta zuwa gida, Aboulkhair ya ce, “Me ya sa ki ka gaya masa ba kya
amfani da kudin da yake ba ki? Ai ba zai ji dadi baâ€.
Ta gyara zamanta da lullubin kanta, ta ce, “Saboda ya san ba ni da matsala ni, kada in
zamo mai hadama. Ga aiki ya sama min ana biyana albashi mai tsoka, kuma yana bina da kudi
kusan kamarsu duk wata, ai na zama mara godiyar Allah. Zai yi tunanin me nake yi da su, ga
mijina bai rage ni da komai baâ€. Girgiza kai kawai Aboulkhair ya yi, har yau Aalimah ba ta san Mu’azzam ba. Bai kuma san
irin bayanin da zai mata ta fahimce shi ba. Ba ruwanshi da abin da kowa ke ciki ko me wani ke
gudanarwa a rayuwarsa. Shi kansa bai damu da rayuwar da yake ciki ba. Ba komai cikin ransa
sai kwarewa da aikinsa na hakowa da tace man fetur (Exploration and refining petroleum). Tana
wahalar da kanta wajen son ya fahimci me ta ke ciki, ba fahimta zai yi ba. Wani saint (waliyyi)
ne shi a cikin turawa, kowa ya je ya yi abin da ke gabansa.

A karshen sabuwar shekarar da ake ciki sun yi shawarar za su dauki hutu lokaci daya saboda
su samu zuwa Nigeria daidai lokacin haihuwar Basma. Kuma watan haihuwarta ne watan bikin
Khaleesat. Duk da rashin wadatacciyar lafiyar ita Aalimahr ita ma tana fama da laulayin ciki
wata hudu, boye rashin karfin jikin nata ta ke ga Aboulkhair tana kwarara kanta a gabansa, don
kada ya hana ta zuwa. She missed Basma so much yadda ba za ta iya bayyanawa ba duk da
suna waya a kowanne karshen sati, ga dokin ganin abin da za ta haifa mata tunda kuwa dan
Yaya Aboubacar ita za a haifa mawa halak-malak. Fatanta ma a nan gaba in za su amince su
bata ta hada da wanda za ta haifa ta rike a nan Las Vegas.
Mu’azzam ya samu karin ‘yan uwa masu kula da walwalarsa, ta san in ya hana kowa
damunsa ba zai hana ‘ya’yansa ba. Tun daga lokacin da ta san wanene shi, ta damu da
al’amarinsa sosai.

KANO-NIGERIA
Sun sauka a birnin Kano ranar alhamis. Ba matar ba, ba mijin ba, kowannensu ya yi ‘yar
kyakkyawar kiba kib-kib ga kumatu luwai-luwai a fuskar Aalimah wanda a da ba ta da shi. Yaya
Aboubacar ne ya zuba su Sabrina a mota suka je filin jirgin saman Malam Aminu Kano suka
dauko su. Basma na ta kiran waya tana ita a wuto mata da Aalimah ba ta yarda ta fara zuwa sultan road a
bata mata lokacin ganinta ba. Aalimah na ba ta hakuri tana gaya mata ba za ta iya kara minti
goma ba ta ga Mama ba alhalin tana cikin Kano, ta mata alkawarin har kwana za ta yi a gidanta
in ta huta, saboda an hana basma fita saboda ta shiga EDD ga cikin mai wani irin girma. Sun yi waya da su Mummy su sai bikin Khaleesat saura sati daya za su samu tahowa, yau
kuma saura sati biyu.
Mama ta fito kofar shiga falo tana kallon Aalimah na fitowa daga mota da dan matashin cikinta
tsab da ita cikin wata irin shiga ta doguwar riga ruwan hanta kirar Abu-Dhabi, takalminta ma
kalarsa kenan marasa tsayin dunduniya dan kasar Italy. Ta yi wani irin haske mai nuna yanayin
rayuwar da ta ke ciki wanke hannu ka taba. Aboulkhair da Aboubacar suna cikin motar ba su
fito ba, suna maganar da ba ta san ta mece ce ba (zancen tafiyarsu Nijar suke daga Kano don
fara shirin auren kannen su Hamoud da Khaleesat sati mai zuwa idan su Daddy sun iso). Su
Suhaima sun rirriko hannayenta kamar sa cinye ta don murna. Shi kansa Aboulkhair din da ta
hango ta cikin glass ya yi kyau da kibar da da gani ka san na zaunuwar wadata da kwanciyar
hankali ne, fiye da lokacin da yake neman auren Aalimah. Godiya ta shiga yi wa ubangiji a fili
tare da binsu da addu’a iri-iri a zuciyarta.
Daidai lokacin da ta ji Aalimah da tattausan jikinta da kamshin jikinta sun rungume ta. Dariya ta
yi ita ma ta yi mata kyakkyawar runguma. A yadda Aalimah ta zama matar Neuro-psychiatrist da
yawan tu’ammali da patients din Aboulkhair ko duba su da yake tana zaune, da yawan
tattaunawa da suke kan cututtukan, ita kanta tana da experience mai dumbin yawa a kan
mental health illnesses. Ta fahimci akwai ci gaba sosai da stable treatment a tare da Mamanta
fiye da baya.
Shi kansa Daddy da ya dawo nan-nan yake ta yi da Aalimah da maigidanta. Ya rasa ina yaka
saka-ina-yaka-aje da su. Kowa ya yi kewar kowa. Shekaru uku cif kenan ba su ga juna ba.
Baban da Aboulkhair

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login