Showing 54001 words to 57000 words out of 128821 words

Chapter 19 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf

boye masa abubuwan da suka shafi Mu’azzam tun
daga kan auren katsahan din da suka yi masa shekarun baya, dawowar matar daga America da
karewar auren. Tun daga lokacin yake cewa ba shi da lafiya ya dinga sa shi a addu’a bayan
shi bai ga wani alamun rashin lafiya tare da shi ba, ko a watanni uku baya ya zo Nigeria. Ya siya
masa wannan gidan da yake ciki, ya ce ya bar New site gidan gwamnati ne in ya yi retire zai
bukaci gidan kansa gara ya kama gidan tun yanzu shekaru turawa suke yi, me ya hana
Mu’azzam aure har yau?
In rabuwa ce ta shiga tsakaninsa da wadda ya aura, me ya hana shi sake aure? Tukunna ma
wane rashin lafiya ke damunsa da Baban nasa ke dauka da muhimmanci haka? Har da zai goyi
bayansa ya ki yin aure? Ya sa a ransa gobe zai yi wa Yayansa Ishaq Raazee wadannan
tambayoyin ko da ba zai amsa masa ba. Washegari Yaya Aboubacar ya ba su layin wayar Mtn dukkansu. Godiya sosai suka yi,
musamman Aalimah, Basma na daga gefensa zaune, Aalimah da Sabrina na gefe tana mata
kalba a dogon gashin kanta. Ya sassauta murya yadda su Aalimah ba za su ji ba, ya ce da
Basma, “Sai ki ji dadin kiran saurayinkiâ€.
Da sauri ta dago suka hada ido, ba shiri ta dauke idonta. “Ya Allah!†Basma ta ce a hankali
idonta a kasa, “Believe me, I don’t have (ka yarda da ni, ba ni da shi)â€.
Aboubacar wani irin sanyi ya ji a ransa, amma nan take zuciyarsa ta shiga cautioning din shi,
tana gaya masa ya danne ko ma mene ne yake cin ransa a kan Basma, ta fi karfinshi. An haife
ta a U.S, ta girma a can, rayuwarta gaba daya tana can. Shi ba kowa ba ne face karamin
ma’aikacin banki. Gidan da suke ciki a yanzu ma Yayanta ne ya saya musu. Ya aure ta ya

kai ta ina? Ban da giggiwa irin ta zuciya?
A sanyaye ya tashi ya bar falon. Basma ta bi shi da kallon mamaki da wata irin ragaita cikin
kwayar idanunta.
Sosai ya janye jikinsa da zama cikin gidan. A ganinsa ganinta da yake yi ne yake jaza masa
komai. Basma kuma rashin ganinsa a cikin gidan sai ya sabbaba mata rashin walwala, duk ta
zama wata irin sukuku. Har Aalimah ta soma zargin ko zaman gidansu ne ba ta so. Ko ta kasa
jure irin tasu rayuwar? Ko kuma tunanin gida ne ya addabe ta? Da ta ishe ta da tambaya ta ce
kome ta ke tuhumarta ta je ta yi ta tuhuma, ta yi abin da za ta yi, amma ta daina damunta da
magana. Haushi ya kama Aalimah ta ce, “To ko in dawo da booking dinki jibi ki koma ni na
taho daga baya?â€
Saura kadan ta mare ta, Aalimah na iya ganin hakan cikin idanunta.
Dariya ta yi, ta ce, “To Basma na kasa gane miki. Kin zo da walwala kwana biyu kin koma
min hakaâ€.
A fusace Basma ta ce, “Lokacin da ki ka fara son Monsieur Aboulkhair, na takura miki da
tambaya? Ba idanu na sa miki har na gano da kaina ba? Amma ni kin sa ni gaba kin sa min ido,
har da sharri da kazafi. Wai na gaji da Najeriya. To in gajiyar na yi kunyarki nake ji da zan kasa
gaya miki?†Aalimah ta kama baki tana kallonta, “Me ya kawo wannan tambayar?â€
“You want to know?†Basma ta fada a raunane.
“Yes, I doâ€. Aalimah ta amsa.
Sunkuyar da kai ta yi.
“Yaya Aboubacar ya daina shigowa gidan nan saboda ba ya son ganinaâ€. Sai hawaye.
Aalimah ta karasa kusa da ita sosai, tuni ta fahimci matsalar ‘yar uwarta. Hannayenta biyu ta
kama, “Kina nufin damuwarki kenan?â€
Basma ta daga kai, “Mu kuma kaddararmu kenan, son ‘yan uwanmu?â€
Da sauri Basma ta cira kai ta dube ta,
“Sonsa nake yi?â€
Murmushi Aalimah ta yi, “Ask yourself, not me. It’s your heart, not mine (tambayi kanki
ba ni ba, zuciyarki ce ba tawa ba)â€.
A hankali Basma ta zare hannayenta daga na Aalimah ta juya mata baya, “Idan dai yadda
na damu da lamarinsa din nan da rashin ganinsa shi ne so, Aalimah ina son Yayanki…â€.
Kalaman da suka shiga kunnen Mama kenan, ta juya ta fasa shigowa kada Basma ta gane ta ji
zancenta. Aalimah ta dafa kafadunta, ta ce, “Basma!â€
Ta juyo ta dube ta cikin damuwa, “Idan har za ki iya zaman Nigeria auren Yaya Aboubacar
ya fi komai sauki a gare ki. In ba za ki iya ba ne da matsala. Amma kada ki bari ya gane kin
damu haka. Ki dawo cikin walwalarki, tun zuwanmu ina lura da shi shi ma ya damu da lamarinki.
Ki bi shi da duk ta inda ya billo, insha Allahu tsakaninku alheri neâ€. Da sauri Basma ta rungume Aalimah.
“Ni ko a jeji ne zan iya zama da shi Aal. Ba Nigeria ba, ko cikin bukka neâ€.

******
Ya aka yi-ya-aka-yi? Cikin hira Aboubacar ya gaya wa Mahmoud zuwan Aalimah. Kwanansu

bakwai sai ga shi a Kano. Gidansu na New site ya fara zuwa, inda aka gaya masa sun tashi. Ya
kira Aboubacar a waya, shi ya kwatanta masa sabon gidansu da ke Sultan Road.
‘Yammatan biyu na zaune a falo sun dau wanka, kowacce da abin da ta ke yi. Basma tashar
Arewa 24 ta ke kallo ana diramar Dadin Kowa, sosai abin ya dauki hankalinta yadda ake nuna
typical Nigerian life da ba ta sani ba. Aalimah chatting suke yi da Abulkhair, wani abu da ya
zame musu jiki tun zuwanta saboda ta roke shi kada ya kira ta ko sau daya, ba ta so Mama ta
san akwai wani abu a tsakaninsu, za ta shiga damuwa a kan karatunta. Za ta yi tunanin ko ma
ba karatu ta ke ba, tunda a gidansu ta ke.
Abulkhair ya fahimce ta, kuma shi ma yanzu ta kansa yake yi, ya shiga shekara ta biyun karshe
a karatunsa, ko lokacin da yake chatting din da ita ma squeezing dinsa yake yi, saboda yana so
ko me ta ke ciki ya sani, kada nisa ya nesanta shi da ita.
Aboubacar ya shigo, Mahmoud a bayansa, bayan sun yi sallama. Aalimah ta amsa ba tare da ta
dago ba, komin canjin da rayuwa za ta kawo Mahmoud ba zai kasa gane Aalimah ba. Jikinta ne
ya ba ta ana kallonta, kuma kamar yaya Aboubacar ba shi kadai ba ne ya shigo. Da sauri ta cira
kai, suka yi ido hudu da Mahmoud. Sai da gabanta ya fadi, yana nan a yadda ta sanshi sai dan
gogewa da ya yi. Yana sanye da shudiyar shadda kansa babu hula. Ajiyar zuciya ta yi ta janyo
mayafinta a gefe ta lulluba, ya samu waje kusa da Aboubacar ya zauna, jikinsa a sanyaye.
Yanzu ya kara tabbatarwa ya rasa Aalimah a bisa dalilai da dama.
Aboubacar da Basma sai kallon-kallo, kwana uku kenan bai shigo gidan ba sai yau a dalilin
abokinsa ta ganshi. Aalimah ta rusuna ta gaida Mahmoud cike da jin wani irin nauyi domin har
gobe Mahmoud mai kima ne a idanunta. Ba ta ji dadin abin da Abulkhair ya yi masa ba, wanda
shine ya raba tsakaninsu, sannan bayan ya goge lambarsa daga wayarta ya yi masa kashedin
sake kiranta ita din ba ta kara bi ta kansa ba, ko wajen Yaya Aboubacar ba ta karbi lambarsa
ba. Idanunta sun rufe sun makance da soyayyar dan uwanta, wanda ya shigo cikin rayuwarta
da wani irin karfin mulki, ya hana ta mallakar kowanne tunani sai nasa.
Hawaye ne suka ciko idanunta, “Ni mai laifi ce Mahmoud, ka yi hakuriâ€. Abin da ta iya
furtawa gare shi kenan.
Murmushi Mahmoud ya yi, “I understand. Na dade da sanin haka za ta faru Aalimah. Shi ya
sa na ce miki I’m scared da tafiyarki America. Da ni da ke duka babu mai iko da kansa ko
zuciyarsa, sannan shi mijin aure rubutacce ne ga mace tun halittarta. Da ma ba ki yi min
alkawarin ba za ki so kowa ba. Cewa ki ka yi you are hoping that destiny tied us together… to
fatan bai karbu a wajen Ubangiji ba. Dan uwanki ya kira ni daga baya…â€
Da sauri Aalimah ta dago ta dube shi. Abulkhair wane irin mutum ne? Tsoronta Allah, tsoronta
kada ya kasance zaginsa ya yi.
Mahmoud ya yi murmushi ganin yadda ta tsorata. Ya ce, “Abin da ki ke tunani ba shi ne ba.
Rokona ya yi in sonki nake na yi masa alfarma na bar masa ke, don ya fi ni sonki. Sannan yana
mai tabbatar min babu sauran muhallina a zuciyarkiâ€.
Aalimah ta dafe kai. Mahmoud ya ci gaba, fuskarsa dauke da murmushi.
“The guy is smart! Na kuma yi rantsuwa ni da kaina yana sonki. Na kuma yarda ya fi ni
sonki. Na jinjina wa karfin zuciyarsa. Ina son mutum mai nuna kwanjinsa a kan macen da yake
so. Ina yi muku fatan alheriâ€.
Aalimah sai ta ji hawaye sun sake ciko idonta. Mahmoud ya sanya hannu cikin aljihunsa ya
fiddo abu cikin ambulan ya matsa ya mika wa Aalimah. Ta goge idonta ta karba, ta bude. Da

sauri ta dube shi. Murmushi ya yi, “ni ma ‘yar uwata na nema. Na ga abin ya fi danko
idan da alakar jini, kada in je wani waje in sake shan kaye a karo na biyuâ€.
Duk halin da ya sanya ta na tsananin tausayinsa, sai da ta yi murmushi. Katin daurin aurensa
ne, sati biyu masu zuwa da cousin dinsa.
“Allah ya sanya alkhairi Mahmoud. Na gode, na gode. Ina kuma fatan hakan ba zai shafi
tsakaninka da Yaya Aboubacar ba, ni kadai ce mai laifiâ€. Ta fada cikin sanyin murya.
Murmushi ya yi, ya ce, “Aboubacar ai ba ke ki ka hada mu ba, balle ki raba. Ki je ki ji da
rigimammen saurayinki. Wannan in ya aure ki ki shirya shan kulle. Yana sonki fiye da kima,
yana kishinki fiye da zatonki. Ni ma sakona gare shi ya gaggauta ya killace ki, in ba haka ba shi
ma zai sha kaye, zai samu mai sonki fiye da shi. Saboda ke Aalimah daban ki ke. Soyayyarki ba
ta yi wa maza sassaukan kamuâ€. Ya mike.
A zuciyar Aalimah ta ce, ‘ba amin ba, Abulkhair kawai nake so, daga nan har gaban abada!
Juyawar nan da za ta yi, Yaya Aboubacar ne da Basma, yana zaune a gabanta a kan kilishi, ita
kuma tana kan kujera kamar dalibi gaban malaminsa. Maganganu suke yi kasa-kasa, wadanda
daga su sai Ubangijinsu suka san me suke cewa. Mama ba ta gidan da ma, ta je asibitin Malam
wanda ta ke zuwa duk karshen wata, su Sultana na makaranta. “To kai yayan kwabo sai ka zo ka raka ni, zan tafiâ€. Mahmoud ya ce da Aboubacar yana
kallon Basma cikin mamaki, sabida yadda idonsa ya rufe da ganin Aalimah bai ma lura da ko
wace ce ba. Aalimah na da twin sister ne? Kai! That cannot be possible. Wannan ta fi ta aji, ta fi
ta wankakken ido, me yiwuwa ‘yan uwan nasu ne na canâ€. Ya bai wa kansa amsa. Aboubacar ya mike suka fita yana ce da Basma, “Ba doguwar rakiya zan yi masa ba, tasha
zan kai shi ya hau motar Katsinaâ€.
Dariya Aalimah ta yi tana kallon Basma, wadda annuri kadai ke fita a fuskarta, da gani sun
daidaita abin da suke ganin matsala ne a gare su. In wani ya gaya mata Aboubacar Mansour ne
wannan a gaban mace ba za ta taba yarda ba. Hakika soyayya abu ce mai girma, mai birkita
rayuwar ‘ya’ya maza fiye da mata. Kafin hutunsu ya kare su koma U.S, hatta Daddyn su Aalimah ya san da soyayyar Aboubacar
da Basma, ba Mama kadai ba. Sai dai cikin su duka babu wanda ya zura jiki cikin al’amarin
a bisa dalilai kwarara da dama. Ido kawai suka zuba musu, suna ganin da ta koma shi kenan za
su manta da juna. Sun dawo Massachusetts ranar asabar, litinin suka koma makaranta.
6/28/21, 7:36 AM - Buhainat:
â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©
â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©
💙💙💙💙💙â¤â¤â¤â¤â¤â¤â¤â¤â¤â¤ğŸ’›ğŸ’›ğŸ’›ğŸ’›ğŸ’›ğŸ’›ğŸ’›ğŸ’›ğŸ’›ğŸ’›ğŸ
’›ğŸ’›ğŸ’•💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💓💓💓💓💓




******
Haka Aalimah ta ci gaba da karatu a gidan Kawunta a Boston (Massachusetts) duk shekara
suna zuwa gida su yi hutu su koma. Duk kuma zuwan da za su yi da Basma suke zuwa, inda

suka girka wata irin soyayya ita da Yaya Aboubacar, yayan Aalimah. Wadda labarinta har Niger,
har kunnen Malam Raazee. Da fari bai ce komai ba, don shi ba irin kakannin nan ba ne masu
katsalandan cikin maganar auren ‘ya’yansu ko jikokinsu. Aalimah tana shekarar karshe,
ita kuma Basma ta gama saboda karatun Aalimah na shekaru biyar ne, Aboulkhair ya kammala
shekarar da ta gabata ya fito a cikakken likita mai kwalin MBBS. Ya tafi speciality a kan
kwakwalwa a shahararriyar jami’ar da ta yi fice a duniya a kan ilimin psychiatry (wato John
Hopkins University), wadda ke garin (Baltimore, Maryland).
Duk kawaicin Malam Raazee wannan lokacin ya yanke shawarar tsawatarwa ga
‘ya’yansa biyu kan wannan zuzzurfan ilmin boko da suka dora ‘ya’yansu akai,
daga mazan har matan babu mai tunanin yi musu aure a cikinsu. An gaya masa batun
Aboubacar da Basma, amma har gobe bai taba jin komai a kan Aalimah da Khaleesat ba,
wadda ke aji biyu a jami’a yanzu haka. Idan sun ce karatu, to shi wannan karatun ba shi da
iyaka ne, ko ko ba shi da madakata? Kada dauke idonsa ya sa a shiga keta haddin Allah.
Aunty Gumsu ta haihu shekaru biyu baya, ta haifi ‘ya mace Nurat. Don haka wannan zuwan
da suka yi Niger har Mummy Zulaiha, ya ce a kira masa Mansour yana son ganinsa, ya zo su
hadu da sauran ‘yan uwansu a yi ta ta kare kan ‘ya’yansu, ya gaji da ganinsu babu
aure bakidaya. Cikin shekarar nan yake son ganinsu a dakin aure bakidaya, daga matan har
mazan. Mu’azzam kuma sai sun gaya masa abin da ya hana shi aure.
Mu’azzam ya dade da sulhunta Mummynsa da dangin mahaifinsa bakidaya. Har nata
‘yan uwan. Tare da ita suke zuwa duk karshen shekara. Tsakaninta da Inna Kasisi yanzu sai
sam-barka, da ma matsalar daga gare ta ne, kuma da ta nutsu ta bude zuciyarta kamar yadda
dan nata ya shawarce ta, ta tadda abubuwan yadda ya gaya mata su. Ita kadai ta dauka da zafi,
su mutane ne masu son junansu da kaunar duk wanda ya shafe su ba tare da nuna bambanci
ba. Sai dai in ka nuna musu su ba wata tsiya ba ne cikin rayuwarka za su nuna maka ka yi
kadan ka keta alfarmarsu, ko mene ne takamarka.
Don haka wannan zuwan har da Mummy aka zo Niamey. Kwanansu biyu kawu Mansour da
Maman Aalimah da kannenta suka iso. Aboubacar bai biyo su ba, sabida aiki. Ba su samu
zama da Malam ba sai da daddare. Ya sallami matan ya zauna da manyan ‘ya’yansa
maza bakidayansu. “Oussama kai ne babba, kai ne kuma za ka zame min shaida kan cewa tunda ka fara
haihuwa ka ke aurar da ‘ya’yanka ban taba shiga ba, ban taba cewa da kai ga abin da ya
kamata ba, saboda kai ka san ya-kamatan, ‘ya’ya mata ba sa wuce shekara sha shidda
a gabanka. Kaninka Edrissa ya biyo bayanka da wannan kyakkyawan koyi. Amma wadannan
(ya nuna Ishaq da Mansour) guguwar zamani ta debe su tana neman kai su ta baro.
Babu Allah a ransu sai ilmin nasara wanda iyakarsa duniya babu amfanin da zai yi musu a
lahira. Sun aje balagaggun ‘ya’ya maza da mata ba sa ko tunanin yi musu aure. Bayan
cikinsu babu wanda ban yi wa auren gata ba, tun kafin ya kama kwalin ilmin bokon don dai in
fita hakkin Allah. Nauyin auren bai hana ku zama abin da ku ke son zama ba, don haka ku
zama shaida, ko yau na fadi na mutu Ishaq da Mansour su suka yi ajalina.
Sun ki aurar da ‘ya’yansu, sun ki gaya min matsalar Mu’azzam, kullum abin nan na
damuna a zuciya, da shi nake kwana nake tashi. Shi ma Mu’azzam din ba ya son na yi
masa zancen aure, daga shi har Abulkhair ba su da niyyar yi musu aure, balle kannensu mata.
Ga Aboubacar shi ma ya dade yana aiki, amma babu abin da suka yi a kan zancensa da

Basma, wanda na dade da ji yana yawo a bakin su Bintou.
Yau ga su a gabanku su gaya mana gaskiyar lamarinsu. Me suka dauki rayuwar duniya?
Wallahi ba inda za ta kai ku idan ba ku bi dokokin Allah baâ€.
Ya soma matsar kwallah, duk kuma maganar cikin harshensa Temachek yake yinta.
Shiru ta ratsa a falon Malam Raazee. Daddy Ishaq idanunsa sun kada sun yi jazir. Jijiyoyin
kansa sun fito rada-rada. Baban Aalimah bai ce komi ba, ko shi yana son jin mene ne matsalar
Mu’azzam. Tambaya ta karshe da ya yi masa shekarun baya zuwan Aalimah na farko hutu,
da ya tambaye shi cewa ya yi da shi, Mu’azzam addu’arsu kawai yake so, amma ba
abinda yamadidi da lalurar tasa zai amfana masa.
Don haka yau shi ma ya zuba masa ido a qagare da son jin amsar bakinsa. Maganar
Aboubacar da Basma ya santa ba tun yau ba, bai taba daukanta da muhimmanci ba ne saboda
a ganinsa Aboubacar ba shi da abin da zai rike Basma, kuma ba za ta iya adopting tashi
rayuwar ba. “Kai muke saurare Ishaqaâ€. Uncle Edrissa ya katse masa dogon shirun da ya yi. Ajiyar
zuciya ya yi, yau kam ya san ba shi da mafita ban da gaya wa mahaifi da ‘yan uwansa ko
wane ne Mu’azzam. In ba haka ba za su yi zaton bai dauke su a bakin komai ba, kuma
yana nufin ‘ya’yansa ba nasu ba ne. Mutuncin Mummy Zulaiha a idanunsu yake tattali
wanda Mu’azzam din ya samu ya farfado da shi ba da jimawa ba.
Ina ga in sun ji ita ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login