Showing 15001 words to 18000 words out of 41234 words
Chapter 6 - WALIJAAM BOOK 2 Hausa Novels by Maman Teddy .pdf
Shatu kamin ya girgixa mata kai da cewa" babu mai tafiya dake indai ina
nan ,ke Ai amana ta ce ba xan ta6a yarda wani yayi mun farraku dake ba. Don haka shiga daga
ciki...
A kullum Anwar din maganganun shi na kara mata karfin gwiwa ko me ya fadi mata tana saurin
yarda da gasgatawa musamman tasan Anwar din jarumin namiji ne baya fadin Abu don dadin
bakin shi...tom amma a yau taga wasu jaruman wanda mgnaganun Anwar babu daya zata iya
fadowa wanda yace ,sai dai kawao taji tsoron sa kwarai ,musamman tuno da karon da suka fara
haduwa a farko da yanda yaso yi mata lalata ta karfin barta.
Da sauri ta cika hannun Anwar cike kuma da sakin jiki ta ra6a shi tana kokarin wucewa...Aisha!!
Taji muryar Abbas ya kira sunan nata ,wanda yanda ya kira sunan nata sai da taji faduwar
gaba... Kar ki tafi ,indai ina a raye baxan bar kaunan ki a xuciyata ba ,kuma Anwar ba sonki
yake ba ,yana yin komai da plan nashi na nan gaba ,daga wannan lokacin ne zaki fahimci waye
Anwar?? Ni ne mai sonki da gsky.....Kirjin ta ne ya cigaba da dukan uku uku ,wanda da sauri
tayi bedroom din ta....don ji tayi sam batason jin wani sauti ko murya na Abbas...waye shi
din...ni zaka Yaudara Anwar??? Tambayar da take mawa kanta kenan ,kamin ta rinka tariyo da
mgnan Abbas da yake kiran sunan Anwar yana fadin shi xai yaudara!!
Allah shi kyauta...ai wlh ko Hamma yace naso wannan mutunin baxan so shi ba,mugu ne....tayi
mgnan a sarari tana rintse idon ta hadi da tunano lokacin da Ya manna jikin ta da nashi a jikin
moto...
Jin haushin Abbas take har A cikin zuciyar ta...hayaniyar da taji ne daga wajen Windown ta
yasata lekawa cikin sauri ,Abbas ta gani da Sadeeq yana jan sa ,sam bataga Anwar a wurin ba
yyn da batayi aune ba taga ya bugi glass din murfin moton yana ratsatsakewa lokaci daya glss
din ya caki cokan hannun shi...
Sai jini sharrrrr sharrrrrr da gudu Shatu tajah baya tana hayewa saman gadon ta hadi da jan
bargo gaba daya ilahirin jikin ta rawa yakeyi ,bata ta6a ganin jini nq zuba hakan ba ".
Shikam Bangaren Anwar da Abbas sai da Shatu ta shiga daga ciki ne ,suka fara masifa kunsan
dai fadan sojoji yi suke kaman su kashe kansu..
Malama Safiya ne ta shiga gaban Anwar tayi ,yayin da Sadeeq yaja Abbas da sauri ya fitar
daashi daga falon ,don yasan zuciyar kowa...Abbas fitina ne ,shikam Anwar baiki a mutu
ba...sunan miskiline amma yafi mai baki Kunar bakin wake....
Abbas kam jan moton nashi yayi a matukar fusace yana figarta cikin wani irin mahaukacin
gudun da rabon da yy irin shi ya manta....haka ya fice daga barikin sojojin ....babban titi ya hau
wanda ko kallon na gaban sa baiyi bare Na gyefen sa....wani mai acaa6a ne Abbas din yayi
gaba dashi...yana wucewa bai ko tsaya bin ta kansa ba.....wata moto ya kuma gara mawa
wanda babu abun da ya wade kunnuwan mutane sai karan karuwan moto da moto ji kake
k'iiiiiiiii k'uuuuuuuuu...................
Mmn teddyí ¾í·¸
*í ½í°„WALIJAAMí ½í°„*
_*Littafin na kudi Normal grp 200....Vip grp 500...Spc grp 1k...zaki iya turo da katin MTN ta
wannan number 08081202932.....ko kuma ta wannan Account din Farida Hashim Stanbic
0028799846....Yan niger zakuna iya tuntu6an wannan number +22797780373 .*_
44_45
Sun hade da juna karar kwaruwar abubuwan hawa sun hade a saman kwaltan nan k'iiiiii...rintse
ido jama'a sukayi suna ambaton Allah don sun san wannan kwaruwar moton da wuya a wanye
lafiya". A takaice dai Abbas Asibiti aka nufi dashi don baya a hayyacin shi sam ,bai ma san
duniyar da yake ciki ba".
Shatu kuwa sai rawar jiki take tana narka bargon saman jikin ta ,itaba sanyi take ji ba ,ba zafi ba
kuma ba sanyi ba tsoro ne takeji yana wani irin ratsata...Aisha!!
Taji muryar Anwar yana kirar ta hadi da yaye bargon don yasan tsoron halin da ta gansu ne
yasata shigewa tana hayewa gadon hadi da rufa kanta da wannan nannauyar bargon.
Cikin sauri ta mike tana amabaton Hamma shine din ko? Shine wannan mutumin na ranan
nan...Shiiiiii ya isa haka Babu abun da zai maki kinji ki kwantar da hankalinki ba gani tare dake
ba?.
Daga masa kai kurum tayi tana kallon fuskar sa ,wanda kasan babu abun da yafaru tsakanin sa
da Abbas.
Hamma nidai kar ka bari ya tafi dani ,wlh da ya tafi dani gwamma ka maidani rugar mu , yace
fah sai ka bashi ni!!
Tayi mgnan tana matsawa kusa dashi...Magana zai mata ne wayan sa ta hau ruri ,kaman baxai
daga ba saboda sunan Abbas da ya gani a screen din ,amma sai y kai zuciyarsa nesa hadi da
daukar wayan....
A zaune yake amma sai Shatun taga ya mike lokaci daya jikin shi yy matukar sanyi ,a wani
asibitin aka kwantar da Abbas...kuna ina???
Abun da Anwar yace kenan cike da daga murya idon shi lokaci daya ya kada yayi jah".
Ina zuwa" abun da yace ma Shatu kenn yana ficewa daga bedroom din cikin gaggawa.
Itama Shatun mikewa tayi daga zaune tana tsayawa hadi da dafe kanta...Wayyyo ni Shatu
wannan wacce irin rayuwa ce? Kar da Abbas yake ko wane ya jamun masiba...mai ya sameshi
,yaudara ta xakayi ina sonki Aisha...mgnan tasa ne ya fara dawo mata kwakwalwa ,ina sonki??
Tom me yake nufi ne??? Abun da take fadi kenan hadi da dafe kanta.
Muryan Mama Rahmatu tajiyo a falo sama sama wannan yasa ta saurin ficewa daga bedroom
din...itace din ko ta gani tana mgn da Daniel ,da gudu Shatu ta nufeta tana fadin Oyoyo mama
rahmatu ,dama kince zaki zo??.
Rungumeta Mama tayi tana fadin Kwarai kuwa gashi na zo!! Mama mu tafi yanxu kurum gobe
sai mu wuce School din ko?
Cike da mmki Mama rahmatu take kallon Shatu ,duk da tasan dama ta kosa ta kaita makarantar
,amma ai Da Anwar zasuje tare.
Ina shi Anwar din yanxu kuma ai sai gobe ne zamu je na gani...A'a Mama Hamma na baya nan
,mu tafi kawai gobe da safe sai ki kaini.
Tab Aisha kefa matar Aurece ,da mijin ki bana tafi dake gidana ba ,sai da sanin sa.
Shiru Shatun tayi don ita tafara gajiya da zaman barack din ,sai kawai cewa tayi"To Mama ki
kirawo shi nasan xaice ki tafi dani.
Yowa Aisha mu zaauna to...sai a sannan su duka suka zauna mama tana danna wayan ta hadi
da kirar Anwar....Ringing take kusan sau uku amma bai daga ba....
Wanda ganin haka yayi mugun daga hankalin Shatu...Tsawon lokaci suna a haka har daniel
yakawo mawa Mama Rahmatu ruwa da lemu ,ita kuma shatu ta mike don ta dauro alwala.
Kusan karfe biyar ta yamma ne Anwar ya biyo kirar Mama Rahmatu ,wanda a lokacin suna
zaune tare da Aishan ,nan Mama take fadi maasa tana so ta tafi da Aishan gidan ta...Shiru
Anwar yayi duk da bayaa a natsuwar shi ,amma bayason yaga yayi nesa da Shatun tasa koda
na mintoci bare har tayi kwana daya a gidan Mama Rahmatu .
Mama kibani Shatun muyi mgn".
Cewan Anwar din yana lumshe segxy eyes din shi.
Murmushi Shatu tayi ganin An bata wayan xatayi mgn da Hamman nata...Hamma! .
Na'am Aisha na wai zaki bi Mama?? Ko zaki zauna dani anan"
Uhm uhmmm....Jin ta tsaya kame kame yasa shi cewa ko zaki bi Mama ne? .
Eh to Hamma xanbi Mama . Shikenan goben xan zo in dauke ki.
Mika mawa mama Rahmatu wayan tayi kan suyi mgnan da bataji mai suke cewa ba ,Don tuni ta
nufi Bedroom din ta tana hada kayanta duk da taasan kwana daya xatayi a gidan Mama
rahmatun....
Dariya sosai mama rahmatu take tana mai jin dadin ganin yanda Shatun ke daukin zuwa gidan
nata .
***********
Abun kaman A mafarki ,Hjy Haula ce da Hjy Baraka wato yayar ta mahaifiyar Zabeeena gaban
malamin tsubbo yana ta tsubburkai...kamin mutumin ya dago jajayen idanun sa cikin wata irin
murya marar dadi yace " Hajiya ku bani aikin ku ,xan maku aiki zan zauta maku zuciyar yaron
nan ,Sai ya rabu da matar tashi ko ba yaso....!! Idan ma na kisa ne zamu kashe shi a dare
daya".
Mamaki ne ya kama Hjy Haula don ita duk zuwan ta nan wurin ba abun da yakawota kenan ba"
aa rankayadade malam ba haka muke nufi ba.
Keeeeeee yimun shiru tsohuwar banza ,Ni ba malam bane boka nake ,don bana fara aiki na sai
mun sha jini....bama yanka sai dai mu murdi kan wuyan dabba duk girman shi haka duk
kankantan shi murde wuyan muke har ya mutu......bana da imani komai nawa baki yake...kun
taho mun da bakar shanun?? Cewan wannan boka yana ware manyan idanun shi masu ban
tsoro...
Jikin Hjy Haula ne ya dau rawa ,don ita bata ta6a zuwa wurin wannan bokan ba ,ita bata bin
bokaye irin na yar uwar tata". Hannu tasa cikin jakarta tana ciro rafa biyu tana ajiyewa gaban
bokan.
Wani dariya bokan yaasa Hahahaha....!!! Wanda sai da dakin tsubbun tashi ta amsa don
mabiyan sane y amsa .
Na rantse da aljanuna bakake na rantse da dan gitsu dan gulgul dan gulbin....sai kunga yanda
yarinyar zata koma a muxance ,sai yy mata korar cin mutunci da hannun sa...sai y auri
Zabeeeenaaaaaaaahhhh ya wani jah sunan sosai .
Dariya Hjy Haula tayi da baraka ,tana cewa "Haka muke so boka...yanxu ka faara korar Yarinyar
ne sai mu aura masa zabeenan daga nan zamu kwashe duk arxikin sa sai ku karshi don dama
uwar sa asarar haihuwa tayi.
Shiru Hjy Haula tayi kamin tayi mgn ne bokan yace " shyasa nace bakar shanu zaa siya karama
,ba yanka zamuyi ba murde kanta zaayi a haka har y mutu ,kinga wannan shine jinin bakaken
aljanun fulani mun basu ,zasu cika mana aikiiii Hhhhhhhhh..... Ya kara bushewa da wani irin
dariya kamin cikin fada yace " ke na lura Kaman bakyason a cutar da yaron!!
Yy mgnan yana kallon hjy haula ,kyeleta boka tana son wahala ne ,don dan da banaka ba ,ai
gwamma mu kashe shi muci arxiki ...kema zakicemun ehhh ne Hjy Haula haba don Allah".
Nisawa haula tayi kamin tace" Aa banki ayi komai ba ,amma ni banaso a cutar mun dashi ne
,saboda ko banice mahaifiyar sa ba ,ni na raineshi a cikin jiki na ,ni na shayar dashi na bashi
nonon jiki na ko bakomai akwai wannan shakuwar...
Banki a cutar da wancen yarinyar ba ,amma shi kar ayi masa komai ,kaawai a mallaka mun shi
ne.
Ganin Taki fahimtar su yasa su amincewa da mgnan nata akan zasuyi ma shatu da Anwar
farraku ya korata har rugar su .
*****
Asmau kam da teemah sun barada suma wurin nasu bokayen don dama sun saba ,amma har
yau tana xaman jiran zuwan Anwar da kafanshi kaman yanda Boka yace mata ,amma shiru
babu shi babu labarin shi. Haka kullum suna aikin dura mawa bokaye kudi suna fadin ai zaizo
da kafan shiiii haka kullum suke sa ran ganin shiiiiiiiiii....
*******
Tun da gari bai gama haske ba Shatu ta shirya tsaf cikin wani uniform na sabon makarantar da
zaa sanyata ,riga milk da karamin hijab iya kafada sai blue din skirt mai ratsi ratsi....Kafan ta
cikin takalmi mai rufi da faran safa combus masu girma sosai tayi matukar kyaun gske...wanda
idan kaga Shatu baxakace Wai a nigeria ta taso ba ,bare har ace tayi rayuwar ruga
........wowwwwwww cewan Mama Rahmatu da take shigowa kenannnnnnnnn..............
Mmn teddyí ¾í·¸
*í ½í°„WALIJAAMí ½í°„*
_*Littafin na kudi Normal grp 200....Vip grp 500...Spc grp 1k...zaki iya turo da katin MTN ta
wannan number 08081202932.....ko kuma ta wannan Account din Farida Hashim Stanbic
0028799846....Yan niger zakuna iya tuntu6an wannan number +22797780373 .*_
46_47
Murmushi Shatu tayi tana fadin Mama Amma wannan Skirt din baiyi mun kadan ba jibi fa dan
iyakan shi?. Tana maganan ne hadi da dago skirt din nata wanda iyakarta Gwiwa".
Murmushi Mama Rahmatu tayi tana riko hannun Shatun kana daga bisani tace"Baiyi ba Shatu
,Duk haka kukesawa kinga ma taki ta dan sauka saboda yanda Anwar yace Ayi bayason karami
shiyasa suka bayarda wannan.
Kara ware idon ta tayi tana dariya kamin tace"ta6 Yanxu Mama Wannan ne karami ?? Dariya
Mama Rahmatu tayi kurum suna nufan Dinning don kammala breakfast din nasu.
Tare da Mama Rahmatu sukayi break kasantuwar mijin ta ba nan zaria ne wurin Aikin shi ba
,hakan yasa baya gida sai Weekend yake dawowa . Kuma Yarinyar Mama Rahmatu daya ce
Muhsina kuma itama yanxu bata nigeria da mijin ta ,tun da tayi Aure suka tare a malasia har
yanxu basu dawo ba yaron su daya acan".
Tun daga kan Muhsina Mama Rahmatu bata sake haihuba ,sabida dama Hakan wannan
Familyn Hjy yalwa yake ,sam basa da yawan Zuriya ,idan aka samu mace tahaifo yara biyu
murna ake ana mata san barka ,ba mazan ba ba matan ba duk hakan suke .
Idan mutum yy aure sai ya shekara fiye da goma babu da kuma ba juya ba ,Sai kuma kwatsam
aga juna biyu daga matar sa...A wannan lokaci Dangin nashiga cikin matsanancin farin ciki
marar misaltuwa .
Idan ko ka haifo yaron ko mace ko namiji tom shiknnn sao idan kuma Allah ya kadarta. Wannan
yasa Familyn keda son y'ay'a akan yaran nasu zasu iya komai....yana daga daya daga cikin
abun da Anwar yafara samun tangarda ta lalacewa a rayuwarsa har yake shan abun da bai
kamata.... Alhji jalingo yafi shekaru goma da Aure amma allah bai basu zuriya ba ,karshe harda
Hjy Yalwa akaje kasan india anan ake tabbatar masu cewa" Hjy Haulat bazata ta6a haihuwa ba
duk da kasantuwar zata iya daukar d'an ,amma bata da kwanyin haihuwa". Amma bangaren
Alhji Jalingo lfy yake....jin hakan yayi matukar daga hankalin Hjy Haulatu wanda a haka suka
dawo gida nigeria...itakam Mahaifiyar sa Hjy Yalwa tun daganan take kara tirsasa Alh. Jalingo
akan sai ya Kara Aure ,amma da yake shi mutum ne mara raayin son Aure aure sai yy ta kwane
kwane...yau xaman lfy gobe bala'i wurin hajiyar nasa , a hakane Alhji jalingo yy ta yawan
kasashe akan lfyr Hjy haulat amma shiru ,a hakanne wani abokin shi Alhji salmanu yakai shi
Rugar SURBAJO wurin Mahaifin Shatu ,don kasantuwar sa malami a wannan ruga kuma yana
bada maganin haihuwa sosai....wannan ne farkon haduwar sa dakuma saladin fara
muamalanshi da Baffa....kwatsam sai ga Hjy Haulatu da ciki...Ya akayi?? Sai dai muce ikon
Allah! Subhanallah ai farin ciki wurin Hjy Yalwa baa mgnan ,zan iya cewa " tun daga wannan
rana bata kara rufe hakoran ta ba ,da wani faffadan hushiryar ta da duk yaya da jikoki sukayi
gado...
Nan ta dakko hjy Haulatu ta dawo gidan ta don ta rainin cikin nata ,a haka har allah ya sauketa
lfy a gidan.Hjy Yalwa ta sabado kyakykyewan Jarumin d'an su namiji wato Anwar. Hmmm tom
ya akayi hakan ne? Meyasa a yanxu Hjy Haulat take fadin ba itace mahaifiyar sa ba? Bayan
kuma a gidan Hjy yalwa ta raini cikin har ta haifo?? Ma daiji a gaba inshaallh".
*********
Bayan Shatu ta kammala breakfast din ta ne ta mike tana fadin Mama ina jiran ki a waje".
Mikewa Mama rahmatun tayi tana gyara Mata schoolbag din ta ,hadi da mika mata wani jaka
wato lunchingbox da akayi shi ta xamani amaimakon da d ake daukan basket...
Mama meye wannan kuma? Lunchng bag dinki ne koda idan an tashi break sai kici wani abu
,gashunan ga Sweat ma da choco zuba ciki. Tayi mgnan tana bata sweats din.... Mama Nafa
koshi ni yanxu dai muje schl din!
Dariya mama rahmatu tayi tana fadin ohh ni ramatu wannan doki haka ,saka su ciki mu tafi to.
Kar6a tayi tana zuba chocolates din ciki kamin Mama Rahmatu ta yafa mayafin ta cikin shugarta
ta manyan kasaitattun mata ta kama hannun shatun tana rike da School bag din ta ,ita kuma
Shatu tana rike da lunchng bag din ta sukayi wajen farfajiyar gidan...Mama rahmatu na tafe
mayafin ta na jan kaasa saboda irin yafen da takeyi ,abun ka da manyan mata....yanda suka fito
sai kin rantse da Allah a komai.Shatun yarinyar tace ta cikin ta ... A komai da komai".
Moton mama suka shiga kamin mai gadi ya bude masu gate ,mama ce take driving suka fice
daga gidan. Cikin Sabon gari suka shiga ,Hadi da nufan unguwan mai gwado muchia
roundabout......nan suka nufi gyafen randan da tun daga farkon wurin roundabout din taga
babban Singboud An rubuta C.T.C ACADEMY ZARIA. with Allah we will make it. Abun da Shatu
taga an rubuta kenan a daga kasa.....batare da ta lura ba taga har sun isa Wannan makaranta.
Fitowan Mama rahmatu kamin ta bude murfin moton nan taji wata dattijuwa tana bude moton
hadi da fadin Wlcm dear ,wlcm to CTC. cike da jinn dadi da doki Shatu ta fito daga moton tana
murmushin da sao da gyefe da gyefe na kuncin ta suka lo6a.
Tnhks Mah". Cewan Shatu tana fitowa gaba dayan ta...Rungume ta matan tayi tana rike da
hannun ta Suka gaisa Da mama rahmatu kamin su shuga daga ciki ,yanda suke fira da Mama
rahmatu yasa shatun fahimtar tun tuni dama sun dade da sanin suna ne da Mama".
Tun shigar su ta hango yara dalubai tun daga JS1to SS3 a asamblygroud suna wani wake da
Shatu hankalin ta ya koma kan su duka tana sauraren abun da suke fad cewa taji suna" _WE
SHALL MAKE CTC ACADAMYí ¼í¾¶....RIGHT NOW HANDS FOREVERí ¼í¾¶_ suna yi hadi