Showing 12001 words to 15000 words out of 41234 words
Chapter 5 - WALIJAAM BOOK 2 Hausa Novels by Maman Teddy .pdf
ta... Ka tabbata? Ehh na...hannun ta tasa
tana rufa masa baki kamin tace tom na yarda".
Hmm gyara zaman ta tayi tana sauka daga saman cinyan shi ,hadi da cewa ka bani daman na
zaben?..Daga mata kai yayi yana murmushi .
A'a Hamma ba haka zaka ce mun ba...kace ne "Eh na baki dama".
Kaji Hamma wai me yasa idan kana kallo na sai ka rinka wani tunani na dabam ne?? Saurin
saisaita kansa yayi kamin yace " Ina jinki me kkso nayi maki yanxu fadamun naji ,ashirya nake
nayi maki shi kinji Aishan Hamma Anwar.
Dariya tasa tana kallon shi hadi da cewa "To Ni Hamma babu abun da nakeso shine guda daya
,don Allah". Tayi mgnan tana rike masa hannu .
Nifa nayi maki Alkwari ki fadamun zan maki inshaallh.
"Hamma Ina sone ka kaini makarantan Yan binni ,ina so na girma nan gaba na zama babban
mutum kamar kai. Tayi mgnan tana dariya".
Tsintar kanshi yayi cikin wani yanayi na haka kawai ,kirjin shi yaji yana buga maasa...Kusan
minti biyu yakasa bata amsa...hakan yasa Shatu rike hannun sa tana fadin Don Allah Hamma
kaji,ina so na.....Kamin ta karake mgnan ne yace Zan maki komai Aisha don ganin farin cikin ki
,amma abu daya nake son ki mun alkwari!
Cike da jin dadi da murna tace"Hamma fada mun meyeshi zanyi maka nayi maka Alkwari!
Hummm wani jan numfashi yayi kamin yace"kimun alkwarin baxaki manta dani ba ,koda raina
ko babu...baxaki gujemun alokacin danake da bukatar ganin ki tare dani ba.... Cike da rashin
fahimtar inda zancen sa ya nufa tace "Nayi maka Hamma na ,kasan daga yau nafara sonka tun
da zaka sani a makaranta nayi karatu nayi ilimi na zama kaman kai.
Murmushi kurum yayi dan bangare daya na zuciyar sa babu wanda yake tunanowa sai Abbas
,yasan Sharrin shi kwarai ,kuma yasan abune mai wuya Abbas ya hakura da Shatun a lokaci
daya.
Tabbas Abbas bazai hakura da Shatu ba sai an kai ruwa rana ,shuyasa sam bayason a dai dai
wannan lokacin tayi nesa dashi....Amma kuma babu yanda zaiyi don Sa Shatu tayi ilimi yana
daga cikin fatan Mahaifin shi na ganin hakan.
Hamma"..."Hamma amma kai naji kana cewa baka sona ,kuma kana mun fada bayan tafiyar
wani dake kusa damu ,me yasa ,kuma da gske ne baka sona..ni naji ina sonka saboda kana da
kirki".
Yanda tayi mgnan ta bashi dariya matuka , Amma sai ya danne dariyar tasa yana cewa" Ina
sonki Aisha ,amma ba irin son da Mom ke mgn akai ba...Ina son ki fiye da yanda ko wani
mutum zai nuna maki,banason ganin wani abu ya sameki ,ina jinki acan cikin zuciyata..
Dariya tasaka har tana karawa jin a zuciyar da yace ,kana tace dama Hamma Anwar So
kala_kala ne?.
Emana!.
Ganin mgnan nata yaki karewa ne yasa Anwar mikewa yana riko hannun ta hadi da nufan
saman dirning don suyi dinnar.
Anan ne tayi shiru ,Ta natsu ..bayan sun kammala Falon suka dawo ya taaasa ta tana ta masa
zuban surutu ,haka kawai ya tsinta kansa cikin nishadi.....Anan wurin bacci ya dauketa...bai
tashets ba sai da ya kammala ayyukan shi kamin ya tattara koman sa yana daukar Ta cak
kaman baby yana nufan bedroom din ta.. A saman kayataccen gadon ta ya kwantar da ita
kamin ya nufi waldrob yana fiddo mata da Sleepdrees
Tabbas ya fahimci nauyin baccin Shatu don Da kanshi ya sa mata Kayan duk bata tashi ba ,duk
da dama yanayi mata yanda bazata ta shun bane....rufe ta yy da lallasar bargon kaman na
jarirai ,sannan ya rage hasken dakin yana mata Addu'a sannan ya rufo mata kofa.
Koda y isa bedroom din shi privacy ya nufa yana watsa ruwa ,kamin ya shirya kansa cikin kayan
bacci yana daukar Cofee din da daniel ya ajiye masa yana zama hadi da fara sha hankalin sa a
kwance.
Tuno da mgnan Shatun yasa shi daukar wayan sa yana kirar wata number danaji yana mawa
matan bayani akan yana son ganin ta.
Sorry for d late updateí ½í²ƒ
*í ½í°„WALIJAAMí ½í°„*
_*Littafin na kudi Normal grp 200....Vip grp 500...Spc grp 1k...zaki iya turo da katin MTN ta
wannan number 08081202932.....ko kuma ta wannan Account din Farida Hashim Stanbic
0028799846....Yan niger zakuna iya tuntu6an wannan number +22797780373 .*_
40_41
Matso kusa uwar gida kiji wani sirrií ¾í¶»í ¼í¿»í ¼í½‡í ¼í½‡
"Idan zaki kwanta ki kwaba lallai ki diga miski kadan da man hulba sai ki shapa agabanki bayan
30 minutes sai wanke da kanki zaki ban lavari idan kikaji bananar oga A cikin HQ din kií ½í¸œí ¼í½Œ...
_________________________
"Datse kiran yayi yana lumshe wa'annan Segxy eyes din nashi yana cigaba da shan cofee din
nashi a hankali yana tunanin yanda zai tsara mawa Shatun tashi rayuwar ta....
Bangaren Abbas kuwa tun daga wannan rana baya rufe sati baije rugar Surbajo ba ,yana zuba
mawa Fulani kudi kan su Fadi masa inda Shatun tayi aure ,amma har yau mgnan daya ce su
ma basu sani ba,kuma gskyar suka fadi masa don ba kowane ya sani ba. Da kyar ne yaci sa'ar
haduwa da wani mutum daya daya yy masa alkawarin nemo masa ta hanyar tambayan
mabanbantan mutane...aiko hakan akayi don a kullum Manu bai da aiki sai tambyar shin ina Ne
Shatu tayi Aure ,tun ana basa amsan ba'a sani ba har aka fara gajiya .
Haka rayuwar Abbas ya kasance kullum yana aikin sukurkutan Zulai mai aikin shi ,kamin wani
dan lokaci yagama sukurkutata ,tayi wani irin saki saboda tsaban jaraban shi...tom kullum abu
daya babu sassauci ,kun kuma yawan Sex na lalata mace kwarai...Barikin ma yanxu bai xaman
ta ,sam baya ta kan Auren da Abokin nasa yayi ,kullum Sadeeq mgnan sa yakamata suje gidan
Anwar suga Amarya amma sai Abbas yace abari sai sun gama cin Amarci....hakan sosai yake
mawa Anwar dadi ,don bayason makirin fuskan Abbas ya hadu dana Shatu".
Anwar kam baayi kwana biyu ba ya sama mawa Shatu mai mata lesson har gida take zuwa
,acewan shi daganan ne Idan takara gogewa sai akai ta school asata ajin da ya kamata...Don
komai yin shi yake with plan indai akan Shatun tasa ce...kamin wani lokaci kadan shatu ta
chanja ta saki sosai da Anwar rayuwa take na jin dadi da kwanciyar hankali...Don a lokaci
kankani Anwar yayi kokarin mantar da ita wani duk damuwa da ta afaka a rayuwar ta ta
baya....da wani kunci a kullum ji take tamkar su dauwa a tare kar wani abun ya rabasu a karo
na farko .
Shi kam Anwar a kullum yana kokarin kawar da duk wasu damuwar shi ,duk wani sha'awar sa
a kullum yana kokarin shan mgnin kawar maasa da shaawa ba tare da ya bari yayi wani abu da
shatun ba...don ya xame mata tamkar yaya kaman yanda take kiran nashi da hamma haka km
ya zama mata...
Anty Safiya itace mai koyar da Shatu karatun lesson ,Wanda a dan kan kanin lokaci shatu ta ke
fahimtar karatun sosai ,don karatun biyu ake mata ,idan Anwar ya dawo gida da yammaci ya
tambayeta abun da Anty Safiya tayi mata abun da ta manta ya tuna mata ,sannan su dora daga
nashi.... A hakanne Shatu a kankanin lokaci ta chanja har wayewa Ta kara gogewa saboda
zaman ta da Anty safiya komai nuna mata shi take tana koya mata .
*********
A yau safiyar laraba ,kasancewar Shatun ta san Anwar da Asuba yake ficewa saboda yaran
sojojin da yake sawa a masu training kamin a turasu garurruwa.....
Hakan yasa ka Shatu ko break ba tayi ba ,tana wanka ta shirya kanta cikin English wears riga
da skirt mai saki rigar roba ce sai ta daure gashin ta da ribom ,tana fitowa hadi da fadawa
Bedroom din shi.....A gaban mirrow ta ganshi yana Gyara belt din wandon shi jikin shi kuma
sanye da Singlete fari alamu yana kimtsawa ne...
Jah baya tayi da sauri ganin sa cikin wannan yanayin...wanda tun shigowar ta ya hangota ta
jikin madubin".
Zata fita ne ya kira ta cikin miskilalliyar muryar sa yana fadin "Aisha ina zaki koma kije..." saurin
tsayawa tayi cakkkk kamin ta dan kame kame tana fadin "Hamma ai ban gan ka bane!
Murmushi yayi yana daukar rigar sa yana sanyawa hadi da gyara komansa kamin yace tom
gani kin tashi lfy dai ko...?
Takowa tayi zuwa inda yake kamin tace"Hamma ina kwana " Lfyl Alhmdllh.
Hamma yau muyi karatun safe ne plx kaga na iya na jiya".
Murmushi yayi kamin yace "kin tabbata Aisha tom muje nayi maki...Cike da jin dadi ta riko
hannun sa sukayo falo don anan ne suke lesson din.
Sosai ya sha mmkin jin yanda ta iya karatun da yy mata sarai ,hakan yasa shi sanar mawa da
Wani soja kan cewa yace sai karfe tara na safe zai fito masu training.
A wannan Safiya sosai sukayi karatu da Shatun tashi ,anan ne kuma ya gasgata mgnan Anty
Safiya nacewa Yakamata Shatu ta fara zuwa Schl.
Abbas kam da Sadeeq sun sha mmkin jin wai Anwar din yace ba zai fito ba sai 9am. Wannan
yasa su sa dariya suna zagin Anwar da sokana kaman yana gaban su ,Sadeeq ne mai cewa ya
kamata muma muyi auren nan muji yanda akeji.
Ji bika don Allah ,Me ko akeji banda wanda ka sani a wurin matan dakasaba muamala dasu
,kawai dai kace ne Yau zamu shiga muga Amaryar tasa...ba tare da ya sani ba..... A haka kam
suka tsaida matsayar shiga gidan Anwar da ya fito su kuma zasu shige ba tare dayasani ba a
cewan su sun lura bayason sugane masa mata ne.
Tare sukayi break da Anwar kamin ya tafi barack , Karfe 11am Anty safiya tazo suka fara fura
kamin daga bisani sufara karatun nasu ,wanda yawanci tambayoyi take mata akan na baya....
Knocking taji anayi wanda cikin sauri Shatun ta mike tana nufan Kofa don ta bude mawa bakin
nata ,a hankali tace ku shigo ganin kofan ba key.
Abbas ne da Sadeeq suka shigo bakin su dauke da sallama ,wanda duka sallaman tasu ce ta
makale ganin wanda basu xata ko tsammani ba wani irin kallo Abbas yake mata mai cike da
tambayoyi da ma'anoni kamin da kyer ya iya furta me ya kawo ki nan MATATAí ½í¹„..................
GNí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒ
*í ½í°„WALIJAAMí ½í°„*
_*Littafin na kudi Normal grp 200....Vip grp 500...Spc grp 1k...zaki iya turo da katin MTN ta
wannan number 08081202932.....ko kuma ta wannan Account din Farida Hashim Stanbic
0028799846....Yan niger zakuna iya tuntu6an wannan number +22797780373 .*_
42_43
Saurin Jah baya Shatu tayi don kallo d'aya tayi mawa Abbas ta shaidashi wannan dalilin yasa ta
saurin jah baya tana yin bayan Anty Safiya da itama idon ta ke akan su Abbas ,don ita tayi
masu farin sani ,don tabbas indai kasan Anwar tom zaka san Abbas da Sadeeq.
Kai wannan wace irin mgn ne ,kawai da ganin yar mutane sai ka wani kama ce mata matar ka ?
Yo ta ina ta zama matar naka da har kk tambyar ta mai ya kawo tanan? Kasani ko Yar uwar
tace Matar Anwar din tinda itama ai bafullatana ce....cewan Sadeeq yana kama hannun Abbas
da idon shi ke akan Shatu har a lokacin ji yake kaman ya sungumeta ya tafi da ita.
Sadeeq ne ya jah hannun sa suka shigo daga cikin falon ,wanda Safiya kam ita kanta mmki ne
ya hanata mgna ,wanda data rasa Abun da zata ce masu sai cewa tayi " Kar dai Leutanant kace
mun baka san Matar Anwar ba...to ai itace matar da Anwar ya Aura!!!
A da baya zama Abbas da Sadeeq ke kokarin yi ,amma dajin mgnan Safiya yasa su duka
saurin mikewa hadi fadin mene kikace Safiyya?? Ta6 ni Anwar zai yaudara ,Ni xai Aure mawa
matan da nadade ina mafarkin Aura? Wlh sai ya rabumun da Aisha na aureta ,don kuwa dani
Aisha ta dace ba da wani ba...kuma a yau sai na tafi da Matata...!!
Wacece matar taka Abbas?? Aishan ce matar ka ? Kana hankalin ka kuwa?... Cewan Anwar da
sam basu lura da shigowan sa ba sai dai maganan tasa... A zafafe Abbas ya juyo ga Anwar
kamin yayi mgn ne Shatu da gudu cike da tsoro tayi bayan Anwar tana rungume shi da cewa
"Wayyo Hamma na tsoro nakeji...Wai xai tafi dani ,kar ka bari ya tafi dannni don Allah! Maganan
take gaba daya a birkice don ta cukukuye Anwar sosai... Wannan yaasa Abbas jan burki yana
bin Anwar da wani irin kallo...
Juyowa yy yana kallon Shatu kamin ya girgixa mata kai da cewa" babu mai tafiya dake indai ina
nan ,ke Ai amana ta ce ba xan ta6a yarda wani yayi mun farraku dake ba. Don haka shiga daga
ciki...
A kullum Anwar din maganganun shi na kara mata karfin gwiwa ko me ya fadi mata tana saurin
yarda da gasgatawa musamman tasan Anwar din jarumin namiji ne baya fadin Abu don dadin
bakin shi...tom amma a yau taga wasu jaruman wanda mgnaganun Anwar babu daya zata iya
fadowa wanda yace ,sai dai kawao taji tsoron sa kwarai ,musamman tuno da karon da suka fara
haduwa a farko da yanda yaso yi mata lalata ta karfin barta.
Da sauri ta cika hannun Anwar cike kuma da sakin jiki ta ra6a shi tana kokarin wucewa...Aisha!!
Taji muryar Abbas ya kira sunan nata ,wanda yanda ya kira sunan nata sai da taji faduwar
gaba... Kar ki tafi ,indai ina a raye baxan bar kaunan ki a xuciyata ba ,kuma Anwar ba sonki
yake ba ,yana yin komai da plan nashi na nan gaba ,daga wannan lokacin ne zaki fahimci waye
Anwar?? Ni ne mai sonki da gsky.....Kirjin ta ne ya cigaba da dukan uku uku ,wanda da sauri
tayi bedroom din ta....don ji tayi sam batason jin wani sauti ko murya na Abbas...waye shi
din...ni zaka Yaudara Anwar??? Tambayar da take mawa kanta kenan ,kamin ta rinka tariyo da
mgnan Abbas da yake kiran sunan Anwar yana fadin shi xai yaudara!!
Allah shi kyauta...ai wlh ko Hamma yace naso wannan mutunin baxan so shi ba,mugu ne....tayi
mgnan a sarari tana rintse idon ta hadi da tunano lokacin da Ya manna jikin ta da nashi a jikin
moto...
Jin haushin Abbas take har A cikin zuciyar ta...hayaniyar da taji ne daga wajen Windown ta
yasata lekawa cikin sauri ,Abbas ta gani da Sadeeq yana jan sa ,sam bataga Anwar a wurin ba
yyn da batayi aune ba taga ya bugi glass din murfin moton yana ratsatsakewa lokaci daya glss
din ya caki cokan hannun shi...
Sai jini sharrrrr sharrrrrr da gudu Shatu tajah baya tana hayewa saman gadon ta hadi da jan
bargo gaba daya ilahirin jikin ta rawa yakeyi ,bata ta6a ganin jini nq zuba hakan ba ".
Shikam Bangaren Anwar da Abbas sai da Shatu ta shiga daga ciki ne ,suka fara masifa kunsan
dai fadan sojoji yi suke kaman su kashe kansu..
Malama Safiya ne ta shiga gaban Anwar tayi ,yayin da Sadeeq yaja Abbas da sauri ya fitar
daashi daga falon ,don yasan zuciyar kowa...Abbas fitina ne ,shikam Anwar baiki a mutu
ba...sunan miskiline amma yafi mai baki Kunar bakin wake....
Abbas kam jan moton nashi yayi a matukar fusace yana figarta cikin wani irin mahaukacin
gudun da rabon da yy irin shi ya manta....haka ya fice daga barikin sojojin ....babban titi ya hau
wanda ko kallon na gaban sa baiyi bare Na gyefen sa....wani mai acaa6a ne Abbas din yayi
gaba dashi...yana wucewa *í ½í°„WALIJAAMí ½í°„*
_*Littafin na kudi Normal grp 200....Vip grp 500...Spc grp 1k...zaki iya turo da katin MTN ta
wannan number 08081202932.....ko kuma ta wannan Account din Farida Hashim Stanbic
0028799846....Yan niger zakuna iya tuntu6an wannan number +22797780373 .*_
42_43
Saurin Jah baya Shatu tayi don kallo d'aya tayi mawa Abbas ta shaidashi wannan dalilin yasa ta
saurin jah baya tana yin bayan Anty Safiya da itama idon ta ke akan su Abbas ,don ita tayi
masu farin sani ,don tabbas indai kasan Anwar tom zaka san Abbas da Sadeeq.
Kai wannan wace irin mgn ne ,kawai da ganin yar mutane sai ka wani kama ce mata matar ka ?
Yo ta ina ta zama matar naka da har kk tambyar ta mai ya kawo tanan? Kasani ko Yar uwar
tace Matar Anwar din tinda itama ai bafullatana ce....cewan Sadeeq yana kama hannun Abbas
da idon shi ke akan Shatu har a lokacin ji yake kaman ya sungumeta ya tafi da ita.
Sadeeq ne ya jah hannun sa suka shigo daga cikin falon ,wanda Safiya kam ita kanta mmki ne
ya hanata mgna ,wanda data rasa Abun da zata ce masu sai cewa tayi " Kar dai Leutanant kace
mun baka san Matar Anwar ba...to ai itace matar da Anwar ya Aura!!!
A da baya zama Abbas da Sadeeq ke kokarin yi ,amma dajin mgnan Safiya yasa su duka
saurin mikewa hadi fadin mene kikace Safiyya?? Ta6 ni Anwar zai yaudara ,Ni xai Aure mawa
matan da nadade ina mafarkin Aura? Wlh sai ya rabumun da Aisha na aureta ,don kuwa dani
Aisha ta dace ba da wani ba...kuma a yau sai na tafi da Matata...!!
Wacece matar taka Abbas?? Aishan ce matar ka ? Kana hankalin ka kuwa?... Cewan Anwar da
sam basu lura da shigowan sa ba sai dai maganan tasa... A zafafe Abbas ya juyo ga Anwar
kamin yayi mgn ne Shatu da gudu cike da tsoro tayi bayan Anwar tana rungume shi da cewa
"Wayyo Hamma na tsoro nakeji...Wai xai tafi dani ,kar ka bari ya tafi dannni don Allah! Maganan
take gaba daya a birkice don ta cukukuye Anwar sosai... Wannan yaasa Abbas jan burki yana
bin Anwar da wani irin kallo...
Juyowa yy yana kallon