Showing 102001 words to 105000 words out of 132190 words

Chapter 35 - Matar Makaho Compelet Book by Rukayya Ibrahim Lawal.doc

waje, Amma sumayya kinsan rayuwar Abuja ba d'aya bane da Taraba koh? gidan nan da nake ciki dubu dari biyar ne a shekara , haka mijina ke biya.

"Karki damu indai kudin hayan ne zan biya laila ba damuwa, har school nake son ki taimaka naje na saka khadija"

Sumayya kamar nawa kika shigo dashi abuja ne wai?

"Million d'aya da dubu d'ari hudu"

Hhh lallai sumayya don kunzo da wa'innan kudi kike tunanin zama a Abuja, nifa bawai na yarda dake da abinda kikace bane, na sanki sarai da zurfin ciki, Amma fa ki sani wallahi wa'innan kud'aden da kikazo dasu wallahi bazasu miki kome ba, saidai in kin shigo da result naki nasa mijina ya nema miki aiki koda a office insu ne?

"Laila banzo da kome daya shafe karatuna ba, sannan ni ina da sana'a wanda nake saka tsammanin zan iyya neman na kaina da shi, kuma yarinyar nan kanwar mijina ce, marayu ne su biyu Iyayen su suka haifa,mijina bayanan shiyasa narike ta a hannu na, kuma karatun ta nada muhimmanci aguna"

Toh wani sana'a kenan kike bayan Lalle sumayya? Ita khadijar bata da dangi ne?

"Harda make-up kuma khadija ta iyya kitso inso samune shago nake so na kama sai mu fara muga yanda Allah zaiyi damu"

Anya kuwa sumayya gaki da ciki in kika haihu d'awainiyar abinda kika haifa zai dawo kanki, ga khadija ga kudin haya ga kayan da zaki sawa d'akin da zaku kama, ga kudin makarantar ta anya abinnan zai hadu kuwa?

"Insha Allah laila Allah zai dafa mana, yanzun dai so nake kimin hanyar da zansamu dakin gidan nan da kikace ya saura, don so nake kafun mijin naki ya dawo mun bar muku kofa, tunda kikace jiya ma kinje d'aukosa a tasha kika samu bai iso ba, motar su ta samu matsala"

Ba kome tashi toh muje gidan, mai gidan yana tsallaken titi bara na kira mijina na fad'a masa.

Ok sumayya tace suka wuce gidan mai gidan hayan, bayan laila ta nemi izinin mijinta a waya.

Bayan sunje a take sumayya ta wuce bank dayake babu halin transfer, tunda ba sim a wayar ta, kudin hayan suka kawo wa mai gidan,bayan sun dawo kudi sumayya ta baiwa khadija da laila suka tafi kasuwa, ita kuma bude d'akin da suka kama tayi, sashen mai kyau two bedroom da falo ga daining area ga toilet a cikin koh wani daki, ga kitchen a ciki daki dai mai kyau dashi yasha tiles kamar d'akin laila, kome a ciki.

Bayan su khadija sun dawo katifa suka sayo babba, da zanin gado sai hot plate mai kai biyu, da sandan moping sai bokati biyu, soson wanka dadai d'an abubuwan Amfani daidai talaka, bujuwan su biyu, khadijar ce ta ibi ruwa a panpon gidan ta wanke musu d'akunan tayi moping, yana bushewa suka shimfid'a katifar a falon, suka kai sauran kayan da suka saya kitchen, suka shigar da akwatuna su cikin d'ayan d'akin, suka kwanta a katifar su ita da khadija a falo sosai gidan ya musu d'adi ganin kowa na d'akinsa babu tsegumi kamar gidajen hayan da suka sani.

***********
Ta bangaren Al'ameeen, suna zaune a gindin bishiyar ga gajiya ga yunwa, Gidado dake gefene ya fashe da kukan bakin ciki, Al'ameen da yaron fulanin nan sukayi wajen sa da sauri, duk da raunukar dake jikinsu, don gabaki d'aya kafafunsu kayoyi sun bula gashi hannun muhammad sai yanzu yake jin tsamin sa ga giransa dake ciwo, Gidado lafiya kuwa ?sukace har suna had'a baki.

Kuka gidado ya sake da karfi, sai kuma ya bude baki Amma ya kasa magana, da hannu kawai ya nuna musu gefen jikin bishiyar da yake.

A matukar kidime muhammad yace, innalilahi wa'inna'ilahi raji'un sarin ka yayine gid'ado............
('Ruqeenjalal('

[10/24, 2:18 PM] +234 903 356 9641: >???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~



Page 8? 0? &8? 1?
Maciji ne babba duk da darene amma macijin fatarsa na sheki, Girgiza kai gidado yayi Alamu dai ba sarinsa yayi ba, da gudu Muhammad ya jawo wani katon reshen itace babba, ya bugawa macijin da karfi akai, ya sake buga masa take kan macijin ya wargaje, mikewa muhammad yayi ya taimaka wa gidado suka mike, ganin maciji a wajen yasa su cigaba da tafiya duk da dare ne, saida suka isa wani wajen yashi kafun suka yad'a zango, agun suka kwanta.

Basu suka farka ba sai washe gari, harma gari ya waye kafun suka farka, taimama sukayi, sukayi sallah zuwa lokacin hannun Muhammad yayi mugun kumbura sosai, badaru ne ya tsinko wani ganye ya mursuke yasaka masa a ciwon, mangoro suka tsinko mai yawa suka sha ga ruwan korama suka iba, sukaci gaba da tafiya.

A haka su Al'ameen sukayi ta tafiya kusan sati biyu, suna fasa hanya saidai su shiga wannan dajin su fita suyi wannan, gabaki d'aya wahala ya canja su, hannun Muhammad yayi dan sauki, kafafunsu tun yana musu rad'adi har suka saba, ga giransa daya tsage, da ace a garine dinki za'a masa, Amma haka sukaci gaba da tafi giran na warke wa, amma fa fatar bai hade ba sai yayi kamar tsagun wuka wajen yayi, sai yayi matikar karawa fuskar tasa kyau.

Saida su Al'ameen sukayi kusan wata biyu, suna tafiya a kafa bayan zama da sukad'anyi a wasu kauyuka, yaukam tsintar kansu sukayi a sahara mai zafin gaske, Allah yasa ma sunyi guzuri saboda kauyen da suka baro sun sanar dasu gabansu sahara ne, suna tsallake sa nijar zasu shiga.

*********
Ta bangaren sumayya basu farka ba sai????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? mangariba, Bathroom suka shiga sukayi Alwala, bayan sunyi sallah sumayya ta kalli khadija"ki shiga kitchen a cikin cefenen da kukayin nan ki d'auka ki dafa mana koh abu mara nauyi ne"

Toh Aunty khadija tace ta wuce wa kitchen in, dayake duk a falo yake basai ta fita waje ba flat ne babba, khadija na shiga kitchen saiga yar laila mai shekara biyar ta shigo d'akin da sallama

Amsa mata sumayya tayi ta karbi kulan da ke hannunta, ina kwana aunty, ta gaida sumayya.

Murmushi sumayya tayi tace"Ina wuni dai baby"

Ina wuni?

"Lafiya munira, Dady ya dawa koh?

Eh ya dawo gashi momy ta bani na kawo miki, tace tana mikawa sumayya kulan

" wai gaskiya mungode wa momy kinji kice nama dady sannu da zuwa.

Toh yarinyar tace tana fita a falon, kwalama khadija kira sumayya tayi, bayan ta fitoh ne sumayya kece mata, Laila ta kawo musu abinci tabar girkin, ta d'auko musu pure water biyu dake kitchen in, A plate d'aya sumayya ta zuba musu abincin, tuwo ne miyar shuwaka da kifi busheshe, sosai sukaci tuwon suka sha ruwa tashi khadija tayi tarufe musu kofar falon, tabar kee a jikin kofar wanka sukayi dayake Abuja akwai nepa yasa ta kunna AC dake makale a falo, don sunyi sa'a akwai Ac a falo, shiyasa sumayya tace susa katifa a falon in, kwanciya sukayi akatifarsu.

Washe gari tie da kwai suka karya dashi khadija ta wanke musu d'an plate insu da kwanon laila,khadija ce ta maida mata kwanukan da safe, sumayya had'a laila tayi da khadija da zata fita aiki akan suje ta kai khadija makarantar da yaranta ke zuwa, tunda transfer ne ba sabon register zatayi ba.

Khadija ta samu gurbin karatu a school in, sai dai fa kudin makaranta 50k ne duk team nan ma wai makaranta daidai gwargwado kenan,sai kudin school bus, a ranan suka bawa khadija uniform nata Daman tazo da kome na makarantan ta harda note book, shiyasa washe gari da safe tana karyawa ta sanya uniform nata, siket ne da riga sai necktie da baby hijab, bayan khadija ta tafi makaranta dayake school bus na jiranta a bakin titi, Karyawa sumayya tayi ta koma ta kwanta tama rasa me zata kama, ta gaji da zama waje d'aya tashi tayi ta shirya ta fita, da kwatance taje clinic don yanzun cikin na neman 4 months shiyasa takeson fara zuwa awo abinka da yar boko dakanta, ta gane asibitin, ta bude file a wajen sannan zatana zuwa clinic harta haihu, daga asibiti kasuwa ta wuce tad'an saisai musu kayan masarufi.

Bayan ta dawo wanka tayi ta dafa musu abinci sai yamma khadija ta dawo, uniform nata ta wanke ta had'a da kayanda Auntin ta ta saka jiya, tayi moping tayi musu girkin dare, yayin da sumayya ke kwance akan katifa tana kallo a system nata.

Bayan mangari ba saiga laila ta shigo lokacin sumayya da khadija nacin abinci a kasan tiles, sumayya na zaune akan filo saboda yanayin ta da ba'aso ta dabasu a kasa.

Ah ah hajiya sumy haka ake makwantakan koh nokin babu.

"Kai laila kin cika iyayi maigida ya dawo basai mu baku waje ku sarara ba, tukunna"

Karasowa falon laila tayi, lallai ma sumayya wani irin bamu waje, kaman sabbin aure

Ina kwana Maman munira?

Lafiya khadija ya school in?

Lafiya klau, tace tana iban abinci a wani plate ta wuce daki.

"Kai laila ga abinci bismillah"

Zama tayi a bakin katifar, sumayya nayi magana da baban munira yace min za'a samu shago, amma nidai gaskiya sumayya hankalina bai kama ki bude shago yanzun ba, duba da halinda kike ciki ba
[10/24, 2:18 PM] +234 903 356 9641: >???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~


Page8? 2? &8? 3?
Mikewa Sukayi da sauri suka nufi kofar gidan, ba tare da wani tsoro ba suka zare sakatar, me zasu gani?bawan Allah nan ne aka d'ago rababe-rababe kamar kayan wanki, cikin hanzari suka bawa mutane biyu da suka d'agosa hanya suka shigo dashi cikin gidan, direct d'aki suka nufa dashi suka kwantar.

Al'ameen dake binsu a bayane ya tambaye su meya faru dashi?

Wani a cikin sune yake tsanar dashi wai ashe faduwa mutumin yayi a gidan da yake aiki, kafarsa ya karye shine aka kaisa asibiti aka d'aure kafar, amma yaki zaman asibiti wai sai dai a dawo dashi gida yayi jinya.

Allah ya kiyaye na gaba Su Al'ameen sukace suna komawa d'akin mutumin.

Kallon kafar da aka d'aure muhammad yayi, Sannu baba Allah ya kiyaye na gaba?

Amsa masa yayi da, Ameen Al'ameen.

Sannu baba, gidado da badaru sukace a tare, Amsa musu yayi a hankali, tashi Al'ameen yayi ya fita a d'akin, murhun inda ya gani na karfe d'an karami ga gaushi a ciki, nitsuwa yayi ya hura wutan ya d'aura butan shayi, atakaice dai shayi ya had'a a cikin butan ya had'a da kofi ya kaima mutumin, ba musu mutumin yasha kad'an, Al'ameen ya sake fita ya d'aura ruwan zafi, yana dumi ya d'auko a roba ya had'a da tsumma yazo ya gogewa mutumin jiki, ya shanja masa kaya, sosai mutumin yaji dadi yayita sama Muhammad Albarka.

Da dadare ma su gidado sun koma dakin su, yayinda Al'ameen ya kwanta da mutumin a d'akinsa tare, tsakar dare mutumin ya farka da taimakon muhammad yayi fitsari ya sake dawo dashi ya kwantar, a hankali mutumin ya kalli muhammad sai kuma ya bude baki ya fara magana, Allah ya dubi halinda zan shiga ya aiko mini ku muhammad, da ace yau babuku a gidan nan bansan halinda zan tsinci kaina ba, bani da kowa gashi ba Aure nake dashi ba bare yara.

Babu kome Baba fatan mudai Allah ya baka lafiya.

Ameen muhammad, Akwai wani taimako da nakeso kamin, in babu damuwa d'an nan?

Ba kome baba indai har baifi karfina ba, kuma bai sab'awa shariya ba, zan maka kome da kake bukata, kayi mana kome baba tunda ka bamu matsuguni a gidan ka.

Muhammad a gidan da nake aiki tsawon shekararu a gidan, tun lokacin da mahaifina ke aikin a matsayin da nake yau, ina binsa muje tare har Allah ya d'auki Ransa, ni na cigaba da aikin kamar shi, a yanzun bani da kowa ba uwa ba uba ba yara ni kad'a nake rayuwa ta a gidan nan, sai yanzun da Allah ya turo mini ku, in ba damuwa so nake muhammad kaje a matsayina, kaci gaba da aikin da nake har Allah yasa na samu Lafiya, kaga bazanso ace aikin da nake tsawon shekaru, yau a samu wani ya karbe mini ba, tunda ciwon bana kwana biyu koh uku na warke bane?sai nayi jinya mai tsawo.

Shuru muhammad yayi na d'an wani lokaci kafun yace, ba kome baba zanje nayi aikin har Allah ya baka lafiya, Amma wani irin aikine don ni baba banyi karatu mai zurfi ba?

Murmushin karfin hali mutumin yayi, bafa aikin da ya shafi ilimi bane, aikin gidan sarauta ne, kuma nine sarkin shayi na gidan.

Muhammad ne ya kalle sa da mamaki, Gidan sarauta kuma baba?

Eh d'an nan zakaje ka zauna a matsayina tun jiya na sanar dasu zaka fara zuwa aiki gobe.

Aini baba ban iyya dafa shayi irin naku ba, kadai ga yanda na had'a shayin d'azun baiyi irin wanda ka had'a mana ba.

Karka damu muhammad akwai wa'inda zan turaka wajen su, 'yan gida nane suna taimaka mini wajen raraba shayi a gidan, Na sarki ne kawai nake kaiwa da kaina, kaima yanzun kaine zakana kai masa,sannan shayi kala uku ake, akwai na sarki shinasa dabanne, akwai na family akwai na bayi.

Baba anya zan iyya aikin nan kuwa, gidan sarauta fa kace?

Zaka iyya muhammad ka taimaka kaje kaji?

Shikenan Allah ya kaimu goben lafiya, Amma baba wazai nuna mini gidan, don ni bako ne , bansan ina ne gidan sarkin garin nan ba?

Karka damu muhammad akwai yaron makwantan mu gobe zan turaka gidan su saiya kaika.

Shuru muhammad yayi ya kwanta, Amma ya kasa bacci haka kawai yaji yana fargaban zuwa gidan kodon bai taba zuwa bane oho.

Washe gari muhammad ne yayi wa mutumin Alwala da ruwan zafi ya saita sa gabas, sukuma suka wuce masallaci.

Bayan sun dawo kamar jiya suka kimtsa gidan yau harda karyawa suka had'a mai kyau, bayan muhammad yayi wanka, baba kaya ya sakasa ya d'auka irin na buzaye, wando kato da rigansa mai aiki a gaba sai rawanin su, muhammad kasa nad'a rawanin yayi, Amma haka mutumin nan a bashi da lafiya saida ya nad'awa muhammad, rufe masa fuska yayi da rawanin babu abinda ake gani a fuskar sa sai kwayar idanunsa, sosai Al'ameen yayi mamaki harya kasa hakuri yayi magana, baba basai an rufe fuskar duka ba?

Ah ah muhammad ina son koh kaje gidan karka bude fuskar ka, ka barsa a haka, kuma kayi taka tsamtsam da kowa na gidan, karka yarda da kowa kayi abinda ya kaika ka dawo, ga wannan in kaje get sai kanuna, kafun a barka ka wuce ciki.

Karba muhammad yayi yana karanta abinda baba ya basa, get pass ne d'auke da rubutun larabci, a jiki saidai bai gane me aka rubuta ba, kasancewa yare aka rubuta da harufan Larabci sai hoton zaki a bayan get pass in, Muhammad fita yayi bayan yama su gidado bayanin inda zashi, sosai suke da Zuzuta karbar da kayan ta masa kamar buzun gaske, bayan ya fita a gidan, gidan makwancin su ya wuce ya masa bayani kamar yanda baban yace masa, had'asa da yaron sa mutumin yayi, ya rakasa gidan da baba ke aiki.

Tunda suka sauko a machine yakejin wani irin masifeffen bugun zuciya, ga wani irin fargaba dake cikin ransa ya rasa dalilin da yasa? ya tsinci kansa da tsoron zuwa gidan, tun daga nesa ya hango wani irin gini mai d'aukar hankali gini ne irin dogin nan masu masifar tsaho, ga wani fankamemen get fari mai d'auke da hoton zaki babba a jiki, gidane na Alfarma koh ince unguwa guda tun daga nesa zaka tambatar gidane na sarauta, masuji da mulki,yanda suke matsowa gidan haka bugun zuciyar Al'ameen ke kara yawaita, karasowa sukayi bakin get in, masu tsarone sanye da bakaken kaya hannunsu d'auke da manya manyan bindigogi cikin tsawa d'aya daga cikin su ya dakawa su muhammad da karfi cikin yare yake musu magana.

Daskarewa muhammad yayi jin yanda mutumin ya hayayyako musu kamar zaicisu d'anye, gashi sai yare yake shikuma baji yake ba, Allah yasa yaron da suka zo tare yana gun shiya musu bayanin zuwansu cikin yare tare da sanar dasu muhammad d'an uwan Sarkin shayi ne, zaizo ya karbe sa daidai yaji sauki.

Basu barsu sun shiga ba har saida Al'ameen ya nuna musu get pass da baba ya basa kafun suka barsu suka shiga ciki, mutuwar tsaye muhammad yayi lokacin da idanunsa suka sauka a compound na gidan, duniyace babba gida mai matukar girma, a haka suke taka tsakar gidan daidai sun iso tsakiyar gidan muhammad yaga gunkin zaki babba mai matukar girman gaske, An kawatashi a tsakar gidan a zaune kamar mai rai, wucewa wani shashe sukayi da yaron sai gasu a wani kayatancen falo mai masifar kyau da d'aukar hankali, kujerune na Alfarma a cikin su, zarce wa sukayi cikin wani kofa dake gefen falon, shidai muhammad idone nasa yake bin koh ina da kallo, har suka shiga cikin d'akin, wow shine abinda ya fitoh a bakin sa ganin wani irin kitcheen na Alfarma mai dauke da kayan Alatu na zamani, sai samari guda biyu dake kitchen in a tsaye suna aiki,jin motsen su muhammad da sallamar suce yasasu juyowa.

Amsa sallamar sukayi, bayan sun gaisa da yaron yake musu bayanin Al'ameen ne zai karbi, sarkin shayi harya warke, sannan sarkin shayi yace su koya masa had'a shayi, sannan shi zaina kaiwa sarki shayi kullum, duk da yare yaron ke musu bayani.

Muhammad kamfa ya shiga tsaka mai wuya don shi dai ba yare yake jiba, tayaya zai iyya zama da wa'innan mutane wai daman babu hausawa ne a nijar koh dai wannan garine baida hausawan oho?kuma gashi baba ya iyya hausa?

Yaron ne yajuya zai fita a kitchen in da sauri muhamamd ya bisa a baya, da mamaki yaron ya juyo ya kalli muhammad cikin mamaki yake tambayar sa yaya kuma zaina binsa?

Gaskiya nifa ban gane ba kowa a gidan nan sai yare yake mini, nifa baji nake ba.

Dariya yaron yayi karka damu kaji, wasu a cikin su suna ji sai dai in an ganka za'ayi tunanin koh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login