Showing 66001 words to 69000 words out of 132190 words

Chapter 23 - Matar Makaho Compelet Book by Rukayya Ibrahim Lawal.doc

mamaki meya kawo sumayya gunsa bayam tace gidan deputy zata, tashi yayi ya matsa gefe

Binsa sumayya tayi inda ya tsayan ba mutane, itama tsayawar tayi batace kome ba

Lafiya?

"Lafiyar kenan koh laifine in nazo wajen ka"?

Babu laifi...

"so nake ka rakani"

Rakaki ina?da mamaki a fuskar sa

"Gidan da zanin mana"

Hala baki gani ne?

"Ah ah ina gani so nake ka rakani"

Bazani ba, yace yana tafiya

Ai da sauri sumayya ta riko rigansa

Keee menene haka? koh baki ganin a gaban mutane muke ne

"Toh sai me in a gaban mutane muke koh ba mijina na rike ba kuma wallahi in baka shige mun tafi ba saina rungume ka a gabansu"

Uhmm Allah ya kyauta shige mu tafi


Mutumin da ke saida ruwa kusa dasu Al'ameen ne ya dubi abokin sa, Kai Amma yariyar nan bata da kunya har masallaci zatabi miji bata maji kunyar idon mu ba muna zaune? wama yasan dalilin da yasa aka aura masa yarinya kamar wannan?

Gaskiya ne haruna daga gani idon yarinyar a tsatsaye yake..


Haka sumayya tasa muhammand a gaba har gidan kanwar deputy har falon baki aka kai Al'ameen aka had'asa da abin motsa baki sumayya kuma ta shiga falon matan gidan

Har yamma suna gidan sallah kawai ke d'aga Al'ameen yaje yayi ya dawo

Sai kusan 5:43 na yamma suka fitoh gida gaskiya sumayya ta yaba da karamcin y'an gidan don Take Away na abubuwan da aka shirya na biki aka iba mata" yanzun ina zamu"?

Sama jannati zamu, Al'ameen ya bata Amsa

"Ni kake fad'awa bakar magana"?

Eh an fad'a in ai nafi mai Ashar kuma bakar ma agunki na koya

"Badai aguna ba kuma in kayi tsiya saina gudu na barka ka bata"

Kanki kika ma Asara bani ba.

"Akan me xan ma kaina asara kuma"?

Aikan mijin da kike dambe mana

"Dambe ni banyi dambe akanka ba"

Au habba daman tabaryar ta burgane?

"Ai na razana tane, karka wani zata fad'a nake akanka"

Na nawa kuma.

"Allah ba wani"

Ke kika sabi dai mutum sai taurin kai

"Kamar kai"

Shuru ya mata don ya fahimci sumayya inya biye mata fuskar da ya d'aure bazai san lokacin da zai sake ba.

Keke suka hau suna isa gida ana kiran mangari ba masalaci ya shiga ita kuma ta wuce cikin gida

Bayan ya dawo sallah take Away in ta bude musu donut da kaza rabi sai drinks d'ayan take away in kuma fried rice ne da lafiyayyen naman shanu suna kammala ci, muhammad kam kwanciyan sa yayi

Sumayya TV ta kunna ta koma ta kwanta tana kallo a kwance"yayan khadija"ta kirasa tana kallonsa ganin ya natsu waje d'aya yana tunani, jin bai Amsa ba yasa ta dafa kafad'an sa

Da sauri yace Am Ammar kudin nan basuyi yawa ba, sai kuma da sauri ya fara kame kame don sam subutar baki ne abinda ke zuci shiya fitoh fili

"Wani kudi kuma Waye Ammar"?

Am ba kome.

Akan me zakace ba kome duk kabi kasa kanka a damuwa in ma bashi ake binka bazaka fad'amin na biya ba duk kudin da nake tarawa Wallahi tatali nake maka naga kudin yayi yawa sosai kafun na baka ka kama sana'a mai d'an kauri mu samu murufawa kan mu asiri, amma ina dalili ina dana rufin asiri kabar kanka a rikici"

Ba haka bane sumayya ba'a rikici zansa kaina ba wannan magana ne daban.

"Wace magana kenan?koh bankai naji damuwar kaba"?

Daman Ammar ne ya mini magana jiya zai bani jari dubu d'ari uku na kama shago kafun azumi tunda saura sati biyu ne ga kayan marmari a azumi akwai kasuwa.

"Bazai yuba wani ma Ammar inne d'aya? akan me zaice zai baka kudi tun da baisan zai Taimake kaba sai yanzun"

Sumayya bamu fa dade dashi ba kuma insha Allah ba abinda zai faru

"Gaskiya ban Amince ba ka bari inna gama had'a kudin saina baka kabar masa nasa"

Gaskiya sumayya gwara na karbi nasan kawai na gwada kasuwar tunda ba kyauta yace ba koh bashi saina tambaye sa in kyauta ne ni karan kaina bazan Amince ba Amma in bashine saina karba ke kuma saiki tara kudin ki wata rana zai mini Amfani.

"Yanzun ka zabi karban nasa akan nawa kenan"?

Ni bance ba Amma dai gwara nasan akan bashin tsakanin mata da mijin nan bana sha'awarsa sai in ya zama dole

"toh ce maka akai bashi nace ne"?

Koma dai yayane kiyi hakuri bazan iyya karba ba

Sumayya juyawa kawai tayi ta kwanta bata kara magana ba a hankali yasa hannu ya d'agota kwantar da ita yayi a jikinsa cikin sanyi yake mata magana, don Allah badon niba sumayya ki daina Ashar koh don yaranda zamu haife su tashi da kalami mai kyau a baki banji dadin abinda ya faru ba koh kad'an yau ace anzo an d'auki matata a motar yan sanda wannan ba mutuncin matar aure bane sai in ya zamo mata dole

" insha Allah bazan sake ba"ta karasa maganar da kara kwanciya a jikinsa

Allah yasa...

"Ameen" shuru sukayi dukansu biyu ba wanda ya kara magana a hankali Al'ameen yasa hannu ya yaye hijab da sumayya tasa don yau sanyi ake sosai

"Sanyi fa nake ji"

Nima ai sanyin nakeji kinga nasa abune?

"Ai kai daban ni daban"

Nida ban, inji wa?

"Sumayya"

Uhmm muyi bacci

"Banaji"

Saboda?

"Sanyi "

Uhmm toh bara na rufeki sai kibar jin sanyin, yana maganar yana hawa kanta

Saboda sabo da hakam yasa bai dame sumayya ba baccin ta kawai ta kamayi bata san ma yaushe yayi nasa ba


Washe gari Ammar yazo Akan maganar su Al'ameen ya Amince, Tare da tambayar Ammar kyautane koh bashi kai tsaye Ammar yace bashine don ya fahimci muhammand kalansa daban ne mutum ne wanda baison banza damuwar sa kawai ya nemi na kansa

Cikin sati d'aya Ammar ya sama ma muhammad shago mai kyau ta tsallaken first bank kaya ya cika masa makil a shago kama daga mazar kwaila dabino kayan marmari ba wanda babu su dangin Apply duk ba'a barsu a baya ba,yaune Aka kammala had'a shagon kai masha Allah shago kam saidai makiya suji haushi


Muhammad Anya zaka iyya kasuwancin nan babu yaro a kusa dakai kaga yanzun shagon nan babba ne idanun barayi zai sauka akai bare an ganka baka da ido za'a iyya baka d'ari ace dubune, Amma in kana da yaron daka Aminta dashi mai hankali a Unguwan naku sai yazo ku zauna tare kana d'an basa nasa ladan sai inga kamar zaifi?

Gaskiya ne Ammar daman Akwai wani yaro shagari d'an wani makwancin mune daya rasu toh yaron ba boko ba Arabic tunda iyayen sa suka mutu dai abin sai a hankali ba kula dashi ake ba saina d'auko sa yazo mu zauna tare

Amma muhammad yaro irin wannan da ba boko ba arabic bazai cutar dakai ba kasan fa halin yaran yanzun?

Ba kome insha Allah bokon ma iyya secondary ya tsaya arabic in tunda iyayen sa suka rasu ya daina zuwa saboda rashin mafad'i Amma najashi a jiki kaga inda rabo sai kaga Allah ya dad'a nitsar dashi

Haka ne kam sai kaje wajen bappan nasa kuyi magana saika d'auki yaron

Insha Allah Ammar nagode Allah ya tsaka maka da Alkhari ya bani ikon biyan abinda ka bani

Ameen, ni bara na wuce Allah ya kawo kasuwa

Ameen, Al'ameen yace yana rufe shagon gida ya nnfa fuskar nan a washe

Bayan ya shigo gidan da sallama lokacin sumayya nama wasu lalle

Amsa masa tayi tana kallon sa ganin sai murmushi yake"yayan khadija lfy"?

Lafiya kun gama lallen ne ?

"Saura hannu d'aya meya faru"?

Babu kome ki gama dai sai muje ki gani

Toh sumayya tace da sauri sauri ta kammala musu don ta kagu taji menene" na gama muje"

Kiye wanka dai kisa kaya da hijab amma daga gama lalle sai fita

"Nidai gaskiya Ah Ah muje inna dawo zanyi"

Hannunta kawai ya kama har ban d'aki ya fitoh ruwa ya iba ya kai mata, kiyi wanka malama

Ba yanda sumayya ta iyya haka tayi wanka ta shirya ya saka ta agaba har shagon sa sosai sumayya tayi mamakin girman shagon da abubuwan da aka zuba masa gwanin sha'awa kai gaskiya "masha Allah waje yayi waje"

Gaskiya ne nima ina ji wajen ba karamin kyau zaiyi ba

"Ya mayi Amma dai ya kamata kane mi abokin zama saboda tsaro"

Eh munyi magana da Ammar, gidan su shagari zani koh xa'a amince ya tayani zaman shago

"Gaskiya ne hakan yayi kyau sosai wallahi Allah ya kawo kasuwa"

Ameen, muje ki rakani gidan su shagari

"Toh"sumayya tace tare suka tafi gidan su shagari kuma Alhamdulilah sun Amince

Cikin sati d'aya ba karamin mamaki yan sintali sukayi ba ganin muhammad da babban shago gashi bai fad'awa kowa kome ba inka tambaye sama sai yace Allah ne ya rufa masa Asiri yayi shuru , sosai yake cefene yanzun kome na gidan sa ya d'aukewa sumayya duk yanda taso hanata yake gashi Allah yasawa abin Albarka Arana d'aya yana cinikin dubu goma gashi Shagari ya kaisa wajen wani mai kayan marmari ya had'asu da dilan yan gembu yanzun masa ordern kaya ake daga gona sai dai kawai ya tura shagari tasha in kaya ya sauka a d'auko masa.

yanzun kam Alhamdulilah sumayya kudi na shigo mata wallahi kowa ya ganta zai zaci daki Ac falo Ac mota AC office Ac ne tsabar yanda ta dawo tayi kyau tayi fresh sosai har wani yellow yellow tayi yanzun koh tunanin gidan su batayi ita karan kanta tana mamakin yanda take mantawa akwai abie A duniya, wata rana har mamakin kanta take saitaji kamar ta kirasa sai kuma ta fasa

hatta shi muhammad yanzun in ka gansa zaka san kwanciyar hankali ya samu matsunguni.

ga suturu masu kyau yanzun shima da kudin sa yake sayan kaya ya saka duk ya watsar da tarkacen kayansa hatta khadija yanzun daban ta koma kamar ba khadija ba gata ba yaya ba, ba Aunty ba

Yaune aka ga watan Ramadan gobe za'a tashi da azumi sumayya yau da khadija kasuwa suka shiga sosai sumayya ta musu sayayyan azumi kome buhu buhu katon katon ga kaji ka kifi, vegetables daman bata da matsalan fruit
bayan sun dawo kasuwa kowa ka gani fuskar sa a washe Adalilin gobe azumi

Bayan isha muhammad ne da sumayya suke cin abinci a waje, zazaune suke akan taburma don yanzun sumayya ta saya

Assalamu Alaikum

"Wa'alaikumu salam"muhammad da sumayya suka Amsa " sannun ki da zuwa sumayya tace tana tashi, ta d'aukowa bakuwar kujera don a tunanin ta koh customer ne

Ah ah ba zama nazo ba magana zanyi dake

Ni kuma?sumayya ta maimaita

Eh ke dai, ina dai kice sumayya Abdulsalam shugaba?

Eh nice

Nazone na shaida miki koh na gargade ki Akan i................




08146017245 *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar*
*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*


*1 Gumbar kankana da ayu* 2 *Gumbar ayu zallah* 3 *Gumbar Madara da kwakwa* 4 *Kaza mekwai* 5 *Zabo me zuma* 6 *Kaza me allurai 7 *Kwallin idonka inadona* 8 *Tauwadar mata* 9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*
11 *Maganin nono. Sahihi*
12 *Maganin hips and bobbs*
13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*
14 *nakasan Mara babban sirri*
15 *kafi jijjibi*
16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*
18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*


*Maman haidar Bata tsaya anan ba*
*takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeta awannan number* 08146017245

>???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~


('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=?L?
free book >?'?

Page5? 4? &5? 5?
Akan ibada don naga d'an changen rayuwa da kuka samu haryasa kuna sanyi da ibadan koh, toh bari kuji irin wannan daman makiyan ku suke jira sumu ku mai gabaki d'aya in kukayi sake da ibadah toh tabbas zasuga bayan ku sarkin yawa yafi sarkin karfi, watan da muka shiga wata ne mai Albarka ni'ima da falala ku dukufa wajen neman tsari da kariya a wajen mahaliccin mu.

Sake baki sumayya tayi tana kallon matar da bata santa bama gashi dare ne ba nepa bare ta mata kallon sap"malama wani irin magana ne haka sannan suwaye makiyan mu"?

Baki bukatar ji nidai na fad'a miki tace tana fita a kofar

Sumayya kam kamar doluwa haka ta kuma sai bin hanyar da matar ta fita kawai take tana Al'ajabi"yayan khadija kaji wani magana kuwa"?

Uhmm sumayya maganar matan nan koh bamu gaskata ba, Amma tunda ibadah tace toh mu dage koh ba makiyi Addu'a makamin mumini ne

"Gaskiya ne" sumayya tace duk jikinta yayi sanyi sosai abincin ma kasa cigaba daci tayi

Al'ameen dake cin abinci tsayawa yayi jin sumayya shuru hannu yasa ya tabata sumayya yadai?

"Uhmm babu kome kawai dai ina mamaki ne"

Mamakin me kuma? inna matan nan ne ai ba abin mamaki bane don duniya da fad'i kika san menene Alakarta da su kedai mu rike ibadah hannu bibiyu insha Allah ba Abinda zamu gani sai Alkhari kici Abinci pls?

Toh tace tana cigaba dacin abincin"yayan khadija me zan dafa mana na sahur"?

Me kike so?

"Uhmm aikai na tambaya koh"?

Nima saina tambaye ki

"Toh ai mata ke tambayar miji abinda za'a dafa"

Au yanzun kam an yarda ni mijine kenan?

"Oho dai nikam ka fad'a mini abinda zan dafa so nake mu kwanta da wuri samun mu tashi da wuri"

Ki mana tuwon shinkafa miyan shuwaka

"Nama koh kifi"?

Duk wanda ya dace ki saka

"Ok" kawai tace tana tashi kitchen ta shiga ta barshi zaune akan taburma

Girki sumayya tayi sai kusan 10:30 ta kammala aikin girki juyewa tayi a kula takai d'aki tayi tatan kamu da khadija ta karbo mata a inji tana gamawa tattara taburman tayi, ta rufe kofar su zuwa lokacin Al'ameen yayi bacci tuntuni itama kwanciyar tayi bata tashesa ba don bacc???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i takeji itama

Misalin karfe 1:30am Al'ameen ya farka jin sumayya ajikinsa yasa sa tata bata, sumayya!! sumayya!!

"Menene"?

Ki tashi mana

"asuba yayi ne"?

Baiyi ba sallah zamuyi tashi maza kinji

"Uhum"tace tana mikewa sauka tayi akan gadon ta kamo hannunsa suka fitoh waje bayan ta kunna hasken wayan ta Alwala sukayi suka tada sallah

Sai karfe uku suka sallame sosai suka dukufa suna Addu'an neman tsari wajen mahallincin mu da neman gafaran sa

3:41 sumayya ta d'auko musu tuwon ta bude da zafin sa kamar yanzun akayi zuba musu tayi sukayi sahur basu koma bacci ba sai data cika ruwan randa a laida fari ta d'add'aure ta cika firij nata bayan asuba suka koma bacci

Dayake Cikin Ramadan ba'acika sayan kaya da safe ba sai yamma yasa Al'ameen yabiye wa sumayya suka cigaba da bacci basu suka tashi ba sai kusan 9 Al'ameen ya tafi masallaci tafsiri sumayya ma islamiyar unguwan taje wata babbar malama ke tafsir wa matan aure a ciki

sai bayan Azahar Al'ameen ya fita shago, sumayya kam sallah tayi ta shiga kitchen abinci ta dafa dankali ne da kwai ta soya sai ruwan tie ta musu macaroni da miya duk ta zuzzuba a kula ta zuba wasu goggo ma a manyan kula guda biyu, kiran yaro tayi ya kira mata khadija bayan ta dama kunu cikin bokatin penti fari babba, wanka ta shiga kafun ta fitoh saiga khadija ta shigo bayan sun gaisa ta bata boket in da cups na roba wanda ta saya jiya ta had'a mata takai masallaci sadaka sai ruwan da tasa da asuba a firij sunyi guda shima boket ta cika ta d'aurawa Almajiri yabi khadija

Rarra bawa khadija tayi a masallaci sosai jama'a ke sawa abin Albarka don koh masu kudin unguwan basa kawo kome a azumi sai talakawa ke kokarin ciyar da masu azumi (Allah ya kyauta)

Bayan khadija ta dawo da bokata yen, kulan abinci sumayya ta bata ta kaima goggo suyi bud'a baki

Al'ameen ne ya had'a kankana da dabino sai sweet milo, yasa a laida biyu ya rike a hannunsa barin shagari yayi a shago hade da basa kudi yasai abin bud'a baki shima

Gidan goggo ya wuce ya bata laida d'aya ya kamo hanyar gida

Tun akan hanya ake ta masa godiyan kunu da kankara sosai yayi mamaki wani kunu kuma amma baiyi magana ba amsa musu yayi ya shiga gida daidai lokacin aka kira sallan mangari ba

Assalamu Alaikum

"Wa'alaikumu salam"

Jin bakin sumayya cike da abinci ta amsa sallamar yasa sa da mamaki yace toh yau koh jira babu hajiya har an kai loma?

"Ai a azumin nan ba jira kaji in gaya maka ana kiran sallah sai ci yaushe zan jiraka kuma"

Uhmm yayi kyau yace yana zama akan dakalin da take, mika mata laidan yayi ganin yau koh karba batayi ba sai jin karan shukali kawai yake

Amsa tayi ta bude dabino ne guda biyar ta damka masa a hannu sai ruwan shayi a kofi

Karba yayi ya bude baki da addu'a bayan yaci dabinon ruwa ya kurba kawai yayi Alwala ya tafi masallaci

Sumayya kam sai da ciki ya d'auka kafun ta zakud'a itama sallar tayi bayan ya dawo masallaci shima yaci nasa Abincin sauran kayan marmari da ya rage ta saka a firij

Da misalin karfe 11 bayan ta gama aikace aikacen girkin asuba yake tambayar ta akan kankara da kunu

"Yanzun don zanyi aikin lada saina fad'a maka yayan khadija watan azumi ne fa"

Allah ya karbi ibadun mu

"Ameen, FATAN MU(next novel)kenan insha Allah"

Ta bangaren kamila Alhamdulilah jiki yayi sauki sosai harma an sallame ta sai dai fa fatar hannu kam ba kamar nada ba
Yau dai gidan kawarta ta nufa
Assalamu Alaikum
Wa'alaikumu salam wanake gani anan koh dai idanuna ne kemin gezo lallai kamila duniya ashe ana iyya tunawa damu

Ke matsalar ki kenan Harira daga mutum yazo gunki koh wajen zama baki bani ba kin kama mini korafi

Ai dole na miki kamila tun auren ki na sake saki a idanu na? koh wayarki na daina samu sai dai inji a gari kinzo kin koma yar buru uba har zaki ce ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login