Showing 48001 words to 51000 words out of 132190 words

Chapter 17 - Matar Makaho Compelet Book by Rukayya Ibrahim Lawal.doc

Yusuf ya Tashi matuka don har kwanciya yayi a gadon asibiti Akan zancen danginsa da Alhaji ya matsa Masa akai

Karshe dai fa ubangari yaga abin fa nayine yasa sa hakura da tambayar Yusuf shi yashiga maganar auren Yusuf

Da yake ubangari ya jima tare da Yusuf kowa gani yake kamar Yan uwane hakan yasa ba dogon zance aka basa auren Aisha don Suma sun Matsu tayi aure ganin ta girma a gida

Ta bangaren zainab Yar ubangari Kam in hankalin ta yayi dubu ya Tashi tayi kuka tayi kuka Kamar zatayi hauka Amma khairat ta taka Mata birki tare da Mata alkawarin sai Yusuf ya aureta amma tabare ayi auren taga matakin da zata d'aukar Mata

Bayan auren Yusuf sumul da Aishan ADARA, Alhaji yaki yarda Yusuf ya Kama gidan haya a gidansa sukaci gaba da zama, soyayya suke shimfid'a wa Mai tsafta sosai Aisha ta nutsu suna zaune da yaran ubangari da matansa lfy Sam bata nuna musu Yar Hali sai daifa basa shiri da zainab ganin kallon banza da take mata

Sai Bayan shikara uku da auren Aishan ADARA da Yusuf kafun Allah ya baiwa Aisha ciki sosai sukayi farinciki da wannan cikin da Allah ya azurtasu,sukaci gaba da rainon cikin cikin farin ciki

Bayan Aisha ta haihuwa sun samu d'a namiji Mai matukar Kama da mahaifinsa Kamar an tsaga Kara, mahaifinsa yasa Masa suna muhammad.
Mahaifiyarsa na kiransa Al'ameen.

Da sauri Sumayya ta d'aga ido tana kallon Al'ameen dake Bata lbr"kana nufin kace mini gidan n........"

Bai bare ta karasa ba ya girgiza Mata Kai Yana Kara kwantar ta ita a jikinsa,ki aje tambayoyin ki Inna Gama saiki tambaya

Kai kawai ta gyad'a Masa

Ya cigaba.....har lokacin zainab Bata saduda da soyayyar Yusuf ba don a lokacin ta kammala secondary school nata,Amma Taki aure Dole yasa babanta nema Mata wani makarantan gaba da secondary taci gaba

Bayan haihuwa Al'ameen da shikara uku Aisha ta Kara haihuwar wani da namiji yaci sunan Salim, tun daga lokacin Aisha Bata sake samun ciki ba,sukaci gaba da kula da yaransu don a lokacin Alhaji ya budewa Yusuf shago yabar aikace aikacen gida basuda wata matsala sai na d'ansu Salim Wanda ke fama da mummunan ciwon zuciya,duk bayan wata D'aya sai sunga likita Kuma sai anci kudi.

A hakan rayuwa tayita tafiya yau Dadi gobe akasinsa Al'ameen da Salim suna matukar samun kula daga iyayen su suna Isa shiga makaranta aka sakasu yarane da suka shagu da junansu matika Kamar wasu tagwaye Dayake Salim nada gaban girma tuni ya tsara da yayansa har lokacin Aisha Bata San cewa Yusuf ba Dan uwan Alhaji bane duk da tana yawan tambayan sa labarin Yan uwansa Amma Yusuf daga tayi tambar saiya hau hada Mata fuska

Bayan wasu shikaru lokacin Al'ameen nada shikara 11 Salim nada shikara 8 a duniya. Aisha na d'auke da karamin ciki.

wata ranan juma'a da zuriyan yusuf bazasu taba mantawa da ranan b a tsawon rayuwansu ba har Abada ciwon bazaibar zukatan su ba

Da misalin karfe bakwai na dare yusuf ya dawo gida,Yana kokarin shiga shashen su sai ga khairat taresa tayi cikin kuka Wai zainab ba lfy tana dakinta Alhaji yace yaje su kaita asibiti

Da gudu yusuf ya bi bayan kairan zuwa shashen Yan matan gidan,shiya fara Shiga d'akin Yana shiga khairat taja kofar ta rufe kofar ta waje da makulli.

Yusuf na shiga d'akin ya ware ido ganin zainab ba Kaya daga ita sai d'aurin kirji a zaune akan gado

Tambayar ta yusuf ya farayi, zainab menene haka Kuma ki nemi riga ki saka yace Yana Mai kokarin bude kofar

Dariya zainab ta sake hade da furta wallahih kaji na rantse maka Yusuf tunda ka hofantar da soyayya ta kasa kafa ka shureta Nima saina jazamaka bala'i inda zaisa ka aureni Dole wannan itace kad'ai abinda zanyi na mallakeka,ka 'dauka Koh shurun da nayi na hakurane?
Ah ah wallahih ban hakura ba tanadi nake maka.

Subhanallah shine abinda yusuf ya furta cikin gigita, zainab Ashe bakida hankali wani irin shirmene haka

Hauka zakace ba shirme ba tabasa amsa tana matsowa garesa hade da fizgo kwalar rigansa ta yaga sosai tana ihu

Sosai yusuf ya razana ya Shiga kokarin k'wace kansa


Khairat Kam tana rufe d'akin ta tsaya kamar minutes biyu kafun ta fara rafka salati a tsakar gidan wayyo jama'a wani zaima zainab fyade a d'akinta yanzun nazo shiga kawai naji kofa a rufe zainab nata kuka ku kawo d'auki

Da gudu Yan gidan harda Aisha da makwanta Dayake darene ga madalisa a kofar gidan suka ruga da gudu zuwa d'akin zainab da suke Jin kukanta na tashi har lokacin

Jin kofar a rufe yasa matasan samarin unguwan suka dauko katon itace suka bugawa kofar take kofar ta balle,cikin mamaki tsoro Al'ajabi suka zubawa d'akin ido ganin abinda ke faruwa kamar a mafarki y................










*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* =؃?


Contact them vie
>؀?08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense

>???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~


('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=?L?
free book >?'?

Ummu Muhammad Zainab mansur Surayya
Page4?? 0?? &4?? 1??
Yusuf ne kwance akan zainab suna dambe

Salati dumbin Alumman dake wajen suka sake,zainab Kam da sauri ta sake Yusuf ta matsa gefe tana kuka da rawan jiki

Yusuf Kam ya kasa magana sunkuyar da Kai kawai yayi don bazai iyya hada ido da ubangari ba

Yusuf Ashe Kai Maci Amana ne Yusuf Ashe Kai mugune Yusuf shiyasa tsawon shikarun nan kake zaune Dani da fuska biyu azzalumi maha'inci kawai wallahih nayi Dana sanin zama dakai, Allah ya isan mini tunda ka rasa Wanda zakabi sai Yar cikinka,yace hawaye na taruwan Masa a ido,matasan samarin nan basuye wata wata ba suka rufe Yusuf da duka duk yanda yaso musu bayani Basu basa dama ba

Aisha Kam ba karamin shock ta Shiga ba Daman Yusuf ba D'an uwan ubangari bane? shiyasa inta tambaye sa Ahlinsa sai yahau fushi Ashe baida gaskiya ne kwata kwata, Aisha Kam kuka take tana dana sanin Yusuf, ya zubar Mata da mutunci ya ha'ince ta

Matar ubangari waya ta d'auka ta Kira police lokacin Amma Yusuf jina jina Koh tsayuwa baya iyyayi,ga matan sa da yaransa duk suna kuka, A lokacin yaran basusan me uban yayi ba Amma tabbas sunsan ba lfy

Police na zuwa daker suka k'wace Yusuf ganin ana kokarin kisan kai, lokacin da police suka Kama Yusuf za'a fita dashi cikin tsananin azaba yake rokonsu su barshi yaga MATARSA zai Mata magana.

Ba musu domin tabbas su kansu police a lokacin sunji tausayin sa sosai da sosai,wani ne a cikinsu ya taimaka Masa suka nufi wajen da Aisha ke duke tana kuka

Yusuf na Isa dukawa yayi yasa gwuwarshi a kasa cikin galabaita ya fara magana, Aisha Koh kowa zai yarda akan abinda yafaru don Allah Aisha ke kad'ai ki yarda Dani, yardan ki kawai nafiso akaf fad'in duniyan nan bayan yardan Allah,don kece abokiyar rayuwa ta in kowa zai juyamin baya ke Kika rungumeni bani da kaito Aisha Ina neman Wannan alfarman. ya karasa maganar hawaye nabin fuskar sa

Aishan ADARA Kam yau Hali ya motsa jikinta har bare yake cikin kakkauran murya ta mike ,Yusuf Yusuf wallahih nayi Dana sanin haihuwa da Kai Yusuf, nayi Dana sanin auren ka Yusuf ka cuce kanka ka cuceni Yusuf bana bukatar ka a rayuwa ta ni daga yau mijina ya mutu.

Sosai Yusuf ya fashe da kuka maicin Rai Wai waye zai fahimce sane kowa bazai yarda dashi ba kawai don an gansa a d'akin yarinya Babu bincike sai kawai ad'au mataki, me yasa tunani bazaizo musu ba duba da cewa ya rasa inda zai nemi zainab sai a cikin gidansu?

Yunkurin magana yafara ais......,da saure Aisha ta d'aga Masa hannu Yusuf Koh Babu Kai zamu rayu da yarana Koh bakai Zan iyya rayuwa Koh ba Kai rayuwar zata Mana Dadi,Amma zaman ka acikin mu shine kuncinta ka tafi bana bukatarka a yanzun,tace tana Mai kokarin baren wajen.

Da sauri yusuf ya Kama hannun Aisha,bataye wata wata ba ta tsinka Masa Mari.
Da sauri Yusuf ya sake Mata hannu

Da sauri Al'ameen Yayi wajen babansa cikin kuka ya rungume sa,abbajo menene Kaye musu suke dukanka abbajo ga fuskarka duk jini,abbajo muje asibiti a maka treatment kaji abbajon mu ka bawa police hakuri karsu tafi dakai,kuka Yusuf ya sake hade da rungumar d'ansa Dayake Jinsa Kamar bugun numfashin sa, cikin su biyun yafi kaunar Muhammad sosai.

Karka damu muhammad Zan dawo kaji laifin da ba nawa bane aka d'aura mini Wanda duniya kaf ni ake gani da laifin ,Yusuf yace ma d'ansa Yana Mai d'aukar sarkan dake wuyansa fari Mai azabebben kyau da walkiya ya d'aurawa Al'ameen a wuya, Muhammad ka kula da mamanku da kaninka kaji in mamanku ta haifi mace kace asa Mata khadija Inna mijine asa masa Shitu,Yana fad'a Masa hakan police sukazo suka Tisa keyarsa zuwa cikin mota

Bayan an tafi da Yusuf, Alhaji ubangari da danginsa Koran Kare sukama Aisha da yaranta,sosai Aisha tayita kuka tana tattara kayanta zubawa tayi a ak'watin karfe ta d'aurawa Al'ameen da salim,suka Kama hanyar sintali.

Gari gabaki d'aya ya d'auka zancen Yusuf yayi kokarin mawa Yar ubangidansa fyade,bayan isar Aisha gidan ADARA zuwa lokacin labari yazo kunnensu Dayake unguwan da suke da sintali ba nisa

Bayan isar Aisha gida ta sake haduwa da wani tashin hankali shine mahaifinta yace sai ta mayarda yaran Yusuf gun danginsa kafun ta zauna musu a gida Dayake mahaifiyar ta tarasu tun kafun auren ta,yasa ba Wanda yayi yunkurin baiwa baban ta hakuri

Aishan ADARA ta shiga tashin hankali ba kad'an ba na rashin sanin asalin Yusuf abin yayi mugun daga Mata hankali,ta rasa Ina zatasa kanta taji Dadi,don da ta koma gidan ubangari tunda shine waliyin Yusuf ya fad'a Mata inda dangin Yusuf suke Amma rashin mutunci da aka Mata a gidan Koh kyaun gani Babu,karshe dai wani abokin Yusuf ne Wanda sukaye mutunci sosai ya taimaki Aisha bayan Jin labarin abinda ya faru tabbas shima ya shiga tashin hankali Amma Sam Bai yarda Yusuf ne zai aikata wannan abinba, d'auko Aisha yayi ya Basu d'aki a gidansa duk da MATARSA ta tsani zaman su Aisha Amma ba yanda zata iyya Aisha ta koma gidan abokin Yusuf da zama.

Wannan zaman gidan abokin Yusuf shine mafarin haduwar
Al'ameen da kamila

An Kai Yusuf kotu,Amma bashi da hujjan Kare kansa haka yanaji Yana gani,laifinda ba nasaba aka yanke Masa hukunci.


Bayan Shari'a abubuwa sun ma Aisha yawa na rashin mijinta don abinda zataci ma gagaransu yake Dole karatun su Al'ameen a private ya gagara ta ciresu ta maidasu Government school, sukaci gaba da zuwa,itakam wankau take Koh daka take sama musu abinda zasuci sosai Aisha take fama da rayuwa ga bakin cikin_ abinda Yusuf ya aikata,ba karamin bakin jini ya shafawa yaransa ba

Hankalin Aisha Bai Kara tashi ba Saida lokacin komawar Salim asibiti Amma Bata da Koh sisi haka ta d'aukesa sukaje asibitin Amma abin mamaki duk yanda suka Saba da zuwa ganin likita Amma yau kawai da basu da kudin magani haka suka dawo gida kayan sakawarta Aisha ta tattara da kayan dakinta take sayarwa a hakan ta ringa ma Salim jinya da kayyakinta don abokin Yusuf d'aki kawai ya Basu Amma abinci Kam sai dai ta nema musu,

Ta bangaren zainab Kam tayi Dana sani Dana saninda har abada bazata daina yinsu ba sai yanzun take ganin wautarta na biyewa khairat harta aikata wannan mumunan kazafi wa Yusuf gashi abin Bai tsaya iyya Yusuf ba ta raba ma'aurata ta raba uba da yaransa ganin Yusuf da take taji Dadi yanzun Babu shi gashi Koh samarinta ma yanzun duk sun gujeta a dalilin labarin da suka samu

Zainab rayuwa ta Mata zafi Koh baccin kirki Bata iyya wa taso sanar da iyayenta gaskiya Amma kairat ta kwabeta don hakan zai iyya zubar Mata da mutunci fiye Dana yanzun da take ciki.

Al'ameen da kamila yaran makwanta ne gidansu kamila.na kusa da gidan bala abokin Yusuf,

Kamila dalibar makaranta i private school ne Wanda ke kusa da goverments day da Yusuf ke ciki

Farkon haduwar kamila da Yusuf a hanyar makaranta zai tafi itama zata fita.

Tunda kamila.taga Al'ameen take yawan shige Masa har gidansu take zuwa tun Al'ameen baya kulata hardai ya fara kulata Aisha Karan kanta da farko bataso mu'amalar Al'ameen da kamila ba ganin Al'ameen lokacin shikara biyar ya bawa kamila Amma haka ta barsu ganin karatu Yusuf ke koya Mata kullum insun hadu

Bayan wata uku lokacin cikin Aisha ya Shiga wata bakwai,zuwa lokacin Aisha Bata da kome a dakinta sai taburma sai sarkan wuyan muhammad sai tsummo karansu saboda duk kudin sun Kare akan kudin maganin Salim ga rayuwa dai anata gargarawa


Yau ranan juma'a Al'ameen da Salim sun dawo makaranta bayan sun kara kamila gida don yanzun shakuwane Mai tsanani a tsakanin su wanda in kamila bataga Al'ameen ba zatazo gidansu haka shima, suna zaune dumamen safe da ya rage shine Aisha ta Basu itakam haka ta hakura saboda yau sun tashi bako sisi,zainab ce ta shigo gidan da sallama a bakinta

Aisha ta amsa Mata Dan Sam bata Jin haushin family ubangari don Koh itane abinda Yusuf ya aikata saita Masa fiye da haka

Kallon zainab take Wanda duk tabi ta rame kallo d'aya zaka Mata kasan Bata cikin hayyacinta,bayan sun gaisa zainab ta d'aga ido tana kallon Aisha Bata San ta Ina zata fara ba yau tayi Alkawarin zata Fad'i gaskiya Koh zata samu sassauci a rayuwan ta

Hawaye ne ya cika idanun zainab ta bude baki a Hankali tace,maman Muhammad akwai wani magana da zanfada Miki bansan ya Zaki d'auki maganar ba Amma na g'wammaci na karbi Koh wani hukunci akan Wanda nake ciki

Cikin mamaki Aisha kam ke kallon zainab a iyya zamansu da zainab Bata taba ganin ta Mata magana a mutunce ba Kamar yau,toh zainab Allah yasa naji alkhari

Gaskiyan abinda ya faru maman Al'ameen babu ruwan Yusuf aciki,tace tana kallon Aisha

Kamar ya bangane ba zainab?

Eh tabbas Kamar yanda nace , Yusuf Babu ruwansa a ciki nice da khairat Muka had'a kome a tunanin mu Koh in aka Kama Yusuf xai mini fyade babana zai tilastashi ya aure ni Amma ban taba tunanin abinda na aikata ba daidai bane Saida Naga yanda na wargaza muku farin cikin na dasa muku bakin ciki, wallahih maman Al'ameen nayi nadama,Dana biyewa khairat ban tashi nadama ba Saida naji jiya tana Hira da kawarta a waya suna mini dariya, na tsokancin danayi harna yarda da abinda ta gayamin Ashe itama son Yusuf take,ta karasa maganar hawaye ya zuba akan fuskarta

Aishan ADARA Kam daskarewa tayi a zaune itakam wace irin mace ce Mai mantuwa me yasa ta kasa yarda da Yusuf, namijin daya yarda zai rayu da ita Bai damu da tarbiyan gidansu ba Koh halinta ba ya aureta Koda Yusuf Zina yayi hukuncin da ta yanke Masa yayi tsauri,wani irin murdawa mararta yayi na tashin hankali atake jini ya balle Mata durkusawa Aisha tayi tana Kiran sunan Allah.

Da gudu matar Bala dake tsaye tun d'azun tanajin bayanin da zainab keye tazo da gudu,tana kwalawa mijinta Kira da gudu ya fitoh su uku suka ciccibi Aisha zuwa asibiti

Al'ameen Kam Kama hannun Salim yayi suka Kama hanyar gidan ADARA,suna Isa kakansu suka samu a kofar gida suka fad'a Masa mamarsu ba lfy an kaita asibiti, hankali baban Aisha ya Tashi matuka don shi Karan kamshi korinda Yama Aisha na haushin yaran Yusuf ne, Amma Yana son yarsa tura su Salim yayi gidan Amina (Goggo) shi Kuma ya wuce gidan Bala agun ya samu wa'inda ke zaune aka fita da Aisha, aka Masa kwatancen asibitin da aka Kai Aisha

Bayan zuwansa ne yaji labarin abinda ya haddasa ma Aisha nakudar Dole abakin Matar Bala,shima sosai ransa ya baci duk da Bai gamu da zainab a asibitin ba Amma ransa ya matukar baci gida ya koma ya sanar da yaransa da yaran Yan uwansa akan suje su fara d'aukar mataki akan zainab kafun hukuma ta shiga

Ayarin gidan ADARA daga Yan Mata har zaurawa da samari sukaye Ayari guda suka fasa unguwa da kafa suka taka har gidan ubangari.

Zainab Kam gabaki d'aya ta rasa nutsuwarta Koh zama takasa waje Daya, tunda ta gudo daga hospital karshe dai Saida mamarta ta tambaye ta Koh meke damunta haka? tunda abinnan ya faru ta fahimci walwalar zainab ya d'auke, zainab Kam kin fad'a Mata gaskiya tayi

Suna zaune dukansu a gida dayake yau Friday ne ubangari ya dawo aiki da wure haka Yan makaranta,ji kawai sukaye an bankado get in gidan an shigo ciki kafun ma su gama tantance suwaye ne har kanwar Aisha ta nufi d'akin zainab jawota sukaye har kofar gidan da gudu su ubangari suka Mara musu baya.

Rufeta da duka ADARA sukaye, saiga khairat tafitob gida makwantan su, Aiko kamota sukayi suka Had'asu suna jibga duk yanda Yan unguwa da ubangari suke kokarin k'wace zainab da khairat abin ya gagara ganin zasuye kisan kai don zainab ta Suma Amma haka Ayarin gidan Adara Basu daina jibgarta ba Saida ta farfado da duka

Police aka Kira lokacin unguwan ya cika makil day'an kallo, abinka da Friday kowa na gida,

bayan zuwan police kafun aka samu aka k'wace su zainab anso Kama Yan ADARA Amma Ina abin ya gagara don fad'ane ya kusa zama na police da Yan gidan Adara,ganin jaraba irin na Yan gidan yasa polisawan tambayar musabbabin fad'an don dai sunyi sunyi su bisu station aye kome agun Amma sunki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login