Showing 63001 words to 66000 words out of 132190 words

Chapter 22 - Matar Makaho Compelet Book by Rukayya Ibrahim Lawal.doc

tare dama police in kallon banza, babu inda zani wallahi akan me banyi kome ba Awani ce za'a tafi dani


Babu wanda zai tafimin da mata ba tare da sanin laifinta ba, Al'ameen da yafitoh d'aki da sauri yake fad'a musu haka

Kai ka iyye bakinka fa kasan a gabansu wa kake babu ruwan mu da makantar ka wallahi koya maka hankali zamuyi.

Sannu uwar sa koya masa hankali na rantse kika tabamin miji ubanki za'a taba, station ne dai baza......

Bata karasa ba taji saukar mare tasss a fuska police in ta tsinketa dashi ai kafun ta sauke hannunta Al'ameen ya watsa mata rabonta itama duk da ba'a fuska ya saita ba amma ta maru kam

Kutturu hukuma ka mara yau daga kai har matar taka sai munga gatan ku a jala yau innan, waya tayi wasu mazan yan sanda biyu suka shigo aka rufuwa Al'ameen da sumayya da karfin cin tuwo za'ayi waje dasu Al'ameen kam anfa kasa tafiya dashi sai kokuwa suke, yau sunga ikon Allah kama MAKAHO ya gagare su sumayya kam an fita da ita waje bayan ta sanya hijab

Ammar ne yayi packing mota da sauri ganin yanda jama'a suka cika kofar gidan ga sumayya an tisata a gaba cikin sassarfa ya karaso wajen yana tambayar ba'asi ganinsa da daula yasa police in saura ransa suka masa bayanin sunzo kama sumayya ne Al'ameen ya mari police

Cikin gidan Ammar ya shiga da mamaki yake kallon Al'ameen dake ta fama da police da sauri ya karaso wajen hannun Al'ameen ya kama ya rike hade da kiran sunan sa

Tsayawa da kokuwar yayi, Ammar kaine?

Eh wai meke faruwa ne, meka musu?

Wallahi ba musan me muka musu ba daga zuwa wai zasu tafi da sumayya na tambayi dalili wai sai munje office insu kajifa.

Gaskiya ne Al'ameen ba'a fad'awa mutum laifinsa sai a station kazo muje ba abinda zai faru mundin kaine da gaskiya

Binsa Al'ameeen yayi police kam sai hararan Al'ameen suke da kitsima irin dukan da zaisha a hannunsu in ya shiga cell

Alfarma Ammar ya nema a barsu sumayya su shiga motar sa inyaso sai police shigo ciki

Bayan an isa station kenan officer ya had'asu da iyayen kamila a office insa sannan ya kalli sumayya, an kawo mana karanki kinyi kokarin zubawa wata Acid a fuska Allah ya kiyaye ta, ya zube a hannu bayan haka baki barta ba kika mata duka yanzun haka tana kwance a police clinic don haka zamu rikeki anan don iyyayenta zasu kai kara kotu

Amma dai yallaboi kafun a kamata ai sai an tambaye ita sumayyar ba'asi itama aji tata jawabin sannan kamila ta kawo shaida ku kuma saiku kamata ku rufe, Amma daga fad'a muku magana kuma sai ku rufe mutun ba bincike haka ake Hukunci?Ammar ne ke maganar yana nuna officer in

Toh kai kuma malam asuwa har zaka nuna mini abinda ya dace nayi koh kafini sanin doka ne?

Ban fika sani ba haka zalika bazan barka ka rufe baiwar Allah ba dalili ba akan me?

Kai malam dakata kasan a gaban wa kake kuwa? d'aya daga cikin police in yake Tambaya Ammar

Koma waye ne shi, nadai gama magana sumayya fad'a musu menene Ainahin abinda ya faru

Sumayya ba tsoro ta bayyana gaskiyar hakika nin abinda ya wanzu tsakaninsu da kamila

Kuna daiji koh asalima kamilar ce bata da gaskiya koh a hukunce wanda yazo ya sameka har cikin gidan ka kuma yajaka da fad'a kome akai masa shiya kai kansa, sannan a maganar nan ba ruwan sumayya haka zalika Al'ameen bada niya ya zubar da acid in a jikinta ba haka zalika itace take kokarin cutar masa da mata kunga kenan duka wannan abinda ya faru ba ruwan sumayya da Al'ameen duka, kuma jama'ar gidan ne suka mata basu ba ya karasa jawabin yana bin officer in da kallo


Kaima ai yanzun gashi ka yanke hukunci ba tare da bincike ba menene hujjar ka? nace wa kamila ce taje da acid in, baban kamila ya tambayi Ammar

Ku tura d'aya daga cikin yaran ku officer aje a d'auko goran acid in Allah dai yasa sumayya baki taba bako?

"Eh yana nan ata gefen kitchen a kasa"

Ok aje a d'auko saiku saka a gwada yatsun hannun wanda aka gani a kai wannnan ma ai hujjane koh?

Wai kai a matsayinka nawaye har zakana bamu order kai waye?

Hannu Ammar yasa a Aljuhu ya zaro ID card nasa ya nuna

Ai da sauri duka police inda ke wajen suka kame tare da sara masa

A gaskiya station nan yana bukatar gyara tunda bakusan aikin kuba A matsayin ku na hukuma masu kare hakkin wa'inda aka zalunta shine zaku zamo masu tauye masu rauni ku aje hujja akan masu kudi, Ammar ya karasa maganar da tsantsan bacin rai

Don Allah sir kayi Hakuri wallahi kuskure aka samu Shiyasa kuma duba da irin rauni dake jikin ita yarinyar da aka ma dukan shiyasa muka d'auki matakin gaggawa officern ke magana cikin magiya

Mtwss Ammar yaja tsaki hade da rufesu da fad'a sosai, muje koh muhammad, yace yana kamo hannun Al'ameen

"Ina da magana yallaboi"

Wace magana kuma sumayya bayan an kashe case, Al'ameen ya karasa maganar da kamo hannun sumayya su tafi


Ah ah Al'ameen ka barta muji meke tafe da ita.

Ah ah Ammar mu tafi kawai yafi

Sumayya yi maganar ki, Ammar yace bai saurare Al'ameen ba

"Yauwa so nake Amana iyyaka da kamila Amata iyyaka da mijina Arubuta a ajiye don ban yarda da ita ba wanda yayi niyar zubama acid wata rana zai dabama wuka"

Keee ki iyye bakin ki yar tamu yar daba'ce? da zata daba miki wuka wallahi karki kuskura ki kara jefin yarmu da mummunan kazafi,

Kallon d'an sandar Ammar yayi

Da sauri yace an gama sir, ku kuma daga yau ku jama yarku kunne karta kuskura muji koh mu gani tsakanin ta da sumayya koh muhammad

Suna Fita a station in motar sa suka hau sumayya a baya Muhammad a gaba da Ammar

Don Allah kuyi hakuri da abinda ya faru sannan ke sumayya gaskiya banji dadin abinda ya faru ba yara irinsu kamila da basusan kwaba babu Alkhari rigima dasu .

"Gaskiya ne Ammar ni karan kaina danasan wannan fad'ar zata kai ga haka daban fara ma tanka kamila ba"

Allah ya kiyaye na gaba

"Ameen"

Al'ameen kam kala baice ba shuru ya musu fuskar nan a hade don yau sumayya ta kular dashi tunda yake police basu taba kamasa ba yau ta janyo har station ya shiga=?? kad'an ya rage bai shiga cell ba

Suna isa kofar gidan Ammar yayi packing sumayya ce ta sauka tayi cikin gida abinta

Ammar kam maida kallonsa yayi akan Al'ameen dake kokarin sauka a motar, abokina kayi hakuri don Allah kasan halin mata kuma duk da bansan ainahin abinda yake tsakanin ku da kamila ba na fahimci kishine kawai ke damun sumayya, kuma koh wace mace iyya abinda zata kwatanta kenan

Ba kome Ammar amma wallahi naji haushi sosai yau innan gashi sumayya harda Ashar

Hakuri zakayi sai kuma ka mata fad'a a siyasa karkace zaka d'aga jijiyoyin wuya, mata sha'aninsu sai su

Ba kome Ammar nagode da taimakon ka gareni ashe kai police ne?

Eh muhammad

Amma babba koh naga suna baka girma

Eh, wani aiki kake ne muhammad? kullum nazo a gida nake samun ka badai bara kake bako irin yanda wasu keyi?

Ah ah ammar ina sana'a bana bara

Sana'ar me?

Mongoro, abakin titi

Amma meyasa kullum bana ganin ka a wajen sana'ar, inna zo?

Shuru Al'ameen yayi yanajin kamar ya fad'i gaskiya kamar karya fad'a, a hankali yace jarin nawane ya karye don mangoro yayi Araha yanzun ba ciniki shiyasa bana fita

Toh dame kake ciyar da iyalin kuma?

Had'a fuska Al'ameen yayi jin Ammar na masa tambaya kamar ya masa sata

Kayi hakuri muhammad ina ta tambayar ka Abinda bai maka dadi ba

Ah ah ba kome, daman ita ke kwalliya da lalle tana mana cefene da sauran abin bukata.

Gaskiya hakan bai dace ba Al'ameen ace kana namiji mace ke d'awainiya dakai ya kamata ka samu ka dogara da kanka, zan baka jari kamar na 300k sai ka kama shagon haya tunda azumi yazo kaga zama afi ciniki kayan narmari cikin azumi ga kankana ga lemo ga sweet milo harda dabino saika had'a, kana saidawa kaga saika kula da matar ka, ita kuma kudin da take samu saita kashewa kanta da kanwar taka hakan zaifi maka mutunci a wajen mace koh bata maka gori ba, koh bata nuna wani abinba Amma dai inka kasance kaike ciyar da ita kimarka daban yake a idon ta

Ammar ni......

Da sauri Ammar ya tare numfashin sa kaje kayi shawara da matar taka yanzun dai bana son jin kome bayan kwana biyu xan dawo inji Amsar ka eh koh Ah ah kawai nake bukata.

Shikenan nagode, Al'ameen yace yana fita a motar

Ta bangaren kamila kam da bacin rai iyayen ta suka shigo cikin clinic in tana kwance akan gado inda kasan wance tayi Accident haka ta koma gwanin tausayi sai kawarta dake gefe a zaune

Amma dai ke kamila bakijin bari ba saida namiki tsakani da yaron nan ba shine tsabar rashin zuciya kika ibi kafa kika tafi gidansa harda zuwa watsama matar sa acid kamila?

Nifa mama wallahi bani bace itace ta d'auko zata watsa mini

Uban me ya kaiki gidan ta?

Koyan kwalliya naje

Kwalliyar ubanki?dabani na haifeki ba sai ki gayamin wannan zance na d'auka yarinyar da bata jiran kanta.

Habba Rabi da wanne zataji ne da ciwon da ke cinta koh da fad'anki? babanta ya fad'a

Fita mamar kamila tayi,
Kamila tambayar baban ta tayi ya aka kare a station

Bai boye mata kome ba ya fad'a mata, tare da fita a d'akin

Kamila tun farko saida na fad'a miki karki fara abinda bazaki iyya ba matar Al'ameen ba wawuya bace kamar yanda kike zatoh mace mai shikara 26 koh 25 kema kinsan bazaki nuna mata tawaye ba shiyasa nace kibi abin ta bayan gida.

Wani banzan kallo kamila tama kawar ta, kinsan Allah sadika sai sumayya tayi dana sanin sanin muhammad saina dasa mata bakin cikin da yafi wanda nake ciki, muhammad kuma nawa ne tunda nayi aure nasan dadin abin kinga yanzun na gane ba kyau koh ido ne jin dadin aure ba keda kanki kinsan Al'ameen zaije duk inda ake so,
Don haka yanzun ma jira nake naji sauki mai gabaki d'aya zan musu.

Me kike nufi?

Uhmm ba sun mini iyyaka da su ba toh Malamai zan shi.............


08146017245 *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar*
*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*


*1 Gumbar kankana da ayu* 2 *Gumbar ayu zallah* 3 *Gumbar Madara da kwakwa* 4 *Kaza mekwai* 5 *Zabo me zuma* 6 *Kaza me allurai 7 *Kwallin idonka inadona* 8 *Tauwadar mata* 9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*
11 *Maganin nono. Sahihi*
12 *Maganin hips and bobbs*
13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*
14 *nakasan Mara babban sirri*
15 *kafi jijjibi*
16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*
18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*


*Maman haidar Bata tsaya anan ba*
*takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeta awannan number* 08146017245

>???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~


('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=?L?
free book >?'?

Page5? 2? &5? 3?
Malamai zan shiga, ke koh yawo tsirara zanyi don naga bayan sumayya sai nayi

Amma dai kamila baki da imani habba don Allah kin wulakanta bawan Allah ya fita a Rayuwan ki sannan yanzun kice zaki wargaxa masa farin ciki ai wannan baso bane

Wace farin cikin bayan nice farin cikin sa har gobe ina da gurbi a zuciyar sa

Hhh hayya lallai kamila kina da gurbi a zuciyarsa ya hankad'aki akan matar sa koh an gaya miki so na dauwa mane a zuciya? duk mai sonka muddin baka kyautata masa toh fa kamar fure ka shuka baka ban ruwa tum tana bushewa aje aje wata rana zata mutu

Kee sadika na fahimci daman ke yar hassada ce shiyasa kwata kwata tafiyyar mu bata kyau dake

Nidai gaskiya nake fad'a miki kamila kuma gaskiya d'aya ce da wannan haukar ai gwara kije garesa da soyayya koh xai dawo ku daidai ta kinga sai ayi na biyu dake

Ina ma yake fita kullun yana gida, naje inda akace min yana bude sana'a ma naje Amma shuru bantaba ganin sa ba, kuma ni nafi karfin kishi da sumayya sai dai ta fita tabar min shi

iii in kamila karkije kikai kanki a mahallaka wallahi wani rabon kashe ki zaiyi

Ya kashe ni mana indai akan Al'ameen ne kowa ma ya mutu

Wallahi badai kowa ba, nidai mai sonki ce zan fad'a miki gaskiya koh kinki koh kinso rabuwa da bayin Allah nan shiyafi miki mutunci Akasinsa kuma bismillah zaki ga.


Bakin ki ya sari d'anyen kashi ba abinda zan gani sai Alkhari

Ai baki neme Alkharin ba mutumin da keson kashe Auren wasu shine zaiga Alkhari?tace tana
Mikewa tayi ba tare da tajira Amsar kamila ba tayi mata sallama ta fita a asibitin


Sumayya na shiga cikin gidan kofar su ta wuce da mamaki take kallon kadija dake zaune tana rusa kuka"ke khadija lfy"?

Da gudu ta tashi zuwa wajen sumayya rungume ta tayi tana kuka'Aunty ina yaya? ina dawowa daga makaramta ake ce mini wai an tafi dake da yaya,.

"Babu inda akaje damu khadija yayan ki na waje shine kika kama kuka koh uniform baki cire ba kika zauna haka"

Toh ni Aunty fisabililah yazanyi na cire uniform yayana da Aunty na na station

"Toh gani na dawo ki ibi ruwa kiyi wanka na baki kaya kisa dai dai yayan naki ya shigo"

Toh kawai tace tana d'aukar boket, wanka tayi sumayya ta bata kayanta ta saka abincin da suka girka na karyawa daba su ciba shi ta ibawa khadija

Khadija na cikin cin abinci sai gashi ya shigo da sallama

Amsa wa khadija tayi hade da gaidashi, yaya sannu da zuwa

Yauwa khadija ya makarantar

Lafiya yau subject 6 aka mana a rana d'aya Assignment biyu

Masha Allah ki gama ci sai muyi assignment in


Hhh yaya ka iyya ne?

Toh khadija ba nayi secondary ba koh azatan ki duk abinda na koya ya gudu ne?

Yi hakuri yayana

D'akin ya shiga sumayya kam daman tana kitchen

Bayan khadija taci abinci wanke uniform nata tayi ta shanya,school back nata ta d'auko ta bude Assingment ne aka busu na physics sai English, yaya na gama inzo muyi Assingment in?

Bara na fitoh khadija,

Toh yaya

Fitowa yayi suka zauna a dakali sumayya na kallon sa yana ma khadija bayanin assingment in yanda zata fahimta sannan yana fad'a mata Amsa tana rubutawa

Bayan sun kammala gida khadija ta tafi tabar uniform nata a shanye, mikewa yayi ya ibi ruwan wanka ya shiga yana fita yayi Alwala ya wuce masjid

Bayan fitarsa da ido sumayya ta bisa haka kawai yau taji tana jin shakkarsa sosai abinci ta juye a kula takai d'aki tayi sallah sanin baya dawowa sai bayan isha yasa tayin wanka d'akin ta shiga zani fille da T-shirt ta saka sai hulan bacci. TV ta kunna tana kallo gabaki d'aya yau ta rasa nutsuwar ta gabaki d'aya zuciyarta cike yake da tsoro

Bayan ya dawo sallah abinci ta gabatar masa baiyi magana ba kawai ya zauna ya fara ci

Itakam taji ba dadi koh fad'ane ya mata akan wannnan shariyan ba karamin damunta yake ba

Bayan sun kammala cin abincin wanke baki sukayi, Al'ameen kwanciya yayi a gadon yayi shuru baice mata kome ba

Sumayya dake kwance a gefensa hawaye ne ya cika a idanunta itakam ta shigesu da mutumin nan

Sunfi, minutes 30 a haka baice kome ba itama batayi magana ba Amma kowa yasan d'an uwansa baiyi bacci ba

A hankali sumayya ta matso garesa kwanciya tayi a gabansa sosai ta shige jikinsa

Al'ameen yana jinta kala baice mata na shuru kawai yayi don so yake ya mata horo ta ruwan sanyi yanda gobe baza tayi
Abinda bayaso ba.

Hannu tasa a hankali ta na cire botur in shirt insa nan ma baiyi magana ba

"Ni da wannan fushin ai gwara duka da wannan shariyan"

Kala baice mata ba sai kama hannunta dayayi wanda ke yawo a jikinsa

"Dan Allah ka kulani"

Kinsan Allah sumayya in baki rabu dani ba sai na sauka a gadon na koma kan kujera habba Ana dole ne?

"Kayi hakuri bazan kara bafa"

Sauka yayi niyar yi da sauri ta riko sa hade dasa ihu"wallahi nidai ban yarda ba kayi hakuri toh na tuba"

Fasa saukar yayi ya koma ya kwanta itama kwanciyar tayi a gabansa sosai ta mannu a jikinsa

Haka suka kwana tsakanin su babu shiri sumayya dai na makale da muhammad duk yanda yaso cireta a jikinsa taki

Washe gari haka suka tashi salam Al'ameen yasha mata mur sosai duk yanda tad'au abin da sauki abu fa ya wuce nan don da gaske muhammad yake

Bayan sun karya ta d'aga ido tana kallon sa"yayan khadija"

Na'am

"Daman maganar make-up inda zan ma yar kanwar Deputy ne saboda tsaro bazasu iyya zuwa ba shine wai naje na musu a gida har kwana biyar ana biki"

Saikin dawo kawai yace yana fita a d'akin

Sosai shariyan Al'ameen ya damu sumayya, haka dai ta lallaba ta shirya tad'au hijab nata ta saka rufe kofar tayi ta fita.

Bakin titi ta tsaya idonta ya sauka a kan Al'ameen ne zaune a bakin masallaci kusa da masu bara suna hira dasu, kara sowa tayi inda suke bakin ta d'auke da sallama, "Assalamu Alaikum"

Mutanen bakin masallacin gabaki d'aya suka zubawa sumayya ido suna mamakin ina zata, wa'alaikumu salam su Al'ameen suka had'a baki wajen Amsawa shikam cike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login