Showing 120001 words to 123000 words out of 132190 words

Chapter 41 - Matar Makaho Compelet Book by Rukayya Ibrahim Lawal.doc

Ammar yayi ai yana jim muryar Ammar da sauri ya rungume sa, cikin farin ciki suka hau hira har cikin gida muhammad ya shigar da Ammar suka gaisa da yan uwansa da mahaifinsa, sai a lokacin yake sanar dashi ai shagarine ya kirasa yake sanar sashi muhamamd ya dawo, yana gidan sarki kuma ya basa number Amma shuru Al'ameen bai kirasa ba shiyasa yabuga sammako yazo ya gansa.

Abinci aka kawowa Ammar, suna zaune a d'akin da aka sauke muhammad ana hira da labarun abubuwan da suka faru a baya harda Ramadan, kawai saijin muryar jama'a sukayi a sashen sarki, dayake window d'akin da aka sauke muhammad yana saitin sashen.

Mikewa sukayi gabaki d'ayansu suka zagaya zuwa falon sarki,family shugaba ne, suka gaishe dasu abie, aka daura zancen batan sumayya kowa na kawo shawaran sa, karshe dai akace za'a dage da rokon Allah da sadaka sannan za'a zuba jami'an tsaro a bincike su, kafun kowa ya watse, daman yan gidan su sumayya gaida yusuf sukazo da mahaifiyar sa tare da bada hakuri akan abinda ya faru kuma ba laifi sun nuna musu bakome, kome ya wuce Allah ya kiyaye na gaba.

Satin yan nijar biyu a taraba ba'aga sumayya ba, gashi kaf gidan su an duba hotonan ta duka ba'a gani ba, hatta dakin su muhammad ya koma yayi bincike sap baiga wani hoto ba, don sumayya ta tafi da hotunan su, gashi na wayar maimuna kanwar Ammar ma, wayar ta lalace harma ta saida ta, bare su samu ho?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 tunan su, da yake yanzun zamani ya sauya ba kamar daba, mutun ya bata a gari ma ba'a ganesa sai da rabo bare a kasa sukutum, dole tasa Yusuf komawa dasu ramadan aka bar mahmah da muhammad, kafun su tafi saida aka sai musu gida mai shegen kyau a Amazon suka koma ciki su uku harda goggo, kasancewar mijinta ya rasu bayan tafiyar sumayya hakan yasa muhammad d'aukar ta suka koma gidan su suna zaune tare da mahmah.

Wasa wasa saida muhamamd suka share wata biyu a jalingo Ana kan bincike har yanzun shuru ba'aji duriyar sumayya ba, koh khadija sosai abin ya dame muhammad koh abinci baya iyyaci sosai, ba irin tunanin da baiyi ba don shi gani yake saceta akayi tunda makiyansa suka iyya saka a kashesa, Amma ammar na yawan kwantar masa da hankali ba kad'an ba.

Ta bangaren safina dai tunda ta farfado a gadon asibiti ta makance bata gani kwata kwata haka magana ma bata iyyawa saboda bakinta daya koma gefe, fuska ya karkace ya murd'u ya wainu wanda likitoti sun tabbatar hawan jinine daya hau lokaci d'aya, daya bugar da ita ta fadin nan, shine ya kaushar mata da fuska, sai dai makantar ne basu gano sila ba, kuma kaf gidan babu wanda ya damu da lamuranta sai dada ita ke jinya amma hatta abie yaji ya tsaneta hakama y'an gidan wanda basu san dalili ba, dada ma daurewa take Amma ba kaunar safinan take ba yanzun.

Ammar ne zaune a falon gidan su shida kannen sa, abinci yake ci gabaki d'aya hankalin sa nakan TV, yayinda iyayen sa ke hiran batar sumayya da dawowar Al'ameen wanda Ammar ke kawo musu zancen, don iyayen sama sunje har gidan muhammad, suka masa jaje, kaninsa ne kawai baya falon.

Kwala masa kira yaji kaninsa yayi daga d'aki sai gasa ya fitoh da gudu hannunsa d'auke da waya yana zuwa baiyi magana ba, kawai ya mikawa Ammar wayan.

Kallon wayan yayi hotunane akayi posted nasu a instagram guda uku, Khadija ce sanye da uniform ita da wani bakin yaro wanda zaiyi sa'ar ta koh ya fita da kad'an shima da uniform in nurse suka d'auki hoto a unguwa mai kyau, sai na biyun tana sanye da uniform in islamilayya nan ma su biyu sai na ukun ita da yaron suna sanye da kayan hausa atamfa da shadda.

Jikin Ammar na rawa yake tambayar Abdul wanene yaron nan?

Aboki nane kalamu-wahid, school namu d'aya dashi a abuja naga yayi post kuma naga kamar khadija?

Ba kama bane Abdul itace, yanzun kasan inda yaron yake takamamme a Abuja?

Eh na sani yaya don inban manta ba kafun mu dawo hutu yayi ciwo danaje asibiti dubasa na samu an sallamo sa, so yamin kwatancen gidan su naje.

Waya kawai Ammar ya fitar a Aljuhunsa yana lalubar numban muhammad gabaki d'aya yabi ya gigice.

*******************
Kalamu yaji sauki har ya dawo da normal life nasa, a haka sukaci gaba da rayuwa abinsu cikin farin ciki duk da basa rasa kalubalen rayuwa.

Sumayya ciki ya shiga wata tara duk rashin tausayin mutun inya ganta sayya tausaya mata, cikine yayi kato matuka yayi tsayi ga nauyi don yanzun koh tafiya bata iyyawa sai dai rarrafe abin tausayi bata fita koh ina daga falo sai toilet khadija ke kome wani sa'in kalamu zaizo ya tattara wankin ta ya kai mata dana khadija, wani sa'in har girki yake zuwa ya taya khadija in ayyuka sun mata yawa, sumayya kam yanzun sai a hankali, koh riga bata iyya sawa sai wasu manya manyan vest na gwanjo da zani shine kayanta, sosai laila ke tausaya mata.

Yau laila da mijinta harda yaranta sunyi tafiya zuwa Adamawa wajen dangin mijinta, bayan isha'i kalamu yazo ya kawowa sumayya balankun nama, amma ta kasa ci saboda ciwon kanda ke damunta, suka sha hira da khadija suna cin nama, bai koma gida ba sai kusan 9 ya ma khadija sallama ya wuce, don zuwa lokacin sumayya ta dade da kwanciya.

Da misalin karfe 1 na dare sumayya ta farka jin wani irin matsetsen fitsari daya kamata, mikewa tayi zaune a hankali jin fitsari ya cika mata mara, gashi dare ne batason shiga hakkin khadija, yasa ta rarrafawa ta shiga bedroom da rarrafe har cikin bandaki, tsungunawa tayi, tayi fitsari ai tana gamawa taji bayan ta ya kama ga wani irin c................

('Ruqeenjalal('



>???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~


Page9? 4? &9? 5?
Bayan ta ya rike sosai ga wani irin ciwo da taji a maranta lokaci d'aya ta gigice tana salata tunda take bata taba jin ciwo irin na yau ba, Ambaton Allah kawai take a ranta gabaki d'aya ta had'a gumi, jin wani abu na zuba babu control ya sata tsorata ruwa ne yake dundula, salati ta sake hade da kwalawa khadija kira.

Khadija dake bacci kamar a mafarki taji muryar sumayya mikewa tayi ta nufi ban d'akin da sauri ta bude wazata gani? sumayya ce duke jikinta sai rawa yake gabaki d'aya ta had'a gumi a tsorace take tambayar ta haihuwa ne? sumayya bata samu Amsan bata ba, nuni kawai ta mata ta kira mata mota su tafi asibiti, ba musu khadija tad'au hijab tasa akan kayan baccin jikinta, ta ruga da gudu ta fita a falon, sakatan get in ta zare ta fita bakin kwalta, abinka da dare koh tsuntsu bata samu ba koh ina shuru, kuka ta sa da gudu ta dawo cikin gidan, kofar d'aya makwanciyar su ta wuce tana buga wa, amma basu bude ba gashi kaf gidan babu mai mota koh mijin laila ma ba motar bane dashi.

Haka da dawo sashen su, tana shiga zuwa lokacin jikin sumayya ya kara tsanani sosai koh zama ta kasa har lokacin tana tsungune.

Da sauri ta d'auki wayar ta layin kalamu ta kira, sai da ta masa kusan 4 miss call kafun ya d'aga cikin muryar bacci yake tambayar ta lafiya?

Ai tana sanar dashi da sauri ya mike ya zura jallabiyar sa ya fitoh a d'akin sa, harya tura kofar falon su zai fita saiga nannen sa ta fitoh daga dakin ta, tambayar sa tayi ina zaije a daren nan?

Sanar da ita yayi Auntin khadija ba lafiya tana labour, tambayar sa tayi mijin tafa,Amsa ya bata shidai bai taba ganin mijinta ba, yama ga alamu bata da miji, jin haka yasa nanne d'aukar hijab nata ta sanar da mijinta zasukai sumayya asibiti, suka fitoh tare dashi mota kalamu ya fitar suka shiga sai get insu sumayya, fita nanne dashi sukayi zuwa ciki.

Zuwa lokacin sumayya tayi laushi sosai koh gane wake kanta bazata iyya ba, dayake dare ne nanne da khadija ne suka ririketa yayinda kalamu ya diauki akwatin ta, data jima da shiryashi a zaune, rufe musu kofar yayi suka tafi asibitin da sumayya ke awo.

Suna zuwa aka karbesu nanne na zaune a waje ita da khadija, kalamu keta hidima na sayyan abubuwan da aka bukata koh zama bai samu, har 4 na asuba sumayya haihuwa ya gagara, gabaki d'aya karfin ta ya gama karewa sai da aka kira Assalatu kafun haihuwa yazo gadan gadan, cikin hukunci Allah sumayya ta haifi yaran ta guda biyu wanda koh sanin wani iri ta haifa bata sani ba, tsabar wahalar da tasha, tadai san ta haihu sau biyu, Alluran hutu aka mata bayan an kimtsata a take bacci ya d'auke ta.

******************
Bugu d'aya Al'ameen ya d'auka a take Ammar ke sanar dashi anga wajen da khadija take, suna Abuja.

Ai muhammad baisan lokacin da ya wantsalo daga kan kujeran falo, a take yayi sujjada akan tiles yana wa Allah kirari, goggo da mahmah dake zaune a kasan falo suna cin abinci da sauri suka mike suna tambayar sa lafiya?ai da sauri ya mike ya rungumi mahmah cikin farin ciki yake sanar da ita anga sumayya anga sumayya tana Abuja.

Ai sosai suka nuna farin cikin su goggo harda kuka, a take Muhammad ya fitar da waya ya kira abie ya sanar dashi akan yanzun nan zai tafi gidan su Ammar zasu wuce abuja.

Hanasa Abie yayi yace ya bari sai da safe sai subi fly zai sa a nema musu ticket sai su tafi tare da abie, ai a take goggo ma tace zata mahmah ma tace ita ma, dada dake kusa da abie tace itama baza'ayi ba ita ba, duk yanda abie da muhammad sukayi da tsofinnan su zauna a Taraba, su zasuje su dawo da sumayya amma kememen sukace kafar su kafar su abie, haka ba yanda abie ya iyya duka aka musu booking in fly tare da kiraye kirayen waya har nijar aka sanar dasu an samu wajen da suke, suma sun sanar dasu a cikin satin nan suna zuwa gabaki d'ayan su.

Washe gari tun sassafe suka bar Taraba muhammad koh bacci jiya kasawa yayi, dada ma haka ta watsar da safina tace sai taje taga jikallen ta, Ammar ma tasa Abdul yayi a gaba tare zasu ya nuna musu gidan su kalamu.

Karfe 9 su muhammad suka dira a Abuja, dayake yana da aboki, tun a taraba ya kirasa akan suna zuwa, tarba suka samu daga wajen abokin abie shiyazo ya d'aukesu a Airport, direct gidan su kalamu suka wuce, Amma abin haushi basu sami kowa ba wai Suna asibiti, haka mai ganin ya sanar dasu Alfarman ganin baban kalamu abie ya nema ba musu, mai gadi ya shiga ga sanar dashi, aiko sai gasa bayan sun gaisa ne sukace masa suna son sanin asibitin da kalamu sukaje in ba damuwa.

Ganin girman su da kudin su, gashi kamar ba lafiya ba, hakan yasa baban kalamu yace musu bara ya bisu asibitin, shiga mototi sukayi ya kira nanne ya tambaye ta asibitin da number room nasu, da mamaki yake tambayar ta koh lafiya jin muryar ta ya dishe-dishe alamu dai ba lafiya ba, koh tayi kuka, ya tambaye ta lafiya tace masa ba kome, kashe wayar yayi ya sanar dasu abie ga asibitin da suke.

Suna isa asibitin muhammad da gudu ya ruga bayan sanar dashi block inda suke koh kunyan su abie baiji ba da gudu yayi block in mutane sai kallonsa suke, da sauri sauri ya shiga d'akunan one by one yana dubasu, ana ukun ne ya shiga koh sallama babu ganin mace kwance akan gado ga yara sa'o'in juna zaune rike da jinjiraye a hannayen su, da sauri suma suka juyo jin mutun a d'akin babu sallama.

Ai da sauri khadija ta mike ta kwala ihu yaya!!!!!!!! Da sauri kalamu dake kusa da ita rike da d'ayar babyn da sauri ya cafke wance ke hannun khadija, don saura kad'an ta buga jinjira, da gudu khadija tayi wajen muhammad batayi wata wata ba ta rungumi d'an uwanta tana fashewa da kuka yaya, kaine koh mafarki nake?

Khadija nine nine khadija ina Aunty ki?

Allahu akbar yaya kalli nan tace tana nuna masa kan gadon da sumayya ke kwance har yanzun tana bacci.

Da sauri ya ware idanun sa yana kallon sumayya sai kuma ya juya ya kalli kalamu, ya sake kallon khadija?

Gyada masa kai tayi tana murmushi, shima murmushin yayi sai kuma ga hawaye, tare da matsawa kusa da gadon da sumayya take kwance, dukawa yayi akan gwuwar sa hannu yasa a hankali yana shafa fuskar sumayya, dake kwance sanye da kayan asibiti, tayi kyau tayi fresh irin na masujego, wannan ce sumayyar tawa ashe haka take da kyau masha Allah?

Itace yaya kaga wa'innan jarirai nakane.

Da sauri ya juya yana kallon kalamu da sauri ya mike tsaye hannu yasa ya Amshi babies in yana kallon su, yarane mata masu tsananin kama da junan su tamkar An raba kunu a kofi, gasu masu tsananin kama dashi kome nashine a fuskar yaran, gasu farare tass, rungumarsu yayi ya fashe da kuka.

Toh ragon maza baka da aiki sai kuka, mahmah da suka shigo cikin d'akin tun d'azun, amma basu ma san da su ba.

Da sauri ya nufi mahmah yana ce mata, mahmah kalli yaran nan, wai yarana ne kallesu fa ga sumayya mahmah kyakkyawa fa sosai?
.
Sunkuyar da kai abie yayi yana mamakin surkin nan nasa yau koh dai ya mantasa a wajen ne, shima da sauri ya nufi wajen da yarsa ke kwance, zama yayi a bakin gadon yana shafa gashin kanta daya hargitse koh ribon babu.

Mahmah ce ta karbi baby d'aya dada ma ta karbi d'aya goggo kam baki kawai ta sake tana bin kowa da ido, kalamu kallon babansa yayi dake gefe, ya gaidashi, amsawa yayi yana tambayar sa mai jiki.

Matsawa kusa da abie muhammad yayi ganin sumayya ta fara motse, a hankali ta bude idanunta dalilin kukan da yaranta suka sake dukan su biyu.

Tana bude idanunta bata sauke sa akan kowa ba sai muhamamd dake kanta a tsaye, kamar a mafarki haka ta kalli abin da sauri ta mike zaune har tana kokarin zamowa kasa, da sauri ya tarota, bi a hankali sumayya jikin ki ba kirfi.

Ai jin abinda yace da sauri ta riko hannunsa gam tana kwalama khadija kira, Amsawa khadija tayi da sauri ta karaso wajen"khadija yayanki ke mini gizau na kamasa "

Aunty ba gizau bane yayane

"Yaya kuma khadija mijina fa baya gani yau kuma naga wannan na gani"?

Aunty ya warke ne.

Ai sumayya najin haka ta sake dariya cikin farin ciki koh damuwa da jikinta batayi ba ta rungume mijinta, don ita sam hankalin ta vaikai wajen mutanen d'akin ba.

Mikewa abie yayi dasu mahmah zasu fita a dakin su basu waje don sukam kunya ne zai kashe su.

Nanne dake toilet tana wanke kayayyakin sumayya daya baci, tun d'azun take jin surutai a d'akin mikewa tayi tsaye da boket na kaya a hannunta ta bude kofar toilet ta fitoh, Wai khadija da kalamu anya kuna da hankali kuwa mara lafiya na bacci kuke surutai da wa......bata karasa ba tayi turus ganin jama'ar dake shirin fita a d'akin dasuka juyo suna kallonta.

Dada ce ta kama salati tana tafa hanneye, wanake ganin nan?

Abie ma da sauri yace Hafsa??

Nanne kam bata wani nuna reaction ba, dayake tun daren jiya data gane sumayya tasan tabbas zata ga su abie, duk da saurin da take tabar asibitin kafun suzo don ita batasan sumayya gudu tayi ba, haka ma batasan itace Aunty khadija ba sai daren jiya.

Nanne bata wani Amsa ba bare ma ta nuna tasan abie, sai tsayuwar da tayi tana kallon sumayya data sake muhamamd tana kallonta sosai irin kallon nan na kewa da soyayya, cikin kuka tace" ummi"?

Sai a wannan karo nanne tayi magana, Na'am momcy?

Da sauri sumayya ta sauka akan gadon tana takawa a hankali cikin dauriya tayi wajen mahaifiyarta fad'awa tayi jikinta tana kuka yau kam ta rasa ina zata sa kanta, murnan samun babies koh murnan ganin mahaifiyarta koh mijinta dole tayi kuka, ummi karan kanta hawaye ne ya cika a idanunta tana shafa kan sumayya ya isa haka momcy yi shuru kinga ba lafiya bane dake koma ki kwanta, tana maganar tana rike da hannun sumayya har ta kaita bakin gadon ta aje ta.

Waini yau hafsa nake gani ne koh gizau idanuna kemin koh mafarki nake ne?

Itace dada Abie yace yana dafe kansa cikin takaici da bakin cikin abubuwan da suka faru a baya.

Mijin hafsa ne yace, Hafsa kin sansu ne daman nina d'auka koh iyayen yarinyar nan ce?

Baban kalamu ne da kakarsa wannan kuma Addansa ce ta nuna sumayya.

Daga sumayya har kalamu da Abie a tare suka jefowa Hafsa tambaya lokaci guda, baban kalamu wani kalamun?

Da sauri abie yace hafsa ban gane ba wanene kalamu.

Nuna masa kalamu tayi dake tsaye cikin shock na abinda nanne tace, yanzun wai sumayya Addansa, ta yaya kamar ya?baigane ba?

"Ummi kina nufin kalamu d'an uwa nane"?

Hafsa kina nufin wannan yaro, yaro nane?

Kallon sumayya da abie hafsa tayi jin tambayar da suka jefo mata, eh kawai tace tana kama hanyar kofa zata fita tare da kallon mijin ta, yauwa Alan guburo mutafi naga dangin ta sunzo zasu zauna a gunta.

Ah ah hafsa zuwan mu bazaisa ki daina hidima da yarki ba.

Ah ah dada zan tafi , Allah ya sauwaka momcy.

"Ameeen ummi in zaki dawo a kawo mini sabulun wanka"

Toh momcy muje kalamu koh zaka zauna ne?

Ah ah nanne muje yace yana kallon abie da mamaki wai wannan ne babansa, shi abin ma yajisa wani banbara kwai.

Kokarin fita a dakin suke a hankali abie ya kama hannun kalamu daya wucesa zai fita a d'akin, kalamu bazaka ma abie magana bane?

Murmushi kalamu yayi sai kuma yaji hawaye ya taro masa, abie ashe kanason na maka magana, shine zaka kyamace ni ka kyautata rayuwar yar uwata, amma ka wofantar da nawa rayuwar ka barwa uwata ni, na zauna a matsayin agola a gidan da, bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login