Showing 60001 words to 63000 words out of 132190 words

Chapter 21 - Matar Makaho Compelet Book by Rukayya Ibrahim Lawal.doc

yayi dadi"tace tana fita a kitchen in

Baiyi magana ba kawai wuka ya d'auka yafara feran doyan

Ruwa sumayya ta iba tayi wanka kaya tasa ta kwanta duk da Al'ameen ya hanata amma baccin tuni ya sace ta

Al'ameen na tsaka da feran doya yaji salaman yaro, amsa masa yayi

Wai ana sallama da MAKAHO

Inji wa?

Nima ban sansa ba yace dai in masa sallama dakai

Ok kaje kace masa ina zuwa

Toh, yace yana fita a kofar

Tashi Al'ameen yayi ya wanke hannun sa ya shiga d'akin, sumayya!ya kira sunanta jin shuru bata amsa ba sai numfashin ta dake sauka akai akai, girgiza kai kawai yayi ya d'auki sabon riga da wando da sumayya ta sai masa ya saka ya cire 3quiter dake jikinsa, waje ya fita yana mamakin waye yazo gunsa yau haka


Waje ya fita yana tattaba jikin ginin kofar gidan don jin ina mai sallama dashin ya tsaya jin baiji motsen saba ya sakasa, kara maimaita sallamar

Wa'alaikumu salam Al'ameen

Laiiiiii wana kejin muryarsa kamar Ammar?

Baka mantani ba Al'ameen ka rike sunana baka manta ba.

Habba Ammar wanda ya maka hallaci irin wanda kamin ai ba mutumin da zaka manta dashi bane

Hakane Ya mai jikin?

Da sauki sosai Ammar, ya aiki ya gida?

Lafiya kasan yau kusan wata biyu da dawowa na ina zuwa unguwan nan ban gane kaba wallahi har Hospital in na koma sukace ai an mata tiyata ma har an sallame ku tuntuni

Eh kam satin mu d'aya aka sallame muma tuni.

Allah sarki yamai jikin toh?

Da sauki fa sosai kamar ma ba'a taba yanka taba, na barka a tsaye muje bakin dakali

Ok toh in ba damuwa naga dakalin da rana kazo mu shiga cikin mota mana?

Tsakake Al'ameen yayi yana nazari kutt anya zai yarda ya shiga motar mutun da bai sansa ba(lokacin da ya taimake ka ka sansa ne) Am daman ina d'an aikine a gida nama manta na d'aura tukunya

Murmushi Ammar yayi watoh har yanzun Al'ameen bai yarda dashi ba kenan, toh ba kome nima bara na wuce naga yamma tayi sai na sake zuwa

Toh shikenan nagode da ziyara Ammar

Toh aje a cigaba da aiki mijin hajiya hhhhh

Hhh Ammar kenan, ya fad'a yana mikama Ammar hannu sukayi musabaha a karo na biyu

Bayan tafiyar Ammar cikin gida Al'ameen ya wuce yana tunane tunane sai kuma yaji bai kyauta ba da Ammar nason cutar dashi da randa ya d'auke sa da sumayya ya cuce su, ta wani bangaren kuma sai yaji gwara masa hakan babu ruwansa da mutanen duniya sai mutunci yanzun bai yarda da kowa ba haka zalika tsoron shiga mota ne dashi tunda masu mota suka makantar dashi, kauda tunanin yayi ya cigaba da aikinsa, daya ya gama fere doyan ya zuba a roba wankewa yayi ya tsame a kwando ya zuba gishiri kunna hot plate in yayi ya kama Aiki.


Bayan kammala girkin Al'ameen juyewa yayi a kula ruwan shayi koma a flask wanka yayi yashiga d'akin, har lokacin sumayya bacci take, hawa yayi kan gadon a hankali ya kamota d'agata yayi cak yayi waje da ita ajeta yayi a kan dakali

Ido sumayya ta ware jinta a sama kafun ma ta gama nazartar inda take taji an ajeta a dakali"menene haka"?

Mangariba ake kira baccin ya isa haka, watoh bakiji bakisan baccin mangariba akwai matsala bako

"Baccin kwasheni yayi ai"

Sai kiyi Alwala nikam na tafi masallaci, bai saurare abinda zatace ba ya fita abinsa

Itama samayya Alwala tayi ta shiga d'aki...

Bayan sallan isha Al'ameen ne ya shigo kofar su, kitchen ya wuce ya d'auko kulan da
Sumayya dake kwance fuskarta sanye da glass ta d'aura system inta akan cikinta tana daddan nawa,d'ago kanta dake kan fillo tayi tana bin Al'ameen da kallo ganinsa d'auke da kula sosai tayi mamaki matuka, don ita harma ta manta da zancen zaiyi girki" ikon Allah wai da gaske kake kayi girki"?

Idanunki zai nuna miki, yana magana yana fita a d'akin bayan ya aje kulan hannun sa da plate da shukula, sai kuma gashi ya dawo dauke da flask da cups, ajewa yayi a hankali akan cafet ya zuzzuba doyan da kwai sai yaji a gefen plate ya tsiyaye tie a kofuna

Itakam sumayya sai ido kalala take kallonsa dashi"wai duk wannan kaika soya"?

Eh man bakin raina ni ba an gaya miki in mutum baida ido shikenan sai akace bazai iyya abinda masu ido keyi ba, ai harma yafi namasu ido muna iyyawa

"Ah ah kwadai kwatanta Amma badai yafi ba malam"

Au karya zan miki kenan?

"Bance ba,ina nawa doyan naga ka zuba plate d'aya"?

Eh namu ne yau tare zamuci a plate d'aya

Sumayya batayi magana ba sauka kawai tayi akan kujeran hannu kawai tasa ta fara cin doyan " kai maggi yayi yawa"

Kiji tsorin Allah fa sumayya

"Toh da tsoron ka zanji"

Amma dai k'wan nan babu maggin da yaji inba sharri ba

"Nikam naji, k'wan maggi ga Albasa doyan kuma bai soyu ba, tie in kuma sugar baiji ba"=??

Hannu yasa ya d'auke plate in gabanta da cup in tie in ya rike a hannunsa

"Yaya haka kuma"?

Ki miko mini kudi inje in sai miki abinci amma badai wannan zakici ba kowa ma ya hakura Almajiri zan kira na bawa, karasa maganar yayi yana shirin fita a d'akin

Da sauri sumayya ta biyosa hade da kamo rigansa"dan Allah yayan khadija ka aje abincin mana waikai bakasan wasa bane?wasa fa nake maka"

Wasa koh?toh ni da gaske nake kuma sakar min riga karki yaga

"Habba don Allah yaga riga sai kace wata mai farashunan mayu"

Toh waya sani

"Yasan me"?

Sakarmin riga hajiya

"Ayya ka bani abincin mana wallahi wasa nake doya yayi d'adi haka tie ma k'wai innan inda kasan dafin Turai"

Mika mata plate in yayi shima ya koma ya zauna abinci suka cigaba daci

Bayan sun kammala ci yaukam ita ta d'auki kwanuka, bayan ta kaisu waje brush tayi shikam Aswakin sa ya d'auka ya goge bakinsa d'akin suka koma kayan bacci sumayya ta saka rigane da wando cotton mai laushi da socks na sanyi a kafarta, jin an fara yayyafi yasa Al'ameen fita waje ya tattare musu ruwa
shima kayan baccin sa da sumayya ta sai masa ya yasa

Sumayya gado tahau iyafis ta d'auka ta jona da wayan ta ta manna a kunne tana kallon film a ciki

Shima bayan ya gama shiryawa d'akin ya rufe ya hau kan gadon, tattaba kan gadon yake har yaji ya tabota kwanciya yayi kusa da ita yasa hannu ya zame hular kanta

Hannu tasa ta cire kunne d'ayan ta makala masa a kunne

Kwanciya yayi akan filon da take gabaki d'aya ya nutsu yana sauraron abinda ke kunnensa, sai kuma yasa hannu ya taba sumayya hade da kiranta, sumayya!

"Na'am"

Uhmm Amma wannan indi'an film ne koh?

"Eh..ya akayi ka gane"?

Muryansu mana duk da Turanci suke magana amma dai sai kiji suna maganar sari koh bauta

"Gaskiya ne kasan sunan film in"?

Ah ah

"this is fate, watoh kaddarar Rayuwa na Arewa 24"

Oh film in karam koh?

"Eh shine ma ke magana yanzun"

Ai da sauri ya zare abin kunnesa tare da sa hannu ya zare na sumayya, kinsan Allah bazaki kalli film innan ba

"Ikon Allah akam me bazan kalla ba"?

Nidai kawai bazaki kalla bane.

"Toh me kakeso na gani"?

Wani film banda wannan

"Uhmm nikam gaskiya shi nakeson kallo" tace hade da karban abinta ta mayar kunne

Da sauri ya fizgo abin gabaki d'aya ya had'a da system in yana kokarin sauka akan gadon

Da sauri sumayya ta cakumosa baya hade da kokarin karban system in

Duk yanda taso kwatar abinta abin yaci tura duk inda tayi saiya zillar da hannunsa karshe ma hakura tayi takoma gefe tana maida numfashi

Tashi yayi jin ta kwanta, zuwa yayi ya aje system in akan kujera, ya dawo ya kwanta abinsa

Ganin ya aje yasa ta saurin mikewa zaune cikin azarbabi take kokarin sauka ta gefen kadon a hankali, tana sauka saboda matsen d'akin yasa dole saita biyo ta bangarensa kafun taje kan kujera, a hankali take tafiya

Shikam tun tashinta zaune da saukarta duk a kunnensa shuru kawai yayi yana son ganin gudun ruwanta

Tazo daidai dashi har zata gifta a bazata kawai taji ya fisgota baya ta fad'a kansa

Kokarin tashi take, ya sake maidata, wai sumayya meyasa ne bakijin bari sam

"Me nayi kuma"?

Yanzun ina zaki?

"Waje zan fita"

Me zakiyi a wajen?

"Fitsari mana koh an hana fitane in aka kulle kofa"

Jin amsar da ta basa ya saka hannu ya mannata da jikinsa sosai kamar zai maidata ciki

Karan shagwaba ta sake da karfi"wayyo"

Ke menene haka saikin tara mini jama'ane

"Toh ba kaine ka matseni ba"

Toh ai ke ince bakiji koh kad'an kannan naki taurine dashi fa

Eh naji kaina taurine dashi kuma ni ka sakeni fit.........

Bai bari ta karasa ba kawai ya manna bakinsa da nata sosai yake kissing inta yana dad'a matsota garesa kamar zai maidata ciki

A hankali tasa hannu ta kama kansa da karfi ta danke gashin kansa masu yawa sosai, hade da ajiyar zuciya

Washhh ashhh kawai Al'ameen yace bayan ya zame bakinsa a nata, hannu yasa ya kamo hannunta data rike masa gashi ya d'aura a kirjinsa, da sauri ya maida bakinsa cikin nata

Sosai yau sumayya da Al'ameen suka farantawa junansu duk da tafiya tayi nisa sumayya ta copsa Shi kuma Al'ameen tsoro.

*RANAN MONDAY*
Yaune fa hajiya khadin Goggo zata makaranta jiya koh baccin kirki bata iyya ba, da sassafe ta tashi tayi wanke wanke shara kafun 6:00 har tayi wanka dumamen da goggo ta duma shi taci, uniform nata tasa fari kal wando da hijab harda riga duka farare ne socks ta saka fari ta d'aura bakin d'an kwali(kallabi)ta zura hijab, sandal inta da Aunty ta tasai mata kala biyu d'aya =?_? ne d'aya sandal, =?_?in ta d'auka bakine shima don a dokar makarantar baki da fari suke so, tasa a kafarta sai agogo shima baki turare ta fisa fuskar nan washe kamar gonan Auduga takema goggo sallama hade da d'aukar school back nata shima baki mai kyau, ta fita a gidan

Sumayya da Al'ameen ne a kitchen suna girkin karyawa kamar kullum yauma hakan take watoh ana aiki ana fad'a

Assalamu Alaikum

"Wa'alaikumus sallam, yan makaranta"

Kai Aunty ina kwana?

"Lafiya khadija harkin shirya gaskiya ne Allah yasa hakan ya d'aure banda littin"

Ameen Aunty, ina kwana yaya?

Lafiya khadija harkin shirya?

Eh yaya na shirya

D'aki sumayya ta shiga naira 200 ta d'auko sai drinks d'aya da goran faro d'aya ta fitoh "ungo khadija wannan kudi yayanki ne ya bada na baki koda zaki zo ya fita ashe da rabon zaku hadu ma kihau keke sauran d'arin saiki rike a hannunki ga wannan kuma kisa a school back naki kinji, banda kawayen banza banda abota da maza kinga makaranta ne da Christian sukafi yawa sosai kuma benchi d'aya ake had'a maza da mata don haka babu ruwan ki da yaran Christian abinda ya kaiki shi zakiyi kinji ki maida hankalin ki akan abinda ya kaiki Allah ya tsare mana ke"

Hannu khadija tasa ta karbi kudin da drinks in hade dama sumayya godiya, yaya na tafi

Al'ameen kam ya rasa ma me zaice da sumayya sumayya Alkhari ce garesa matar rufin asiri, toh khadija saikin dawo kindaiji abinda Auntin ki tace miki koh?

Eh yaya..

Adawo lfy

Bayan fitar khadija sumayya kam kitchen ta koma taci gaba da aikin ta Al'ameen na tayata

Assalamu Alaikum

"Wa'alaikumu salam" sumayya ta amsa tana fita a cikin kitchen in da sauri jin muryar wance ke sallamar

Aiko itace da mamaki sumayya ta bita da kallo,
Al'ameen ma da sauri ya fitoh a kitchen in jin muryar me sallamar

"Lafiya" sumayya ta tambaye ta

Eh lafiya daman n................










*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* =؃?


Contact them vie
>؀?08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


>???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~


('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=?L?
free book >?'?

*HAPPY INDEPENDENT DAY*
Page5? 0? &5? 1?
Lafiya daman nazo akan maganar make-up inne, naji shuru baki kirani ba inna kira ba'a picking call in.

"Ok toh ai na zaci koh kina da fahimta ne, ki gane me nake nufi"

Kamar ya sumayya ban gane ba?

"Ok toh kamila bara na miki gwari gwari, bazan koyar ba"

Akan me? bayan kince sai mijinki ya yarda kuma a gabanki yace ya Amince.

"Eh ya amince nima haka yace mini sai dai ni ban Amince dake ba har kizo gidana kina kare mini tanadi"

Kamar ya bangane ba me kike nufi?zanzo gidan ki in kare miki tanadi?ina ma gidan yake bare

"Hhhhh hayyeeee nanayeeee ashe gidan ba yanda yake akazo cin moriyan masu shi"

Ke sumayya nafiki rashin mutunci don naga baki dashi ya daga abin Arziki sai tsiya ya biyo baya matsalanka da matsiyaci kenan bai gaji arziki ba


"Ehhhhhh yariya tsiyama waje ya samu ki kalleni da kyau daga ni har mijina kinga Alamun yunwa a tare damu, kuma ki kallen sama da kasa koh uwar ubanki bataci arzikin da naci ba harta mutu ke uwarki data aure ubanki har yanzun bataci arzikin danake ciba.

A'uzu sumayya wani rin , zagine haka kar in sake jin kin tanka mata shige ki wuce d'aki, don Allah kamila kiyi hakuri

Kutt ni kike xagi? ai kamila super tayi da jakarta tayo kan sumayya da mugun sauri

"Sumayya da gudu tayi kitchen tabarya ta rarumo ta rike"don uwarki kizo yau saina rusa miki kai shegeya harni zakima bariki kizo mini da yaudara da sunan koyan kwalliya"

Ai da sauri kamila taja birki, in ba tsoro ba ki aje abinda ke hannunki yau saina nuna miki true colour na.


"Shegeya akan me zan aje nasan dame kikazo kizo kima mijina asara a banza "

Shammatar sumayya kamila tayi tana magana, da sauri tayi kanta gadan gadan da kwalba a hannu

Ai ji kawai tayi Al'ameeen ya hankad'ata gefe, don duk abinda suke hankalinsa na kansu, keee kamila kin isa kizo har gida kice zaki bugarmin mata kimin asara akan me? Ke kin kini na samu mai zama dani shine zaki bugeta

Wayyyo nashiga uku na lalace wayyo hannu na innalilahih kun kasheni, kamila ke ihun nan tana rike da hannunta wanda Acid ya zube mata akai

"Subahanallah daman abinda kike da niyar watsa mini kenan Algunguma shegeya, aikokin watsa min bashine yake nufin karewar auren mu ba tunda ba idone dashi ba bare yaga yanda na koma"

Sumayya meke faruwa ne haka meya sami hannun nata naji kina cewa zata zuba miki

Kamila kam ihu take kamar ranta zai fita

Ihun kamila shiya jawo da hankalin jama'ar gidan kofar su Al'ameen, da sauri daga maza har mata yara da manya suka nufi kofar donjin ba'asi

"Ruwan Acid tayi niyar watsa mini Allah yasa ka shureta shine ya zube a hannunta hannun sai d'ayewa yake"

Subahanallah Al'ameen yace yana nufar inda kamila take, kee kamila tashi muje asibiti tashi tashi yau an bonu


Kaiii karka kuskura ka taba ta kaji ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na fad'a maka, keee Kinsan su waye a gidan nan har kika iyya d'aukar Acid zaki zo ki zubawa mutum a cikin gidan Adara? kutumar uba iro yace yana nufar kamila

Salame ce ta Lailayo Ashar ta maka, Ci ubanta dan uwarta(wa'iyyazu billah) koh dabban gidan Adara bama bari aci zalinsa bare mutum

Ai kafun Al'ameen yace wani abu tuni iro ya fara wanke fuskar kamila da ruwan maruka ji kawai kake kauuu kauuuu kauuuu


Ihun kamila ke tashi yanda kasan ranta zai fita bugunta suke tana kokarin gudu wasu su kamo ta, Al'ameen karan kansa hankalin sa ya tashi da kukan ta kamila keyi duk yanda yaso kwatarta abin yaci tura karshe ma salman turesa yayi saura kad'an ya fad'i sumayya ta taro sa

Jama'ar kofar gida su suka shigo gidan jin kukar mace kamar me, shigowa sukayi ganin abinda ke faruwa yasa su rugawa a guje suka kwace kamila

Ai kamila na ganin ta tsira da wani irin matsifeffen gudu ta falla waje kamar walkiya ga hannu duk ya d'aye fatar

Bayan gudun kamila suwaiba ce ta d'auki jakar kamilar, Kai Allah ya mini ga jaka mai azaban kyau maybe ma harda cash a ciki, takara sa maganar da fita a kofar


Bayan fitar jama'a a kofar Al'ameen rai a bace ya fara magana sumayya yanzun kin kyauta fisabilillahi daga abin arziki saiki kama zagin yarinya

"Ok watoh laifina kake gani kenan na zagi budurwan ka koh"?

Waike sumayya meye haka duk wacece ummulkaba'isin wannan matsifar tun farko me yasa zaki zageta akan wani dalili yanzun mutuncin kine ashar koh zamanki a gidan nan ne kika koya, ni fad'a nake miki a matsayina na mijinki ba saurayin kamila ba, yana karasa maganar yayi d'aki ya barta tsayi kamar an dasa ta

Sai yanzun sumayya tayi data sanin biyewa kamila koh yaushe kamila tazo gidan saita had'ata fad'a da mijin ta ina bazai yuba, kitchen in ta shiga taci gaba da ayyukan ta, don batason basa hakuri yanzun ganin ransa ya baci sosai


Da misalin karfe 11:20 saiga yan koyan make-up inta sunzo a waje suka zauna ta shinfid'a musu taburma suka fara training don yau kwanan su biyu da fara koyo


Jin d'uriyar jiniyar motar yan sanda sukaji ya tsaya a kofar gida, ba'a wani jima ba saiga matan yan sanda sun shigo gidan har kofar su sumayya

Sallama dai...

"Yauwa sannunku da zuwa lfy"?

Lafiya ba lau ba don duk wanda yagan mu baiga lfy ba, wacece sumayya?

"Ikon Allah nice wani abinne ya faru"?

In munje station zakiji dalili, shige muje d'ayar yar sandan tace tana kokarin kama hannun sumayya

Da sauri sumayya ta fizge hannunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login