Showing 54001 words to 57000 words out of 132190 words

Chapter 19 - Matar Makaho Compelet Book by Rukayya Ibrahim Lawal.doc

masallaci saboda rashin jagora, ya hadu da pol ji kake Gauu ya buga goshinsa jini ya balle Masa duk irin azabar da yaji hakan baisa ya kasa tashi ba haka ya mike a daddafe yayi randar masallaci dumbulo ruwa yayi Yana kuka Yana sauri ya karaso kusa da Salim tsungunawa yayi ya d'ago kansa jikinsa na rawa Jin Salim ya daina kakarin Amai gashi kansa yayi nauyi daker ya d'agasa ya d'aura akan cinyarsa lalubar bakin salim yayi ya kafa Masa mod'an Amma Ina ruwa baya tafiya sai bin Gefen bakin yake Yana zuba,dagajin haka Al'ameen ya k'wala Kara

Yayi daidai da lokacin mutumin ya fitoh da machine da sauri ya karaso gunsu Jin ihun Al'ameen

Yana zuwa cikin hanzari ya haska su idonsa ya sauka akan Salim kwance ido ya kafe a sama jiki a sake Wanda Koh ba'a fad'a ba yasan lokacin Salim ne yayi Innalilahih wainnailaihir rajuun kalmarda ta fitoh a bakinsa kenan

Aiko Wannan kalmar ita ta Kara tabbatar wa Al'ameen lallai ya rasa kaninsa, a karo na uku Yana rasa mutanen da sukafi soyowa a ransa, farin cikinsa,duka a gabansa suka Amsa Kiran mahalincin su(Allah Kasa mu cika da imani,muyi kyakkyawan karshe)

Ji kawai mutumin yayi Al'ameen ya Fad'i timmmmmm.............









*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* =؃?


Contact them vie
>؀?08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


>???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~


('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=?L?
free book >?'?

Page 4?? 4?? &4?? 5??
Al'ameen ne ya yanke jiki ya Fad'i,sosai mutumin ya rikice yahau salati cikin kidema

Hayaniyar sa shiya matashe samarin dake kwana a d'akunan kofar gida,Suma dai sosai mutuwar Salim ta shigesu ruwa aka watsawa Al'ameen Amma Ina Koh farfadowa baiyi ba Dole tasa wasu daga cikin matasan d'aukar sa zuwa asibiti

Usman makwancinsu shiya d'auki gawar Salim zuwa gidansa

Washe gari agidan malam Usman aka shirya salim.

Al'ameen dake asibiti kam Yana farfadowa da asuba ya tashi hankalin kowa sai ya dawo ankai Salim tare dashi

Haka aka kamasa g'wanin tausayi zuwa gidan malam usman,Yana shiga gida aka Kaisa Kan gawar D'an uwansa a hankali ya zauna Kan cafet in hannu yasa Yana lalube ya bude gawan jikinsa na bare yasa hannu ya shafa fuskar Dan uwansa murya na rawa hawaye nabin kuncinsa yake ma D'an uwansa Addu'a

Salim sosai ya samu jama'a kamar me don duk wanda yasansa, kuma yaji mutuwarsa yazo,tare da Al'ameen aka kai D'an uwansa kabari.

Bayan mutuwar Salim sosai kewa da kad'aici ke damun Al'ameen Koh bacci baya iyya wa saboda kewan D'an uwansa shikenan yanzun baida abokin Hira baida Wanda zai fad'awa damuwar sa baida Wanda zai kwana tare dashi sai Yar kanwarsa khadija ita Kuma mace ce

Mai gidan Salim shiya bawa Al'ameen kudi Ya sari mangoro Koh a bakin kofar gidane ya fara saidawa don Bai dace Yana tsallake titi kullum zuwa kasuwa zaman shago ba

Ba musu Al'ameen ya karbi kudin yad'an fara business dashi,Kuma Allah yasama abin Albarka Yana samun na abinci da biyawa Khadija D'an hidindimun makaranta


Zancen kamila Kam baiyi fushi ba duk da Bata Masa ta'aziyar D'an uwansa ba haka ya sake Kama Khadija don lokacin ta d'anye wayo sukaje gidansu kamila.

Kamila ce tsaye da kawayen ta a waje tare da wasu samari uku A bakin mota

Al'ameen suna Isa kofar gidansu kamila,yaji hayaniyar maganar mutane Kamar harda ta kamila hakan yasa cikin murna yau dai zasu gana, tunda ya jima Yana zuwa baya samun ganin ta

Da saurinsa yace wa Khadija suye wajen da Yake jin muryan mutane

Ba musu Khadija na rike da sandar sa suka nufi wajen, Assalamu alaikum

Waalaikumu salam D'aya daga cikin samarin ya Amsa Masa

Ina wunin ku, Al'ameen ya gaidasu

Lafiya samarin suka amsa d'ayan ya zare kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija,ungo Yan mata

Khadija Kam kin karba tayi don bata Saba bara ba koma yayanta ya hanata roko Koh karban abin hannun Wanda Bata sani ba

Karba Mana yarinya D'aya daga cikin kawayen kamila ta fad'a don Bata San Al'ameen ba

Yayana ya hanani karban kudin Wanda ban sani ba, Khadija ta fad'a musu tana noke kafad'a

Da mamaki samarin ke kallon su Al'ameen mutum ya fitoh bara abasa yace bazai karba ba,toh lfy meya kawo ku gun mu inba bara ba

Am don Allah Ina da tambaya ne? Al'ameen yace

Allah yasa mun sani

Yauwa Kamar muryan kamila nakeji d'azun a cikin ku?

Eh ganinan lfy?kamila ta basa Amsa

Lafiya kamila in ba damuwa inason magana dake ne

Ina jinka,tace tana Masa kallon banza

Don Allah mu koma gefe

Kai MAKAHO akan me zaku kebe da matar da Zan aura Kai asuwa d'aya daga cikin samarin yace

Wani abune ya cake zuciyar Al'ameen shikenan kamilar ma ya rasata shikam yaushe zai samu farin ciki ne duk mai kokarin faranta Masa wata Rana gudu yake ya barsa

Kamila aure zakiyi?yace Yana kokarin faduwa tsaban shock

Eh aure zanyi Koh kana da matsala da hakan ne

Kamila Ina Alkawarin mu?

Alkawari kana nufin na aure ka kana MAKAHO Kuma talaka da wanne zanji da ciyar dakai Koh da ciyar da yaranka Koh da maka jakora Koh d'awainiya?Zan dai iyya auren ka a Talaka Amma banda kana MAKAHO kam.

Sosai zuciyar Al'ameen ta tsinke

Dariya matasan da Y'an Matan suka sake na shekeyanci,Kai kamila bakida mutunci wallahi =?? soyayya ce fa saikuje kusha love da lalube D'aya daga cin Yan matan ta fad'a tana dariya

Budurwar da ke gefe sanye da hijab itace kad'ai Bata ma Al'ameen tozarci ba

Kama hannun Khadija taye hade tacewa Al'ameen su tafe

A hankali Al'ameen ke tafiya Kamar k'wai ya fashe Masa a ciki Bai d'auka Koh nakasa zaisa kamila gudunsa ba Koda kowa zai gujesa

Suna sharan kwanan nayin, kawar kamila ta dube Al'ameen,kaga bawan Allah don Allah Ina Mai rokon alfarma a gareka shine ka rabu da kamila Koda itace autar Mata ka barta duniyace ai Koda zata rabu dakai bada tuzarci Koh kushen halitta ba Amma ita Bata dube hakan ba y
Ta wulakanta ka kaima ka barta bari na har Abada,Kaye hakuri Allah Yana tare da musu hakure.

Insha Allah baiwar Allah na rabu da kamila Nima na hakura da ita Allah ya had'a kowa da rabonsa,

Ameen ta basa amsa tana Mai komawa layinsu tabarsa tsaye da Khadija

Wannan shine Ranar da Al'ameen ya fita a Rayuwan kamila.

Bayan wasu shekaru karatu ya fara zama sai da kudi, a hakan yake ta faman ganin Khadija tayi karatu Koh ba kome zata tallah fawa kanta, Amma Ina kudi ya gagara don yanzun mangoron ma sai a hankali Bai wuce a Rana yayi cinikin 200 Koh kasa da hakan. Gashi a ciki Kuma yake ciwa cikinsa hakan yasa karatun Khadija tsayawa iyya Junior.

*An dawo labari* ...........
Khadija Kam kuka take kaman me,haka ma Sumayya Allah sarki Ashe haka rayuwar wa'innan bayin Allah yake, tasu kaddarar kenan,a cikin Yan watanni nan da mahaifinta ya juya mata baya taji kamar tafi kowa matsala,ashe itakam ma in an had'a kaddarar ta dana Muhammad nata ba kome bane tunda har tayi karatu ta tashi cikin kudi da lfyr ta Amma shifa ga maraici ga kuncin rayuwa da Talauci.

D'aga ido tayi tana kallon Al'ameen dake zaune a kujera fuska tayi ja"yayan khadija baka bani lbrn auren mu ba"?ta tambaye sa

Khadija tashi ki tafi kinji kukan ya isa haka, Al'ameen yace batare da ya amsawa Sumayya tambayar taba

Mikewa Khadija tayi zata fita a d'akin cikin kuka abin g'wanin tausaye"Khadija"Sumayya ta Kira sunan ta

Na'am Aunty

"Khadija kiyi hakuri kome na rayuwan duniya Mai karewane Sannan Yana da iyyaka kinji"?

Toh Aunty tace tana share hawayenta

"Ki d'auki doyan nan ki tafi dashi gobe da safe sauki kawo mini ducuments naki kinji Khadija"

Toh Aunty kawai tace tana d'auki laidan doyan ta fita

"Yayan khadija na tambaye ka shine kaci no face"

Sumayya nagaji wallahih ki barni nad'an huta Mana waima me zakiye da ducuments in Khadija ne?

"Oho ba'a sani ba Ina maka magana kana tambaya ta Nima naki fad'an"

Shuru ya Mata tare da lumshe idanunsa

Itakam ganin ya Mata shuru tasan dai akwai abinda bayason fad'a matane,tashi taye a hankali ta Isa garesa faduwa tayi a kansa da gangan

Washhhh yace yana gyara Mata kwanciya

"Don Allah ka fad'amin Mana"

Kinga Sumayya nifa banason na fad'a Miki abinda zaizo Yana d'aga Miki hankali.

"Allah bazan d'aga hankalina ba kawai ka fad'a mini"

Ok toh shikenan Amma sai da dare Zan fad'a Miki

"Gaskiya Nina gaji da abinda kake minin nan wani irin sai dare Kuma Wannan ai Jan Raine"

Banace Zan fad'a ba ki barni Mana zuwa Daren in ban fad'a Miki ba saiki Tuhume ni

"Uhmm toh yanzun me zakayi"?

Bacci,ya Amsa mata

"Bacci a hakan"?

Eh.....

Tashi Sumayya tayi taje ta d'aura abincin dare ta barsa a d'akin

Bayan fitarta sosai yake tunani akan ya fad'a matane Koh karya fad'a Mata karshe dai ya yanke shawaran ya fad'a matan kawai

Bayan isha'i Sumayya ce da Al'ameen kwance akan gado Sumayya taye matashe da cinyar Al'ameen sunfi minutes 20 a haka,tunda sukaci abincin dare sukayi sallah, suke a haka Amma Al'ameen baice mata kome akan labarin ba abin sosai ya dame ta Amma ta danne tunda yace zai fad'a zata barsa ya fad'an da kansa.

Sumayya!!ya Kira sunanta Yana Mai shafa gashin kanta mai tsawo da kamshi

"Na'am"ta amsa Masa

Sumayya banso fad'a Miki dalilin auren mu ga ganin cewa kece kikafi kowa sanin hakikanin gaskiya don bana tunanin har yanzun ana cikin zamanin da za'a ma mace aure batare da tasan miji Koh miji ya santa ba.

"Me kake nufi"? Sumayya ta tambaye sa fuskar ta a hade Jin abinda yake fad'a Mata

Yanzun masifa Zaki mini Koh Jin lbr zakiyi?

"Aiba labarin kake bani ba sukata kake"Sumayya tace,tana kokarin sauka a gadon

Sorry toh, yace Yana kamota

"Nikam ka sake ni "

Kin saketan yayi yana rungume da abarsa, naki sakin kin in kajimin mata fa

"Allah ni ka sakeni nace maka"tace tana kokarin xame kanta a jikinsa

Fushi kikayi ne Gimbiya?

" waye Gimbiyar"?

Sumayya mana.

"Gimbiyar wa"?

Al'ameen...

Uhmmm kawai tace bata kara magana ba

Kinga na miki Alkawari, zan fad'a miki gaskiyan abinda na sani akan auren mu?

"Nima nafasa ji yau sai gobe"ta fad'a tana mai sa hannu ta d'auko wayarta dake gefen filo, airp inda ke makale a jikin wayar ta manna a kanne

Sai magana yake baiji ta amsa masa ba hannu yasa yana tattaba ta, Gimbiya ina magana kin mini shuru

Duk da sumayya taji Al'ameen ya taba ta Amma taki koh sauraransa

Shikam gane fushi take yasa sa dagota sama daga jikinsa ya jefata gefen gadon

Ihu sumayya ta sake bawai zafi taji ba don laushin katifar dana blanket bazai bari taji zafi ba tsorata kawai tayi don bata tsammaci hakan ba" wayyo wuyana ya karye"

Nashiga uku sumayya inga wuyan da gaske kinji zafi dan Allah kiyi hakuri ban dauka zakiji zafi ba, yace yana matsowa kusa da ita

Sumayya kam langobewa tayi wai wuya ya bugu"wayyo wuyata shikenan ya kasheni jama'i

Don Allah kiyi shuru muga wuyan wallahi bada niya nayi ba

Sumayya kam kara lafewa tayi jin ya cicibeta ya daura a cinya kamar wata baby

Sannu sumayya koh muje asibiti ne?

"Nidai goyona nakeso kayi"ta karasa maganar da make murya

Jikinsa na rawa yace, toh... toh... hau, yana dukawa a kan gadon

"Nika d'agani bazan iyya tashi zaune ba"

Cicibar sumayya yayi ya goya haka ya ringa lalube yana zaga d'aki zuwa baranda da ita sai kusan 10:00 sumayya taji gyangyadi kafun tace masa, " ka kwantar da ni bacci nake ji"

Ai da sauri bawan Allah yayi d'aki da ita da lalube ya shimfid'ata a gadon duk ya gama gajiya ba kad'an ba shiyasa daya samu taye bacci ba karamin dadi yaji ba gudun fitina ma koh tabata bayyi ba a gefe ya kwanta yanata tunanin wuyan sumayya don harga Allah ya d'auka da gaske ne


Da asuba ma hakan take sashi tayi ya d'auketa har waje tayi alwala ya dawo da ita d'aki kafun ya tafi masallaci.

Misalin karfe 9:12 na safe Al'ameen ne ke bacci a d'aki bayan dawowar sa sallan asuba

Sumayya data gama aikinta a nitse tayi girki duka don bata tashesa ba saida ta gama harda wanka tayi kafun a Hankali tashigo d'akin wayanta ta d'auka ta danna play in waka ta kara volume, ta saka Eirps kunnen Al'ameen ta mannawa

Ai kam yana cikin baccinsa yaji abu tibbbtibb ga waka kamar a kwakwalwarsa, da sauri ya mike zaune hade da furta, innalilahi sumayya wuyank........sai kuma yayi shuru jin dariyan sumayy a kusa dashi

Hannu yasa sosai ya damkota kwantar da ita yayi a gefensa yahau kanta sosai yayi lamo yana daidaita bugun zuciyarsa har lokacin abin na kunnensa

"Wayyo menene haka"?

Shikam koh jinta bayayi, sai dad'a lumshe idonsa yake jin wakar da ke tashi a kunnensa sosai yatafi dashi

Da sauri sumayya ta zare eirps in jin sai magana take baya kulata

Da sauri ya bude ido, tare da kamo hannunta data cire masa abin kunnensa, mena cirewa? wakarfa bai kareba

"Inata magana kamin banxa badole na cire ba"

Toh mekike son na miki kenan guda daya? tunda jiya ma ai magana nake miki kika saka abinnan a kunnenki kika manna mini nima, duk wai akan maganar jiyanne kiketa fushi koh?

Shuru sumayya tayi

Dalilin auren mu.......
nidai bazance Miki nasan kome akan auren mu ba illah dai bazan manta ba wata Rana wani mutum yazo ya sameni agun sana'a ta yasai Mangoro ya tafi bayan kwana biyu Kuma sai gashi ya dawo Amma baifita a motarsa ba aika yaro yayi ya kirani nakai masa mangoro bayan naje ne yace na Shiga motarsa, Yana da magana Dani,ni kuma naji tsoro gudun kar Amaimaita na baya(Randa aka makantar dashi) shiyasa naki Shiga motar duk yanda yayi Dani ki nayi,karshe dai agun mukayi magana,Kamar haka

Ni sunana mamman Ina da yarinya Naga hankalinka da nutsuwarka shine nayi maka kwad'ayin Koh zaka Amince in baka auren ta?

Sosai naji mamaki nida bana gani ad'auki yar Mai mota sukutum a bani gani Talaka haka kawai sainaji Raina Bai Kama zancen ba, shiyasa nace Masa bana bukata batare da Kuma sauraransa ba nayi tafiya ta

Bayan sati D'aya kawai bappa sulaiman yakirani Wai za'a mini aure,sosai abin yaban mamaki za'a mini aure kuma kamar mace,bappa aure Kuma Kamar Yaya?na tambaye sa

Kamar yanda kaji bappa sulaiman ya bani Amsa

Duk Azana Yar gidan nan za'a bani Amma bappa yace Wai Yar shugaba family ne tunda naji haka kawai nasan lallai wannan aure mai dalili ne ba auren Angani anaso ba,da farko naso nunawa bappa illan auren nan Amma ya murza ido yace sai anyi daga karshe ma cemin Yaya Wai yarinyar tanada Wanda zata aura matsala aka samu bayan anyi test shine aka samu tana d'auke da c................











*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* =؃?


Contact them vie
>؀?08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense

>???
>د? *MATAR MAKAHO* =?h?
>د?
~ Na ~


('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=?L?
free book >?'?

Page 4? 6? &4? 7?
Wai yarinyar tana d'auke da ciki shiyasa sukeso na rufa musu asiri na aure ta

Sosai nayi mamaki kuma zuciya ta takasa Aminta akan zancen cikine kawai ba, tunda yaran masu kudi da yawa suna cikin shege Amma ba'a bawa talakawa saini MAKAHO sam nakasa yarda.

Dana matsawa bappa da tambaya ma cemin yayi koh naki koh naso sati mai zuwa d'aurin aure

Harga Allah banso auren ba sam, don inaji a jikina ba batun ciki bane, imma cikin ne taya za'ayi a d'aura aure da ciki a jikin budurwan kenan, koh an zubar?karshe fa akafi karfine kafun sati d'aya ba wanda baisan zancen auren mu ba saidai sam ba wanda yasan dalili kuma duk wanda yaji batun auren saiya digawa auren ayar tambaya

Amma ke sumayya menene dalilinki na aure na?

"Auren ka, ina ma na sanka kajimin mutumi fa" ?ta fad'a cikin kuka sosai abin ya mata zafi watoh bayan auren kaskanci da akaso mata har b'atata akayi a wajen mijin don aga abinda yafi wanda suka sata=?-?muni

Sumayya nif???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a tambaya kawai nayi kuma abinda nayita gujema kenan, kika ga nake gudun fad'a miki gaskiyar abinda na sani, ya karasa maganar da kara rungumarta jikinsa

"Shikenan yanzun koh inada cikin sai ka yarda ka zauna dani" ?

Indai har cikin babu a jikinki koda kin tabayene zan zauna dake a hakan ma naji dadi ai, na samu mata

Kuka sumayya ta sake sakewa watoh duk zaman da suke da Al'ameen na kokonto ne tayi ciki koh batayi ba kai wai meta tsarewa dangin mahaifintane, na mahaifiyarta kamma bata sansu ba bare

Kiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login