Showing 1 words to 3000 words out of 128821 words
Chapter 1 - Aalima Book 1,2,3,4 Completed Hausa Book Na Takori .pdf
¹Aalimah*
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870*
FREE PAGES 1
Jirgin ‘American Airways’ ya sauke AALIMAH MANSOUR a birnin Massachusetts na
kasar Amurka a ranar ashirin da biyar ga watan Mayu, na shekara ta dubu biyu da goma sha
shidda(2016). A sannu ta bi jerin gwanon masu saukowa daga jirgin rataye da matsakaiciyar
jakar hannu ta mata. Sanye ta ke da doguwar riga da veil dinta kirarTahran (maroon colour) ta
zagaye fuskarta da veil din rigar. Takalmin kafarta baki ne mahadin jakar hannunta marar tsayin
dunduniya. Taku ta ke cikin nutsuwa har ta taka kwaltar filin jirgin (Boston Logan International
Airport) ta shiga van din da sauran fasinjoji ke shigawadda za ta karasa da su zuwa ainahin
ginin cikin filin jirgin, inda aka yi mata duk wasu immigration checks, daga karshe ta dauko jakar
kayanta ta fito.
Hasken sassanyar ranar da ya soma ketowa ya dallare mata ido, ta sanya tafin
hannunta ta kare saman idanunta daidai lokacin da masu taxi suka soma isowa gare ta.
Tambayarta suke inda za a kai ta. Ta diregajiyayyun dara-daran idanunta a kansu
kamar mai kiyasi, kamar kuma mai tantance wanda ya kamata ta zaba,da ganinta ka ga bakoa
kasar da bai taba zuwa ba, kafin ta tsaida idonta a kan wani dan tsamurmurin bature ta nuna
mishi adireshin inda zai kai ta, wanda ke rubuce cikin jotter dinta, wadda ta fiddo daga jakar
hannunta. Daukar jakar tata ya yi ya sanya a bayan motarsa ya bude mata kofar baya, ta shiga
ta zauna. Ya zagaya ya shiga mazauninsa, ya tada motar.
Tafiya suke sannu kan hankali a kan kwaltar manyan titunan birnin Massachusetts tana karewa
kyawawan titunan kallo.
Birnin Massachusetts na daya daga cikin manyan biranen da kasar Amurka ke tinkaho da su.
Ya kuma kunshi al’ummatai daban-daban, daga yarekala-kala na duniya. An kiyasta
population din birnin Massachusetts a shekarar (2017) da adadin (685, 094 population).
Yana kusa da Cambridge daga gabas, tana iyaka da Hampshire da Vermot daga Arewa, daga
yamma zagaye yake da babban birniNew York, daga Kudu da birnin Connecticut da Rhode
Island. Daga gabas kuma zagaye ta ke da Atlantic Ocean. Birni ne daga Arewa maso gabashin
USA.
Mai taxi ya tsayar da motar a cikin estate din (Martha’s Vineyard) a kofar wani kyakkywan
lodge cikin birnin BOSTON (Capital of Massachusetts).
Aalimah Mansour, ta yi ajiyar zuciya, ta lalubo adadin kudin da ya bukata ta ba shi, ya ba ta
canjinta, ya kuma fitar mata da jakarta daga bayan motarsa. Sannu a hankali ta karasa kofar
gidan tana nazarin kayatacciyar unguwar. Tana daga cikin manyan estate (kebantattun
unguwanni) a birnin Boston. A saman kofar gidan an rubuta lambar gidan da kuma sunan
mamallakin sa ‘ISHAQ RAAZEE’.
Kararrarwar kofar gidan ta shiga dannawa, sai da ta danna sau uku kafin ta jiyo muryar mace
na fadin tana zuwa cikin harshen Nasara. Gabanta ya ci gaba da lugude kamar zuciyarta za ta
fado daga cikin kirjinta. Ba ta da idea na irin karbar da za ta samu daga Kawun nata, haka ba ta
da sanin irin karbar da za ta samu daga matarsa Mummy Zulaiha da ‘ya’yanta, matar da
kowa a family dinsu ya kwana da sanin ba ta son kowa ya rabe ta, daga mijintasai
‘ya’yanta. Kada a rabi inuwar arzikin da suke ciki. Balle kuma su, da nata mahaifin duk
cikin zuri’arsu shi ne mai karamin karfi. Banda Mamada ta dage ba za ta yi zaman hostel
ba, alhalin ga Kawunta da iyalinsa a kasar da ba abin da zai kawo ta gidan Kawun nata.
Ta tabbata sai ta fi samun nutsuwa a zaman hostel din, amma ya ya za ta yi da umarnin
iyayenta? Ta riga ta dora zuciyarta a kan son karatun nan, kamar yadda ta ke son rayuwarta.
Sannan ba ta san kowa ba a kasar bayan su. Asstrict as her Mum is, (sabida tsantseni irin na
mahaifiyarta) a kan tarbiyyah, ta tabbatar mata ko dai ta zauna gidan Kawunta ta yi karatun a
gabansa, ta fuskanci kowannne irin kalubale na matarsa da ‘ya’yansa, ko ta hakura ta yi
aure. Hankalinta zai fi kwantawa ita ta hakura da nata burin akan karatun nata.
Mahmoud, saurayi daya data ke da shi a rayuwarta, ko ta ce wanda ya taba cewa yana son ta
da kalmar aure, dalibi ne shibai shirya ba, yanzu ne yake shekarar karshe a jami’a, sun
kulla soyayyarsu ita da Mahmud Kaita ba tare da sanin iyayenta ba, karewa ma boye tarayyarta
da Mahmud ta ke don muddin Mama ta san tana da tsayayye, duk sonta da karatun ga ‘yar
tata, za ta hakura ne ta yi mata aure. Banda babban Yayanta Aboubacar (Abubakar)babu
wanda ya san da maganagr Mahmud a gidansu, shi ma ya sani ne a dalilin Mahmud din
abokinsa ne, kuma ta dalilinsa suka san juna.
Duk wannan tunanin Aalimah na yin shi ne a tsaye a kofar gidan Kawunta kafin a zo a bude
mata kofar, cikin mintunan da ba su gaza biyar ba. A daidai lokacin ne kuma Easther (‘yar
aikin) Mummy Zulaiha ta bude mata kofa. Kallon juna suka tsaya yi na rashin sani ita da
Easther din na ‘yan sakanni, kafin ta ba ta hanya tare da yi mata alamun ta wuce ciki ba
tareda ta tambayeta wanda ta zo nema ba. Ba kuma komai ya sanya Easther bai wa Aaalimah
hanya babu tambaya ba, sai kamanninta da ta gani mai dimbin yawa da yaran gidan,
musamman matan.
Aalimah ta wuce ciki tana jan jakarta cikin nutsuwa. Easther ta mayar da kofar ta rufe. Daidai
lokacin da Mummy Zulaiha ta bullo daga upstairs a shirye tsaf, tana taku kwaf-kwaf akan tsanin
takalmin ta irinna matan da duniya ke yi da su, suka kuma sameta dai-dai da ra’ayinsu,
makale da jakar hannu da mukullin mota alamar fita za ta yi. Sakin baki ta yi cikin madaukakin mamaki tana kallon ba’abziniyar budurwar da ke shigowa.
Doguwa, sambaleliya, fara tas! Mai dogon hanci da manyan fararen idanu, labbanta sirara jazur
da su, ma’abociyar yalwar sumar kai, wadda ta fallasa kasantuwarta daga ruwa biyu, wato
kallo daya za ka yi mata ka fahimci ba cikakkiyar bahaushiya ba ce, jinin su maigidanta Ishaq
Razee ce. Yarinya ta karshe da ta yi tsammanin gani a kasar America, kuma cikin gidanta, a dai
cikin family din maigidanta.
Aalimah ta saki murmushin yake, wani lallausan murmushi mai ban sha’awa na nuna
ladabi, ta russuna tana gaida matar Kawunta, wadda mamaki ya hana ta ce mata kanzil. Sai da
ta gaishe ta har sau biyu, Zulaiha ba ta farfado daga suman mamakin wucin-gadin da ta yi ba,
har sai da karamar ‘yarta Yasmin ta taba ta, tana fadin,
“Mummy ana gaishe kiâ€.
Firgigit ta yi, ta dubi Aalimah tana ayyana abubuwa da yawa a cikin ranta, me ya kawota? Wato
Ishaq wuyansa ya yi kaurin da zai soma kwaso abzinawan danginsa yana kawo mata gida ba
tare da shawara da ita ba? Abin da ba za ta taba dauka ba kenan. Amsa gaisuwar ta yi
kadaran-kadahankafin cikin shaqaqqiyar murya ta ce, “Ke da wa ku ka zo?â€
Aalimah ta sunkuyar da kai cikin muryarta mai sanyi, ta ce,
“Ni kadai ce Auntyâ€.
“Ke kadai tun daga Nigeria?â€
Ta daga mata kai alamar “Ehâ€.
Kamar za ta ce wani abu, sai kuma ta fasa ta ci gaba da saukowa daga stairs din. Ta dubi
Easther cikin rashin walwala ta ce,
“Ki ba ta abinci ki nuna mata dakin kwana, ni fita zan yiâ€.
Easther ta amsa, “Yes, Ma!â€
Ta dubi Aalimah cikin hadiye fushi ta ce, “Ki wuce ku je. Sai na dawo. Zan kai Yasmin
makaranta ne, daga can zan koma officeâ€.
Cike da ladabi Aalimah ta amsa, ta bi bayan Easther, Mummy Zulaiha da ‘yarta Yasmin suka
fita.
Gidan Ishaq Raazee karamin ‘American lodge’ ne, ginin sama da kasa. A saman, dakin
maigidan da na matar gidan har ma da na yaransu mata guda uku yake. A kasa kicin ne da
babban English parlour wanda a cikinsa dakin manyan ‘ya’yansu maza yake. Mai aikin
gidan, wato Easther ba ta kwana, zuwa ta ke da safe ta tafi da yamma in ta kare girkin dare.
Don haka Easther ta rasa dakin da za ta kai bakuwa Aalimah, gidan ba a gina shi da niyyar
karbar baki ba, tana ganin bai kamata ta kai ta sama ba, tunda maigidan a sama yake, bai
kuma kamata ta ajiye ta a kasa ba babu kowa sai ita kadai. A falon kasan, akwai wani daki
bayan na Yayansu dake makaranta, amma a rufe yake ba ta taba ganin an bude shi ba, balle
tayi tunanin ajiye ta anan, don haka sai ta kai ta dakin su Yasmin kawai, wanda ke daura da na
mahaifiyarsu. Cike da zullumin ko ta yi ba daidai ba. Ta koma kicin ta hado mata abinci a kan
‘tray’ ta ajiye mata a gefen gado. Ta yi mata sallama ta koma bakin aikinta.
Kafin Aalimah ta yi komai, wanka ta shiga don ji ta ke jikinta har wani danko-danko yake mata.
Ga ta da son wanka dama kamar agwagwa komai sanyi, balle kuma a lokacin zafi. Hatta gashin
kanta ji ta yi yana mata kaikayi – kaikayi, duk da yau kwananta uku da wanke shi. Ta sunce ta
dauko kayan wankanta daga jakarta ta shiga toilet din da ke cikin dakin. Ta tsaya na dan lokaci tana nazarin bandakin. Ba ta taba zuwa kasar waje ba, amma kuma
hakan bai maida ita bakauyiya ba. Nazarin bandakin ta shiga yi wanda ke dauke da bathtube na
jacuzzi, kalarsa light blue komai da ke cikin bandakin kalarsa kenan. Ta mika hannu ta zare
ribbon din da ta daure tulin gashinta ya wargaje a kafadunta, baki sidik mai tsayi da salki, na
abzinawan usli.
A cikin toilet din har da hand dryer makale a gefe. Ba karamin jin dadin hakan ta yi ba. Ga
shampoos nan kala-kala masu tsada a jere, wannan na da nasaba da kasancewar su ma yaran
gidan mata guda uku, gashin gare su kamar ita. A lokacin ta manta da komai ta tara ruwan dumi
cikin jacuzzi ta shiga ta soma abin da ta fi so a rayuwarta, wato ‘wanka’. Ta jima tana
kalkale sassalkar fatar jikinta kafin ta soma wanke sumar kanta tana cudawa da kumfar(head&
shoulder). Ta gama ta busar da shi da hand dryer, ta dauro alwala ta fito. Doguwar rigar atamfa
(fitted-gown) ta sanya ta dauko hijabin sallarta ta tada sallah. Sai da ta rama sallolin da ake binta sannan ta samu nutsuwa tazauna ta soma cin abincin.
Faten dankalin Turawa ne da aka yi da Mushroom da zallar tsokar naman kaza. A gefe kuma
gasasshiyar hanta ce a cikin bowl na tangaran ta sanya fork tana cin hantar a hankali bayan ta
gama da faten dankalin. Da ta gama, ta kora da lemun kwali na Apple mai sanyi, sannan ta
kishingida a sofa tana hutawa.
Mamanta, Daddynsu, kannenta da masoyinta Mahmud suka fado mata a rai. Ta san suna can
suna sauraron kiran wayarta. Da sauri ta sauko daga gadon ta lalubo wayar a jakarta. Tana
kunnawa ta tuno ba ta da internet connection, kuma ba ta da credit na kasar. A rashin saninta
da cewa gidan (WiFi) suke amfani dashi. Ta maida wayar gefe ta ajiye ta dauki kayan da ta ci
abinci da su ta sauko kasa.
Kofofin falon ta shiga nazari tana son gano wacce ce ta kicin?Sai ta jiyo karar kwanuka kamar
ana wanke-wanke da karar zubar ruwa daga famfo. Nan ta gane kofar da ke can karshe ita ce
kicin. Ta karasa ta tadda Easther suka yi wa juna murmushi na rashin sabo, Easther ta karbi
‘tray’ din ta hada da wadanda take wankewa, sai ta kasa komawa daki ta jingina da
cabinet din kicin suka soma hira.
Aalimah ta ce tana so ta taimaka mata su ci gaba da aikin tare. Easther ta ce ta rufa mata asiri
ta koma daki kada ta yi laifi wajen uwar dakinta, tunda ba ta ce ta sa ta aiki ba. Amma ta kasa
komawar, sai ta samu daya daga kujerun karamin dining da ke cikin kicin din ta zauna, Easther
na aikin suna hira jefi-jefi da turancinta mai rauni. Easther ‘yar Africa ce, wato bakar fata wadda aka haifa ta kuma girma a kasar Amurka,
wadanda ake kira black- American. Ta ke gaya wa Aalimah su ‘yan asalin kasar Ghana ne
daga Kumasi, iyayenta da kakanninta duk a nan aka haife su sun rayu tsayin rayuwarsu suna
yi wa Turawa bauta. Ta tambayi Aalimah amma ita ‘yar uwar Daddy ce ko? Don ta ga tana
kama da shi da ‘ya’yansa. Aalimah ta gaya mata cewa; “Wan babanta ne Ishaq
Razeeâ€.
Daidai lokacin da suka ji shigowar motoci har guda biyu, daya ta maigidan, daya ta Mummy.
Yaransu ne suka fara shigowa daya bayan daya suna ta hayaniya, Aalimah ta dawo kofar kicin
tana kallonsu. Basma ce a gaba, sai Khalisat sai auta Yasmin. Rabonta da su shekara shidda
kenan zuwansu Nigeria na karshe. Lokacin Aunty Zulaiha na da cikin Yasmin. Duk sun yi wani
irin girma mai ban mamaki da ban sha’awa, irin girman ‘ya’yan Turawa. Ba mai cewa
Basma sa’arta ce domin ta yi biyunta a girman jiki. Mai bi mata Khalisat, Aalimah ta girme ta
da shekaru biyu, shekarunta goma sha hudu. Ita da Basma za su yi sha shidda da ‘yan
watanni. Bayan haihuwar Khalisat Mummy Zulaiha ta dade ba ta haihu ba,sai da Khalisat ta yi
shekaru takwas,sannan ta haifi autarta Yasmin.
Haihuwarta ta farko da ta biyu ‘ya’ya maza ne. Su ma tsakaninsu ratar shekaru biyar ne,
haihuwa irin ta turawa Mummy Zulaiha ke yi, haihuwar Khaleesat data yi shekaru biyu bayan ta
Basma (unwanted pregnancy) ne wanda ba yadda zata yi da shi.Data haife tan kuma, sai tafi
sonta fiye da dukkan ‘ya’yanta mata. Itama Khalisan bata aje Mummy kusa da kowa na
gidan ba a kauna da shakuwa. Idan ka dubi Mummy Zulaiha ba za ka ce ta haifi wadannan
zaratan ‘ya’yan ba saboda hutu da kula da jiki. Shekarunta sun kusa hamsin, amma
tsammani za ka yi talatin da biyar gare ta.
Daga ita har maigidanta Ishaq sun yi auren wuri, aure na soyayya, irin makauniyar soyayyar da
iyayenta suka gwammace su cire ta daga makaranta tun tana aji biyar na sakandire su aura wa
Ishaq. A lokacin yana shekara ta uku a jami’ar Ahmadu Bello. Ko abin da zai rike ta ba shi
da shi, ga hidimar karatu, don haka ya dauke ta ya tafi da ita kasarsu Niger Republic ya ajiye ta
a family house dinsu, inda aka ba su daki a babban gidan na zuri’ar Mal. Ibrahim Raazi. Ya
maida ita makarantar sakandire a nan garinsu, Yamai, duk da ba ta jin faransanci har a hankali
ta koya, in ya samu hutun semester ne yake zuwa gida shi din ma ba kowanne ba.
Tun yana yaro yake son kasar Nigeria da son zama a cikinta, ko da ya gama sakandire ya ce da
mahaifinsu Malam Ibrahim Razee shi a Nigeria zai yi jami’a yana sha’awar harshen
turanci, bai hana shi ba, amma ya ce ya tafi tare da kaninsa ‘Mansour’ wanda ya samu
double promotion sabida hazakarsa suka gama sakandire a shekara guda, shi ma ya yi karatun
a can zai fi jinsa kamar a gida in suna tare.
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:30 AM - Buhainat: **🌹 *Aalimah**🌹
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870
FREE PAGES 2
Ba su sha wahalar samun gurbi a jami’ar Ahmadu Bello ba, kasancewar a wancan lokacin
neman masu yin karatun gwamnati ke yi ido rufe, ga kuma takardunsu sun yi kyau, wadanda
aka yi wa fassarar takardun Nigeria, suka kuma shiga wani tsari na koyon harshen turanci da
jami’ar ke yi a wancan lokacin, kasancewar sun yi karatunsu ne da harshen faransa. Komai
tare suke yinsa a A.B.U kasantuwar baki da basu da kowa sai junansu, sannan kuma uwarsu
daya ubansu daya.
A gida ba sa jituwa kasancewarsu sakonnin juna, kowanne kamar yana ganin hanjin dan
uwansa. Amma da suka zo Nigeria ba su da kowa, dole suka rungume junansu. Wannan kuma
wata hikima ce irin ta iyaye, mahaifinsu ya yi musu ba tare da saninsu ba.
Daga Mansour har Ishaq dukkansu gifted ne a karatu. Ba fanni daya suke karanta ba, Ishaq na
nazarin International Relation, yayin da Mansour ke karantar Mass Communication. A hostel
suke rayuwa, duk abin da suke bukata mahaifinsu na aiko musu ta banki.
Mahaifinsu babban malami ne ta daya bangaren kuma babban dan kasuwa a babban birni
Yamai, yana sana’ar kasuwancin kayan abinci yana kuma taba kasuwancin rakuma da
kiwonsu, wanda ya gada iyaye da kakanni. Matansa na aure guda biyu, wadanda ke haifa masa
‘ya’ya kusan a tare, don in wannan ta haihu yau, bayan sati daya ko wata daya za ka ji
dayar ma ta haihu.
Inna Bintou da Inna Kasisi, sune matan Malam Raazee. Ishaq da Mansour ‘ya’yan Kasisi
ne, wato uwargida. Haihuwa suke kusan duk shekara, don haka ‘ya’yan Malam Ibrahim
ashirin da biyar a duniya kafin haihuwar ta tsaya wa matan nasa. Ishaq ba shi ne babba ba a
‘ya’yan Kasisi, yana da yayye har biyu, sannan shi, sai Mansour. Ba duka ‘ya’yan Malam Razee ke son karatun boko ba, hasalima mazan duka ba sa so,
sun fi son sana’ar mahaifinsu in ka cire Ishaq da Mansour, matan kuwa suna gama
sakandire yake yi musu aure. Dalili kenan da sanda Ishaq ya zo masa da maganar ya samu
matar aure a Nigeria yana so ya yi aure bai ja zancen da nisa ba,