Showing 123001 words to 126000 words out of 180927 words
Chapter 42 - GARKUWA Book 1 Original Pdf By Garkuwar Fulani.txt
Hibba.
Sai ƙarfe uku dai-dai Shatu ta tashi.
Cikin kasalan baccin da bai gama isarta ba, ta miƙe ta shiga bathroom.
Wonka tayi tare da al'wala.
Bayan ta fitone, ta tada Hibba, ita kuma ta kabbarta sallah.
Kafin ta idarma Hibba ta fito, gefenta tazo itama ta kabbarta sallan.
Basu tashi bisa sallayan ba, sukaji kiran aallan la'asar.
Haka yasa sukayi sallan. Suna idarwa Hibba ta miƙe ta nufi ɗakin Umaymah.
Ita kuwa Shatu ninke sallayar tayi kana ta dawo gaban dreesing mirror.
Mai ta shafa tare da ɗan murza fauda a fuskarta, kama ta shafa man baki.
A cikin sanyi taje gaban drower'nta,
hannu tasa ta buɗe drower'r, wata tattausar doguwar riga mai masifar kyau ta zaro.
Kalar rigar Black blue mai sheƙi, saman rigar a ɗan tsuke daga ƙasan ƙugunta kuma a buɗe,
yanada wasu duwasu kamar na Daimond daga sama har ƙasan gaban rigar.
Hannunta kuma masu faɗi.
Tayi kyau sosai cikin rigar, dogon gashinta ta haɗa ta tubke wuri ɗaya ta kitse jelar kana ta nannaɗe jelar a ƙeyarta,
sannan tayi rolling kanta da mayafin wanda dai dai inda zai zauna a goshin akwai duwatsun.
Turare ta fesa, kana cikin sanyi da kasala ta nufi, falo.
A falon ta samu, Hibba a kwance tayi shiru.
Ganin bata gan fitowarta banema,
Yasa ta nufi inda take gefenta ta zauna tare da cewa.
"Hibba ɗauko mana awaran".
Cikin sanyi Hibba tace.
"To". Kana ta miƙe ta nufi falon, jin shiru ba kowa a cikine, yasa ta nufi kitchen a hankali-hankali.
Foodflaks ɗin da suka sa awaran da suka soya ta ɗauko.
Tana dawowa ta zauna kusa da Shatu tare da cewa.
"Gashi". Kai ta gyaɗa mata tare da nuna mata kitchen ɗin ta, tace.
"Ɗauko mana plate da roban yajin da Gimbiya Aminatu ta aiko mana.
Kizo mana da ruwa".
Ba tare da tace komaiba ta juya ta tafi.
Bayan ta dawone suka zauna suka fara cin wanda suka zuba.
A can falon Hajia Mama kuwa,
duk mgnar da Umaymah da Ummi keyi, shiru tayi ta zuba musu ido.
cikin sanyi Umaymah tace.
"Addana kiyi haƙuri, kin san yaran sai a hankali, dan Allah kada kisa wani abun a ranki wata ran ko ance tayi miki bazatayi ba".
Murmushi tayi mai cike da ma'anoni kana tace.
"Uhummm ba komai Khadijah jekici gaba da shirin tafiyarki, karki damu kinji".
Ido suka zuba mata domin duk basu gamsu da mgnarta ba, to amman ya zasuyi tunda tace ba komai.
Haka suka tashi suka dawo falon.
Yau su Jalal ma basu zoba.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, tunda aka idar da sallan azahar ya dawo, ya wuce su Umaymah a falon ba tare da yace musu ƙalaba.
koda ya shiga ɗakin ya samu yayi bacci tsakanin azahar da la'asar kamar yadda ya saba, hakan bai samuba.
Sabida abubuwan dake ranshi.
Bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, tare da fara yage towel ɗin dake hannunshi.
haka yake tsaye a ƙasan ruwan har saida yaji an kira sallan la'asar. Nanne ya fita ya tafi masallacin.
Bayan an idar da sallan ne ya dawo gida.
Ganin babu kowa a falon ne yasashi zama, bisa kujerarsa.
Ƙafarshi ɗaya ya ɗaura kan ɗaya.
A haka su Umaymah suka sameshi.
Gefenshi Umaymah ta zauna bisa kujerar dake kusa dashi.
Ummi kuwa gabanshi ta zauna bisa carpet.
A hankali ya buɗe kwayar idanunshi.
Cikin tarin ɓacin rai ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi ina wannan fitsarerren abun da bai san darajar manya ba!?."
Cikin sanyi Ummi tace.
"Allah ya huci zuciyarka tuba takeyi, in sha Allah bazata sakeba, Hajia Mama da kanta ta yafe mata".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Ummi ko dai kece kika bata dama da matsayin yiwa Mama hakane?".
Cikin sauri tace.
"Wanne ni wlh bani bace".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Umaymah da itama shi take kallo cikin ɓacin rai yace.
"Umaymah har akwai wani abun da zai hana mama shigowa sashina? Har yaushe waccar babyn robar ta samu dama da ikon bada izinin shiga da fita cikin sashina da abinda ya shafi rayuwata?
Me take nufi dani da iyayen nawa."
Kauda ido Umaymah tayi daga kallonshi kana a hankali tace.
"Ba isa bane! Akasi aka samu! Nifa inaga har yau Shatu'n bata gama sanin mutanen masarautar Joɗa da kuma dangantakar makusan tankaba, ayi mata haƙuri a mata uzuri a dai wannan karon".
Juyowa yayi ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi a kira min waccar abar".
Da sauri Ummi ta miƙa tare da cewa to.
A falon ta samesu, cikin fuskar da babu yabo babu fallasa ta kalli Shatu dake gefen Hibba da alamun ta cire hannunta a cin awarar kanta ta ɗan kauda tare da cewa.
"Kizo Sheykh yana kiranki".
Kai ta gyaɗa tare da cewa "Toh". miƙewa tayi taje Dinning area ta wonke hannunta, kana tazo tabi bayan Ummi.
A gabanshi Ummi ta zauna ganin haka itama ta zauna a gabanshi.
shiru tayi tana kallon yatsun fararen sawunshi. Shi kuwa kanshi na gefe ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace.
"Ke ki shiga hankalin ki, kisan abinda kikeyi da wanda zakiyi! Ke har kin kai matakin da isar da zaki ƙaddamar min da iko da isa a cikin gidana? Ko dai ce miki akayi gidan nakine?".
Kai ta gyaɗa mishi alamun eh ance mata gidan natane!.
Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da ci gaba da mgna dan shi bai ga sanda ta gyaɗa kanba hakama Umaymah, sai Ummi ce kaɗai ta gani, su kuwa sai murmushi sukayi.
Cikin kausasa murya yace.
"In baki san darajar manya da iyayeba, to ki zama kurma bebiya makauniya a cikin giddannan kafin Ubangiji ya zantar da Hukuncin da ikon zamanki da barinshi dan ikone na Allah bana waniba.
Har kin isama Mama tazo ki koreta dan idonki basu da ɗigon kunya.
Ko karen gidannan baki da ikon hanashi abu da sakashi bare Mama.
ke ta bawa abun ne da zakice bakya so.
Kece mai bakin mgn uwar fitsararru ko?".
Sam abinda bai saniba zuwa yanzu hankalinta, tunaninta nitsuwarta, jinta, da ganinta duk suna kan farar ƙamarshi ta dama, da zanen maciji ke liƙe kamar macijin na tafiya.
Wani irin ba hagun numfashin ta sauƙe a hankali,
tare da rufe manyan idanunta da azaban ƙarfi.
Sabida gani takeyi Tamkar macicijin ne ma da kanshi ke manne a jikinshi yana kuma motsa ɗan bindinshi dake saman babbar yatsarshi.
A hankali ta buɗe idanun kana tabi kan rumfar ƙafar da ido, inda take ganin zanen maciyar yabi.
Kasan cewar a zaune yake ya kuma ɗan tattare al'kyabbar jikinshi.
Shi yasa tana iya ganin har ƙarshen rumfar tafin ƙafar nashi.
Inda iya nan jallabiyar jikinshi ta rufe.
da sauri ta ƙara rusunar da kanta wai ko zata ga ci gaban tafiyar macijiyar.
Umaymah ce ta ɗan kalleta cikin wata iriyar murya tace.
"Ki tashi muje ki bawa Hajia Mama haƙuri, ku nemi yafiyarta ki kuma kiyaye gaba, kinji".
Cikin sanyi tace.
"Toh".
Still Bata miƙeba, cikin ɗan ɗaga murya yace.
"Tashi muje yanzu ki bata haƙuri, in ta haƙura kinyi babban Sa'a".
cikin sanyin jiki ta miƙe tsaye.
Shima miƙewa yayi, Ummi kuwa da sauri ta nufi ɗakin Shatu.
Jim kaɗan ta fito da wata kekyawar al'kyabbar matan masarauta ta zuramata.
Bayan ta gama gyrashi ne, tasaka hular.
Shi yayi gaba ita kuwa.
Tabi bayanshi Umaymah da Ummi suka biyo bayanshi.
Suna isa bakin mashigar farfajiyar Side ɗin Hajia Mama,
ta tsaya gis tare da yin ƙasa da kanta.
Ummi ce tace.
"Muje mana".
Shiru batayi mgna ba, jin hakane yasashi juyowa, karon forko kenan da ya zubawa tsawonta ido.
cikin ɓacin rai yace.
"Muje ki lashe aman da kikayi da kanki".
Cikin sanyin sauti tace.
"Ni bazan shigaba".
Da mamaki Umaymah tace.
"Innalillahi wai ke Ayshs wani irin taurin kaine dake? Menene manufarki?".
Murya can ƙasa yana rawa alum zatayi kuka ta kalli Umaymah tace.
"Kiyi haƙuri Umaymah ki gafarceni, amman ni bazanje ba, in kuma zanje to ku ku koma, zanje ni ɗaya zan bata haƙuri".
Cike da al'ajabi Umaymah tace.
"To sabida me bazaki je da muba".
Cikin faɗa Sheykh yace.
"Sabida muna furci mana, ba zuwa zatayi ba, shiyasa zatace sai dai in ita ɗaya zataje, maza wuce muje a gabana zaki bata haƙuri".
Cikin sanyi Umaymah tace.
"Jazlaan barta mu tsaya mu jirata anan in dai zataje ita ɗayan".
Kanshi ya dafe tare da cewa.
"To wai Umaymah mu bayaninta ne da zamu tsaya muna jiranta".
Ummi ce ta mishi alamun yayi haƙuri ya yarda.
Shiru yayi tare da komawa gefen jerin bishi yoyin namiji kwanɗa ya zauna bisa kujerun silver dake zagaye da wurin wanda ko wani side akwaisu.
Itama Umaymah da Ummi zuwa sukayi suka zauna.
Ita kuwa Shatu a hankali ta fara taku ta nufi cikin farfajiyar, suna hangota har ta isa bakin ƙofar.
turawa tayi ta shiga, kana ta maida ƙofar ta rufe.
Bayan kamar 37 minutes ta fito.
Cikin wani irin tafiya mai baiyana tsantsar jin daɗi, fuska cike da fara'a ta nufosu.
A hankali ta isa gabanshi ciki ɗan ɗaga murya tace.
"Na bata haƙuri ta yafe min, ta samin al'barka. Kaima kayi haƙuri ka yafe min".
Da mamaki suka kalleta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wari irin kallon tuhuma yayi mata, kana ya miƙe tsaye tare da cewa.
"In ma ƙarya kikayi, ni ba'amin ƙarya".
Sai ya kuma kalli Umaymah tare da cewa.
"Umaymah kuje ki ƙarisa shirinki bari inje wurin Hajia Mama".
To tace kana taja hannun Shatu suka tafi. Shi kuwa da Ummi suka nufi cikin Side ɗin Mama.
Bayan sallan isha'i, cike suke a falon. Gaba dayansu, Umaymah zaune a tsakiyarsu da jakarta, Sheykh Jabeer na yi mata addu'o'in isa lfy suna amsawa da Amin Amin.
Bayan sun shafa addu'o'in ne ta miƙe tsaye, tare da kallon su baki ɗaya, murya na rawa tace.
"Jazlaan zan tafi, zan bar hankali na, a nan ko na koma banda nitsuwa, kullum ina cikin taraddadin abubuwanda yake faruwa, Jazlaan na sani kaine GARKUWAR yayanka da ƙanneka. Ga wani sabon nauyi ya ƙarun maka.
Aysha baƙuwace bata san komaiba kam al'amuran Masarautar Joɗa, dan Allah in tayi abinda ba dai-dai ba kuyi mata uzuri.
Ita komai a sabon abu zata ganshi abinda bata taɓa ganiba.
Mun rabata da iyayenta yayunta ƙannenta mun kawota tsakiyarmu, mu kasance mata adalan masu masauƙi.
Na sani Jazlaan ka fini sanin haka da kuma haƙƙoƙinta da suka rataya gareka."
Sai ta kuma kalli sauran yaran yar uwarta ɗin tace.
"Jalal, Jamil, Aysha matsayin yar uwarku take, yayarku ce, matar yayanku. Bana son raini especially kai Jalal, ban gamsu da irin mu'amalat ɗin ka da itaba.
Babu wanda yake nuna min yadda nakeso a kanta sai Jafar, a duk sanda ya ganta zaiyi mata murmushi kamar yadda yake min, in yaga bata nan zaiyi ta dube-duben da nasan da yanada baki zai tambayeni lfyarta.
Zan bar Hibba saboda itane, bana son taji kanta a matsayin bare."
Shiru sukayi gaba ɗayansu sabida yadda take kuka da yin mgna tamkar mai bar musu wasiya, ko wacce wani tsohon damuwa ya taso mata.
Sharce hawayenta tayi tare da cewa.
"Ummin Jabeer zan tafi zan barki da sauran aiki, dan Allah ki kula da Shatu da mu'amalarta da Hajia Mama, ki nuna mata uwar miji ba abun rainawa bace".
Sai kuma ta miƙowa Aysha da taketa kuka hannun ta jawota tsaye ruggume ta tayi cikin zubda hawaye tace.
"I dan akaga damuna ana zaton yabanya zatayi kyau, kallon damuna nakeyi miki a cikin ahlin yar uwata.
Ina jin zaki zamo mana haske mai yaye duhun daya maye ganinmu, tun kafin yau ni na sanki a mafarkina Allah ke nuna min ke a matsayin matar Jazlaan ɗin na, kuma Allah yana nunamin abubuwa da dama a kanki a cikin mafarkaina, wasu kuma sunma tabbata na gansu.
dan Allah ki riƙe min Jazlaan amana, ki lura da ƙannenshi yadda zaki lura da naki ƙannen ki kula da Jafar kada ki tsoraceshi bazai cutar da keba ki ɗaukeshi a
Matsayin wa".
Cikin zubda hawaye Shatu tace.
"In Sha Allah Umaymah zan kiyaye zan kuma zamo yadda kike zatonta, koda sanadin haka zan rasa jigo biyu na rayuwata rai da lafiya ta".
Kalaman Umaymah da Aysha kuramen baƙine da su kansu ɗaya bata fahimci abinda ɗaya take nufiba, hakama ɗayar, bare su Jalal dake tsaye.
Jawo Hibba tayi ta haɗa su ta ruggume,
kana ta jawo Juwairiyya tace.
"Ku duk yara nane ku zauna lfy".
Gaba ɗaya da to suka amsa.
Cikin sauri Umaymah ta sakesu kana ta miƙa wa Ummi hannu sukayi musababa, tare da bar mata sallahun yaran.
Daga nan suka fita, gaba ɗayansu.
Sai Shatu da Hibba da suke kuka, ganin hakane Ummi ta dawo ta zauna dasu.
Jabeer da Jafar da Umaymah kuwa Side ɗin Mama sukaje, tayi sallama da ita, suka rabu suna hawaye.
Daga nan Side ɗin Lamiɗo da Gimbiyar shi sukaje.
Nan sukayi sallama dasu kana suka fito, inda suka samu Jamil da Jalal sun kawo musu motoci. Daga nan suka shiga suka tafi Airport tare da rakiyar motocin fadawa guda uku ya zama motoci biyar ne suka tafi kaita Airport.
A gida kuwa, da kyar Ummi ta samu ta lallashi Shatu da Hibba da cewa in basuyi shiruba, zata, sa akai Hibba Airport ta tafi da Umaymah.
jin hakane yasa Hibba tayi shiru. Ita kuwa Shatu dama ba kuka mai sauti takeyi ba, zubda hawaye takeyi.
Ƙarfe tara dai-dai jirginsu Umaymah ya tashi zuwa jihar Tsinako.
A gida kuwa tuni Shatu da Hibba sun shiga kuma har sunyi bacci sabida kukan da sukayi.
Ita kuwa Ummi tana falo, saida taga dawowarsu sannan taje ta shiga ɗakinta dan yanzu ta dawo da zama a nan kenan ɗakin da Umaymah ke sauƙa in tazo.
Washe gari ranar asabar kuwa,
haka suka wuni gidan shiru ba daɗi gaba e kewar Umaymah ta hanasu jin daɗin gidan.
Ranar ne kuma duban forko na watan Ramadan.
Tunda magriba tayi, al'ummar musulmai keta cekinta labarin ganin wata.
Wannan ya tambayi wancan wancan ya tambayi waccan.
Jira kawai akeyi aji lbri ko gani.
Yayinda duk irin wannan rana duk inda yanki musulmai suke a faɗin duniya suna jimirin da tsumayin lbri.
A wasu wuraren har matasa maza da dattawan kanyi dandazon da fuskanta yamma dan ganin watan
Har dai akayi sallan magriba babu ƙaƙƙarfan lbrin ganin wata.
Bayan anyi sallan isha'i ne, Sarki Nuruddeen Lamiɗo kenan ya tara hakima shi a fada suna jiran ko akwai ta inda labari zai riskesu.
Kasan cewar ana yanayin damuna ne yasa ba ko ina keda yaƙinin ganin watarba.
Sheykh Jabeer kuwa, wanda ranar bai samu yayi salla a masallacin Masarautar Joɗa ba.
Sabida wata ƴar tafiyar da yayi, sai bayan Isha'i ya dawo.
Kai tsaye Side ɗinsa ya wuce.
Yana shiga falon wayarshi dake cikin al'jihunsa ta fara suwa a hankali.
Gefen Ummi ya iso tare dayi mata sallama.
cikin kula tace.
"Sai yanzu?".
Kai ya gyaɗa mata yana mai amsa wayar.
Sannu da hanya tace mishi.
Cikin sauƙe numfashin alamun gajiya yace.
"Yauwa Ummi sannu da aiki".
Sai kuma ya kara wayar akunnen shi cikin nitsuwa yace.
"Wa alaikassalam".
Ɗan jim yayi kana yace.
"Alhamdulillah".
ya ƙarshe mgnar yana shiga cikin falonshi.
Shatu kuwa dake gefen Ummi shiru tayi tare da binshi da ido.
A can falon shi kuwa zama yayi bisa kujera tare da fara zare al'kyabbar daka hannunshi, wayar na kunnenshi yake cewa.
"Eh Jadda Alhamdulillah rahotanni sun nuna cikin Ɓadamaya al'umma da yawa sunga watan Ramadan.
Kuma nima naga watan Ramadan da idona".
Cikin jin daɗi Jadda yace.
"Alhamdulillah, ko yanzu mun samu gamsassun hujjoji daga bakin salihan bayi,
Dan jihar Tsinako sarki Abudulfata da kanshi ma yaga watar ya sanarmin.
Hakama jihar Noki, Jaltarba, Magom, Shibb, da dai sauran jihohi mu na arewaci anga wata sosai tako ina.
Kana yanzu kuma munyi mgna da Sheykh Abdulkareem shima yace anga wata.
Mu nan jihar Leddi julɓe kusan kowa yaga wata."
gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"To Alhamdulillah. Allah ya nuna mana ƙarshen sa lfy, yasa muribantu da watar al'farma Annabi da Alqur'ani".
Amin Amin Sarki musulmai Jalaluddin, yace.
Kana ya sallameshi.
Daga nan aka bada sanarwan anga wata, inda shi Sarki Jalaluddin ya kira manyan masarautun gargaji yana shaida musu.
Kana manema labarai duk sukayi dandazon zuwa, nan aka sanar tako ina musamman kafafen yaɗa labarai na yanar gizo.
Nan take ko ina ya ɗauka.
Suna zaune a falon suna cikin hira.
Sukaji wani irin ƙara mai firgitarwa da bada tsoro.
darararam-dam sautin ƙarar bindigar toka mai ƙarfin amo.
Wani irin tsalle Shatu tayi tare da motsowa jikin Ummi, tare da toshe kunnuwanta, sabida sake jin ƙaran.
Gaba ɗaya jikinta kerma da kerketa yakeyi,
Cikin tsoro take cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, hasbunallahiwani'imanwakil!".
Da sauri Ummi ta riƙon hannunta datasa ta toshe kunnuwanta cikin ɗaga sauti take cewa.
"Shatu ba komaifa, kada ki razana bindigar sanarda ganin watane! Shaidar gobe zamu tashi da azumi".
Cikin tsinkewar zuciya tace zamo daga kan kujerar ta zauna a ƙasa kusa da sawun Ummi, wani irin duka ƙirjinta keyi didib didib, didib.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Aunty Aysha tsoro haka".
Cikin yamutsa fuska tace.
"Ya kamata ku gayawa duk wani baƙo wannan bahugawar al'adar taku in ba hakaba wata rana tsoro zai kashe irina".
Sheykh da tun ihunta na forko yana bakin corridor yana kallon yadda take karkarwa,
wani irin murmushin muguntane ya tsubce mishi.
Sai kuma ya tsuke fuskarsa kamar bashi yayi gajeren murmushi ba, cikin faɗa yace.
"Nifa bana son sakarci sam bafa na son anamin ihu a ka da hargowa a gida".
Cikin tura baki ta bishi da ido.
Shi kuwa fita yayi yana murmushi a cikin zuciyarshi tare da magar zuci.
"Ga rashin ta ido ga tsoro, ga tsiwa da fitsara ga makirin karaya.
Ai da anyi ta sakin sautin bindigar har sai tayi fitsari a zani".
Da haka ya wuce ya nufi fada,
nan suka fara tattauna yadda lamuran zasu tafi.
Ummi kuwa murmushi tayi ganin irin kallon harara da Shatu ta raka Sheykh dashi.
Cikin murmushi tace.
"Taso ki zauna muyi mgna".
A hankali ta miƙa ta hau bisa kujerar da Ummi take ta zauna, Hibba kuwa, tuni ta nufi Side ɗin Aunty Juwairiyya.
Gyara zama Ummi tayi tana fuskantar ta da kyau,
Cikin nitsuwa tace.
"To Alhamdulillah kinga anga wata gobe zamu tashi da azumi in Allah ya kaimu, akwai ƙarin aiyuka a Side ɗin nan wanda ko da can baya ko Sheykh bayanan yana ajiye komai na buƙatar rayuwa akanyi girki a nan kamar akwai mace, sabida anan su Jalal, Jamil, Hashim Sulaiman Imran Affan in yana nan suke shan ruwa."
To yanzu bana Sheykh ba inda zaije sabida a jerin jadawalin malaman tabsir da ake turawa jihohi bana ba'a turashi ko inaba tunda ya girma ya fara tabsir sau ɗaya yayi azumi a nan shekarar da ciwon Jafar ya tsananta, to anane naga zahirin yadda yake gudanar da al'amuran rayuwarshi cikin Ramadan.
To bana ma. Anan cikin Ɓadamaya zaiyi tabsir ɗin shi.
To aiyukan mu sunada yawa.
Dole kisan yadda tsarin komai ke tafiya."
Cikin sauƙe numfashin ta gyara zama ta fuskanci Ummi da kyau kana a hankali tace.
"To".
Itama gyara zama tayi da kyau kana tace.
"Azumi goma sha biyar zaiyi a nan, ƙarishen 15 ɗin a ƙasa mai tsarki zaiyi su.
Ma'ana zai tafi Umrah.
Sannan yanada masallatai uku da yake tabsir a kullum.
Da safe misalin karfe sha ɗaya na safe zai tafi masallacin jumma'a na cikin kasuwa, a can zaiyi tabsir sai ƙarfe shabiyu saura mintuna goma