Showing 102001 words to 105000 words out of 180927 words

Chapter 35 - GARKUWA Book 1 Original Pdf By Garkuwar Fulani.txt

28 Aug 2025

1838

hankali tace.
"To".
Haka nan taji duk wani yarda na duniya ta sauƙeshi kan wannan kekyawar mata mai fara'ar nan.

A hankali tasa yatsunta ta kamo niƙab ɗin ta ɗin ta yayeshi.

Wasu irin tagwayen numfarfashi Umaymah ta sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!".
Da sauri ta juyo ta ruggume Jakadiyarsu a hankali tace.
"Alhamdulillah Ummin Jabeer itace. Wlh itace".
Cikin wani irin tarin jin daɗi Jakadiyarsu ta ɗan kalli Shatu, tare da yin murmushi mai cike da ma'anoni.

Jakukkunan dake hannunta ta ajiye, kana ta iso kusa da ita ido ta zubawa fuskarta kana tace.
"Ɗiyata menene sunanki?".
Cikin yin ƙasa da ido Shatu tace.
"Aysha".
Kusan a tare sukace masha ALLAH.
Nan Umaymah kam ta juya da sauri ta fita.

Ita kuwa Jakadiyarsu Jabeer shirya mata kayan data shigo dasu takeyi a drower'n.
Tare da bata umurnin taje tayi al'wala.

Umaymah kuwa tana fita kai tsaye Side ɗin Jabeer ta nufa.

Shiru ba kowa, da kamar duk sun tafi masallaci ne.

Aunty Juwairiyya da Hibba kuwa suna sashin Juwairiyyan.
Ummi kuwa na can wurin Shatu.

Kai tsaye ɗakin da nanne masaukin ta, ta nufa.
Bathroom ta faɗa ruwa ta ɗan watsa tare da yin al'wala kana tafito tazo ta kabbarta sallah.

Ita kuwa Shatu zaune take bisa sallayan.
Tunda ta idar da sallan bata tashiba.
Sai kanta data jingina jikin gadon da take gefenshi.
A hankali ta rumtse idanunta tare da motsa laɓɓanta tana karatun al'ƙur'ani cikin sanyin murya, Ummey da Junainah ne suka faɗo mata a rai shine ya sata zubda hawaye wasu na korar wasu.
Kewarsu da begensu, ya tuno mata su Ya Gaini da marigayi ya Lado.
Ummi kuwa itama bisa sallayan take tana lazumi.

A haka har lokacin sallan isha'i yayi.

Jin wata zazzaƙar murya mai matsifar daɗi na karatun.
Hannun tasa ta share hawayenta dan jin karatun takeyi yana ratsa mata zuciya ya tsananta zubar hawayenta.

A hankali ta miƙe itama ta kabbarta sallan isha'i.
Hakama Ummi.

Bayan an idarne. Ummi ta miƙe tsaye ta ninke abin sallan, kana a hankali take taku har kusa da ita.
Cikin sanyi ta zauna bakin gadon tare dasa hannunta tsakiyar kanta a hankali tace.
"AYSHA kuka kikeyi!?."
Da sauri ta jujjuya kai alamar a a tana mai share hawayenta.
Cikin kula Ummi tace.
"Kuka mana kikeyi, gashi kinata zubda hawaye! Kiyi haƙuri kinji ko Aysha ki bar kuka, in kinji kewan mamanki ki kalleni a matsayinta, in kinji kewar yayarki ki kalli Juwairiyya a matsayinta, in kuma yayu maza kikaji kewarsu ki kalli Jalal da Jamil a matsayinsu.
In wani abu na damunki ki gayawa Sheykh, shine mijinki kuma majiɓancin lamuranki in kinji kewar ƙanwa mace ki kalli Hibba a matsayinta,".
Bata hafimtar kalaman wannan matar,
bare tasan me take nufi saboda babu mutun ɗaya da ta sani cikin mutanen data kira mata.
Abu ɗaya ta fahimta Sheykh shine wanda wai tace shine mijine ko majiɓancin lamurane, bata sanshiba bai kuma santaba ta ina zai jiɓanci lamuranta,
Shin ta yaya zata zauna a wannan gidan da tun shigowarta take ganin ababe masu ban tsoro."
Jin tayi shirune yasa.
Ummi shafa bayanta tare da cewa.
"Jikinki na rawa zazzaɓi kikeyi ne?."
Cikin sanyin murya tace.
"A a sanyi nakeji".
Da sauri ta ɗan miƙe tare da cewa.
"To bari in rage gudun A/C'n".
Ragewa tayi kana tazo ta zauna kusa da ita.


Umaymah kuwa tana idar da sallan isha'i, ta miƙe ta dawo sashin Gimbiya Aminatu.
Tayi matuƙar mamaki ganin batun auren Jabeer ya karaɗe masarautarsu gaba ɗaya,
taki wani sashi kawo abincin amarya akeyi.

Ita da kanta da Gimbiya Aminatu sukayi ta shigar da Foodflaks ɗin abincin cikin ɗakin da take suna jerawa a gabanta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer bayan an salla.
Ya fito kamar koda yaushe su Jalal na biye dasu a baya.
Haroon kuwa suna tafiya a jere,
suna cikin tafiya duk suka tsaya fuska a haɗe Jabeer ya juyo ya kalli gefen hagunshi da yaji an dafa kafaɗarshi, Jadda ne ya ɗan kalleshi kana ya kauda fuskarshi ba tare da yace mushi komaiba.
Murmushi Jadda yayi cikin sakin fuska yace.
"Ƙarfe tara dai-dai jirginmu zai tashi. Zamu koma da kawunan naku duka".
Cikin muryar dake nuna cewa yana cikin tsananin ɓacin rai yace.
"Allah kiyaye hanya". Ya ƙarishe mgnar tare da juyawa yaci gaba da tafiyarshi.

Shi kuwa Jadda murmushi ya kumayi, fahimtar Sheykh yana tsananin fushi da baƙin cikin abinda sukayi mishi.

Lamiɗo ne ya kalli Aminin nashi tare dayi mishi alamun ya barshi.
Su tafi.

Daga nan suka juya duk suka nufi, sashin Lamiɗo, inda aka gama shirya manya-manyan Foodflaks a tsakiyar falonshi bisa wani tattausan Turkey carpet mai masifar kyau da taushi.

Nan suka zauna sukayi Dinner sunayi suna hira,
Tare da yaransu.

Bayan sun gamane, suka miƙe dan tafiya Airport sabinda lokacin tafiyarsu ya kusa.
Kusan a tare suke fito zuwa babban falon dake tsakanin side ɗin Lamiɗo dana Gimbiya Aminatu.

Bayan sun zaunane, Sallama yaje ya sanarwa Gimbiya Aminatu cewa Sarki Jalaluddin yana neman Umaymah da Amaryar Sheykh.

Jin saƙon Sarki Jalaluddin daga bakin hadimanta da Sallama ya isarwa saƙon ne yasa ta miƙe ta nufi ɗakin da Umaymah take.

A cikin ɗakin kuwa, cikin kula Umaymah take gabatarwa Aysha da abin ci dana taɓa ka lashe dana motsa baki.
Adda Rumana kuwa kamar tasa mata abinci har bakinta,
Itako Aysha kanta a sunkuye, ta zubawa kulolin abincin ido tana ganin ikon Allah dake wanzuwa cikin kayayyakin cimar, da sai dai gidan wane da wanen.
Fahimtar kunya ne ya hanata cin komai yasa suka fito falo suka barta, da Umaymah kawai wacce taketa janta a jiki ganin hakane yasa, ta ɗan yarda taci abincin kaɗan.

Suna zaune a nanne Gimbiya Aminatu ta shigo ta sanar musu saƙon sarki Jalaluddin nan, Umaymah ta sake saka mata wata al'kyabbar cikin jin daɗi tace.
"Aysha ki saki jikinki dani, ki gaya min dukkan abinda kikeso, yanzu kinga wurin kakanunki zan kaiki.
Sarki Jalaluddin mahaifina ne, wanda kuma shine mahaifin maman mijinki, ɗaurin auren sukazo shida yayunmu da ƙannenmu maza yanzu zasu koma jiharmu ne.
Kinga wannan kuma Gimbiya Aminatu itace ta haifi mahaifin mijinki.
Kana Sarki Nuruddeen ɗan Sarki Bubayero jikan sarki Joɗa, shine kakan mijinki.
Mu ma mahaifiyarmu na Raye mijinki ne yasa mata suna Sitti, tana jiharmu ita bata samu zuwaba sai daga baya zata zo".
Ajiyan zuciya tayi tare da kamo hannunta kana taci gaba da cewa.
"Mijinki ɗan babban family ne gaba da bayanshi.
A ƙalla zai ɗaukeki shekaru goma cikin masarautar Joɗa data musulmai baki gama sanin adadin dangi da yawan yan uwan mijinki ta gefen mahaifiyarshi da mahaifinshi ba.
Yanzu muje su ganki ki gansu."
Cikin sanyi tace.
"To Aunty".
Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
"Ba Aunty ku bace, Mijinki Malam Jabeer yafi yarda da ita fiye da kowa a dangin mahaifiyarshi, Umaymah yake kiranta".
Kai ta gyaɗa tare da mgnar zuciya.
"Ikon Allah".
Ita kuwa Umaymah murmushi tayi kana tana hannunta suka fita.
A falo suka samu Jakadiyarsu, da sauri Umaymah tace.
"Yauwa kinga wannan itace Jakadiyarsu, itace ta rainesu tun suna yara, bayan mahaifiyarsu babu wanda yasan halin Jazlaan sama da ita a cikin wannan masarautar, ki kasance mai bin umarnin ta, domin itace idonki cikin wannan masarautar, Jazlaan a matsayin uwa mahaifiya yake kallonta ba baiwar gidansu ba".
Cikin nitsuwa Aysha ta gyaɗa kai tare da cewa.
"Nagode".
Ita kuwa Ummi murmushi tayi tare da bin bayansu.

Suna isa bakin ƙofar tayi musu iso bayan ta shiga ta sanar musu da isowarsu.

A hankali suka shiga, cikin nitsuwa take bin takun Umaymah.
Ita kuwa Umaymah har gaban Sarki Jalaluddin da Sarki Nuruddeen taje da ita,
cikin shaƙuwarta dasu, ta ajiyeta a gabansu tare da cewa.
"Jadda ga amaryar Sheykh Jabeer a sanya musu al'barka".
Murmushi yayi tare da kallon Aysha. Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Allah ya sanya al'khairi ya basu zaman lafiya. Allah yasa tazo mana da hasken da zai kore duhun daya meye hasken idanunmu".
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu.
Uncle Abdulkareem ne ya ɗan kalleta cikin sanyi yace.
"Allah yayi miki al'barka dake da mijinki ya baku zaman lfy mai ɗorewa".
Kanta ta ƙara sunkuyawa,
Ita kuwa Umaymah matsota tayi tare da cewa.
"Kinga ɗan ɗago kanki ki kallesu.
Kinga ga Mahaifina. Ga Sarki Lamiɗo".
Sai kuma ta nuna Abba dake zaune cikin murmushi tace.
"Ga wannan shine mahaifin Jabeer mamanshi kuwa sai gobe a bisa ƙaidar masarautar keda shi Jakadiyarsu da Sallama zasuyi muki jagora ku zagaya cikin masarautarsu baki ɗayansu a nuna miki ahlinsu to da ɗakin mamanshi za'a fara kaiki".
Kinga wannan shine babban Yayanmu sarki mai jiran gado.
Ga kuma wa ƙaninmu Abdulmumin."
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
"A a Khadijah a rana ɗaya kikeso ɗiyar taki tasan komaine? Ai abun da wuya, dole sai a hankali zata gane mu".
Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa.
"Hakane kam. Amman gwara an gabatar mata da manya".
Sarki Jalaluddin ne ya gyara zamanshi tare da cewa.
"To Khadijah mu yanzu zamu wuce, ke kuma sai yaushe?".
Murmushi tayi tare da kallon gefen damanta inda Haroon ke zaune da wani kekkyawa mutun mai matsakaici shikara.
Mi kama dashi wanda bisa dukkan alamu babanshi ne.
Kauda kanshi yayi daga kallon da Umaymah keyi mishi, cikin ƙasaita alamun shima jinin sarauta ne, yace.
"Ni kada ki wani kalleni, bance komaiba".
Murmushi dattawan sukayi baki ɗayansu, Haroon ma murmushin yakeyi.
Ita kuwa Umaymah kauda zance tayi da cewa.
"Yauwa Aysha kinga wannan shine Haroon ɗan uwa kuma aboki amini abokin faɗan Jabeer.
Akwai kuma ɗan yayanmu Ibrahim shine shaƙiƙin Jabeer shi yana Cairo, amman kwanan zai dawo ki ganshi."
Jadda ne ya kuma tsareta da cewa.
"Khadijah yaushe zaki koma?".
Cikin sanyi tace.
"Jadda in Abban Haroon ya amince zanyi wata ɗaya rak, sabida ganin yadda lamuran zasu tafi.
tsakanin yaran, ita kanta Aysha tana buƙatar makusanci tare da ita, sabida baƙonci a irin gidajenmu abune mai wuya ga wanda ba irin gidajen ya taso ba".
Murmushi Abban Haroon yayi tare da cewa.
"Ba laifi na Amince, Amman bazaki ɗauki azumi a nan bada".
Da sauri tace.
"Na yarda".
Haroon ne ya ɗan juya idonshi alum lissafi kana yace.
"Ke nan sati uku zakiyi tunda azumin saura wata ɗaya".
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa,
Jadda ne ya kalli Jakadiya tare da bata umarnin su tafi ita da Aysha.
Gane abinda yake nufine yasa ta kamo hannun Aysha suka fita. Gimbiya Aminatu na biye dasu a baya.

Gyaran murya Jadda yayi bayan sun fita, cikin nitsuwa da girma ya kalli Umaymah tare da cewa.
"Alhamdulillah Khadijah, aure dai an ɗaura, duk da tarin tsana da ƙin abin da ɗan naki keyi.
Haƙiƙa baya son wannan abun da akayi mishi. Naga fushi da tashin hankali mai tarin yawa a ƙwayar idanunshi da fuskarshi.
Ina da yaƙini bisa halin Jabeer in ya tsani abu tofa ya tsaneshi kenan har gaban abadan, wannan shine babban tashin hankali na,
Sabida yanada lafiya da tsayuwa kan kaifi ɗaya. Ya gayawa kakarshi Sitti babu wani gari na duniya da yakejin ya tsana sama da wannan garin. Yace baya son garin da mutanen garin. Sabida anci mishi zarafi a garin a gaban kafurai an tozarta shiga ta addinin Musulunci".
Shiru sukayi baki ɗayansu, tabbas sun san hakane mgnar Jadda.
shi kuwa Jadda a hankali yaci gaba da cewa.
"Yanzu kubar Yarinyar a ta kwana a nan.
Kana a ɗan ɗaga kafa har sai an gyara mata inda zata zauna, kamar ko wacce amarya.
Sannan kada kuyi mishi mgnar auren bare ita yarinyar,
in anyi haka fushinsa bazai tsanantaba, zaici gaba da al'amuran rayuwarshi, tunda shi mutum ne mai ibada da kuma aiyuka".
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"In dai baza'ayi mishi mgnarta ba, to wallahi mancewa zaiyi da ita da babinta ma gaba ɗaya".
Lamiɗo ne ya gyara zama tare da cewa.
"Ya isa".
Murmushi Umaymah tayi sabida ta lura har yau su Lamiɗo basu gama sanin Jabeer da halaiyarsa ba.

Shi dai Jadda nan ya jadadda musu cewa, kada suyiwa Sheykh Jabeer mgnar sai an gama gyara komai na sashinta.
Ko gaisuwar su bari sai bayan kwana uku a zagaya da ita cikin Masarautar.

Nan dai sukayi sallama suka, tafi baki ɗayansu.

Suna tafiya, Umaymah ta koma ɗakin da Aysha take, nan ta samu Ummi na zaune da ita. Nan ta zauna ta suka ɗan yi hira ganin alamun gajiya da bacci a tattare da itane yasa, sukayi mata saida safe suka fita suka tafi.

Ratsawa sukayi wurin Gimbiya Aminatu suka mata saida safe kana suka fita suka tafi.

Cikin tsananin jin daɗi suke tafiya, har suka iso bakin.
Mashigar sashinsa, cikin nitsuwa sukaci gaba da tafiya.
Shiru ba motsin komai suna gab da isa bakin ƙofar, suka tsaya cikin zaro ido, suka kalli Laminu da Gimbiya Saudatu, cikin haɗe fuska da zafi Umaymah tace.
"Aoozubikalimatillahi taaa'ammati minshirin makalaƙa!."
Cikin tsantsar tsanarta Gimbiya Saudatu tace.
"A kanki hegu masu jajayen kunnuwa".
Tana faɗin haka taja hannun Laminu suka fita.
Su kuwa Umaymah da sauri sukayi ciki.

A falo suka tsaya. Ba kowa a falon haka yasa tayi sauri ta nufi arear'n Side ɗin Jabeer, a falo ta samu Haroon konce bisa kujera.
Yana ganinta ya tashi zaune.
Cikin gimtse dariyarshi murya a hankali yace.
"Yau duk kayan ahlin masarautar Joɗa sai an yagesu baki ɗayansu."
Ya ƙarishe mgnar yana nuna mata ƙofar ɗakinshi.

A hankali ta kutsa kai cikin ɗakin tare da yin sallama.
Can ta hangoshi kan gadon yana konce rigingine, idonshi a lumshe,
a hankali takeyin taku tana nufo inda yake.
tare da mgnar zuci.
"Wato harda sharrin Haroon zayiwa ɗan Umaymah".
A hankali ta zauna bisa bedside drower'n. Idonta ta sauƙe bisa goshinsa, cikin mamaki ta juyo ta fuskanceshi da kyau ganin yadda Goshinsa ke....!





By
*GARKUWAR FULANI*Wata iriyar zuface ke tsastsafo mishi bisa goshinsa,
Kamar an watsa mishi ruwa.
Ya kamo lip ɗin shi na ƙasa yana taunewa.
Hannunshi dake cikin blanket ta zubawa ido.
Dan son gano abinda yakeyi,
shiru tayi sawon 5 minute kana, a hankali ta ɗaura tafin hannunta kan goshinta,
tare goge mishi zufar, daketa tsastsafowa duk da sanyin A/C dake ratsa ɗakin.
Idonshi ya saisaita lumshe su da yayi, ya sani Umaymah ce.
sabida babu mai shigar masa ɗaki kai tsaye sai ita.
Babu kuma mai taɓa mishi goshi haka sai ita.
Cikin kula tace. "Jazlaan!".
A hankali ya gama buɗe idanunshi da sukayi jazir alamun tarin ƙuna da yakeji a ransa.
A hankali tace.
"Jazlaan!." Ta kuma kiranshi a karo na biyu.
A hankali ya motsa lips ɗin shi alamun zai amsa mata.
Amman Ina zafin da zuciyarshi keyi ya danne harshensa hafimtar hakane yasata, nuna damuwarta a hankali tace.
"Kaci abinci?". Ƙarya ba ɗabi'arsa bace ba kuma halittarsa bace, duk ɗacin gsky zai faɗeta, bare a kan kashi.
Kanshi ya girgiza alamun baiciba.
Cikin sanyi tace.
"To Muje kaci koda abu mara nauyi ne!."
Da ƙarfin ya fizgo mgnar.
"Bazan ci ba".
Ta sani yadda yayi mgnar, ta kubce masane, dan in ransa a ɓace yake baya mgna, ɓacin ran mai limini kenan babu faɗe-faɗe bare hargowa ko buge-buge.
Sanin ko ya zatayi bazai cin bane, kamar yadda ya faɗa mata yasa,
ta miƙe a hankali kanshi ta shafa tare da cewa.
"Saida safe".
Kai kawai ya iya gyaɗa mata,
Haka ta fara tafiya, tana kallon yadda yake motsa hannunshi cikin blanket tabbacin. Wani abun yake yagewa.

Yadda ta bar Haroon haka ta sameshi saida safe tayi mishi kana ta wuce ta tafi.


A can Rugar Bani kuwa. Kamar yadda Ba'ana ya ɗaukarwa kanshi al'ƙawari haka ya bar ƙasar ya nufi ƙasar Cameroon Kai tsaye Yahunde ya nufa, cikin rugagen Fulani, yana tafiyarne da ɗan sauran tsafi da sihirin dake jikinsa.

A haka ya nausa cikin ƙasar Cameroon da yake jihar Ɓadamaya tana bakin bodar ƙasar ne.


Fulanin Rugar Bani kuwa, a daren wannan ranar sukayi gangamin ramuwa, suka faɗawa ƙauyukan kafuran ƙabilun ɓacamawa dake cikin Shikan da kewayenta.
Allah ya basu nasarar yaƙan kafuran nan.
Har suka samu damar ƙona ƙauyem Bonon wanda shine zuciyar ƙabilar ɓachama, kamar yadda Abuja take zuciyar Nigeria.
Cikin daren suka ƙona ƙauye dama dodon tsafinsu Bonon da suka ɗauka a matsayin Ubangiji su sun ƙonashi sun ɓadda shi a doron duniya sai dai tarihinsa.

Wannan labarin shine labarin.
Da gidajen rediyo dana tv da jaridu sukayi.
Breakfast dashi yayinda akayita kuzuzuta cewar Fulani sun zama ƴan ta'adda sun farma garuwa da yaƙi.
Uhummm wannan shine halin da Fulani ke rayuwa a ciki. A zalimcesu, kaji cib duniya babu mai yin mgn su kai ƙorafinsu a koresu. Gwamnatin kasar data jiha suyi kamar basujiba. In fulanin sun rama na lokaci ɗaya sai asa musu sunan ƴan ta'adda ko yan tada zaune tsaye, har ana ikirarin korarmu.😭😭😭

Hankalin ƙabilun Ɓacamawa dake cikin Shikan duk suka ari ta kare.
Hausawa da Fulani kuwa kowa ya koma, cikin gidansa.
Domin Allah ne yabi kadunsu.

Sarkin Shikan da kanshi yayi masifar girgiza da yawan da Fulani sukayi cikin garinshi da kewaye.
Gashi an ƙone dodon tsafinsu nasu kuma babu abinda ya samu fulanin.
Hakane yasa shi kanshi ya arce, sai abu ya lafa ya dawo.


Su kuwa Fulani bayan sun gama.
Suka tsaya suka bawa yaransu da tsoffinsu mafaka, domin su basu kashe yara da tsoffi da mataba.
Anyi an gama, kafin hukuma tazo, ta ƙara sai saita Komai.


A cikin masarautar Joɗa kuwa. Washe gari da safe.
Lbrin ya rinski Sarki Nuruddeen, shine ya bada umarnin kada a kama bafulatani ko ɗaya.

Aysha ce zaune gaban Umaymah Aunty Juwairiyya na gefenta ita da Hibba, cikin kula Umaymah tace.
"Yauwa Aysha kinga wannan ki ɗauke ta matsayin yayarki ita ɗin yar babban Yayanmu ne wanda na nuna miki jiya.
Mijinta kuma ya'yan Jabeer ne, Side ɗinta na kusa da naku.
In kinga duk wani abun da baki fahimta ba ki tambayeta, in kin gaji da zaman kaɗaici zaki iya shiga wurinta, da wurin Mamanku, da kuma nan wurin Gimbiya Aminatu".
A hankali ta ɗan kalli Aunty Juwairiyya, tare da cewa.
"Ina kwana Aunty". Cikin jin daɗi Aunty Juwairiyya tace.
"Lfy lau ya baƙunta". A hankali tace.
"Alhamdulillah!".Hibba ce ta ɗan tsuke baki cikin sanyi tace.
"Shike nan ai, an gabatar mata da kowa sai ni aka ware".
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"To Aysha ga Hibba wutar Umaymah, duk family itace auta a jikokin Sitti na nan ƙasar".
Murmushi ta ɗan yi sabida ganin yadda Hibba tayi sai Junainah ta faɗo mata a rai.
Ita kuwa Hibba motsata tayi tare da cewa.
"My happiness".
Cikin murmushi Aysha ta nuna kanta, alamun "Nice my happiness?".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Yes haka Umaymah tace wai kece farin cikin ahlimu da izinin ubangiji".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta.
Haka nan taji tana jin sonsu a ranta, Especially Umaymah da Hibba.
Aunty Juwairiyya kuwa da Ummi breakfast Suka gabatar mata, kana suka fita.
Umaymah da kantane ta haɗa mata tea mai kauri ita da Hibba kana ta zuba musu abincin da Aunty Juwairiyya ta kawo musu tare da cewa.
"Bismillah kuci abinci".
tana faɗin haka ta miƙa ta fita,
Ita kuwa Hibba da tsauri ta gyara zamanta tare da ɗaukan Fork ta matso gaban plate ɗin da aka zuba mata soyyyan dankali da kwai, hannun tasa ta soki guda biyu tare da ɗagowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login