Showing 162001 words to 165000 words out of 180927 words
Chapter 55 - GARKUWA Book 1 Original Pdf By Garkuwar Fulani.txt
tare da kife tafin hannun ta kan goshin Aysha da yake kamar wuta.
Da sauri ta zauna kan Bedside.
Cikin kula ta kamo hannunnta mai ciwon.
Da sauri ta buɗe idonta tare da tashi zaune, murya na rawa tace.
"Wayyo Ummey na".
Cikin tausayawa tace.
"Afwan hannun yana ciwo ne?".
Kai ta gyaɗa mata alamar eh.
Ita kuwa ido ta zuba mata tana kallon kekyawar fuskarta tace.
"Dame kuma yake miki ciwon?".
A hankali tace.
"Kaina sai kuma zazzaɓi da hannun".
Ɗaya hannunta mai lafiyar ta kamo tare da cewa.
"Shi wannan baya ciwo ne".
"Eh baya yi".
"To faɗuwa kikayi ne hannun yaji ciwo".
A hankali tace.
"A a haka kawai yake ciwo".
Jakarta ta jawo tana kallonta.
Ta buɗe.
abubuwan buƙatar ta, ta ɗauka.
Jininta ta ɗiba, kana.
Ta gwada BP'n ta a take.
Bata da matsalar hawan jini.
Bugun zuciyarta ta gwada.
Shima Normal.
Ganin hakane ta kalli Ummi tace.
"Zan tafi zamuje Valli Pharmacy.
Zan bawa Affan magunguna ya kawo mata, tasha.
Gobe da zafe zan zo.
Ni yanzu asibiti zan wuce."
Cikin gamsuwa da hakan Ummi tace.
"To mun gode Dr Kubra a gaida yara".
Murmushi tayi jin Aysha na cewa.
"Banda allura ko?".
Kai ta gyaɗa kana ta fita.
Koda sukaje da kanta ta shiga ta sai magungunan ta bawa Affan.
Shi ya wuce gida ita kuma ta nufi asibitin.
Cikin ikon Allah kuwa datasha mgnin zazzaɓin da ciwon kai ɗin ya ɗan lafa.
Har ta samu tayi bacci.
A nan Ummi ta kwana a ƙasa.
Hibba na sama gefenta.
Kamar dai randa ta faɗi a ɗakin Sheykh.
Washe gari da safe, kuma tana tashi ta tashi da ciwon hannun.
Kuma bai kumbura ba bai kuma yi ja ba.
Zazzaɓi kuma da ciwon kai da sauƙi.
Bayan Ummi ta gama aikin kitchen ne tazo da kanta ta haɗa mata ruwan wonka.
Ta shiga.
Sannan ita kuma ta fito mata da zani rigar atamfa mai gajeren hannu da maya finshi, da siket da bra and pant.
A cikin bathroom ɗin kuwa,
gaba ɗaya ta kasa yin yadda takeso.
Sabida ko motsa hannun tayi sai taji kamar ta ɗaura hannun a kai tayi ta kurma ihu.
Gashi shine hannun dama, haggun bai iya abubuwa sosaiba.
Cikin tsoro da zubda hawaye take cewa.
"Wayyo Ummey na, shike nan zan zama mai hannu ɗaya,
Wa zai taimaka min bakya kusa Junainah bata nan.
Ya zanyi iyi wonka inci abinci".
Ta ƙarishe mgnar tana goga sabulu a jikinta da hannun gadun.
A haka dai tayi wonkan a karkace
Koda ta fito.
Dole siket kawai da pant ɗin tasa,
bra ɗin barinshi tayi sabida bazata iya juya hannun ta saƙalashi ba.
Rigarma da kyar ta sata nanma saida tai hawaye.
Yunwa takeji kamar zai kasheta,
Hakane yasa ta yafa gyalen.
Ta nufi falon.
A gefen Ummi ta zauna.
Da sauri Ummi ta kalli Hibba dake Dinning area tace.
"Hibba kawo min tray'n nan."
"To". tace kana ta ɗauko tray'n.
A gabanta ta ajiye.
Tea Ummi ta haɗa mata, ta miƙa mata cup ɗin.
Da sauri tasa hannun hagun ta amsa.
Kana ta kai bakinta dan har wani duhu-duhu take gani.
Bakinta ta nufa da kofin.
Amman sai taji abin a karkace hannun kuma sai rawa yakeyi.
Cikin rawan hannun ta manna kofin a bakinta.
Idonta ta ɗan rufe, sabida zafin shayin.
Daurewa tayi ta fara zuƙanshi tanayin abin a karkace.
Hannun daman kuwa shima rawa yakeyi.
Cikin sauri ta shanye tea ɗin.
Wani na ɗan bin gefen lips ɗinta, sabida a karkace kofin take.
Ajiye kofin tayi tare dasa hannun hagun ta goge baƙin ta.
Sam tea ɗin bai isheta ba,
dan jikinta sai rawa yakeyi alamun yunwa.
Fahimtar hakane yasa Ummi sake haɗa mata wani tea ɗin ta miƙa mata cup ɗin tare da cewa.
"Amshi ki ƙara sha kafin Dr tazo".
Cikin sanyi tace.
"Hannuna ya gaji Ummi ajiye min shi in ɗan huta."
Ajiyewan tayi kana ta jawo Foodflaks ɗin,
soyayyan Arish da kwai ta saka mata a plate kana tasa mata.
ferfesun kaɗan a ɗan side plate mai ɗan zurfi.
Kana tace.
"To kici wannan sai kina ɗan shan tea ɗin a kai".
Kallon plate ɗin tayi.
Cikin sanyi tasa hannu ta ɗauki fork sokawa tayi a cikin plate ɗin.
A karkace ta kaishi bakinta tare da dawo da cokalin ta ajiyeshi.
Kana ta fara taunawa. Tare da kora tea ɗin.
A haka dai ta ɗanci kana ta ture plate ɗin tace.
"Alhamdulillah".
A hankali Ummi tace.
"Ki ƙara mana kiga ko rabinshi baki ciba.
Gashi ferfesun ko taɓawa bakiyi ba".
Cikin maida numfashi, tace.
"Alhamdulillah Ummi na ƙoshi".
Kai ta jinjina mata.
Hibba ce ta kalleta tare da cewa.
"Sannu Aunty Aysha".
Kai ta gyaɗa, tana mai taune lip ɗin ta na ƙasa.
Jamil da Jalal ne suka iso tsakiyar falon,
Cikin kula Jamil yace.
"Aunty Aysha ya jikin naki?".
"Da sauƙi". tace a taƙaice
Jalal ne ya ɗan kalleta ganin yadda taketa tsastsafo zufa yace.
"Sannu Allah ya sauwaƙa".
Amin tace.
shi kuwa maida dubanshi yayi kan Hibba yace.
"Ƙara gudun AC mana".
Cikin sauri Hibba ta miƙe ta ƙara ƙarfin AC'n
Daga nan suka fita, sashin Affan suka nufa, koda sukaje basu daɗe ba sabida sun samu Mami Bata nan bata dawo gidansu ba.
Ummi kuwa miƙewa tayi tare da cewa.
"Hibba zauna da ita. Bari inje in sanarwar Lamiɗo halin da ake ciki".
To Hibba tace. Har Ummi ta juya zata tafi sai kuma ta tsaya, jin wayarta na rigin.
Amsawa tayi da sauri ganin Umaymah ce.
Bayan sun gaisa ne Umaymah ke ce mata.
"Ya jikin Jazlaan da Aysha.
Jiya Jalal ke gaya min wai duk biyu basu da lfy".
"To Alhamdulillah jiki da sauƙin, shi kam Sheykh naga ya wore sosai.
Amma fa Aysha kam, sai hannun yayi kamar ya lafa sai kuma kiga ta fara haɗa zufa, can kuma sai ya fara tsikarinta hannun yayi zafi jau kamar wuta, sai kiga yanata karkarwa."
Cikin tsoro Umaymah tace.
"Subahanallahi, abin har hakane, to wai hannun ya.
Kumɓura ne ko me yayi".
Da sauri tace.
"Wlh kuwa bai kumburaba ciwo kawai yake mata."
"Subahanallahi, haɗani da ita".
Da sauri tace to. Kana ta miƙawa Aysha wayar.
Ita kuma ta nufi Sashin Lamiɗo.
Nan ta sanar wa Gimbiya Aminatu, a take tayi mata jagora ta gayawa, Lamiɗo abinda ke faruwa da kanta.
Tare suka koma da Gimbiya Aminatu.
Ita kuwa Aysha cikin wahala tace.
"Ina kwana Umaymah".
"Lfy lau Aysha ya jikin naki?".
Cikin sanyi tace.
"Da sauƙi".
Cikin kula tace.
"To Allah ya ƙara mana sauƙi.
Bari zanyiwa Jazlaan mgn ku tafi asibiti".
Cikin rawan murya tace.
"Umaymah ba ciwon asibiti bane bafa".
Cikin tausayawa tace.
"To bari zanyi mgna da Lamiɗo, karki damu in sha Allah zaki samu lfy kinji ko ɗiyata".
To tace tana zubda hawaye.
Tana katse kiran tayi mgna da Lamiɗo, ta gaya mishi yadda sukayi, yace to ba matsala.
Ita kuwa Ummi da Gimbiya Aminatu da Dr Kubra kusan a tare suka shigo.
Zuwa lokacin kuma zogin hannun ya tashi.
Sai jujjuya hannun takeyi tana cewa.
"Wash- wash Allah na wash Ummey na".
Shigowar sune Yasa ta miƙe tsaye gaban Ummi ta tsaya tana jujjuya kai da taune baki tana ɗan bubbuga sawunta a ƙasa.
Da sauri Ummi ta kamo hannun ta mai lfyan ta ajiye ta kan kujera.
Da sauri Dr Kubra ta matso tare da cewa.
"Subahanallahi hannun ne".
Hibba ce ta gyaɗa kai cikin zubda hawaye tace.
"Eh".
Gimbiya Aminatu kuwa gefensu ta zauna, hakane yasa Aysha ta ɗaura mata hannun kan cinyarta tare da zubda zafafan hawaye tanayi tana haɗa zufa.
A hankali Dr Kubra ta kai hannun ta kamo hannun tana mai cewa.
"To kodai kin taɓa karyewa tsohon karaya ne ya tashi".
Wani irin zillo Aysha tayi tare dasa ƙara ta miƙe tsaye gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Dai-dai lokacin kuma, Sheykh Jabeer ya fito cikin shigar jallabiya da al'kyabbar.
Ido ya zuba mata ganin yadda take karkarwa ga kuma hawaye dake shatata a fuskarta.
Ga zufa da ya jiƙata cakab dan azaban zafi."
Da sauri Dr Kubra ta motso kusa dashi cikin tausaya mata tace.
"Dr ko zamu wuce asibiti da itane".
Da sauri Dr Kubra da sauran duk suka zuba mata ido jin tana mgn murya na rawa take cewa.
"A a ni bazan je asibiti, bazan jeba, bazan jeba".
Kanshi ya girgiza tare da taɓe fuska kana yace.
"To ai shike nan kunji ko".
Gimbiya Aminatu ce, ta miƙe ta kamota
Zaunar da ita tare da cewa.
"Aysha zauna ko".
Kai taketa juyawa, hawaye na zuba.
Shi kuwa Sheykh Jabeer fita yayi.
Dr Kubra kuwa, cikin tausayawa tace.
"To Ummi ciwon kan da zazzaɓin kam da sauƙi ko".
A hankali tace.
"Eh sosai ma kuwa. Yanzu hannun ne kawai ke ciwo".
Numfashin ta fidda tare da cewa.
"Zan turo Dr Imam likitan cancer ne zai zo ya duba hannun."
Cikin sanyi Ummi tace to.
Daga nan Dr Kubra ta fita.
Gimbiya Aminatu kuwa Hibba ta kalla tare da cewa.
"Ke Muhibbatu kira min Umaymah".
To tace kana ta kira mata ita.
Bayan sun gaisa ne tace.
"Khadijah ki kira Jabeer kiji me zaice ayi kan ciwon yarinyar nan, ya fito ya wuce ko kallo bamu isheshiba bafa nason iya hege".
A hankali Umaymah tace.
"Kiyi haƙuri Gimbiya in sha Allah zanyi mgna dashi kuma ma nayi mgna da Lamiɗo yace gobe zai shigo da mai magani. Tunda tace bata son asibitin."
To tace kana ta kashe kiran
A wannan ranar dai haka ta wuni da hannun. in anjima ya lafa anjima kaɗan ya taso.
Haka kuwa da dare ta kwana ita da Ummi ba baccin kirki, domin kuka takeyi sosai sabida azabar da takejin.
Washe gari ma haka ta Wuni Dr Aliyu da kanshi ya shigo ya dubata.
Da yamma Lamiɗo da Galadima da Sarkin bakan masarautar suka shigo.
Bayan sun gaisane Sarkin Bakan ya duba hannun sai yace.
"Laah ba matsala ai wannan abu mai sauƙine bari yanzu zan baku mgnin sai dare in zata konta ku shafa mata a hannun.
A kuma bata tasha, da izinin ubangiji zatayi bacci lfy".
Cikin jin daɗi Ummi ta amshi mgnin tare da cewa.
"Mun gode, Allah ya kaimu daren."
Amin Amin sukace.
Kana Lamiɗo ya tashi sannan suma suka tashi suka bi bayanshi.
Shi kam Sheykh baima san anyi hakaba.
Ƙarfe takwas na dare. Ummi na zaune gaban Aysha daketa zubda hawaye tare da karkarɗa hannun.
Maganin da sarkin bakan ya basu ta kwaba da ruwan zafi kamar yadda yace musu.
Kana ta jiƙa ɗayan da ruwan ɗumi, da kuma citta guda uku.
Miƙa mata tayi tare da cewa.
"Sannu Aysha amshi kisha ko, Allah ya baki lfy".
Da sauri tasa hannu ta amshi kofin a karkace ta kafa kofin a baki ta shanye ruwan fes.
Kana ta miƙawa Ummi ƴan ƙwaryar.
Kana ta miƙa mata hannu mai ciwon cikin rauni tace.
"Gashi Ummi shafa min".
Ta karashe tana zubda hawaye.
Cikin tausayawa Hibba tace.
"Sannu Aunty Aysha".
Kai ta iya gyaɗawa.
Ita kuwa Ummi a hankali ta fara shafa mata mgnin.
Saida ta shafe hannun duka, sannan ta ɗago ta kalleta tare da cewa.
"Allah yayi mana mgni".
Amin tace.
Tare da miƙewa tsaye, hannunta mai lafiyar tasa ta tallabe mara lfyan da ta fara jin wani sabon abu na tsikararshi.
A hankali ta rinƙa taku, har taje gaban dreesing mirror.
Kana ta juyo a hankali ta dawo bakin ƙofar ɗakin.
Cikin kula Ummi tace.
"Sannu ko Aysha zoki zauna ki nitsu".
Kai ta kaɗa ba tare da ta bar zirga-zirgan ba.
Hibba kuwa ido kawai ta zuba mata, tana binta da sannu.
Cikin sanyi ta kuma juyowa hawaye na kwaranya daga cikin manyan fararen idanunta da suka juye zuwa ja.
A hankali ta fara salati tare da kiran sunan Allah.
Jikin gini ta jingina kanta tare da sakin shessheƙan kuka mai cike da azaba murya na rawa take cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun.
Hasbunallahuwani'imal wakil, la haulawala ƙauta illabillah.
Wayyo Ummey na, Wayyo Bappa na, zan mutu baku sani ba."
Wasu zafafan hawaye masu ɗumine suka zubowa Ummi saboda tsananin abin tausayi da ta gani a tare da yarinyar.
Hibba kuwa cikin kuka ta kira Umaymah tana kuka tace.
"Umaymah Aunty Aysha tanata kuka tana cewa, zata mutu Ummeyn ta bata samiba, tunda aka shafa mata mgnin da sarkim baka ya bayar bata sake zamaba sai zirga-zirga takeyi".
Cikin kiɗima Umaymah tace.
"Innalillahi. Ina Ummin ku? bata waya".
Cikin kuka tace.
"Ummi ma kuka takeyi".
A hargitse Umaymah tace.
Ki bata waya nace dan ubanki".
Da sauri ta miƙawa Ummi wayar.
Cikin raunin murya Ummi tace.
"Khadijah Aysha ba lfy, azaba yayi mata yawa fa. Ta ƙasa zaune ta kasa tsaye".
Cikin sauri Umaymah tace.
"Ina Jazlaan!?."
Cikin sanyi tace ban san inda yajeba, amman tunda magriba bai dawoba."
Da sauri Umaymah ta katse kiran
Number Sheykh tayi ta kira.
Sai dai duk layukanshi suna shiga baya ɗagawa.
Cikin tashin hankali ta kuma kiran.
Lamiɗo tayi mishi bayani.
Anan take Lamiɗo ya kira sarkin baka yace mishi, ga halin da ake ciki.
Sai ya bawa Lamiɗo tabbacin.
Eh dama zaiyi iya zafin da anjima zai lafa.
To nan Lamiɗo ya kira Umaymah ya gaya mata.
Ita kuma ta kira Ummi ta gaya mata yadda Lamiɗo ya gaya mata,
ta ɗora da cewa.
"In sha Allah gobe zan biyo jirgi inzo.
Kuma ko ban samu jirgiba Haroon zai kawoni a mota, zanzo Ummin Jabeer hankalina yayi matuƙar tashi kan matsalar nan".
Cikin kukan tausayi Aysha daketa ɗan bubbuga sawunta tana cewa.
"Wahyyy wahhyy".
Tace.
"Eh gsky kam kizo, Umaymah ɗazu ko Hajia Mama da tazo saida tayi ta kukan tausayin Aysha".
Katse kiran Umaymah tayi.
Tare da wucewa turakan Abban Haroon nan ta gaya mishi abinda ke faruwa.
Nan take ya bata izinin zuwa.
Sheykh Jabeer, kuwa sai ƙarfe sha ɗaya saura ya shigo gidan.
Lokacin kuma Ummi ta rufe ƙofar ɗakin Aysha sabida hanyar fita take kamawa.
To hakane yasa sam baiji motsin komaiba ya wuce Side ɗinsa.
Wonka yayi kana yayi nafilfilinshi sannan ya kwanta baccin.
Ummi kuwa da Aysha kwanan tsaye sukayi.
Aysha tana kuka tana zirgani.
Sai can gabanin asuba irin iskar sanyin asuba ɗin nan ta fara kaɗawane wani sassanyan baccin azaba da wahala ya saceta.
Hibba ma sai lokacin tayi bacci.
Nanne Ummi ta samu ta koma ɗakinta tayi al'wala.
Jin ana salla a masallacin ne yasa tace sai tayi salla taje ta tashesu kafin nan ta ɗanyi bacci kaɗan.
Bayan an idar da sallane.
Ta miƙe a hankali cikin magagin baccin da batayi ba, ta nufi ɗakin Aysha.
A hankali ta wuce bathroom.
Abun buƙatar yin wonka duka ta motso matashi kusa,
Hatta makilin saida ta matsa matashi bisa Brosh.
Sannan ta fito, a ta sunkuyo kan Hibba tare da cewa.
"Hibba! Hibba!! Muhibbat!!!".
A hankali ta buɗe idonta.
Cikin sanyi tace.
"Je kiyi al'wala kizo kiyi salla sai ki maida baccin".
Miƙa tayi a hankali tare da cewa.
"Ummi nayi salla".
Jin hakane Ummi ta gane kenan tana fashin salla.
Kai ta gyaɗa kana ta isa inda Aysha take.
A hankali ta sunkuyo kanta tafin hannunta ta kife kan goshinta.
pit-pit haka jijiyoyin kanta ke harbawa.
A hankali tace.
"Aysha! Aysha!! Cikin sanyi tayi ajiyan zuciya mai tsawo tare da buɗe kumburarrun idanunta a hankali.
Cikin sanyi Ummi tace.
"Ya jikin".
A hankali tace.
"Alhamdulillah".
Cike da jin daɗi Ummi tace.
"Masha Allah. Allah ya ƙara mana lfy, yanzu tashi kiyi wonka al'wala kiyi salla sai kizo kiyi baccin ko".
A hankali tace.
"To". Kana ta yunƙura zata tashi da sauri ta zaro idonta waje cikin tsoro take kallon hannun nata.
Ummi ma cike da tsoro take kallon hannun.
Ya kumbura yayi jazir.
Cikin tsoro da jin raɗaɗi cikin fata da naman hannun tace.
"Ummi kalli".
Cikin danne fargabanta, dan kada ta razanata tace.
"Yauwa ba komai kinga abin cikin ya fito ko.
Tashi kije kiyi wanka kizo kiyi salla.
Kisha tea kafin nan ki konta zuwa sha ɗaya dai sarkin baka zaizo shida Lamiɗo.
Cikin sanyi ta miƙe tana mai kallon hannun ta nufi Bathroom ɗin.
Da ido Ummi ta rakata.
Ganin ta maida ƙofar ta rufe ne yasa.
Ummi juyawa durowarta ta buɗe wata doguwar riga ta ɗauko mata mai taushi hannunta guntu kuma tanada ɗan fadi da ɗan kwalinta.
Wondon irin mai tsayuwa iya guiwa nar ta fito mata dashi sai bra turare ta fesa musu kana ta ajiye mata su kan gadon.
Sannan ta fita ta nufi kitchen.
Ita kuwa Aysha, a hankali ta tsaɓule kayan jikinta, kana ta goge bakinta, fes sannan tayi wonka.
Saidai duk abinda takeyi hannun na gefe sabida tana jin yana ɗan zuƙa da tauna.
Wurin yin al'wala ne tayi ta zubda hawaye tana tausayawa masu hannu ɗaya.
Koda ta fito a bakin gado ta zauna.
Wondon ta saka, sannan ta zura doguwar rigar dake mai faɗice.
A hankali ta sa hannunta ta ɗaura ɗan kwalin a kanta a kaikaice.
Bra ɗin kuma, medashi tayi cikin wodurob.
Da kyar tayi salla, tana idarwa.
Ummi na shigowa da kofin tea a hannunta.
Amsa tayi tasha.
Ajiye kofin tayi tare da yin gyatsa a hankali tace.
"Alhamdulillah".
Sannu Ummi tace tare da kallon agogon dake jikin ginin ƙarfe Shida da minti arba'in.
"To yanzu konta ni, bari in shiga kitchen inyi mana breakfast".
Kai ta gyaɗa kana ta miƙe ta dawo, kan gadon ta kwanta.
Ita kuwa Ummi juyawa tayi ta nufi kitchen.
Nan ta samu Saratu tazo fara aikin sukayi.
Ita kuwa Aysha, a hankali ta buɗe idonta data lumshe, sabida jiyo zafin da ta kwana dashi daren jiya, yana tasowa a hankali take jinshi.
Ɗis-ɗas sai kuma ya ɗanyi shiru.
A hankali hasken rana ya bayyana a sararin samani.
Wanda haka yayi dai-dai da bayyanan ciwon da taji jiya, ya mamaye hannunta da jikinta da zuciyarta.
Wani irin yunƙuri tayi tare da tashi zaune.
Cikin zafi tace.
"Sheehhhhhhh Wayyo! wayyo!! wayyo!!! Ummi hannuna yana dawowa."
Wani irin tsalle ta daka tare da miƙewa tsaye.
Cikin tsananin zafin da taji ya mamaye illahirin jikinta ne yasata, sakin wani irin kuka mai baiyana azabar da takeji.
Kife kanta tayi a jikin wodurob, tana bubbugashi tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun."
Da sauri Ummi ta fito daga kitchen ta nufi falon Aysha, jin Hibba na rabka mata kira.
Da sauri ta iso tare da cewa.
"Suhanallali!. Aysha hannun ne kuma".
Da sauri ta ɗago hannun ta nunama Ummi shi, gaba ɗaya hannun rawa yakeyi kar-kar tamkar mazari.
Wani irin juyi tayi da ƙarfi tare da kife kanta jikin gini.
Tare da sakin shessheƙan kuka mai sauti, tana cewa.
"Wayyo Allah na, Wayyo Ummey na. Wayyo Bappa na, zan mutu".
Sai kuma ta kuma muƙewa cikin azabar rawan jiki da alamun a gigice take, cikin rawan murya tace.
"Wayyo Allah na, Ummi ku kaini wurin Bappa na ku maidani gidanmu ku kaini wurin Ummey na".
Ta ƙarishe mgnar tana wani irin tsastsafo zufa mai zafi.
Safa da marwa ta farayi tare da cewa.
Wayyoooooooo hannuna zai tsinƙe".
Sai kuma ta juya a gigice cikin kiɗima da fitar hayyaci.
Ta nufi falo, sabida yadda rana ke ƙara zafi, haka ciwon ke ƙara tunzura da ruruwa.
Da gudu Ummi tabi bayanta tana cewa.
"Shatu! Shatu!! Tsaya mana".
Amman ina kafin ta fito falon tama ita kuma ta isa babban falon.
Ganin hakane yasa Ummi da Hibba biyota a guje.
Da sauri Ummi tasa hannu ta kamo hannun ta, mai lafiyar tana cewa.
"Shatu ki nitsu ki tsaya ina zakije".
Wani irin kuka ta saka mai cike da rauni hannunta ta fizge a hannun Ummi kana ta ɗaurashi tsakiyar kanta.
Dai-dai lokacin Sheykh ya turo ƙofar falon ya shigo.
Jamil da Jalal na binshi a baya,
Cikin al'ajabi ya zuba musu ido.
Jalal da Jamil kuwa da sauri suka nufi inda suke.
Shi kuwa shigowa cikin falon yayi ya ɗan tsaya gefen hanyar fita.
Ita kuwa Aysha aza hannunta tayi tsakiyar kanta, tare da kife kanta jikin gini tana bubbugawa tare da buga sawunta tana cewa.
"Wayyoooooooo Allah na wayyoooooooo hannuna. Ummey zan mutu".
Ta ƙarashe mgnar cikin rauni, abin gwanin ban tausayi.
Hibba kam da Ummi tuni kuka sukeyi.
Hakama sara.
Ummi kuka takeyi tana cewa.
"Sheykh zata fasa kantafa zata yiwa kanta illa".
Wani irin zabura tayi ta juyo a