Showing 156001 words to 159000 words out of 180927 words

Chapter 53 - GARKUWA Book 1 Original Pdf By Garkuwar Fulani.txt

28 Aug 2025

1840

ko".

Tashi yayi yaje ya sha ruwa kana ya dawo ya zauna ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
"Banbancin tsakanin sarautar gefen ƴaƴan ƴaƴa maza da gefen ƴaƴan ƴaƴa mata.
Shine kamar haka.
1 Galadima (must be a prince )
2 Chiroma (crown prince)first born to the king
3 Tafida ( most be a prince )
4 Santuraki (must be a prince )
5 Sarkin dawaki ( prince)
6 Ɗan buram
7 Ɗan isa
8 Ɗan lawan
9 Durbi
10 Wambai
11 Turaki
12 Ɗan maje
13 Yarima
14 Ɗan iya
15 Majidadi.
Dan ɗagowa yayi ya kalleta tare da saƙe yatsunshi da yake naɗewa yana irga mata yace.
"Wannan duk royal family ne mostly biological sons din sarki ne wasu kuma jikokin sarki kuma kunne biyu sukeyi a rawunansu sabida su ƴaƴan sarki ne ko kuma iyayensu ƴaƴan sarki ne.
Kanta ta jinjina mishi alamun ta gamsu tana kuma ganewa.
Shi kuwa a nitse yaci ga da ce mata.
"Anan ake samin chief of staff da kuma senior councillor kamar galadima mostly shine senior councillor shine elders in royal bloodline ana samun galadima yapi sarki a shekaru kuma shi ake bama riqon gari in sarki bayanan.

Sannan duka anan sunayen dana irga miki da fari kowa zai iya yin sarki tunda daga ɗan sarki sai jikokinsa na gegen ƴaƴa maza, shiyasa su kunne biyu sukeyi a rawanunsu.

A hankali ya kalli Ummi data fito da Hijabi a jikinta ta zauna kusa da Shatu.
Tare da cewa.
"To kinji bayanin ƴaƴan ƴaƴa maza na sarki."
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Na gane kuwa Ummi, yanzu gaya min na ƴaƴan yaran sarki mata kuma inji".

Gyara zama Jamil yayi tare da cewa.
"To sukuma sarautar gefen yaya mata sune.

1 Madawaki
2 Garkuwa
3 Makama
4 Majidadi
4 Waziri
5 Matawalle
6 Sarkin yaki
7 Magayaki
8 Jarma
9 Talba
10 Shatima
11 Ubandoma
12 Ɗan kadai
13 Magajin gari
14 Ɗan masani
15 Barma.
Ɗan sauƙe numfashi yayi tare da ci gaba da cewa.
All of these hakimai ne wanda sukeyin kunne daya a rawunansu.
Kuma wasu a cikinsu jikokin sarki ne ta bangaren mamansu, mum dinsu ce yar sarki kamar dai mu a Masarautar su Sitti ko za'a bamu mulki iya waɗannan za'a bamu kinga baza suyi kunne biyu ba shiyasa suke kunne daya amma suma hakimai ne manya kuma yan majalissar sarki also akwai kin makers a cikinsu.
Sai dai su cikin jerinsu babu wanda zai gaji sarautar sarki kamar dai mu yanzu bazamu gaji Jadda ba da masarautar gargajiyace sai dai da yake nasu na musulcine, in Kuma a masarautar Joɗa ne sunayen da na ƙirga miki na forko cikinsu za'a iya bamu, domin yanzu GARKUWA da aka bawa Hamma Jabeer matsayinsa yafi ƙarfin hakan shiyasa Magauta basu damuba."

Ya ƙarishe mgnar da cewa kin gane ko Aunty Shatu,
Kinga shiyasa da aka bawa Ya Jafar Galadima cikin kwana goma aka sabauta manashi.
Ana tsoron kada tarihin Sarki Bala da mahaifinshi Madu ɗan Sarki Sule ya maimaita kanshi a kan ƴaƴan ɗakinmu.
Shiyasa da aka bawa Hamma Jabeer Garkuwa mu bamu soba.
To sauƙin abin ma ɗaya ne da suga sarautar gefen ƴaƴan ƴaƴa mata aka bashi duk da shi jikan ɗan ɗan ɗansa namiji ne".

Ajiyan numfashin tayi kana a hankali tasa hannunta ta tallaɓe habarta, cikin alamun nisan zango na tunani da nazari.

A hankali Ummi ta matso kusa da ita cikin sanyi da kuma yin ƙasa da murya tace.
"Shatu ni kuma in tambayeki wani abu mana".
Kanta ta jujjuya a hankali ta buɗe baki tace.
"Na sani! Ummi nasan abinda zaki tambayeni! Zakimin tambaya ne kan menene yasa da na shiga ɗakin Yah Sheykh na suma na fita haiyacina, ko?".
Ta ƙarishe mgnar wasu hawaye masu ɗumi suna kwaranyo mata a fuskarta.
Cikin sanyin jiki ganin Ummi ta gyaɗa mata kai alamar eh.
Jamil ma jiki a mace ya zuba mata ido.
Tafin hannunta tasa ta sharce hawayenta murya na rawa alamun tana son danne kukanta tace.
"Ummi ɗakin Yan Sheykh ɗakine mai cike da hatsara a rayuwarshi.
Tabbas dan Allah yayi shi mutun ne mai ibada da imani da kekyawar zuciya, da yawan ambaton sunan Allah da zama da al'wala wlh da badan wannan nagartar da Addu'o'in da suka zame mishi abokan rayuwa suka zame mishi GARKUWA ba, kamar yadda Manzon Allah yace.
"Addu'a'u saiful muminin da tuni sun kasheshi sun sabauta rayuwarshi.
Ummi ban san komai ba kan masarautar Joɗa.
Amman dan al'farma Annabi da darajar Umaymah.
Zan taimaki Yah Sheykh iyakar iyawata.
Zan taimake shi akan abinda Allah ya bani ikon gani".
A hankali Jamil ya zamo ya zauna a ƙasa.
Yana mai jin tsikar jikinshi na tashi.
Itama Ummi zamowa tayi ta zauna ƙasa.
Hakama Shatu a hankali ta zauna gaban Ummi hannunta tasa.
Ta kamo hannun Ummi cikin muryar kuka tace.
"Ummi ku yarda dani, ku bani haɗin kai, zan tone duk abun cutarwa dake ɗakin Yah Sheykh. Bazan cutar dashi ba, zan taimake shi kamar yadda Bappa na yake bani umarni duk sanda mukayi mgn dashi.
Ummi keda Jamil ina buƙatar taimakon ku.
Amman kafin nan ki gayawa Umaymah in ta amince,
sai inyi aikin amman kada a gayawa Yah Sheykh dan bazai yarda ba."
Cikin tsoro ido cike da hawaye Ummi tace.
"To Shatu me zancewa Umaymah, me kika gani a ɗakin har ya firgitaki yasaki suma?".
Cikin kuka tace.
"Ummi kada ku tsaya bincike a kaina.
Ni dai ku yarda dani bazan cutar da kowaba na cikin Masarautar Joɗa sai wanda ya cutar da kanshi Ummi bamu da sauran lokaci mai tsawo fa, komai zai iya faruwa da Yah Sheykh".
Cikin tsoro da firgici Jamil yace.
"Ba matsala mun yarda dake, ni yanzu taimakon me zan miki?".
Cikin sauri ta share hawayenta tare da juyowa ta kalli shi kana tace.
"Yauwa Jamilu zaka samo mana mai saka tayis, yazo da katon ɗaya na tayis ɗin irin na bedroom ɗin Yah Sheykh sak da sak.

Sai kuma kayi ƙoƙarin mu samu ya Sheykh in ya fita ya wuni sai dare zai dawo".
Cikin sauri yace.
"Tayis da mai sawa ba matsala, batun in ya fita sai dare ya dawo kuma inaga.
Sai zuwa jibi ranar ne zaije asibitin gwamnatin Genaral Hospital.
To in yaje can wuni yakeyi wani lokacin sai dare zai dawo".
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"To ba matsala.
Ummi ke kuma ki kira mana Umaymah ki sanar mata, muyi abun da saninta."

To Ummi tace kana a wurin ta kira Umaymah tayi mata bayani.
Ba wani neman ba'asi tace.
"A barta Ummin Jabeer na amince, tayi duk abinda ya dace a kan mijinta da yayanshi da ƙannenshi dama duk wani abu nashi".

Cikin jin daɗi ta jinjina kai lokacin da take jin mgnar Umaymah.

Wani irin dogon numfashi taja mai ƙarfi sai gata ta tafi luuuh kan...!



Wasa farin girki? Shatu kadafa allura ta tono garma.




ByTa konta, kamar maiyin bacci kamar wacce ta suma.
Cikin mamaki suka bita da ido kana suka juya suka kalli juna,
Cikin mamaki Jamil yace.
"Ummi suma ta kumayi ne?".
Kai ta jijjiga mishi alamar a a.
Kana tasa hannun damanta ta gyarawa Shatu'n.
Kwanciyarta.
Tare da cewa.
"Bacci ne tayi".
Kai ya kuma gyaɗawa cike da mamaki yace.
"Wannan baiwar Allah'n, itama da akwai abin al'ajabi tare da ita.
Da akwai abinda yake a duhu wanda bamu sanshi ba a kanta."

Cikin gamsuwa da bayan shi Ummi ta gyaɗa kai tare da cewa.
"Na daɗe da dasa ayar tambaya a kanta, sai dai bani da mai bani amsar dole sai zaman yauda kullum zai ƙara fahimtar dani ko wacece ita.
Yanzu dai Jamil wannan mgnar ta zama sirri tsakaninmu.
Da Allah kada kowa yaji!".
Cikin nitsuwa yace.
"In Sha Allah Ummi babu wanda zaiji".

To da haka dai sukaci gaba da hira a wurin.
Cikin Sa'a baccin nata baiyi nisaba ta farka.

Lokacin sallan azahar nayi suka watse.

Bayan sunyi salla da jimawa ne, ta miƙe a hankali ta nufi ɗakinshi.
A falo ta tsaya, tana nazarin to in ta shiga ta sameshi idonshi biyu fa?
Akwai abinda take son idonta ya ƙara gani dan ta tabbatar.

Shi kuwa Sheykh yana ciki, a kwance kamar mafi akasarin lokuta, waya yakeyi da Aunty Hafsat.
Tana ce mishi ya haɗata da amryar zasuyi mgna.
Cikin sanyi yace.
"Bacci, Aunty Hafsat Bacci fa zanyi, afwan ki bari sai anjima mana".
Cikin sanyinta tace.
"Oho Jazlaan, nace ka haɗani da ita shine wannan magiyar yanzu Yezeed yazo ya nuna min hotunanta wai Hibba ce ta turo mishi.
Tamin kyau sosai, ina son yarinyar.
Zakiya ma tana amshi number ta, wurin Hibba tana kira kuma bata ɗagawa.
Jazlaan haɗani da ita nace ko!".
A hankali ya yunƙura ya tashi zaune.
Cikin sanyin baccin daya fara yi yace.
"To ɗan katse kiran in naje zan kiraki."
A hankali ya miƙe tsaye. Al'kyabbar sa ya ɗauka, tare da nufar bakin ƙofar.
Yana mai sa hannunshi cikin rigar al'kyabbar.
Har yazo bakin ƙofar bai gama sa hannun rigar ba ya buɗata da faɗi.

Ita kuma Shatu a hankali ta tura ƙofar.
Ta sako kai ciki dai-dai lokacin kuma shima ya sako kai waje.
Ba zato ba tsammani sukaji sunyi kiciɓis da juna ta faɗa cikin faffaɗan ƙirjinshi.
Cikin sauri ya sauƙo da hannayeshi dake buɗe kuma al'kyabbar na buɗe da faɗinta sanadin sauƙo da hannun da yayine sai ya zama ya sauƙe hannunshi kanta, yayi mata ƙawanya da faffaɗan al'kyabbar jikinshi ya haɗasu wuri ɗaya ya rufesu.

Wani irin harbawa zuƙatansu suka farayi da ƙarfi-ƙarfi, suna jam junansu i ziwa jikin juna tamkar mayen ƙarfe.

A hankali Shatu taji jikinta na macewa.
Kanta ta manna a ƙirjinta kunnenta na dai-dai kan ƙahon zuciyarshi.
Lumshe idonta tayi tanajin wani irin masifeffen ƙamshi turare mai daɗin shaƙa dasa baccin daɗi cikin ƙanƙanin lokaci, koda yake baccin nata baya rasa nasaba da abinda ke wujijjigata.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, shiru yayi yanajin yadda tasa hannunta, ta zagayo ƙugunshi ta riƙe gam-gam da iya ƙarfin ta.
Sai kuma ya ɗan sunkuyo cike da mamaki yakkali fuskarta, tuni tayi bacci cikin ƴan second nin nan.

Cike da mamaki ya zubawa fuskarta kallon tuhuma.
A hankali yasa yatsunshi ya fara ɓanɓaro hannunta,
yanayi yana ja da baya-baya yana komawa cikin ɗakin.

Ita kuwa binshi take amman ba bi irin na takuba,
Cike da mamaki ya ƙara leƙa fuskarta.
Tabbas bacci tayi.
Janyeta yayi daga jikinshi kana ya saketa a hankali ta tafi zata faɗi, bai tareta ba, sai dai yasa ƙafarshi ya tare dai-dai inda yaga kanta zai bugu.
Cikin Sa'a kanta ya sauƙa kan rumfar ƙafarshi.
A hankali ya ajiye ƙafar tashi a ƙasa.
Kana ya janye ƙafarsa, kanta ya konta a ƙasa.

Cike da mamaki, ya juya ya koma can inda yake konciyar.
Bai cire al'kyabbar ba ya konta yana mgnar zuciya.
"Mutun kamar mayya, wannan baccin kuma na meye to".

A haka shima yayi baccin da yasan in bai yishiba, zaiji ciwon kai.

Kiran sallane ya tadashi.
Tanan konce har yanzu.
Al'wala yaje yayi kana ya fito ya kimtsa ya fesa turare.
A hankali yazo kusa da ita.
Ɗan sauran ruwan dake tafin hannunshi ya yarfa mata a fuska.

A hankali ta buɗe idonta, kana ta kuma lumshesu haka tayi kusan sau uku ganin hakane a hankali yace.
"Ke kasa uwar bacci tashi kiyi salla".
Miƙa tayi a hankali tare da cewa.
"To". Shiru yayi yana nazarin muryarta, ba haka muryarta yakeba.
Wannan shine abinda su Ummi basu ganeba, shi gashi ya gane a take,
Su kuwa basu gane cewa muryarna ba tata bace.

Kanshi ya ɗan juya tare da cewa.
"Uhummmm". Daga nan ya fita, ita kuma Shatu da ido ta bishi.
Yana fita ta miƙe kalle-kalle tayi a ɗakin nashi sosai har ƙarƙashin gado ta leƙe.

Tana gamawa ta shiga Bathroom nashi.

Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
"Komai nashi mai kyau da tsabta".

Al'wala tayi kana ta fito, a falo ta samu Ummi da Hibba da alamun a nan sukayi salla.

Sosai Ummi tayi mamakin kenan, tana ɗakin Sheykh ne, murmushin jin daɗi tayi a ranta tace.
"Ikon Allah kenan".

Ita kuwa Shatu hijabin Hibba ta amsa tayi salla.
Suna zaune a nan ya shigo.
Wayarshi na kunne cikin nitsuwa yace.
"To Aunty Hafsat gata nan ɗazu bacci takeyi".
Cikin murmushin tace.
"To bata".
A hankali ya iso tsakiyar falon wayar ya miƙo mata tare da cewa.
"Aunty Hafsat ce ƙanwar Umaymah saura kiyi mata rashin ta ido".
Ya ƙarishe mgnar a hankali yadda ita Aunty Hafsat bazata jishiba.

Ita kuwa amsa tayi tare da karawa a kunne cikin nitsuwa tace.
"Assalamu alaikum".
Fuska a sake tace wa alaikissalam ɗiyata, ya gida ya sanyi".
Muryar matar sak irin ta Umaymah shiyasa cikin jin daɗi tace.
"Lfy lau Alhamdulillah Aunty ya gida da aiyuka".

"Alhamdulillah". Tace kana ta ɗora da cewa.
"Sunana Hafsat Jalaluddin Muhammad Sultan".
Cikin jin daɗi tace.
"Eh Aunty na sanki ai Umaymah ta gaya min sunanki ta nuna min hotonki da Aunty Rahma da Zakiya da Yezeed dama duk sauran".
Cikin jin daɗi tace.
"Masha Allah, to ki amshi number ta data Rahma da Zakiya a wurin Hibba, ɗazuma Zakiya taita kiranki ashe kina bacci ne".
Cikin nitsuwa tace.
"To Aunty yanzu kuwa, ngd matuƙa".
Cikin jin daɗi Aunty Hafsat tace.
"Allah ya muku al'barka ya baku zaman lafiya.
In Sha Allah zamuzo auren Haroon zaki gammu mu ganki".

"Amin Amin. Aunty Allah ya kaimu lokacin ya kawoku lfy".
Tace kana sukayi sallama.

Daga nan suka shiga kitchen.
Jamil kuwa tuni yaje yayiwa wani mai musu aikin gidansu.
Yasa ya nemi irin wannan tayis ɗin. Yace gobe da safe misalin sha ɗaya zaizo ya ɗauke shi.

Washe gari da safe.
Misalin karfe tara, Sheykh ya fito cikin shiga ta al'farma, yau ba al'kyabba a jikinshi riga da wondone sai malum-malum gariya mai kyau.
Getzner ce mai masifar kyau Brownish red color mai ɗan karen kyau da sheƙi, gariyar tasha aiki mai ɗan karen kyau da zaren surfani mai sheƙin piash color.
Hular kanshi da red and piash color, takalmin shi kuwa fatar ta kifa kalar red ɗin.
Yayi kyau sosai ya kafa hular nan cas a kanshi. Kekyawan suman kanshi ya konto gefe da gefe da ƙeyarshi sai sheƙi da ƙelli yakeyi.
Sajenshi ya kwanta lib, gashin girarsa dana gemunshi ɗan cas dashi misalin kamu ɗaya, sai sheƙi suke zubawa.
Ɗan madai-daicin bakinshi mai jajayen laɓɓa sai sheƙi sukeyi.
Yar ƙaramar jakar na'urar System ya riƙe a hannunshi, sai wani ƙamshi mai daɗin ji yake fiddawa, ɗan farin siririn Glass irin na manyan Doctors ya manna a fuskarshi kana ya fito.

A falonshi ya sameta, tana jera mishi breakfast.
Ganin zai wucene ta ɗan biyoshi a hankali ya zama suna tafe a jere.
Cikin kallon suman ƙeyarshi tace.
"You are breakfast is ready".
Bai kulata ba yaci gaba da tafiya.
Ita kuma ƙeyanshi ta mannawa harara.
A haka suka fito.
Ya sallami Ummi da Jamil da tunda suka karya bai tafiba.
Da sauri Jamil yabi bayanshi yana cewa.
"Uhum Dakta sai yaushe zaka dawo ne?".
Juyowa yayi ya kalli Jamil sai kuma yace.
"Kanada matsala ne?".
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da cewa.
"No. I'm very fine".
yayi mgnar yana jijjiga jikinsa.
Kai ya kaɗa ya juya zai fita,
Da sauri Jamil ya kuma tambayarsa.
"Dakta yaushe zai dawone".
Cikin tsuke fuskarsa yace.
"Ban sani ba".
Daga nan ya fita, shi kuwa Jamil tsalle yayi tare da cewa.
"Yesss, Dakta Allah ya kiyaye hanya, a wuni lfy a asibiti".

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Yi maza to ka ɗauki shi".
To yace kana ya miƙe ya fita.
Sanin cewa yanzu Sheykh yana sashin Hajia Mama ne.

Haka yasa ya rigashi fita.

Ummi kuwa miƙewa tayi taje ta rufe ƙofar sabida bata son wani yazo ya shigo.
Kiran Jamil tayi a waya tace in sun isoma ya kirata a wayane zata buɗe mishi.

Tana katse kiran ta juyo ta kalli Shatu dake zaune gefenta tana ce mata.
"Yauwa to Ummi muje mu fara aikin kafin ya iso mun kusa cimma aikin."

Cikin mamaki tace.
"A a keda kikace sai an matsar da gadonshi sannan aikin tono ai bazamu iyaba. Dole sai mazan".
Cikin muryar da har yau Ummi ta kasa banbance shi da asalin muryarta tace.
"A a ba matsala Ummi muje zamu iya".
Ta ƙarishe mgnar tana yin gaba, ganin hakane yasa Ummi Binta a baya.
A hankali suka shiga falon.
Tana mai cewa Ummi.
"A nan ma an mishi wani aikin amman shi bai shiga jikinsa ba, sabida yanada Garkuwar addu'o'in da yakeyi yau da kullum.
Shiyasa duk sabbin sihirurruka basa shigarsa.
Sai dai waɗanda akayi mishi tun bai gama girma ba."
To kawai Ummi ke ce mata sabida jin kamar muryarta na canza mata.

A haka ta kuma nuna mata wani wurin.

Tare da cewa.
"Uhumm Ya Jafar suke nema, su maida majanunin kan bola sai kuma sharrinsu ya zame mishi al'khairi,
Tsawon shekaru baya mgn sai ambaton Allah. Bashi ba zunibi sai tarin lada da yake samu na karatun al'ƙur'ani da ya zame mishi abokin hira.

To ita kuma me take nema a duniya da zata cutar da baiwar Allah da ahlinta duka haka.
In banda lalaci da son duniya na miji ya lalace da bin matsafa yana sawa ana sabauta ɗan uwanshi da yayanshi."
Ita dai Ummi binta takeyi da ido da ƙafa har suka isa bedroom ɗin shi.

Ɗan lungun da ɗaya Bedside drower'n take ta shiga.
Kana ta kalli Ummi fuska a juye tace.
"Naɗe min carpet ɗin nan.
To Ummi tace da sauri ta fara naɗe carpet ɗin.
Bayan ta janyeshi da kyar ne, ita kuma Shatu.
A hankali tasa hannun damanta bisa jikin gadon ba tare da ta ɓallashi ba ko, ta cire wani abu a jikinshi ba, ta yunƙura ta tura gadon tare da cewa.
"Bismillahirahamanirahim".
Da sauri Ummi taja da baya cike da mamaki da tsoron ganin yadda take tura tamfatsetsen gadon mai ɗirkekiyar katifa da ko tura katifar kawai aikine.

Guuuuuuh haka sautin tura gadon yake badawa.

Saida ta turashi har jikin Waldurob.
Kana ta tsaya a tsakiyar inda gadon yake kafin ta turashi.
Dai-dai lokacin kiran Jamil ya shigo wayarta.

Da sauri taje ta buɗe mushi.

Kana suka shigo,. A falon suka bar Ɗalha mai tayis,
kana Jamil ya amshi kayan aikin yabi bayan Ummi yana cewa.
"Yauwa ɗalha ɗan jirani bari inzo mu isa kaga wurin".

To ɗalha yace kana ya fara cin abincin da Ummi ta saka mishi.

Suna shiga suka maida ƙofar falon suka rufe.

A inda Ummi ta barta a han suka sameta.
Da sauri ta miƙawa Jamil hannun tare da cewa.
"Bani gudumar da ma'ɓamɓarin."
Cikin sauri ya iso tare da ajiye ɗan buhun ya fito da gudumar da Maɓamɓarin yana mai mamakin yadda aka tura gadon yace.
"Bari Aunty Shatu nuna min ina zan fasa".
Da sauri tace a a, ku ɗan matsa gefe, musamman ma kai koma can".
Ta nuna mishi gefe.
Sake mata gudumar yayi jin ta fizgeshi.
A hankali ya tashi sabida cewa da tayi ya tashi.
Ido suka zuba mata, ita kuwa, gudumar tasa ta rinƙa buga tayis ɗin dake wurin saida ta fasa uku lafiyeyyu.
Kana ta ture fasassun tasa maɓamɓari tana ɓalle sauran, saida ta ciresu kab.
Sannan ta fara fasa fulon simintin dake ƙasan.
Da mamaki Ummi ke kallon wurin sabida tasan babu wani fulo da akayi kafin asa tayis ɗin.
Fasashi tayi kana ta fara caccaka ƙasan wurin da matonin, tanayi yana fito da ƙasa.

Shiru sukayi ganin ramin yayi zurfi kuma ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login