Showing 174001 words to 177000 words out of 180927 words

Chapter 59 - GARKUWA Book 1 Original Pdf By Garkuwar Fulani.txt

28 Aug 2025

1857

kuma ta kwantar da kai cikin sanyi tace.
"Yah Al'ameen ina Dedde na?."
Cikin sanyi yace.
"Tana lfy ta gaisheki sosai".
Ido ta lumshe tare da sauƙe numfashi
Sai ta kuma kalli jerin ababen da aka jera musu a kan santa table.

Ummi kuwa cikin sakin Fuska tace.
"Ina kwana Bappa kuzo lfy".

Fuska a sake yace.
"Lfy lau Alhamdulillah."

Sai ya kuma juyo ya kalli Umaymah dake ce mishi.
"Sannu da hanya, ya mutan gida?".
"Lfy lau Alhamdulillah. Ya mai jikin sannunku da jinya mungo matuƙa".
Bappa yace cikin kamala.

Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Yiwa kaine ai".
Al'ameen ne ya ɗan kalli Umaymah cikin nitsuwa yace.
"Ina kwana".
Ido ta ɗan zuba mishi tare da cewa.
"Lfy lau ya gida".

"Alhamdulillah ya mai jikin".

"Da sauƙi".

Shiru sukayi dukansu suka maida idonsu kan Aysha data kalli Al'amin cikin shogoɓa tace.
"Yah Al'amin zanci abinci".

Kallonta ya ɗanyi tare da juyowa ya kalli Ummi sai kuma yayi shiru.

A Sheykh ne ya miƙa tsaye tare da cewa.
"Bappa bismillah mu isa can falona."
Ya ƙarishe mgnar yana kallon wayar iphone 12 pro dake hannun Al'amin.
Cikin nitsuwa Bappa yace.
"To bisimilla".
Juyawa yayi gaba kana suka bishi a baya.
Itama Aysha binsu tayi a baya.


Suna shiga shiga falon nashi Bappa ya zauna bisa kujera.
Su kuma duk suka zauna a ƙasa a saban carpet.

Ita kuma Aysha tsakanin Al'amin da kuma Sheykh ta zauna.

Barun kuma ya ɗan zauna gefe.

Cikin girma Bappa ya gyara zamanshi tare da cewa.
"To Jabeer ban saniba ko zaka amince wannan ya duba hannun matar taka, mu gwada nashi mgnin ko Allah zaisa mu dace".
Shiru Bappa yayi tare da zuba mishi ido.
Shi kuwa Sheykh kanshi a sunkuye yana kallon tattausan yadin jikin Al'amin yace.
"Duk yadda kace Bappa ba damuwa, in ka aminta dashi".

Shiru Bappa ya ɗan yi yana nazartan kalaman shi da fuskarshi kana yace.
"In sha Allah ba damuwa".
Kai ya gyaɗa.
Lokacin Umaymah kuma ta shigo da manyan Foodflaks da plate ta ajiye a tsakiyarsu.
Zata fita kenan.
Bappa yace.
"Zauna mana".
To tace kana ta zauna.

Shi kuwa Al'amin cikin kula ya kalli Aysha tare da cewa.
"Matso ya duba hannun ko".
A hankali ta matso kana ta miƙa mishi hannun.

Barun kuwa. Gyara zamanshi yayi tare da kallon su sannan yace
"Wannan ba wani abun tashin hankali bane, yanzu zan mata mgnin kuma zata samu sauƙi sai dai bisa shanu hamsin da nace.
Gsky yanzu ɗari za'a bada".
Ido Sheykh ya zuba mishi cike da tuhuma.
Al'amin kuwa murmushi yayi tare da cewa.
"Kai dai kayi aikinka in ta samu lafi ka faɗi adadin duk shanayen da kakeso bazai gagara ba da izinin ubangiji".
Kanshi ya gyaɗa cikin jin daɗi.
Kana ya zaro wayarshi kamar yadda suka tsara da Ba'ana.
Kiranshi yayi.
Ya saƙala wayar a kunne ya matseta da kafaɗarshi.
Kana ya kalli Umaymah yace.
"A kawo min madarar shanu mai sanyi".
Da sauri Umaymah ta miƙa tare da cewa to.

Shi kuwa Barun. zabirar magungunan da Ba'ana ya haɗo mishi ya buɗe kana ya fara fito dasu.
Jim kaɗan Umaymah ta dawo da madarar shanu mai sanyi ta mika mishi.
Ajiye wayar daya matse a kafaɗa yayi tare da amsar nonon.

Kana ya zuba wani garin mgnin a ciki.
A take nonon ya fara zama kinɗirmo mai kauri.
Kana ya matsar dashi gefe.
Sannan ya fito da wani mgnin yana kwashi da man shanu.
Kiran da akayiwa wayarshi ne yasa ya dakata ganin sunan Ba'ana.
Amsa wayar yayi ya kara a kunne tare da fara mgn ba sallama.
Tsareshi da ido Sheykh yayi ya lura cewa wannan mutumin ba musulmi bane.

Al'amin kuwa hannun Aysha ne riƙe a hannunshi yana mata sannu.

Bappa kuwa shima hankalinsa na kan Barun.

Hakama Umaymah, shi ko Barun.
Kamar yadda suka tsara haka ya fara mgna. Ta tsigar da dole Aysha ta gane waye Barun kuma waya turoshin.

A hankali ta ɗago kanta jin yace.
"Eh naje har cikin gidan an nuna min mara lfyar, to kafin in mata aikin na gaya mata, ƙetaren sihirine.
Nace mata kin mance cewa.
Yana ce miki Mata ki bari in dafaki da kyau gudun kada wata rana wani ya cutar min da ke.
Mata na baki haɗin da idonki zai iya ganin alamun sihiri na mugunta da baƙin hayaƙi tsari ko wani kafiya kuma da farin hayaƙi.
Na gaya mata cewa.
Yace mata Mata kada kiyi gangancin cewa zaki tone wani sihirin tunda kinƙi in dafaki.
Domin zai iya dawowa jikinki ya cutar da ke."

Shiru ya ɗan yi yana kallon cikin idon Aysha.
Ita kuwa tuni Aysha jikinta na tsuma.
Bappa kuwa numfashin ya sauƙe tabbatar da zatonshi hakane wannan ɗan aiken Ba'ana ne.
Al'amin hankalinshi na kan Aysha.
Umaymah kuwa shiru tayi tana kallonshi.
Sheykh Jabeer kuwa idonshi ya lumshe yana sarrafa kalaman Barun da wassafasu da basu cikekkiyar ma'anarsu da jimla a kanshi.
Shi kuwa Barun ci gaba yayi da cewa.
"Eh ogo na gaya mata kuma ta gane.
Don a lokacin tayi shiru.
Na kuma ƙara cemata Ogana yace in cemata duk inda take duk inda ta shiga ko wani motsinta yana cikin tafin hannunshi.
Ya kuma ce in.gaya mata ajiyarta yayi a inda yake, yana son ya gama da aikin da yasa a gabane zai dawo kanta zai kuma ɗauke ta.
Nakuma cemata.
Kace in ce mata.
Duk duniya babu mai bata mgnin ciwon hannunta sai mu, sannan zata worke.
Nace mata kace in gaya mata kana raye tare da ita yana sonki tun kina ƙaramar zai kuma ci gaba da sonki har gaban abadan."

Ba'ana dake can sai murmushi yakeyi cikin jin daɗi.
Yaso ace yana ganin fuskar Shatu to amman wannan mutumin mai shegen hasken ya kareshi.

Aysha kuwa gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Tana mamaki da tsoron taƙadirancin Ba'ana ya akayi ya samu damar turo jakadarsa masarautar Joɗa har cikin sashinta har falon mijinta har gabanta gaban mijinta.

Ido ta zubawa Barun tana mai haɗa zufa.
Shi kuwa Barun kai ya jinjina mata.


Bappa kuwa cikin sanyi yace.
"Wannan wayar taka ba ƙarewa zatayi ba katse kiran ka shafa mata mgnin, lokacin na tafiya kasan mu yau zamu juya."

Cikin murmushin taƙadiranci Barun yace.
"To Bappa an gama".

Gyara zamanshi yayi tare da miƙowa Aysha kindirmon mgnin daya kwaɓa.

Shi kuwa Sheykh Jabeer gyara zamsnshi tare da watsawa Barun wani irin kallo mai tarin ma'anoni kana yace.
"Bar mgnin nan naka bana buƙatar shi a jikin matata! Bar min matata.
Jeka kawai kacewa. Ogan naka.
Akwai mganin da zai workar da ita ba sai nakuba,
Zata kuma samu sauƙi cikin ƙanƙanin lokaci da izinin ubangiji.
Kace mishi, sama tayiwa yaro nisa.
Duk tsallen da zaiyi bazai taɓoshi ba.
Kacewa oganka ya tsaya inda yake hurumin yafi ƙarfinshi".

Cike da Mamaki Aysha, Bappa, Al'amin, Barun, Umaymah suka zuba mishi ido.
Shi kuwa gyara al'kyabbar jikinshi yayi tare da tsare Barun da idanunshi da suka hantar cikin Barun ta kaɗa cikin iya sarrafa harshe yaci gaba da cewa.
"Muda muke da al'ƙur'ani mai girma ai Allah ya bamu dukkan maganin cutar duniya a cikinsa.
*Kada ku sake zaton samun shigowa masarautar Joɗa*, wannan ɗin ma.
Ni naso ku shigo shiyasa ka samu ka shigo ni na bada dama."
Miƙewa tsaye yayi tare da nunawa Barun hanyar fita cikin dakekkiyar murya yace.
"Tashi ka ɓace min da gani.
In kaje kace mishi idon Muhammad Jabeer a buɗe suke basa bacci. Kada ya sake gigin turo wani ƙazamin kafuru, a tsarkakken.
Masarautar Joɗa Especially nan."
Cikin tsananin tsoro da mamaki da kaɗuwa Barun ya juya da sauri ya fita.
Da ƙarfi Sheykh Jabeer ya buɗe muryarshi yace.
"...!



Kuyi haƙuri dan Allah babban uzurin mgn a wayane ya tsareni sai yanzu.


By
*GARKUWAR FULANI*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️



PAGE 25

"Da Mamaki kwallo a maƙabarta.
Wato dai haka za a cigaba da gwara kawunan mutanen. Masarautar Joɗa ana mayar da su marasa tunani?".
Gimbiya Saudatu Ta faɗa tana ya mutsa fuska don ta kasa kallon ƙwayar idon Sheykh.
Banza ya yi da ita duk da ya waiwayo ya kalleta, ya so tanka mata, amman sai ya share yaci gaba da takunshi cikin nitsuwa yana tafe yana tasbihi.
A hankali ya isa falon.

Kanshi ya ɗan juyo ya kalli tsakiyar falon.
Sam bai hango Shatu da Ummi ba dake zaune a falon.
A nitse ya maida kanshi ga inda ya nufa ya juya zai shiga corridor'n da zai sadashi da falonshi. "Ba ka ji me nace bane? Dutse ne kai ko waliy? Wata da watanni a kawo maka mace a ce sai yau ake bada kyautar budurci dan rainin wayo tuntuni kallon hoto kake mata ko me.
Ba ma wannan ba, wanne irin munafurci ne ya sa aka bada kyautar dawakai amarya da ango? Duk yana cikin sahun munafurcin da boye-boyen.."
Cikin tsawa ya dakatar da ita da cewa.
"Bana son shirme fa! Fitar min a gida tunda ba wancan tsohon ne ya gina min shiba".
Da sauri tace.
"Zan fice ba sai ka koreni ba."
Ta ƙarashe mgnar cikin tsananin takaicin tsawar da ya yi mata don sai da hantar cikinta ta kaɗa.
A dake ta jujjuya idanuwanta tare da cewa.
"To wai ɗaga Muryar na meye ne? Tambaya fa kawai nayi nake son amsa.
Wannan sarƙar kuma ta mece ce? Ta asalince wacce ta ɓace ɓat ko in ce ta yi ɓatan-dabo, ko kuma wata ce ta dabam aka ƙirƙiro, don nasan waccer dai bata kai labari ba, daga wuyan waccer ts..."
Bai bari ta cigaba ba ya tare ta da muryarsa a nutse cikin iya sarrafa harshe, ya lumshe idonshi kana ya buɗesu a hankali yace.
"Dakata, tsaya kiji."
Da sauri tace.
"Uhum ina jinka".
Rausayar da kanshi yayi kana a hankali yace.
"Kyauta ce ta girmamawa, wacce ba kowacce mahaluƙiya ce take katari da irinta ba a cikin Masarautar Joɗa, duk da kyautar ta yi kaɗan a wajen wacce ta cancanci ninkin hakan, bana ji akwai abinda za a iya biyan macen ƙwarai da abun duniya ba ko da kuwa za a bata kujerar masarautar Joda wanda wasu wayayan mazaunan cikinta ke wawasun nema ba. Darajarta da kimar kyautar data bada yafi ƙarfin tukuicin da masararutar Joɗa ke badawa, ita ba irinku bace ta wuce hakan".

Shiru Ummi tayi tana mai jin kalamanshi tare da yin wani sassanyan murmushi.

Ita kuwa Aysha a hankali ta lumshe idonunta tanajin kalamanshi masu sanyi da sanyaya zuciya.

Gimbiya Saudatu kuwa. Wani irin baƙin ciki ne ya turniƙe ta, da kyar ta iya saita numfashinta cikin karkarwar jiki da rasa abin cewa ta ce, "Wannan wanne irin yabo ne haka har sai ka haɗa da sarautar gidan nan?"
Yanayin ta ya kalla ya yi Murmushi, wanda ya ƙara tunzirata kana a nitse yace.
"Dan na tabbatar miki da ƙimarta da darajarta ne, ina son kuma hakan ya zauna a cikin ƙoƙon ranki har illa masha Allah..."
Cikin takaici tace.
"Wannan kuma ka yi kaɗan ka sani adana shi a raina"
Kallon da yake mata ne ya hana ta ƙarasa zancen, don daga inda take tana iya jiyo sautin hucin da yake, muddin ta ƙara sa maganarta tsab zai iya wanka mata marin da zai sa ta rasa jinta na awanni.
Da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta fice mishi a gida.
Kamar munafuka ta wuce simi-simi tana gunguni.

Juyowa yayi ya nufi cikin, sai kuma ya ɗan juyo ya kalli cikin falon jin alamun akwai mutun a ciki.
Juyowa yayi cikin falo.
Cikin nitsuwa ya kalli Ummi da Shatu.
Da alamun Ummi lallaɓata take taci abinci,
Idonshi ya ɗan lumshe, haka nan yaji wani irin sanyi har cikin ransa yake jin daɗi.

Wani ɗan guntun Murmushi yayi bayan ya kalli fuskar Shatun data ke kwaɓe har da turo baki.
Wayar Ummi ce ta fara suwa juyowa tayi ta ɗan jawo wayar,
tana dubawa taga Umayma cikin farin ciki ta ɗaga, tare da karawa a kunne kana tace.
"Assalamu alaikum, Umaymah Sheykh."
Cikin tarin jin daɗi Umaymah tace
"Wa alaikassalam Ummin Sheykh ina yaran naki? Ya jikin ɗiyar tawa"!".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"Alhamdulillah suna lfy, ɗiyarki jiki da sauƙi gatasu ma kusa dani".
Cikin kula tace.
"Bata wayar".
To Ummi tace kana ta miƙawa Aysha wayar.
Tare da cewa.
"Ga Umaymah".
Amsa Aysha ta yi ciken jin sanyi tace.
"Assalamu alaikum Umayma barka da rana."
Cikin tsananin kulawa Umaymah tace.
"Waalaikumus salam Habibty, sannu Aysha Addana, Allah ya yi miki albarka, Allah ya saka miki da al'khairi, na ji daɗi sosai, in sha Allah al'khairi da haske yanzu zai bayyana, sannu kin ji my dear, ki kula da kanki sosai, ki dinka shiga ruwan dumi akai akai, sannan kada ki yi wasa da kunun nan da Ummi take miki, kin ji ƴata ki yawaita cin gashin naman da zatanayi miki da shan kunun har na tsawon kwana uku kinji ko Aysha."
Wata azababbiyar kunya ne ta rufeta.
A kunyace tasa ɗayan hannunta ta rufe fuska tana jin inama ƙasa ta tsage ta shige cikinta.
Da ƙyar ta iya ce wa,
"To Umayma."
Jin Muryarta ya sa Umayma yin dariya don tasan kunyace irin na ƴaƴan Fulani ne yasa ta yin shiru.
Cikin murya mai baiyana jin daɗin da take ciki tace.
"Yauwa Aysha, Allah ya yi miki al'barka."
Cikin sanyi da jin daɗi tace.
"Amin Umaymah".
Kana daga nan
Suka yi sallama ta kashe.

Sunkuyar da kanta tayi tare da mikawa Ummi waya, don izuwa yanzu kunya ta gama jiƙeta, kallonta Ummi ta yi tana jin dadi aranta tana kuma addu'ar Allah ya nuna musu ranar da ƙwai zai fasha, don ga alamun nan suna ta tabbata.
Shi kuwa Sheykh ajiyan zuciya mai sanyi ya sauke kana ya juya ya nufi falonshi.

Ummi kuwa Kitchen ta wuce da tray'n a hannunta.


Ita kuwa Aysha Anan falon ta zauna tana tunani kala-kala musamman akan masarautar sam ta kasa gane mata.
A kullum da kalar surƙullen da zai bayyanar mata, ko meye ma'anar zantukan da suke yawan yi wanda bata gane masa ba?.
Dazu tajiyo Gimbiya Saudatau da Sheikh maganganunta sun bata mamaki, lallai akwai wani babban al'amari a cikin gidan nan, wanda da sannu zata fahimci menene wannan abu.
Kuma zata tambayi Ummi wani abu ko zata gaya mata, ko ta samu sauƙin Tsarkakkiyar dakw cinnzuciyarta.
Tana nan zaune har aka kira sallar la'asar ta tashi daƙyar don har yanzun bata jin dadin jikinta.
Bedroom ɗin ta ta wuce.
Kai tsaye Bathroom ta nufa.

Al'wala ta ɗauro don har masallacin masarautar sun tada kabbara.

A hankali take taku sabida har yanzu tanajin jikinta na mata zafin rabuwa da budurci.
Sallaya ta shimfiɗa kana itama ta tada kabbara.

Bayan ta idar da sallah ne,
ta kuma miƙewa a hankali ta fito falo, sabida ta gaji da baccin kwanciya tayi bisa kujera da wayarta a hannunta, tana mgna da Junaidu.

Ummi kuwa tana kitchen.

Murmushi ta ɗanyi jin Junaidun na cewa.
"Dan Allah Adda Shatu kicewa su Bappa su dawo haka nan, zamansu a waccar ƙasar ya isa.
Ina kewar Junainah, Rugar Bani gaba ɗaya muna kewarsu dan Allah su dawo".
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"To Junaidu in sha Allah zan gaya musu, su dawo maka da masoyiyarka dan nima nayi kewar Junnu ina kewar Ummey na".


Ummu dake kitchin ne ta ɗan tsagaita daga motsa naman da take fasawa Aysha
Sabida jiyo sallamar Hajiya Mama da Aunty Zuwairiyya.
Haka yasa ta fito tai musu barka da zuwa kana suka gaisa tare.
Sannan tace su isa Aysha na ciki.

To Juwairiyya tace kana tai gaba Hajia Mama na biye da ita a baya.

Ita kuma Ummi ta koma Kitchen dan kawo musu ruwa.

Ba a jima ba sosai Ummi ta debo drinks ta fito da nufin kai musu.
Sai kuma sukayi kiciɓis a bakin ƙofar falon Ayshan. Sun fito falon Shatu fuskarsu a murtuke, da alamun ransu a ɓace, suka wuce ta.
A hankali ta bisu da ido, tare da tambayarsu.
"Har kun fito ko ruwa baku shaba".
Dukansu babu wacce ta kulata suka fice.
Ajiyan zuciya ta ja ciki da mamaki, sai kuma ta juya ta nufi falon Ayshan.
Tana gab da shiga falon ta ji sautin muryar Aysha na faɗa da ɗan ɗaga murya take cewa. "Mitssssss munafukan banza masu fuska biyu mugaye masu baƙaƙen zuciya. In sha Allah sai Allah ya toni asirinku!".
Da sauri Ummi ta ƙaraso gareta tare da ajiye tray'n hannnunta bisa stoll cikin kula tace.
"Lafiya dai Shatu Meya faru?".
Girgiza kai Shatun ta yi cikin jin haushi ta ce
"Ummi nace bana son su, bana son ganin sun shiga rayuwata, bana son su rinƙa zuwa inda nake saboda na tsani mu'amala da mai fuska biyu."
Ajiyar zuciya Ummi ta yi tana jujjuya zancen Shatun, da kuma tsananin mamakin takun sakar dake tsakanin Aysha da Hajiya Mama.
Numfashin ta ɗan fesar tare da dafa kafaɗarta kana a hankali tace.
"Shike nan ki yi hakuri yanzu ai sun fita."
Ƙwafa Aysha ta yi tare da kishingiɗa sosai tana mamakin yanda mutanen gidan suka kasa fahimtar komai tana matuƙar mmkin in ance wai Hajia Mama itace Mamansu Sheykh kuma ita har yau bata yardaba bata kuma jin zata yarda har gaban abadan.


Bayan ta idar da sallar isha har yanzun jikinta ba kwari haka tana jin ciwo a gabanta musamman in ta miƙe tana tattakawa, miƙewa ta yi a ciccije, "Wash Allah na!".
Ta faɗa haɗe da miƙewar ta fara tafiya tana gwale-gwale kamar ƴar kaciya, kallonta Ummi ta yi tana nazarinta, bayan ta shige ɗaki ta tashi ta bita ɗakin.

A tsaye ta sameta gaban drower'nta.
Juyowa tayi ta kalli Ummin dake matsowa kusa da ita tare da cewa.
"Aysha kin sake shiga ruwan ɗumi kuwa?".
Kai ta jujjuya mata a hankali tace.
"Ɗazu da yamma dai na shiga".
Kai Ummi ta jinjina kana tace.
"Yauwa to kije yanzuma ki shiga ruwan ɗumi zakiji sauƙin abin sosai."
Ya mutsa fuska ta yi irin na mai jin ba daɗi kana cikin sanyi tsce.
"Ummi bana jin daɗi kwata-kwata."
Kusa da ita ta matso cikkn kula tace.
"Na sani, amma shiga ruwan ɗumin zai tai maka kwarai wajen jin daɗinki, don zaki sake sosai, duk wannan ciwo-ciwon zaki daina ji." Kwafe fuska ta yi kamar zata yi kuka.
Yanayinta Ummi ta kalla, ta so yin dariya sai dai kuma danne tare da cewa.
"Yi haƙuri kin ji Ayshs, daure kada ki zama raguwa mana."
"Uhmm".
kawai tace ta miƙe ta shige cikin bathroom.

Ita kuma Ummi ta wuce kitchen tare da ɗauko haɗaɗɗen kunun gero wanda ake yinsa na musamman kuma shi ake bawa amaren masarautar haɗe da farfesun farararen tattabaru, wanda shi ma wani haɗi ne na sirri mai tsuma mace, da yajin da ake barbaɗawa akan tattabarun wanda yake ƙarawa mace wani ɗanɗano na musamman.

Ita kuwa Aysha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login