Showing 3001 words to 6000 words out of 40544 words
Chapter 2 - Aishah-Saddiqa 4 end Complete Novels by Sumayya Takori.pdf
tayi shiru dai, da ya matsa
sai tace “Uncle ko ka kira Nenne ni ba abinda kayi min, hakannan dai kawai ban jin surutu”.
Hamma yayi shiru, daga bisani ya sunkuyar da kai, yace “kan zuwan Haseenah ne ko?”
Sai Aisha ta mike tace “bari in karasa girki na”. Sai kawai ya janyota ta fado cinyarsa duk ta
daburce tana kokarin tashi kawai sai taji yayi hugging dinta ta baya gabadaya.
“Don Allah Uncle ka sake ni….” yai shiru, jin baida niyya itama ta share tayi shiru, baka jin
komai sai bugun zuciyoyinsu. Can kuma Hamma yace (in a cool tone).
“Yes, Haseenah was my girlfriend, naso aurenta, amma (she did something bad) da ya raba
mu. The worst thing da kika sani za’a yiwa masoyin gaskiya.
Kuma a kanta ne na rufe babin mata a rayuwata, wanda hakan yasa I feel Kaman duka daya
suke, dalilin ma kenan da yasa ban kuma neman wata ba, kuma ko an bani cikin ‘ya’yan ‘yan
uwana a family sai ince banaso….
Toh Aisha har saida Nenne ta nemomin aurenki da kanta, aka yi ban sani ba, don ta san inna
sani bazan yarda ba, amma tun ranar dana je asibiti duba Nenne, na ganki, na yaba dake a
raina Aisha, har na gayawa Nenne, nace wacece wannan yarinyar mai hankali haka….
Kinga dai kudin goro na yiwa mata, but you stood out, I was impressed with you”.
Long story short, tun a lokacinma da bansan ke matata bace, naji kin burgeni da attributes
dinki, kuma zama dake da nayi na dan lokaci na sake ganin me Nenne ta ganin min.
Aisha naga meyasa iyayena suka nemo min aurenki suka aura min. Kamar yadda kikace
addu’ar Nenne a filin Arfah ce ta fado a kanki wannan haka ne. don haka ke zabin Allah ce a
gare ni.
You are a light in my life and I am telling you you are shining so bright. Kinga duk ciwon dana
ji na rashin Haseenah? To yanzu godiya nakewa Allah da nayi wannan rashin nata, don I
wouldn’t have met you…
So don Allah ki cire maganar Haseenah a kanki, babu abun fushi a wurin, You my Dear kin
zama ‘ife mi, orun mi, iyawo mi’ kinji Aisha?”
Sai ta daga kai. A zuciyarta wani sanyi na zuba, ashe haka ake ji in mijinka ya fifita ka kan
kowa? That’s the Yoruba husband in action. Sai taji haushinnan yanata tsiyayewa… yana bin
rariya, ta gyara zata tashi ya kara riketa, yace,
“kin fahimceni yanzu?” Tace “yes Uncle” yace “Uncle ya dawo dai? Don Allah ya koma.
Ni ina murna kina ce min Hamma, daga nan in zama honey, watarana in dawo Sweetie, shine
kuma za’a koma Uncle dinnan, haba babyn Nenne da Dade”.
Sai kawai Aisha ta saki murmushi.
Tace “naji Ya Hamma” yace “ko kefa?” Sai tace “me kace dazu da yarbanci?”
Sai yace “ashe kina ji? To ki koya ki fassara mana”.
Aisha tayi dariya, sai lokacin Hamma yaji sanyi a zuciyarshi har da ajiyar zuciya.
Bakinsa daidai saitin kunnenta yace “Babyn Nenne da Dade kuma Babyn Hamma ko?”
Prince ya fada yana jin wani cool feelings for her, sai ta tashi da karfi zata wuce kitchen don
kunya sosai ta lullubeta, tana ‘yar dariya.
Hamma yayi maza ya dawo da ita jikinsa. Yaji dadin yadda yana mata bayani ta sauka, kuma
da gani har ranta abin ya wuce. She’s a very understanding person.
Sai Prince ya sake rungumeta sosai ta bayanta, yayinda take zaune a kan cinyar sa. Itama
Siddiqah sai tayi mukus…. Hamma ya kwantar da kansa bisa masangalin wuyanta… yana
sunsunar kasan wuyanta, duk sunyi shiruuuu na wani lokaci, kamar ruwa ya cinyesu. Bugun
zuciyoyinsu kawai kake ji wadanda ke bugawa a lokaci guda. Murya a sanyaye Aisha tace "Hamma, thank you for the explanation, nasan ba dole bane
kayi min bayaninnan, amman naji dadi da kayi min din, domin ya wanke min zuciya.
In sha Allahu kuma nima bazan qara fushi ba kan maganar nan".
Prince yayi murmushi, voice dinta yana caressing din sa, gabadaya wata kasala ce ma ta
sauko masa, yana ta kokarin dannewa.
Ya dai kasa magana yai shiru, ya rufe ido, listening to her soft sound, tana masa wannan
maganar cikin lumana da gamsuwa da abinda yace mata, and the softness of her skin dake
kwance a jikinsa yana kara tasiri a tare dashi.
Sai Hamma ya samu kansa da dan murza hannunta …. jin shirunsa yayi yawa bai amsa ta
ba, sai Aisha ta juyo kadan haka ta dubeshi. Sai ta ga Hamma da ido a lumshe, kamar mai jin
barci.
A tsanake tayi kokarin tashi daga cinyarsa, ya kuwa rike ta gam, ya dan bude idon yace
"ina zaki?" Aisha tace "abincin zan qarasa" yace "kashe gass din, we will eat out today, just stay
here…".
Aisha tayi shiru, ta koma jikin Prince ta kwanta tayi lamoo! Yace "please Aisha..... muje
outing din?" Tace "toh ai bacci kake ji naga", Hamma yace "bacci? Did i say so?" Ta ce.
"To ai Hamma idonka rufe yake fa tun dazu, ina ta maka magana bakaji ba, gashi ma
muryar bacci kake yimin".
Prince bai san sanda wani kasaitaccen murmushi ya kufce masa ba, he so much loves her
naivety. And she is observant, but totally ignorant ga halin da yake ciki.
Yes, yanayin sa gaba daya ya canza, wata muguwar sha’awa ce ta saukar mashi. It seems
with every word she says kara yayyafa ma wutarsa petrol take, amman babyn Nennen bata
gane ba. Wannan childishness dinnata yana kara burge shi.
Hamma yace "Ayshaaaaa…" tace "na'am Hamma" yace "ba bacci nake ba, I am just in a
mood!" Ya fada yana mata wata kallo, mai shiga rai da sanya kasala.
Har sai da Aisha ta tsargu don ya kara jawo ta jikin sa sosai, this time around juyo da ita yayi
tana facing dinsa gabagadi. Aisha tayi shiru, yace "baza ki tambayeni what mood ba?" Tace "toh
Hamma bacci kake ji, kuma ka kafe kai baka ji" ta dan turo bakin ta gaba, tana fada cikin
shagwaba 'yar gaske. Ai kuwa Prince ya sa ido yana kallon bakin da take turowa so soft and luscious, bai san
sanda yace "I really really want to kiss you saddiqa… "ya matso dab da fuskar ta, har suna jin
numfashin juna, ya kalle ta, cikin idonsa kadai ta ga tsantsar al'amuran dake cin zuciyarsa da
gangar jikinsa. An yi sa’a itama ta juyo kenan sai kawai Hamma ya hade bakinsu wurin guda ya
soma kissing Aisha-Siddiqah in a serious tone and passionate manner.
Da kyar Aisha ta samu ta zame daga Hammah, ta mike jikinta yana rawa a daburce tayi
hanyar kitchenette. Hamma da kyar ya iya mikewa yanakokarinsaita kansa. Yabi bayanta yana
cewa cikin basarwa,
“you know what? Jeki shirya kawai ki bar girkinnan, we are going out, ma ci a waje”.
Tace “toh”, sai ga Nenne ta sake kira.
Tace “ni Hammansu dazu maganar bikinsu Princesses na kira zan maka na manta, an saka
rana, kwanaki goma masu zuwa. Don Allah ka taho da Aisha, kuma kuzo da wuri. Asabar ne
daurin aure wato ranar addu’ar arba’in din Sarki”.
Prince ya ce “toh Nenne, in sha Allah”.
Itama Aisha sai murna lokacin da Hamma ya gaya mata zasu tafi gida Lagos sati mai zuwa,
tace “bikinsu Firdausi za’a yi?”
Yace “eh, za’a hada da addu’ar arba’in na Emir. Shine babban burinsa kafin rasuwarsa wato
auren twins din gidanmu”.
Siddiqah tayi ta murna har ‘yar rawa ta shiga takawa a wajen, ta manta shaf a gabansa take,
irin murnar zata gida dinnan, after a long while.
Hutun Prince ya dade da karewa, zuwan Siddiqah ne yasa ya kai har wannan lokacin a
Argentina.
Sun fita a daren sun shakata, suka ci abincin dare a wani Arabian Cuisine sannan suka dawo
gida.
Aisha ta nufi dakinta tayi wanka ta sha rigar barci mai dan kauri purple ta fesa turarukanta
masu dadin kamshi ta nufi dakin Prince.
Nan ta tadda shi daga shi sai short nicker akan sofa yana shan ‘chamomile tea’ kafin ya
kwanta. Ta na shiga Hamma ya dago yana dubanta da wani kallo da bai taba yi mata ba, domin
sha'awar matarsa ce zallah yau cikin idanunsa da duk abinda yake yi. Aisha ta juya da sauri
zata koma ganin ba suttura a jikin Hamma sai gajeren wando, ga kunya data kamata sai ya aje
kofin hannunsa, yace Aisha wait, ya taso ya isa gareta ya kamo hannunta ya shigo da ita cikin
dakin yana cewa.
"Ya kinzo turakar miji neman albarka kuma zaki koma?"
Aisha duk ta daburce ta rikice tarude, sabida yanayin da Hamma ke mata magana yau ya
sha banban dana koyaushe. Ba don ta kasance mai karfin ji bama, da bazata ji shi ba.
"Dama-dama... zuwa nayi ince maka Hamma saida safe".
Hamma ya dora hannuwansa biyu bisa kafadun Aisha hagu da dama yana murzawa. Ya dan
mutstsuka jijiyar wuyanta cikin wani salo na tasowar muguwar sha'awar da baisan akwai a
tareda shi ba, saida Aisha ta runtse ido sabida tasowar tata sha'awar ta diya mace, kafin
hannunsa ya kai kansa saman kirjinta. Yace "saida safe dinma ai irin haka ake fadarsa Ayshahhh, ba da fatar baki ba. You my dear
I want to kiss you again today!".
Hamma ya fada admiringly idanunsa akan siraran lips din Aisha, yana musu wani inviting
looks. Aisha ta kusa narkewa bakidayanta domin a lokacin Hamma ya matsota sosai ne a
jikinsa, ya isa cikin nutsuwa ya hade bakinsu wurin guda ya soma sumbatar Aisha a tsanake,
sannan ya koma kissing hungrily. Ashe namiji duk dadewar sa babu aure, ba sai an koya masa sumba ta auratayya ba? Ko da
kuwa ya fidda rai da ita, ko bashi da sha'awar ta, sanda zata sameshi zai ji tane tana sarrafashi.
To hakan ce ta faru da Prince Abdulrasheed yau. Da ya samu kissable lips din Aisha yau ya
dinga tsotso tamkar Allah ya aikoshi, saida ya ajiye kishirwar shekaru masu yawa na kuruciya
dana shiga girma.
Aisha kyale Prince tayi ya yi yadda duk yake so yau, ya jagwalgwala ta iya son ransa a duk ta
inda yake so. Ya tsotse duk abinda yake so. Kuma shi da kansa yayiwa kansa limit. Don yana
ganin in ya kauda budurcinta any moment zata iya conceiving, shikuma yana ganin kamar bata
yi kwarin da zata haihu ba. Tunda har ya samu wannan access din zai iya karawa Aisha lokaci. A kwanaki goma da suka biyo bayan wannan ranar, wata wawuyar shakuwa ce ta shiga
tsakanin Hamma da Aisha. Suna kwana a gado guda, Hamma saida ya san yadda yayi ya fara
raba Aisha da dukkan sittirun jikinta in zasu kwanta, yana rabar Aisha da dabara da wayau da
simple hugs, da light kiss masu sawa ta saki jiki da shi, su yi barci manne da juna. Tun Aisha
matukar jin nauyi da tsoro har ta soma sakewa da Hamma sosai. Don ta lura ba shi da nufin
abinda take tsoro. Kusan sati biyu kenan irin rayuwar da suke yi a cikin gidan kenan, full of
understanding, intimacy and love, Hamma ya zama baya iya barci bai raba jikinsa dana Aisha
ba, bai sumbaci bakinta da kirjinta yadda yake so ba amma bai taba wuce hakan ba yake
takawa kansa birki, don a ganinsa har lokacin Aisha bata yi girman data isa ya dora mata
hidimar dake cikin aure yanzu ba kada tazo haihuwa ta samu matsala.
Amma me? A na I gobe zasu tafi Lagos komai kwace masa yayi, ya kasa controlling kansa
yadda ya saba duk kuwa da yana tausayawa Aisha, da kyar da roko da magiya harda kuka
Aisha ta kwaci kanta a hannun Prince domin kuwa gani take duk ranar da hakan ta faru ba wata
wata mutuwa zatayi, in tayi la'akari da irin yanayin da Prince ke shiga a irin wadannan lokutan
akanta.
A satin dasu Prince zasu dawo Lagos Dade yasa aka je aka shirya gidan Prince na Banana
Island, wanda ke daura da gidan mahaifinsa, Prince ya jima da sayen gidan bai taba amfani
dashi ba, tun kafin saukarsu Dade ya gayawa Nenne in sun zo a gidansu zasu sauka. Yasa aka
gyara gidan aka shigar komai da zasu bukata. Tun saura kwana uku daurin aure suka sauka a Lagos. Gidan ya debi murnar zuwan su
ba babba ba yaro, kowa murnar zuwan Hamma yake yi, ga ‘yan biki sun soma isowa daga
sauran jihohi. Kiki ce kawai bata samu zuwa bikin Aunties dinta Princesses ba, don tana shirin
rubuta jarrabawarta ta karshe a Informatics a lokacin. Aunty Murjanatu Taiwo tana Ilorin, sai bayan addu’a zata taho Lagos tare dasu Nenne in sun
je. Dade yace su Hamma su fara sauka a Lagos su huta kwana biyu, in yaso sai su dunguma
duk gidan zuwa Ilorin su samu adddu’ar Sarki ranar asabar, wadda ta kasance kuma ranar
daurin auren su Fatima. Nenne ta rasa ina taka saka ina taka aje da surukarta Aisha, wata sabuwar kauna da
soyayya Nenne take yiwa Siddiqah musamman data gane suna zaman lafiya itada Hamma,
Aisha ta samo kansa shima ya samo nutsuwarta, Nenne bata taba jin Hamma cikin farin ciki da
nishadin data ji shi ciki ranar da suka yi waya itada su, tana tsammanin Siddiqah ciki gareta ba.
don haka tun kafin saukarsu a Lagos yau Nenne da kanta ta shiga kitchen ta shirya abincin
tarbar Hamma da Aisha, ta hada dana Dade, girki tayi masa na musamman data tabbatar
Hamma ya dade bai samu irinsa ba, wato (Locust Beans Stew) da suke kira Dindin da (Ofada
Rice).
Bayan saukarsu da kadan Dade yace ma Prince a gidansu zasu tare, yasa an shirya musu
komai da zasu bukata. Don haka ana gama cin abincin dare Dade yace Firdausi ta dauko keys
din gidan ta baiwa Hamma, ta yiwa Aisha rakiya kuma.
Anan Nenne tace “a’ah Dade, ita kam Aisha ta zauna ta huta anan, a bari sai bayan biki
sannan ayi tarewar. Ta jima bata nan akwai bukatar ta huta tukunna”. Ai kuwa nan da nan
Prince ya canza fuska. Domin a yau kam yayi niyyar angwancewa da amaryarsa Siddiqah babu
daga kafa. In yaso idan ciki ya samu ya tayata nakudar. Yanzu kuma Nenne tana wani zance
wanda zuciyarsa ta gaza dauka, wai Aisha ta zauna da ita har bayan biki, duk kokarinsa na
rainon da yayi tayi wata da watanni ba’a gani ba, sai rana daya da ya saka ran hutawa.
Har dai rashin jin dadin hakan ya gaza boyuwa a fuskarsa, ‘yar damuwa ta nuna a fuskar
Prince, amma dai bai yi magana ba. saidai tuni Dade da yake shi namiji ne ya ramfo shi.
Lura da yanayinsa da Dade yayi, sai yace.
“Kehinde kodai kafi so ku tafi tare yanzu ne?” Zuruf! Aisha tayi tace “Dade ayi hakuri don
Allah ni nan zan zauna gun Nenne har a gama biki, nayi kewar Nenne for long”.
Taki dago ido balle Prince ya kalli kwayar idanunta. Domin ta riga ta san Prince ya gama
kaiwa kul a a dalcinsa. Daren tahowarsu da yaya ta tsira? Balle yanzu a gidansa na gado?
Takaicin abinda Ausha tace yasa shima ya hadiye, yace “a’ah Dade, ba wata matsala a kyaleta
ta sha zamanta”. Amma Kai da ji kasan shagube ne yayi. Ya ajje spoon ba don ya koshi ba, sai don bazai
iya cigaba da ci ba’a gane ransa ya baci ba, da abinda Aisha tayi masa a gaban kowa ta nuna
bata damu dashi ba, ya mike yace zai je gidansa ya huta. Bai sake kallon inda Aisha take ba ya
nufi hanyar fita falon. Anan ne Nenne ta dubi Aisha tace “raka shi zuwa mota mana Aisha” Hamma, wanda a
lokacin har ya kai bakin kofa cikin matukar kulewa zai fice, yace.
“A’ah Nenne na yafe, ta zauna kawai, na gode”.
Wannan gwasalen da Hamma yayiwa rakiyar Aisha, duk ya faru akan idon amare Princess
Fatima da Princess Firdausi, don tare aka zauna cin abincin har dasu gabadaya.
Abin yayi matukar yiwa Fatima dadi, na yadda Prince ya nuna bai damu da Aisha a gaban
kowa ba. ita bata fahimci haushi