Showing 33001 words to 36000 words out of 40544 words

Chapter 12 - Aishah-Saddiqa 4 end Complete Novels by Sumayya Takori.pdf

Abdulmajeed da tazo a lokacin
tareda Taiwo suka kawo lefen gidansu Aisha da daddare.

Sai ga Taiwo har dakin Aisha yau, tana cike da 'guilt' mai yawa, Don gani take hatta lefen
nan sabida ita aka yi shi. Ta kara jin nadama mai yawa. Sai ta bige da yiwa Aisha hirar Kiki, ta
gaya mata Kiki na tafe sati biyu masu zuwa, kuma da tazo za'a saka ranar aurenta da Tosin.
Nenne kuwa taji dadi da akayi hakan, ko ba komai anyi drawing attention dinsu zuwa ga
abinda yake cikon al'adar aure ga Hausa/ Fulani.

Taiwo ta sanar da Haj. Zainab sakon Nenne na cewa ita zata wuce Lagos da Aisha idan ta
gama jamb dinta ranar asabar, to lahadi sai su tafi.
Haj. Zainab dai basu gaya mata zasu kawo lefe ba, don haka duk a dame take da rashin
shirya musu komai bisa al'ada su kuma Nenne sun yi haka ne don kada su tasheta tsaye inji
Nenne, duk da haka sai ta aika Sunusi ya kira Baba Furaira ta karbi lefen. Suka bada tukuici na
kudi Inji Baba Barau. Aka rabu cike da farinciki da godiya ga juna. Don haka Umman Aisha ta dukufa da yiwa Aisha gyaran da tuntuni take son yi mata cikin
kwana biyun daya rage musu. Tasa an yiwa Aisha halawa da Dilka mai kunshi kuma tazo har
guda ta rangada mata irin black and red henna dinnan. A gefe kwararriyar mai kitso tayi nata

aikin, kitso yiri-yiri ta yiwa Aisha kamar da allura ta tsaga shi irin na 'yan Maiduguri.
Sai ga Aisha ta fito tas a cikakkiyar amaryarta tana sheki da sparkling. Abubuwa ne da tun
wancan lokacin Haj Zainab taso tayi mata bata samu dama ba sai yanzu. Don haka Aisha ba
karamin gyaran amarci ta samu ba, ta fito tayi das da ita.
Washegari Asabar Malam Yunus da kansa ya kai Aisha yin Jamb a location din da zata
zana, Jamb dinda Aisha ta kallafawa rai yau Allah yayi an zana ta. Tun 7:30 suka fita karfe 8
suka shiga kuma kafin 10 Aisha ta gama. Abbanta ya jirata har ta kammala ya dawo da ita gida.

A daren Aisha suke sallama dasu Umma. Sun raba dare suna hira, Nenne ma ta bugo taji
yaya Shirin tahowar tasu ta gaya mata ta gama shiryawa, sallama suke itada Umma. Aunty
Taiwo tace sai 11 zasu zo su dauketa su zarce airport.

Hakan kuwa akayi. Malam Buhari da Taiwo a kofar gidan su Siddiqah 11 na safe tayi musu.
Aunty Taiwo ta shigo suka gaisa da Umman Aisha, sukayi sallama, Sunusi ya kai kayan Aisha
mota, ta rungume Umma, ta sake rungumeta. Har ta fita soro ta dawo ta sake rungume Umma
ido fal kwallah. Umma dariya da dauriya duka, tace. "Petel dina, zanyi kewarki! Allah ya tsare yayi albarka mai yawa".
**** **** ****

Su Aisha sun sauka Lagos da tsakar rana, nan suka tadda tarbar Nenne ta alfarma. Ga
abinci (Yoruba traditional food) da fresh juice din kankana da apple Nenne ta shirya musu. Ga
yoghurt da ta yiwa Aisha na musamman. Aisha na bude warmers din taga Ewedu ta hau dariyar
farin ciki, tasan tayi kewar kalolin abincin Hamma har mafarkinsu take amma ashe Nenne ta fita
sanin su take marmarin ci. Nenne kamar tasan me takewa dariyar, tace “shiyasa nayi miki su ai,
na san rabonki da Yoruba food tun barinki Lagos”.

Prince ya gama yiwa Aisha duk wani shirin tafiyarta Qatar tuntuni, a yadda ya tsara
washegari Litinin zata bar Lagos ta sameshi a Qatar. Amma sai Nenne ta ce ta daga tafiyar
Aisha Qatar sai alhamis, saboda zasu tafi Umrah ita da Dade alhamis din, kuma Qatar airways
zasu bi. So zasu taho da ita kawai su kawota da kansu, dama last time bataso tafiyar Aisha ita
kadai ba babu 'yan rakiya don dai umarnin Emir ne.
Don haka yanzu da kansu zasu taho da ita su kawota sannan su wuce Umrah.
Prince ko kadan bai so hakan ba, amma dai yace "toh Nenne Allah ya kaimu".
Wannan daga zuwan na Aisha daga Monday zuwa alhamis da Nenne tayi ya baiwa Prince
damar yin settling sosai, bayan komawarsa Qatar, don ashe aiki ne damqam yake jiransa bai
sani ba, wanda zaiyi in ba shi ba. A cikin ayyukan da ya tarar akwai zuwa consultation na aiki
kasar Singapore sati mai zuwa. Kuma in yaje sai yayi sati biyar acan. Tafiyar ta kama masa sati
daya da dawowar Aisha gidansa, tunda sai upper week.
Har ila yau, daga zuwan nata da Nenne tayi zuwa alhamis sai ya karawa Prince wani irin
dokantuwa da zuwan Aisha fiyeda na baya. Don haka ya shiga gyaran gidansa domin taren
Siddiqah. Yasa aka fidda duka furniture din gidan tun daga gado har kujeru ya saka sababbi
farare sol. In bai manta ba Kiki ta taba gaya masa ya kamata ya sakawa Aisha sababbin
furniture, a wancan zuwan nata Argentina. Tace amarya komai sabo ake saka mata.

Ba furniture kadai ba hatta curtains din gidan da rug carpets saida Prince ya canza da
samfurin zamani kirar jiya-jiya (latest arrivals).
Kayan cefane kuwa ba abinda bai sa an ajiye mata ba, tun daga kan gishiri har tsinken
sakace, kai har da wadanda Aisha bazata bukata bama daga zuwanta, duk Prince yasa yaron
gidansa na Qatar wato Zaid ya ajiye mata.
Wato bayeraben miji in ya tashi soyayya da dukkan zuciyarsa yake yin ta musamman mai
shekaru da cikar hankali irin na Hamma Prince, don babu rawar kan kuruciya a tareda shi da
zuciya daya yake son Aisha yake kuma hidimtawa soyayyar.
Kai lallai shiri ba dan karami ba na hango Kehinde na yiwa Aisha. Sai mu ce amarya Aisha
Allah ya kiyaye hanya ya kawo kazantar daki.

Ya shirya mata lafiyayyen dakin barci dab da nasa, bayan master bedroom da zasuyi sharing.
Babu abin da babu na bukatar mace ‘yar gayu a dakinnan na Petel Siddiqah.

Wannan gidan da Prince yake ciki is not a Ranch House, gida ne da Qatar Refinery suka
bashi don ya zauna yayi musu aiki. Gidan 'penthouse' ne. Ranch House da Polo Horses dinsa
duka suna can Argentina.

To dama Qatar wajen da yake aikinsa ne kawai, baya Polo a Qatar sai ya haura kasashen
turai ko Argentina yake yin abinsa.
**** **** *****

Nenne ta gama ma Aisha duk wani shiri da ake yiwa amare 'yan kabilar Yoruba wadanda za'a
kai gidan miji karo na farko, har ciccibin nagge Nenne ta dafa mata ta cinye ba tareda ta san ko
menene ba. Aisha ta sha mamakin ganin Aunty Taiwo bata koma gidanta ba tun saukarsu, ta
tare ma a dakin Princess Fatima. Kuma da alama zaman gida take. Bata tambayi komai ba amma ta gane akwai matsala a
auren Aunty Taiwo yanzu, shiyasa ta dawo gida.
Ranar Alhamis kamar yadda suka alqawartama Prince Nenne da Dade da surukarsu Aisha
Siddiqah Yunus, suka daga cikin Qatar Airways, daga filin jirgin saman Murtala Mohammed na
jihar Lagos.
Tun jiya Dade ya gaya masa lokacin tasowarsu da landing time.

A cikin jirgin, Dade da Nenne suna a first class Q suites na Qatar Airlines (aisle seats), so sun
rufe kofar ya zama kamar daki suna hirarsu, Aisha kuwa na jikin window ta kwantar da kanta
akan wuyan seat dinta, tayi shiru cikin tunani, tana tuna waccan tafiyar tata ita kadai zuwa
Argentina, da abubuwan tarihi da suka faru cikin tafiyar. Har gobe bata san hikimarsu Dade ta
tura ta ita kadai da farko ba a wancan lokacin, saidai da yake Nenne ta gaya mata daga baya
cewa Allah ya jikan rai Emir ne yayi umarnin hakan.
Ita da kanta daga baya take tunanin watakila hikimar Maimartaba Emir of Ilorin na yin hakan
shine basa son tursasashi yayi welcoming dinta, wato ya zamanto ya karbeta karba irin ta ganin
idonsu, su tafi ya canza mata zuwa true colour dinsa, sun barshi yayi deciding yadda zai
karbeta don radin kansa.

Bata san meyasa ba tafi jin dadi da kwarin gwiwa har ma da karin ‘self-confidence’ na isa ga
Hamma yau, da fara sabuwar rayuwar meaningful aure tare da shi, da ya zama cewa su Nenne
ne suka kawota da kansu yanzu.

Har sukayi landing a Qatar, Aisha bata jin me suke cewa cikin hirarsu, wadda suke yi da
yarbanci, wani lokacin su cakuda da harshen fulatanci, duk dai suna tattaunawa ne akan
sha’anin rayuwar ‘ya’yansu da matsalar auren Taiwo. Da alama a irin wannan trip din kadai
suke samun lokaci su tattauna extensively akan ‘ya’yansu irin haka. Ita daga karshe ma barci tayi, bata farka ba saida aka ce cikin bututun magana kowa ya
daura belt, jirgi zai sauka a Qatriyyah.

Prince daga office dinsa kusan duk bayan minti biyar sai ya duba agogon swatch din dake
hannunsa, tun kafin lokacin saukarsu ya cika ya yanke duk abinda yake yi ya taho filin jirgin
daukarsu Nenne. Jirgin su Aishah na sauka shima yana shiga reception na tarbar baki, don
haka Prince baiyi zaman dogon jiransu ba. Aisha ce ta fara fitowa rike da jakar hannunta data Nenne, kafin su Nenne su biyo bayanta.
Prince ya runtse ido ya bude yana kallon beautiful Aishah… tana takowa majestically zuwa
gareshi, da wani madaukakin murmushin SO a fuskarta, hamdala yake a zuciyarsa, sai kuma
ya hango Nenne daga bayanta itama ta taho, tana taku ita kuma cike da sarauta. Prince ya
karasa da hanzari ya fara rungumar Nenne, sannan Dade, kafin ya dawo ga Aisha ya
rungumeta itama, yace “Aysha welcome oooo, sai yau Nenne ta gama boyon naki ta kawo
min?”
Dade yayi dariya, Nenne ta harareshi, Dade yace “yaushe muka boye ta din? Daga cewa
zamu yi mata rakiya?” Duk suka yi dariya, nan Hamma ya karba mata jakunkunan hannunta, ya
sake rungumota jikinsa yana cewa “welcome Aysha! Welcome oooo!”. Daga haka suka wuce
mota.
Kasancewar Dade da Nenne duk sunada ‘Entry Visa’ na Qatar kuma zasu yi transit na
awanni hudu a Qatar sai suka yi amfani da wannan damar suka rako Aisha har gidanta.
Prince na tuki akan hanyarsu ta isa gidansa, amma hankalinsa rabi na kan Aisha wadda
jikinta duk ya nuna gajiya da lalaci, ta dauko wayarta daga jakarta ta kunna, ta soma kokarin
roaming layinta domin ta samu ta kira Umma da Baba Yunus, ta gaya musu saukarsu lafiya
amma ta kasa connecting. Duk wani motsi da Aisha tayi a cikin motar sai taji idon Prince Abdulrasheed a jikinta, kai har
a ruhinta, ita kuma ta ki yarda su hada ido da gangan kada taje ya bata kunya, don tun daga
rungumar da yake mata a gaban su Nenne ta san komai ma zai iya (that’s his real identity of
Yoruba demon), gashi duk dagowar da tayi sai ta hango Nenne ta cikin mudubin gefenta, wadda
ke zaune a kujerar bayanta, Nenne waya take yi da Fatima a lokacin bata maida hankali a
kansu ba sam. Aisha ce dai duk ta ji ta takura da idanun Prince dake yawo a jikinta. Kuma
idanun nasa sun rikitata.

Finally, Abdulrasheed ya kashe motar a muhallinta wato ‘parking lot’ na kofar gidansa, yaron
dake kula masa da gidan wani baqar fata ne dan Senegal mai suna Zaid, kuma har ila yau, Zaid

is a good Chef for him, tun kafin su iso ya gama girki na musamman na larabawa, ya shirya a
dining sai jiran isowarsu bisa umarnin Ogansa, tunda safe Zaid ya shiga kitchen yake aiki
saboda zuwansu. Zaid ya shirya Lamb mandi, kebabs, fatoush salad, humus, Baba ganoush,
ga kuma desserts da bakhlava ga arabic coffee. Duk ya tanadar musu kamar mai hada wata
‘yar kwarya-kwaryar get together. Saidai ba wai yayi da yawa bane daidai cin abincin mutum
4-5. So already table was set before their arrival.
Suna shigowa Prince ya budewa Aisha dakinta ya shigar mata da akwatinta ya ce “your
room”. Su Nenne ma, ya bude musu wani dakin yace su shiga su yi alwala da sallah, nan ne
Nenne ta gane Hammah yayi gyaran gida sosai, ta yaba mashi bisa wannan kokarin ta kuma
dan tsokane shi da fulatanci “da angon Aisha ka sha kamshi, na Siddiqah bada kanka a sare”,
nan dai duk suka yo alwallah har Aisha, Hamma ya jasu sukayi sallahr jam’i gabadaya, sannan
suka fara cin abinci cikin nutsuwa suna yi suna duba agogo.
Da suka kammala Nenne tace a bata ‘black tea’ (lipton) ta kara, saboda Nenne bata shan
coffee ita. Prince da kansa ya dafo shayin a kettle din dafa ruwan zafi, ya hado ma Nenne a kan
tray da mug cup da liptons kala-kala na alfarma da yake ajiyewa don baki don shi in ka cire
chamomile da lavender ba shayin da ya ke sha, ya ajiye mata bakidaya liptons din kala kala don
ta zabi wanda tafiso cikin su, (and honey instead of sugar) don Prince baya shan sugar sai
zuma.

Nenne na sipping zazzafan lipton Dade ya hada Prince da Aisha yana musu nasiha a tare. Ya
ja hankalinsu kan su hada kansu su zauna lafiya, su zama sirrin juna, su kuma taimaki junansu
akan komai. Yace ma Aisha, ko me Prince zai mata na rashin kyautawa ta doshesu kai tsaye.
(They are always there for her) muddin suna raye. Ya roketa kada ta kara dosar iyayenta da
matsala inba a inda taga sun gaza daukar mataki ba.
Shikuma Prince Dade yace dashi “har kullum ka tuna Aisha mace ce, kuma mai kankantar
shekaru a kanka.
Yadda duk ka mikar da ita a haka zata girma.
Don haka sai ka nuna mata abinda kakeso da wanda baka so a hankali.
In tayi kuskure ka nuna mata ta lalama da jurewa kuruciyarta.
A karshe suka saka musu albarka shida Nenne, a bisa biyayyar da suka yi musu, suka roki
Allah ya basu masu yi musu mafiyinta da gaggawa. Ya kuma sa ‘ya’yansu su kasance nagari
masu bin iyaye kamarsu”.
Dade yace “saura ke Nenne ko?” Tace “ai you have said it all Dade, banida abin cewa,
addu’a kawai zanyi musu, wadda kullum bana fasawa. Allah yayi musu albarka da zuri’a
dayyiba albarka Annabijo”.
Daga haka duk suka mike, Prince ya dauki mukullin mota don ya maida su, yace ma Aisha,
“Ayshah ki rufe kofar falon ta ciki, in na dawo zan bude da key dina, idan Zaid ya tattare
wajennan ya tafi”. Ya gaya mata akwai yaron gidan, mai suna Zaid, amma baya kwana a gidan,
da safe yake zuwa ya tafi karfe 6 na yamma in ya gama masa dinner. Har sun fita tare dasu Dade sai yai excusing dinsu ya dawo kamar yayi mantuwa. Da
sassarfa ya isa ga Aisha ya rungumota ta baya tana kokarin rage nauyin laffayar jikinta. Aisha
tace cikin ‘yar rawar murya “Hammah, mantuwa kayi? Kada suma kasa jirgi ya tashi ya barsu
fa?”

Prince kamar bai ji korafinta ba, ya sunkuya ya sumbaci bakinta dake maganar cikin
shagwaba so lightly yayi sumbar, sannan a daidai kunnenta yace cikin shauki.
“Welcome Ayshah.. welcome to your abode! The lady of my heart, love of my life, mother of
my children, the one that has completely changed and shaked my whole universe. I am coming
back soon to welcome you Baby, kin ji?”
Ya sake kai mata sassanyar sumba a wuyanta da lips dinta, amma Aisha bata barshi yayi
nisa ba ta kwace bakinta cikin jin kunya, tace cikin shagwabar da bata zuwar mata sai in tana
gaban Hammah Abdulrasheed kadai.
“Hamma Abdul mana?! Dade da Nenne, suna bakin mota suna jiranka fah?!”.
Prince da kyar ya juya ya fita kuma da baya da baya, yana sumbatar hannunsa yana huro
mata iskar, ita abinma sai ya bata kunya da dariya, tasa tafukanta ta rufe fuska tana kallonsa ta
tsakanin yatsunta cikin idonsa da wani irin kallon SO, wanda yasa Prince yin tuntube a bakin
kofar fita.
Da kyar Hamma yakai bakin mota, su Nenne dai tuni sun bude sun shige basu kara bi ta
kanshi ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login