Showing 15001 words to 18000 words out of 40544 words
Chapter 6 - Aishah-Saddiqa 4 end Complete Novels by Sumayya Takori.pdf
ni ba, ba ki
da sauran haske a idanuna amma har gobe kina nan a ‘yar uwata sai ranar da ki ka gyara
barnar da ki ka yi min”.
(Duka wannan maganar Prince ya furtata cikin harshen turanci ne).
Daga haka ya fice ya barta a dakin idanunsa sun kada zuciyarsa ta tabu. In duniya da amana
Taiwo bazata zame masa cikas ga cikar farin ciki ba. Komai nashi nata ne da ‘ya’yanta haka
komai yake yi a duniya su yake tunawa da samun farin cikinsu. Bashida wani buri da ya wuce
itada ‘ya’yanta amma ace wai abu guda daya da ya nuna yanaso, Taiwo ta gagara son shi. Dakin Nenne ya nufa, sai ya tarar ta rufe da key ta ciki, don ta san dole zai biyo bayanta da
lallashi akan batun biko ita kuma so take ya dau mataki da kansa, tafi son ya gane da kansa
Taiwo fitinanniya ce abinda bai taba yarda a baya ko za’a shekara ana fadin cewa Murjantunsa
tana da hali. Itada ta haifesu ma ta kwana da sanin hakan amma shi bai taba yarda. Haka ya bi
bayan Dade shima a nasa masaukin, Dade ya ki ganinsa a daren don har ya kwanta, dan
lekowa yayi kadan ta tsakanin kofar bai bashi hanyar shiga masa dakin ba, ya ce.
“Please Kehinde, ka yi duk abin da ya dace da kanka, but count us out akan maganar
Siddiqah da Taiwo, duukansu naka ne, ba wadda zaka zaba ka bar daya, amma akan maganar
aurenka mu mun gama sauke nauyin duk da Allah ya dora mana a kanka, don haka duk wanui
kalubale na rayuwar iyali sai ka nemi hanyar managing dinsa da kanka”. Auren Princess Fatima da Princess Firdausi kenan bai zo wa kowa a iyalin Engr. Idris Akanni
da dadi ba. Taiwo ta bata musu armashin komai don events na al’ada har uku Nenne ta soke, ta
ce za ta koma Lagos. In yaso dangi su kai amaren gidajensu haka, tunda an gama mai wuyar
daurin aure, sa yi dinner washegarin tarewa a gidan mazajensu.
Shi kuma Prince ta ki yarda ma ta ganshi har washegari tana doje masa da uzurin mutane
sun mata yawa bata da lokacin kebewa dashi, shirin komawa Lagos suke yi itada Dade. Don
haka Hamma Abdulrasheed Prince ya zama wani sukuku da shi a gidan, don Taiwo da zai
samu ya kara hucewa a kanta da sassafe ta fice ba wanda ya san ina ta yi, kamar ta san ya ci
alwashin sake cin ubanta da cin mutuncinta in style, ganin ta jawo hatta iyayensa sun daina
sauraronsa akan laifin da ba nasa ba balle Siddiqah data dangwarar masa da wayarsa a inda
yake tsaye, balle ya samu damar communicating da ita ya lallasheta kafin iyayensa su yarda su
saurareshi asan abinyi a kanta.
Ba da sanin Prince ba Dade da Nenne da safiyar washegari suka kira Taiwo ta waya cewa
tazo masaukin Dade suna kiranta.
Ba ta dade da dawowa gidanta ba don ta zame musu, ta yi sammako ta taho gidan ta,
shigowarta kenan daga main house din kiran Dade ya sameta, kuma as usual Toafeeq ba ya
kasar. Daga ita sai babban danta Hakeem a gaban motarta lokacin da dade ya kira ta.
Tare suka zo da Hakeem, tana sane ta taho dashi wai ko sa ga girman danta da yawan
shekarunsa su raga mata, don ta san dai tatsuniyar gizo bata wuce koki ita kuma tunda Kehinde
ya ce ya daina ganin haskenta akan Aisha, to kowa ma yayi kadan yasa ta so Aisha (she is very
sorry to say) hatta Nenne da Dade saidai suyi mata fada irin wanda suka saba ya bi ta bayan
kunnenta a wuce wurin.
Dade ya ce da Hakeem ya je ciki za su yi magana da Murjanatu, don haka Hakeem ya tashi
a falon yayi musu sallama ya barsu, ya koma mota ya tafi gida.
Taiwo ta shigo masaukin mahaifinta, a zuciyarta ta rasa abinda ke mata dadi da abinda
Kehinde yayi mata akan Aisha, wato ya zabi Aisha a kanta, a kan wata banzar yarinya ‘yar
talakawa da bata ko kai matsayin house girl dinta ba Kehinde ya gaggaya mata magana haka.
Ta kara tsanar Aisha Siddiqah, ta kara tsanar duk wasu ‘ya’yan malam Shehu irinta. Tana
wannan tunanin ta yi sallama a kofar dakin Dade ta isa ga kofar falon ta bude. Taiwo ta ga uwa
da ubanta fuskokinsu kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas, ta tuna when last ta ga Dade ya
hade fuska irin haka, Taiwo duk ta tsargu, don ta san ba banza ce ta sa suka kirawo ta ba, ko
daga fuskokinsu, Dade ne ya fara magana inda ya ce
“da gaske ne abinda akace kin yiwa matar Kehinde?
In haka ne kuwa baki yi halin Nenne Sappa ba Taiwo. Balle me sunanki Olori Murjanatu.
An yi asarar kudin tara dai, kin zama babbar banza da wofi”.
Yana fade cewa cikin fushi mai tsanani da harshen yarbanci.
“Mu ba mu gaji cin zarafin dan Adam ba, saboda kawai Allah ya ba mu sarauta, ya ba mu
aron ni’imar rayuwa daga cikin arzikinsa.
Allah da kansa da ya halicci dan Adam ya karrama shi, ke wace ce da za ki wulakanta dan
Adam mai daraja a wurin Ubangijinsa?”
Dade yarbanci kawai yake saki tamkar ya fasa kunnen Taiwo, irin zazzafan yarbancin nan
mara dadin ji da razanar da wanda ake yi mawa.
Nenne da bata taba ganin bacin ran Dade irin na yau ba, ba ta sanshi da fushi irin wannan
ba, don hak ita kanta ta tsorata da temper din da ta gani tare da shi, Taiwo tana durkushe a
gabansa, jikinta na rawa da bari, Nenne kuma ta ce cikin daga murya,
“in duniya da halacci har Taiwo ce za ta zagi matar Kehinde? Ko kunya baki ji ba? Iya kara a
rayuwa Kehinde yayi miki, keda ‘ya’yanki da zurri’arki. Murjanatu baki kyauta ba sam, kin ci
amanar tagwaitaka da zumunci. Haba! ai inda alkawari ko na munafurci ne ya kamata kiso
Aisha, tunda kince kina son abunda yake so, ko ba kya son ta bazaki nuna ba ablle gaba da
gaba haka, hakan shine adalci ga dan uwanki kuma da abinda kadai zaki saka masa dawainiya
da soyayyarsa gareki da Kiki. Wato kiso iyalinsa. Taiwo a shekarunki sama da arba’in kin san hakan, bakya bukatar sai an tuna miki, amma
mun tuna miki, a matsayinmu na iyayenki, ya rage naki ki dauki tunasarwar ko a’ah a wannan
gabar, in kuma halin tsiya halinki ne ki yi ta yi duniya ce. Amma ko Kiki duk wautarta ai ba ta
rashin hankalin dake uwarta Taiwo ki ke yi”. Dade kuma yace “Afuwa daya zan yi miki Taiwo shi ne, in kin je kin gurfana gaban Malam
Yunusa, kin mayar da kalaman da ki ka jefe su da su daga bakinki mara saiti, kin dawowa
Kehinde da matarsa dakinsa”.
Daga haka suka fice. Suka bar Taiwo a durkushe a wurin.
Taiwo sai kuka ta ke tana tsine wa wadanda suka kawo Siddiqah duniya.
Ba su jima da fita ba, Taiwo ta mike ta koma gidanta, nan ta hau hada kayanta.
Bari kawai ta hakura da aikin asibiti daga yau, ta koma wajen mijinta dindindin. Za ta wuce
gidanta na Lagos, daga can ta yi shirin wucewa UK. Ba ta jin nan kusa za ta zo Ilorin balle gidan
iyayenta a Lagos, tunda sun sallame ta a kan Siddiqah.
Ba wani biko da za ta je wa Kehinde, tunda shima yace bata da haske yanzu a idonsa. Yo da
aurensa da wannan yarinyar ai gara mata zamansa yadda yake shi kadai a baya, da
Dawakansa da soyayarsa da da kulawarsa gareta.
“Shin me ke damun Murjanatu-Taiwo exactly?”
Tambayar da iyayenta ke yi wa zukatansu kenan a ranar har suka koma Lagos, Kuma a
washegarin ranar da suka koma suka ji labarin Taiwo ta baro Ilorin itama zuwa Lagos, kuma wai
tayi resigning daga aikinta na asibiti, ba tareda ta yi shawara da kowa nata ba, sannan bata
yiwa kowa sallama daga masarauta ba ta baro Ilorin. Su dai sun san daidai gwargwado sun bata tarbiyya daya da Kehinde, sun mata nuni da
sanin darajar kowanne dan adam, hali ne kawai, wato halayen dan Adam mabanbanta na
halitta da dabi'a wanda bai da alaka da tarbiyyar da ta samu daga garesu.
Ko bahaushe kan ce hali zanen dutse ne. In ka shekara ba ka ga mutum ba tambaye shi
wani abun daban amma banda halinsa. Tun tana yarinya suka fuskanci tana da nakasu a
halayya da dabi’a.
Nenne a zuciyarta sai ta koma addu’a tunda nasiha da tunasarwa bazasu yi ba, ta soma
addu’a tana rokawa Taiwo gyaruwar hali da saukin kai da halin tawali’u, da daukar duniya da
sauki.
Don haka Taiwo ko kai amare gidajensu ba ta je ba, ta wuce gidanta na Lagos ta bar Hakeem
a Ilorin.
*********
An wuce kai amare Lagos Prince ya samu ya sulale ya wuce Gombe.
Don ya gama yarda daga Nenne har Dade babu mai saka hannu ya lallashi Siddiqa ta dawo.
Balle su je masa biko har gaban iyayenta. Ga shi ta ajiye masa wayarsa barin ma ya samu
damar communicating da ita.
Ya sauka a Gombe yamma lis, kuma dama tun kafin ya taso ya gaya wa Malam Buhari
direban Nani Oummana tasowarsa, don haka yana sauka ya tarar da shi yana jiransa. Malam
Buhari akwai wannan kokarin ga iyalin Oummana sabida yadda suma suke kyautata masa.
Yasa baya gajiya da hidimar zirga-zirgarsu a duk lokacin da suka bukata. Prince na da gida wani madaidaicin gida flat a mahaifar Nennensa wato Gombe daya dade
da saya tuntuni a GRA.
Ba zai manta ba, Nani Oummana ce silar sayen gidan da yayi, a wani zuwa da yayi shekarun
baya. Domin ta ce in yana so ya faranta mata dole ya sayi gida wanda iyalinsa za su ke sauka a
Gombe, bazata yarda ta barwa Akannis shi bakidayansa ba, dole sai sun raba shi gida biyu an
baiwa kowanne bangare hakkinsa, ko don ‘ya’yansa in sun taso su basu nasu muhimmancin na
dangin Uwa domin kuwa lokacin da suka bada auren Nenne Sappa ga Akannis, sun ce,
‘ya’yanta dole su zo Arewa.
A wurin Uncle Abdulmajid ya sayi gidan da jimawa, kasancewar likita Abdulmajid din kafin
komawarsa Morocco yana taba sana’ar ginin gidaje yana sayarwa tsakanin Gombe da Bauchi.
Duk da haka Malam Buhari bai wuce dashu gidannasa ba, ya wuce da shi kai tsaye fadar
Gombe bisa umarninsa, yayiwa maigadin gidan a waya da yaron gidan yace a yi masa gyara
yana iya zuwa yau ko gobe. Kai tsaye wajen Oummana ya sauka.
A sassan Uwar gari Hajiya Ummana, Prince ne zaune a gefen damanta, tanata zuba mishi
hira cikin fulatanci. Sannan tana kokarin saka mishi abinci da fura, wadda ta ji kindirmo ga
kananan kankara an zuba a ciki, amma Prince duk sonsa da fura, wadda yake yiwa shan gani
kasheni idan ya zo Gombe, yau ko rabin kofi bai sha ba. Nani ta ce, “Ai na san da zuwan nata, Nennenka ta gaya min komai. In shaAllahu za’a gyara
komai”.
Prince ya ji dadi sosai, iyayensa da kakanninsa ba dai sanin yakamata ba da halin dattaku,
duk abin da ya kamata su yi don saya wa ‘ya’yansu mutunci sun sani, bai san inda Taiwo ta
debo bakin hali na rashin sanin darajar Dan Adam ba. Shi abin da ke daure masa kai da lamarin
Taiwo, ta so Haseenah ma da bata da kowa, bata da nasaba, amma wai duk da haka ta kasa
son Aisha. Aishar da saidai a nuna mata gadon mulki da sarauta kawai.
Ya nisa a hankali yana cewa cikin ransa, “Murjanatu baki kyauta min ba. Saida kika ga na
samu sabon hope, wanda ya farfado dani daga suma na, na fada a wata korama da zaqinta yafi
na zuma, gardinta yafi na madara, wadda ban taba fadawa ba a tsayin rayuwata, sannan ne
zaki kore min wannan farin cikin dana nema na rasa (for over a decade), bisa wasu hujjojinki
akan Aisha marasa ma’ana marasa makama. Aisha ki yafe mu!”.
Nani Oummana da yake ta san hakikanin matsalar da ta kawo Aisha Gombe. Nenne ta yi
mata cikakken bayani a waya. Amma Oummana ta so ta tambayi Nenne me ya sa ta taho ita
kadai? Ta tuna ana tsaka da bikinsu Fatima ne.
Ita ma ciwon kafa ne ya hana ta zuwa Ilorin, amma duk haularta da na Uban kasa wato
yayan Nenne Sarki Ahmadu Jalloh ‘ya’ya da jikoki sun tafi suna can don yiwa Nenne kara. Da
su aka yi komai, don haka Prince Malam Buhari ya sa a gaba ya yi masa jagora zuwa Jeka da
fari. Zuwan Prince na farko kenan gidan iyayen Aisha tun auren su.
Yana daga cikin mota mai duhun gilassai (tinted) yana nazarin gidan su Aisha da Malam
Buhari ya yi parking a kofar gidan. Gidan karami ne, ko kuwa madaidaici, ya sha farin fenti mai
santsi, sannan harabar gidan a share take tas. Soron gidan tsaf-tsaf da shi, tsafta ta zauna
masa, ba dai gida ne na talakkawa can ba, don ko a layin gidansu Aisha ya fi kowanne fita da
haske, kuma fentin da aka yi bai shekara ba, lokacin aurenta aka yi shi watanni tara kenan. Buhari ya bude masa kofa ya fito, Prince yana sanye da yadin filtex sky blue, ya lankwasa
hularsu ta yarbawa a kansa.
A fuskarsa yau ya dora farin glass, wanda ya dora a saman dogon hancinsa, Kamshin
turarensa na ‘Baccarat’ tun daga soron farko sai da ya kai tsakar gidansuAisha. Malam Buhari
ne ya zagaya ya bude masa kofa ya fito ya yi ta rafka sallama don bai ga yaron da zai aika ba.
Wani matashin yaro ne ya fito daga gidan, wato Sunusi yaron da ke ma Umma aike. Buhari ya
ce masa, “Ko Malam na gida?”
Sunusi ya ce, “Eh Malam na nan”. Yace “to don Allah ka gaya masa Abdulrasheed ne yazo
daga Lagos”, Sunusi yace “toh, bari in gaya masa”.
Sunusi ya gayawa Malam Yunus zuwan bakon nasa. Malam Yunus ya dubi Umma itama ta
dubeshi sai yace Sunusi ya shigo dashi.
Prince ya shigo ya tsugunna ya fara gaishesu, Umma da Malam Yunus suka karbi Prince
hannu bibbiyu, fuskarsu ba yabo ba fallasa, Malam ya tambayeshi ya hanya da gajiyar biki da
yadda ya baro su Nenne. Malam Yunus na cewa a ransa Prince baiwa Aisha laifin komai ba
kuma ba shi ya zageta ba. ya gaya masa Aisha tana gidan Yaya Barau don shine waliyyinta
daman, yace babu komai amman dai ka je ka samu Baba Barau magana tana hannunsa. In don
ta ni ne ma Abdulrasheed nasan har yanzu akwai kuruciya a tare da Taiwo mace duk
shekarunta ai baka rabata da halin yara. Kuma iyayenka su sun san su waye mu, ba don haka
ba da bazasu matsa wajen nema maka auren Aisha ba.
Amman dai ina baka shawarar kaje ka samu Yaya Barau. Zan sa a raka ka yanzu”.
Prince yaji dadi sosai ya kara yabawa da dattakun iyayen Aisha. Ya sunkuya yana kara baiwa
Ummanta hakuri, Umma tace “aibabu komai, banda rigimar Aisha ma in nice bazan kula ba”.
nan Abdulrasheed yace “a’ah Umma, gara da tayiwa Taiwo haka, ni kaina bansan yaushe Taiwo
ta zama mai wannan baudadden halin ba sai yanzu, kuma wallahi na mata iyaka da iyali na,
koda wasa abinda ya faru bazai kara faruwa ba in sha Allah. Iyaye ai na kowa ne, wannan ba
tarbiyyar da aka bamu bane, don Allah kuma ina kara bada hakuri”.
Malam Yunus yaji dadi sosai