Showing 30001 words to 33000 words out of 40544 words
Chapter 11 - Aishah-Saddiqa 4 end Complete Novels by Sumayya Takori.pdf
mata ya lalace har jirgi ya tashi ya
barshi.
Yawan shekarun nan nasa, matsayi da girman sarautarsa (mulkinsa na gado gaba da baya),
da 'fame' din nasa na Polo (as African Polo Legend) duk an tashi kansu cikin dan lokaci ya
dawo yaro daidai ita.
Domin tareda shi Malam Buhari din Nenne tayi ta zaryar nemawa Prince auren Aisha. Bata
Lagos bata Gombe, har saida ta tabbatar sun daura auren sun daukota Ilorin.
Nani Oummana ma sai daga ido tayi taga Prince ya dawo. Bayan sun riga sunyi sallama ta
karshe cewa daga can zai wuce airport ya tashi gida Lagos. Ba suyi dashi zai dawo ta nan ba.
Oummana tace "Yaya haka Hammansu? Mantuwa kayi?"
Ya zauna yana cewa "to ya za'ayi? Jirgin ya tashi ya barni Oummana". Wani miskilin
murmushi Oummana tayi masa, tace "garin yaya toh? Kana can kana soyayya ko?" Hamma ya
dukar da kai yana ‘yar dariya yace, "kusan haka, ai bakya karya Oummana" Oummana ta sake
yin murmushi irin nata, ita tasan watarana za'ayi haka. Domin da alama AISHA INDO
SIDDIQAH! Ta shigo rayuwar Yarima da zafinta. Zata murza kambu son ranta, ranar duk da
Prince ya shiga komarta. Yarinyar nada tarin baiwa da kullum take tuna mata da auren Nenne
da Dade.
Kusan tace tarihi ke maimaita kansa akan Abdulrasheed Dan Idris dan Abdulrasheed Akanni.
Tana fatan wannan soyayya da Prince yake yiwa Siddiqah ta dore musu har tsufansu, su zama
(typical replica) na Sappa da Idrisu.
Ganin Oummana bata ce masa komai ba sai murmushi take zabgawa yace cikin basarwa da
hadiye kunyar da yaji.
"Amma gobe in Sha Allah bazan yi wasa ba Oummana, morning flight dani zai tashi karfe
6am, ko sallama bazan je mata ba".
Oummana me zata yi ba dariya ba, tace "to ni me kaji nace ne? Ko nace kayi laifi ne? Haka
akeso abubuwa suyi daidai. Saika koma ka daukota ka kawomin ita yau da kanka. Daman nafi
so in ganku a gabana tare". Yace "In sha Allahu Oummana, Baba Yunus ma da kansa yace
yace inje in daukota in kawo miki, dama na gaya musu kinason ganinta. Da nayi sallahr Isha zan koma na taho miki da ita".
Ya wuce zuwa dakinsa na sassan Oummana kai tsaye toilet ya fada don yin wanka, don
yasan a yanayin da suka kasance da Aisha yau, bai yiwuwa yayi sallah yanzu bai yi wanka ba.
Saida Umma ta tashi daga barci taga Siddiqa a zaune a gefenta, tace "har ya tafi?" Tace "eh
Umma, gashi har jirgin Lagos da zai hau ya tashi ya barshi. Dole sai gobe zai tafi gida".
Sannan cikin jin kunya ta gayawa Ummanta Hamma yace zai dawo su tafi wurin Oummana
anjima, ta aikoshi tana son ganinta.
Nan Haj Zainab ta hau tunanin me zata baiwa Aisha ta tafiwa da Oummana, karshe
tunaninta ya tsaya a kan turarukan ‘Oud’ da ‘Sandaliyyah’ na jiki dana turaka data sayo a
Saudiyyah. Su ta saka a kyakkyawar leda tace Aisha ta kaiwa Oummana tsaraba.
Kafin sallahr Isha Siddiqah ta yi wanka ta kara shiryawa cikin wani tattausan cotton lace mai
tsananin taushi da adon kananan duwarwatsu, kalarsa Orange ne da adon (milk color) furanni,
tun lokacin hajjin bara Ummanta tazo mata dashi daga Jeddah, sannan tayi sallah Maghreb da
Isha. Aisha ta dauko turarenta Fahrenheit ta feshe jikinta dashi. Kana iya jiyo sanyin kamshinsa tun
daga dakinta har tsakar gidansu zuwa dakin Ummanta.
Daidai lokacin Baba Yunus ya dawo, Siddiqah tayi masa sannu da zuwa ta karbi ledar
hannunsa yace mata balangun Ayuba ne ta juye su ci ita da Umma shi sun ci shi da Baba
Barau. Ya kuma ce ta shirya Hamma ya kira shi zai zo yanzu su wuce gun Oummana, Mallam
Yunus ya gyara zamansa akan kujera yace "toh Indo nasan ba sai na maimaita miki ki kula da
kanki ba, kuma ba sai na gaya miki ki zama ambassador din kanki da kanki ba a wurare irin
wadannan.
Waje ne da yake bukatar nutsuwa da kamewa wadanda bana jinki a kansu Siddiqah. Tunda
gidansu mahaifiyar sa ne".
Aisha tace "toh in sha Allah Baba". Daidai lokacin Sunusi ya shigo yace "wai mijin Aisha yazo
daukarta, suna cikin mota".
Siddiqah ta dauki gyalen data tanada wanda yayi matukar shiga da kayan jikinta ta yafa wato
off white, nan ta dauki karamar 'hand bag' dinta tun tana gida take amfani da ita, ta dauki ledar
sakon Oummana ta yiwa Umma sallama. Haj. Zainab tace,
"to sai kun dawo. A gaida Nanin".
Prince ya mika hannun damansa ya budewa Aisha kofa barin hagunsa ta shiga. Malam
Buhari na kokarin fitowa don ya rufe ya hutasheshi. Shi da kansa ya rufe mata kofar. Saukin kan
Prince yana kara masa kima mai yawa a idon dattijon direban. Ya koma ya zauna ya rufe kofa
ya jasu a hankali suka bar Jeka da fari, zuwa babban titin da zai kaisu gidan Sarkin Gombe.
Saida Prince ya san yadda yayi cikin dabara ya sanya tafin hannunshi cikin na Aisha. Ya
sarkesu, sannan ya matsesu cikin nasa hannun. Taushin hannun kowannen su ya ratsa su.
Suna tafe yana mata hira kasa-kasa amma ta kasa sakin jikinta dashi kamar dazu, don
Ummanta ta jaddada mata ta kama kanta, ta rike kunyarta, don gidan su mahaifiyar shi zata je
kuma zuwa na farko.
Da yake duhun dare ya shigo ba kowa ya ankara da shigar su sassan Oummana ba. Suka
sameta har lokacin akan dardumar sallahrta tun bayan data idar da sallahr Isha tana zaune tana
lazimi bata tashi ba.
Shigowarsu tasa ta shafa addu’ar da take yi, ta mike tana cewa "Jabbama da Indo Siddiqah,
barka da zuwa, Indo Aisha". Aisha tayi kasa ta zube a gaban Oummana zata fara gaisheta cikin
girmamawa, tsohuwar ta kamo hannunta ta mikar da ita tsaye, ta jata zuwa kan shimfidar fata
irin ‘traditional rug’ dinnan da akeyi da fata wanda akanshi take zama a falon, da Tum-tum a
kowanne gefe da gefe manya har guda hudu, Nani Oummana ta zaunar da ita a kusa da ita.
Kasancewar Oummana bata zama akan kujera sai wannan shimfidar tata. Prince ne ya
zauna a kan two seater, a gabansa akwai karamin centre table dauke da ‘tray’ shake da kayan
marmari. Prince ya dauki apple guda daya jawur da ita yana yankawa da karamar wuka kaiwa
bakinsa yana ci. Yana kallon Oummana ta rasa ina taka-saka -ina taka-aje da Siddiqah, kaunar da suke mata
itada Nenne, ya tabbata daga Allah ne ta dalilin son da suke yi masa. Domin bayan Oummana
ta zaunar da Siddiqah a kusa da ita, sawa tayi hadimanta suka cika gabanta da kayan motsa
baki na alfarma, wanda ko tabawa da hannunta Siddiqah ta kasa yi, ji take kamar yau ta fara
haduwa da Oummana.
Daga bisani ta gaida Oummana da fulatanci, Oummana ta amsa ta kuma tanbayeta lafiyar su
Ummanta da Babanta da iyalin Baba Barau. Siddiqah ta amsa duka, kanta a sunkuye, murya a
ladabce. Anan Oummana tace maqasudin kiran nata dama don tayi mata nasiha ne. Nan tace
Hamma ya basu wuri. Hamma yace "Nani abin harda kora?" Tace "ai zan kiraka ne inna gama
da ita, akwai abinda ba sai ka ji ba".
Prince ya shige dakinsa ya barsu. Oummana ta fara yiwa Aisha fada da nasiha kamar ita ta
haifeta.
Nasiha ce ta manya sannan mai shiga jikin yaro, inda tace wa Aisha.
"Idan kana aure yana nufin ka girma. Abubuwa da yawa zasu iya faruwa a rayuwar auren
mace, musamman da dangin miji, to idan irin haka ta faru ba komai ake fadawa iyaye ba Indo,
sabida gudun bacin ransu.
Sannan shi aure rai ne dashi. In zama bai kare ba mace da mijinta sai su dawo su shirya, su
manta komai cikin dan lokaci, amman iyaye basa mantawa.
Don haka toh a kiyaye irin haka anan gaba, kuma koda wani abu ya faru to Aysha kizo ki
sameni ni Oummana ko Nennen ku, na tabbatar hukuncin da zamuyi wallahi Umman ki baza
tayi ba. Kinji ko Indo?
Sabida Allah shine shaidata, yadda nake jin Hammansu a raina haka nake son ki babu
bambanci a wurina, kinji?
Shiyasa nake so nan gaba ba fata ake ba abin Allah ya kiyaye, ko da wani abu irin haka ya
faru toh dan Allah Aisha ki koyi magance shi tsakanin ki da mijin ki.
Musamman irin wannan da ya faru da Taiwo, mijin ki na matukar son ki, har Taiwo ta isa tasa
kice kin bar auren ki?
Allah yayi maki albarka ya kawo muku yara masu albarka. Shi wannan da baya son sarautar
nan tamu, wato ya gado ubansa, Allah yasa ya haifo min wanda zai so sarauta.
A zuciyar Aisha tace "Amin". Sai lokacin ta gane Hamma baya falon ya basu wuri itada
Oummana.
Da ya tashi fitowa ba kayan da ya fita dasu ne a jikinsa ba, ya canza su zuwa kananan kaya
farar shirt LV da bakin wandon Jeans. Yace "toh Oummana dare ya fara zan maidata"
Oummana tace "Aisha nagode Allah ya kara albarka" nan Aisha ta mikawa Oummana sakon
Ummanta. Ga Oummana da son Sandal da Oud. Nan tayi ta godiya,ta kuma sa aka miko mata
babbar jakar data shiryawa Aisha tsarabar da zata tafi dashi gida.
A hanyarsu ta dawowa ma Prince na makale da kafadun Aisha Malam Buhari na tuki, ya
sassauta murya yace "Ayshah! Kin ce bazaki je gida na ki gani ba ko? Koda akwai abinda bai
miki ba a canza don shine gidanki da ‘ya’yanmu anan Gombe". Da sauri Siddiqah tace "Don
Allah Hamma Abdul a'ah, ba sai naje ba, zan gani next time". Hammah yace "ai shikenan. Kin
dade baki je ba.
Wanda ya jure yayi rainon Dan shillansa wajen shekara guda, ai jiran kwana bakwai bazai
gagareshi ya fige abinsa ba".
Da haka suka kawo kofar gidan su Siddiqah.
Taimakon da Allah yayima Siddiqah ta fito nan da nan shine Malam Buhari dake cikin motar
nan, wanda ya kure radio yana sauraron wata tsohuwar waqa ta Sani Aliyu Dandawo. Da
Prince bazai barta hakannan ba sai ya kara cakudata.
Duk da haka cike da damuwa Hammah ya rike hannunta yace.
"Babyyyyy. I will miss you kin sani ko?"
Siddiqah ta dube shi idanunta narai narai tace dashi cikin harshen yarbanci "I will Miss you
more Hamma....". Ba zato taji ya kai hannunta ga bakinsa ya sumbata. Da kyar ta samu ta zare
hannunta daga cikin nasa ta shige cikin gida ba ko waiwaye. Don gabadaya Hamma ya saka
mata wata irin kasala (by just mere looking into his blurred eyes).
Umma da Abba sun sha labarin Nani Oummana, irin kirkinta da karamcinta daga bakin Aisha.
Ta fidda kayan da Oummana ta bata har da alkhyabba ta mata da manyan turamen super guda
uku da manyan lesika uku. Ga bandir din filtex na Abban Aisha da Baba Barau.
A ranar sai can dare Siddiqa ta bar dakin Ummanta zuwa nata dakin, sun raba dare suna hira
don ji suke kamar gobe-gobe ne Petel zata tafi ba kwana shidda masu zuwa ba.
Don Hamma ya tabbatar ma Abban Aisha in sun tafi zasu jima basu waiwayi gida ba, don
hutun shekara ya kammala harda kari mai yawa.
Wajejen karfe 12 na dare Siddiqah ta gama komai na shirin kwanciyar ta. Hammah ya kira ta,
Siddiqah ta daga hatta muryarta ta canza don barci take ji sosai tace.
"Hammah, baka kwanta ba?" Yace "na kasa barci ne Baby.... Ina missing furar kinnan da
kindirmo..." Aisha ta rufe ido tana jin kunya kamar Hamma na kallonta, tana kuma tuna incident
din na yau da ya kasa bacewa daga idanunta, feelings din kuma sababbi suka kasa barin ranta.
Hamma yace "Baby you know what?" Ta girgiza kai kawai kamar Hamma na kallonta. Hamma yace "ban taba jin eagerness a rayuwata irinna ranar da zaki dawo min ba. I will be
patiently waiting for you and your annoying Jamb.”
Daga ranar da kika dawo ne zamu fara rayuwa. Kinsan rayuwar mu ta Argentina babu komai
cikin ta sai introduction na AISHA zuwa cikin lonely and pitiful rayuwar KEHINDE.
I reserved the day for you only, as I reserved myself for 43 years waiting for the day. Please
Baby, ki bani dukkan go ahead da juriyar ki da zan bukata, kinji?"
Kunya kamar ta kashe Aisha. Prince ya cigaba da kashe Aisha da kalamai masu dadi yana
gaya mata irin tanadin soyayyar da yayi mata daga ranar data dawo, har zuwa karshen rayuwar
su.
Ashe dai Ishaq da take ji a ranta akan yana gaya mata kalamai da suke zauna mata a rai bai
iya komai ba. Ga inda kalaman fatar baki kadai ke neman narkar da zuciyarta a take. Har hakan
ya saka mata (nervousness) akan zuwan ranar tarewarta dinnan da Prince ke ta maimaitawa,
ba tareda Prince ya san ya saka mata nervousness din ba.
A daren yau Hammah ya gaya mata maganganu masu matukar nauyi. A ciki ya gaya mata
cewa throughout the 43 years of his life he had never had a sex with anyone. Waiting for her….
his dream wife.
As a hopeless romantic, ya jira zuwan true love dinsa tsayin wannan lokacin, and today, he
thank the Exalted Lord Almighty for bringing her to his life.
(Duk da Haseenah ta so ta saka Prince ya kauce hanya Kehinde bai taba yin abinda ya wuce
kissing na shan minti da ita ba. Wanda a yau, wancan abinda ya dan gitta a tsakaninsu ma
regretting dinsa yake yi, yana kara istigfari).
Ya yarda ba wata soyayya ta kwanciyar hankali da sakewa da jin dadi mara misaltuwa kamar
ta auren Sunnah.
Da sanyin muryar Prince dake kasheta da dadadan kalamai cikin kunnenta Aisha tayi barci
akan wayar, sai ji yayi numfashin ta ya canza a hankali mai nuna tayi barci ta bar shi da
wayarsa, batareda ta san lokacin da barcin ya sace ta ba. Shine dai yaga wayar na cigaba da
reading kuma bai kara jinta ba. Dole ya kyaleta ya kwanta shima. Amma kam yau Prince yayi
wahalallen barci na azaba wanda ko zamanin samartakarsa dana tashen balagarsa baiyi irinsa
ba.
Firdaus ta taba gayawa Nenne a cikin gorin da Maman Kiki tayi wa Aisha harda na 'Lefe'.
Ashe Nenne bata manta wannan ba abin yana tsaye a ranta.
Don haka tun ranar da suka koma Lagos ta kira Hamma Abdulrasheed suka gaisa.
Nenne tace "Hammansu akan zancen lefen Aisha ne, na maka aure da dukkan hidimarsa
amma lefe na al'adar Hausa Fulani na tuna ba’ayi ba na bar maka kayi da kanka. Zaka fi sanin
irin dawainiyar dake cikin aure da wahalar sa".
Prince yayi murmushi yace "Nenne kenan, ai da kin fada tuntuni da tuni an yi. Yanzunma
bata baci ‘better late than never’. Nawa zan bayar?" Nenne tace "da yawa. Don sawa zanyi a
hada komai cikin kwana uku kafin Aisha ta baro Gombe ta dora hannunta akan lefen nan" shi ya
san Aisha sarai bata wani damu da abin duniya ba balle wani lefe, kuma ita a wurinta
maganganun Taiwo sun dade da wucewa bata kara waiwayarsu, amma yasan Nennensa sarai
tunda ta rike shi a ranta to fa sai anyi. Hamma yace,
"to Nenne bakomai, ayi amfani da 'Black Card' dina dana baki ajiya kafin na taho, ba limit a
cikinsa. In ce ko shikenan?"
Nenne tayi murmushi bata yi magana ba. Prince ya sake cewa "in ma kin karar da abinda ke
ciki Nenne dana iso zan bada ‘dollar card’ dina a karasa, ince ko hakan yayi miki? Ayi lefe
lafiya".
Yana sauka a Lagos kuwa gidansu ya zarce. Yace "Nenne yaya an gama lefen?"
Tace "an kusa dai". Har ya fita zai tafi gidansa ya dawo. Ya baima Nenne dollar card dinsa
yace "in case wancan ya kare" Nenne na dariya a ranta tace Hammansu da Dade dinsa ‘are
real Yoruba Demons’ akan son matansu basu da na biyu.
Nenne da Taiwo suka hada lefe na gani na fada ranar Friday Taiwo ta taho da lefen Gombe.
Sai Nani Oummana tasa wata Aunty dinsu da matar Uncle