Showing 21001 words to 24000 words out of 40544 words
Chapter 8 - Aishah-Saddiqa 4 end Complete Novels by Sumayya Takori.pdf
ya faru kuma wallahil azim bazan yi kaffara ba, bazai kara faruwa ba. A gafarce ni don Allah.
Baba kar kayi min hukunci da laifin yar uwata. Allah ya Kara hakuri Baba sai jibin in sha Allah". Ya tashi zai tafi, Baba Barau sai yaji duk ya daure shi da jijiyoyinsa, yayi murmushi yace
"Abdulrasheed kenan, ni zaka daure ko?" Yayi murmushi shima yace "ah ah Baba".
Su duka biyun suna murmushi suka rabu.
**** **** *****
TAIWO
Ta sauka gidan mijinta a Lancaster da yamma lis, ta isa ga kofar shiga tana ringing bell. Ana
bude kofa taga wata kyakkyawar bafullatana da mijinta Toufeeq a bayanta, ga yaranta biyu
dasu, da wani kyakkyawan Baby din dauke a hannunta.
Wani irin shock ne ya kama Aunty Taiwo, tace "Toufeeq what is this?" Yayi mata kallon rashin
tsoro ya ce mata "matata ce itama. Sunanta Hauwa-Maijidda".
Ya dubi Maijiddar yace mata "Maijidda this is Taiwo, Maman Kiki da Abdulhakeem".
"What???"
Sai ga Murjanatu ta sulale ta zauna a dandaryar kasa a bakin kofa.
Ta daga ido ta kallo matar, sannan yaran, in zata tuna ta taba ganin hoton yaran yace mata
yaran abokin sa ne, wanda suka je auren sa a Yola….
A nan komai ya dawo mata, zuwan sa Yola auren aboki, ashe nasa auren ne.
A cikin ranta sai tana ayyana alhakin aisha ke bin ta…. Taiwo tace "hasbunallahu wa ni'mal
wakil… Toufeeq......". Sai kuka wiwi.
Toufeeq ya soma yi mata bayani cewa "he doesn't want to hurt her ne, shi yasa yai aure bata
sani ba, don yasan ta da bala'i. He needs peace in his life da matar da zata damu dashi.
Yace ta dawo UK tace baza ta bar aikin asibiti ba, toh shikuma he needs someone close to
him, wadda baza ta ke bashi ciwon kai ba.
Taiwo ta kara jin muguwar nadama, nadama mara misaltuwa, tace komawa zatayi, Toufeeq
yayi ya lallashinta ya kuma fada mata in zata kwantar da hankali ta zauna toh, if not zabi ya
rage nata, amman aurensa da Maijiddar sa ba fashi.
Taiwo a cikin satin ta dawo Nigeria. Koda ta sauka. Gidanta na Lagos ma kasa shiga ta yi
tunda dai Toufeeq ne mamallakinsa. Dole gidan iyayentan dai ta dosa da tarin nadama a tare da
ita, don ta kira wayar Kehinde ya ki dauka, ta je gidansa maigadi ya ce mata ya yi tafiya Gombe.
Zuciyar Taiwo bugawa ne kawai ba ta yi ba, da abinda Toufeeq ya yi mata, ta zama tamkar
zararriya, har magana zaka ga taan yi ita kadai, tana ta gaya wa kanta alhakin Aisha da
Abdulrasheed ne ya hana ta kwanciyar hankalin zaman aure, ya tagayyara nata farin cikin
auren.
Domin don wulakanci irin na Baban Kiki ma cewa ya yi saura ta je ta hada masa bomb a
gida, don ba wanda ya san ya yi 'secret marriage', ko a nashi family din kuwa, don yarinyar
zuri’arshi bazasu barshi ya aureta ba, kasancewar diyar talakkawa ce sosai a garin Yola ya
aurota, shekarun baya yaje yin wani project daga European Union ya ganta tana talln fura da
nono ya aura. Babanta ma baduku ne.
Don haka daga Nenne har Dade babu wanda ya san dalilin zuwan Taiwo gida rana daya, a
taurin zuciya irin nata, da rashin tsoro ko shakkar kowa da kowa ya sani, suka ganta duk ta
sauke kai, ta zubda izza, yanayin da suka ganta a ciki ya basu mamaki sosai.
Kuma tana zuwa gida ranar Friday da sassafe taga ana ta shiri su Nenne zasu Gombe.
Taiwo ta fashe da kuka ta roki su Nenne suyi hakuri tun ba'a je ko'ina ba taga me tagani.
Nan ta fada ma Nenne komi tas, ai kuwa Nenne batayi mamaki ba don yasan Toufeeq yayi
hakuri da Taiwo ba kadan ba, nan ta sake yi mata nasiha mai kashe jiki da huda zuciya. Tace
zasu je ne su yi bikon Aisha, Taiwo tace zata bisu tunda itace tai laifin zata je ta basu hakuri. Su
Nenne suka ce "toh". Da hantsin ranar jirgin DANA Air ya tashi dasu Gombe.
A gidan Oummana aka sauka. Oummana se ganin su tayi daga sama dukkansu, tace "daga
ina haka?" Nenne tace "sunzo biko" Oummana tace "ai ni daman ido na saka muku, da baku zo
ba daman anjima zanje gidansu Aisha da kaina inyi ban hakuri".
Nan Oummana ta hangi Taiwo, aiko Oummana ta ciwa Taiwo mutunci son ranta, tace "Ashe
tareda tabbatacciyar kuke tafe?" Oummana tayi Mata tatas. Uban kasa ma da ya shigo ya ci wa
Taiwo nasa. Taiwo tai kuka har ta gode Allah idon nan sun kumbura pummm.
Sai ga Prince nan ya shigo around 11am, yana zuba wani irin kasaitaccen kamshi, ya sha
fararen kaya, yana riqe da babbar rigarsa a hannu, da hular sa Tonak ash colour, wato kalar
zaren da akai aikin kayan, gabadaya suka juyo suna kallon sa.
Surprise yaga Nenne da Dade bai ma kula da TAIWO ba. Nan ya shigo ya gaishe su, har
suna hada baki sukace,
"ina zaka je haka?"
Prince yace daurin aure zai je, uban kasa yace "a ina?" Hamma yace "Baba Barau ke aurar
da diyar shi" Oummana tace kace "biko kake tayı. Wannan ado haka Hammansu ai dole a baka
Aisha Indo yau!".
Prince ya saki wani kasaitaccen murmushi yace "Allah ya amsa bakin ki Oummana" duk
suka ce "amin".
Dade yace "muma biko muka zo ai, amman tunda biki ake yau zamu bari sai gobe sai muje,
Prince yace "ah ah Dade, yaya kunyi niyyar alhairi zaku fasa kuje kawai yanzu" duk suka hau
dariya, uban kasa yace ban san ka da gaggawa ba, yau da gobe ai duk daya ne. Yana juyawa
sai yaga Taiwo duk tayi zuru-zuru. Sai yaji ba dadi, yace "lafiya ke kuma haka?" Sai kuwa Taiwo
tasa kuka, tazo ta rungume shi tace I am sooo soo soo sorry Kehinde. I love u so much, I
became selfish and possessive ban ma sani ba.
I am extremely regretful of what I did, and i will do anything to make it right. Kayi hakuri.
Iyayen na kallon su da Kakar su, da zuciya daya ya riko hannunta, yace "Allah ya yafe mana
bakidaya Taiwo, Allah yasa kin canza hali kenan har abada", duk aka ce Amin. Sai suka baiwa
kowa tausayi musamman Prince, don yana son yar uwarshi.
Kehinde akwai yi wa mutane uzuri. it was an emotional moment tsakaninshi da Taiwo dinsa
yau. Yana yi mata murmushin afuwa itama tana masa na godiya. Daga bisani ya kalli agogo
yaga lokaci ya tafi, yace "kai bari in tafi kar nayi latti". Ya saka hula yana musu sallama. Uban
kasa yace "ah ah, ai baza ka tafi haka ba, yace da Kawunka zaka tafi ya raka ka. Yau a
basaraken ka zaka je musu, ko Baban Aisha Indo ya daina ja maka rai".
Sarki Ahmadu Jallo Umar yayi gyaran murya sarkin dogarai daga bakin kofa ya ce "Ran sarki
ya dade, ina kusa", Sarki yace "a kira azo a daura masa rawani, a hada mota, kuma a kira
Galadima da Waziri Abdulrashid ya wakilce ni a daurin auren da zashi yau, a hada convoy, a
hada dogarawa!!!". Sarkin dogarai cewa yake "an gama Uban kasar Gombe, maganarka doka ce!".
Nan ya buga babbar riga ya wuce zuwa cika aikin Sarkin sa, jikinsa na zikiri.
Hamma ya bata fuska ya dubi Kawunsa Uban kasa yace "is it necessary? Kar ma suce
‘show off’ ake masu, su sake boye ta a daki?"
Nenne da Oummana me zasuyi ba dariya ba.
Uban kasa ma da Dade sai da suka dara. Wato duk Taiwo ta jawo ya zama a darare yake da
duk abinda zai sa a ce ya raina azikin su Siddiqah. Uban kasa yace "ai dai an gayyace ka
daurin aure ko?" Hamma yace "eh" Uban kasa yace "toh ni nace ka wakilce ni. Gara yau dai a
gan ka a ainahin gaskiyar ka. Sarauta ai ba karya bace Abdulrasheed". Prince yayi murmushi. Nenne tace "gaskiya kam. Allah dai ya bada sa’a, in an gama daurin
aure ka shiga ciki ku gaisa da su Umman Aysha, kace ina gaishe ta". Hamma ya ce "toh
Nenne".
Daman Kuma karfe 12:45 ne daurin auren, da an idar da sallar Juma’a za a daura. Ai kuwa
kan kace meye wannan sarkin dogarai ya cika aiki, an sanar da maganar zuwa daurin auren,
Galadima da Waziri sun shirya, ga dogarawa da motoci na alfarma nan uku an ware, sai motar
Uban kasa itama an fito da ita. Cikin ta Prince zai shiga. A gefe ga masu algaita.
Daga cikin gida kuwa Prince ne zaune za'a nada masa rawani, sai kira yake "shi fa baya son
rawani, zafi ne dashi Oummana".
Nani Oummana tace "ai kuwa dole kaso rawani, don kuwa kayi gadonsa hawa biyu".
Hakanan Hamma ya zauna aka nada masa farin rawani, an masa irin rufin bakinnan, ya dau
'black Gucci shades' kalar dark brown' ya saka, ga hannun nan na dama yana juyawa yana
sheki. 'Patek Philippe Grandmaster Chime' ya saka, not extravagant but extremely classy. Yau
sai jinin fulatancin gabadaya ya fito. Masha Allahu kawai za'a ce saboda Nenne tana zaune
tana kallon sa ya tashi zasu wuce bata san sanda tace "fa tabarakallahu ahsanal khaleqeen.
U'izu bi kalimatillahi tammat min sharri ma khalaq". Ta tashi ta tofa ta shafa mashi. Wallahi
tama manta basu kadai bane. Oummana tace, "je ka Allah ya tsare" yace "amin Nani".
Suka fito tare da Uncle Abdulmajeed shima yasa rawani. Amman Kehinde ya haska.
Dogarawa an samu abin so, shi dama gashi miskili kuma rawanin ba so yake ba, ai sai shan
kunun da yayi yasa komi looks more regal. Suka hau kirari kamar makoshin su ze fita aka shige
mota. Hamma yace don Allah a rage convoy din. Sarkin dogarai yace "ai yayi hakuri tunda sarki
yake wakilta baza su fita qasa da haka ba.
Ya shige motar Uban kasa shi da Uncle Abdulmajeed sai sarkin dogarai a gaba. daya motar
kuma Galadima dayar Turaki da Waziri. Sai ambulance da kuma bus ta dogarai da masu
algaita. Aka wuce tiryan_ tiryan zuwa Jeka da fari.
A hanya Prince ya kira Baba Yunus, yace “yazo zai fito Uban kasa yace lallai ya wakilce shi a
daurin aure, to dai gashi nan a hanya Allah yasa kar yayi wa Baba Barau laifi”. Ashe a ‘hands
free’ yake, Baba Barau na kusa da Yunus yana jinsu, sai Baba Barau yayi masa gyaran murya
yace "wato Abdulrashid kallon sarkin bala'i kake mani ko?" Prince ya zaro ido yace "subhanallahi, ko kadan Baba. Na dai fada ne kada muzo baku sani
ba". Yace "to wa ya taba mayar da wakilcin Uban kasa? Wato don na rike maka Indo, shine
kake so ni a kore ni daga kasar Gombe ko?" Yace "ah Baba, tsaya kaji.....". Ai kuwa Baba Barau
ya fashe da dariya, Mal Yunus yace "wasa yake maka ka ji! Sai kun iso". Du duk a tunanin su shi da wani aka turo. They have no idea it’s the whole convoy.
Nan aka fito aka shiga rumfuman canopy da aka kakkafa a gaban gidan. Aka zazzauna, aka
ce sarki yayi wakilci, wa zai daura aure wakilin Sarki bai iso ba?” Haka nan aka dan tsaya aka
dan ware wuri kamar na mutum hudu da zasu zauna.
Ba jimawa saiga ga jiniya, motar escort na wi-wi-wi-wi. Mata ma daga cikin gida jin jiniya sai
aka hau leke, sai ga Bus din dogarai ta tsaya a gefe, suka fice.
Baba Barau sai da ya dan firgita. Ya mike tsaye shi da malam Yunus da Malam Hassan wato
Baban tsohon saurayin Aisha Ishaq, don shima Mal. Hassan yazo daurin auren. Bakidayansu
suka tashi don sun dauka sarki ne yazo.
Kafin su tantance komai sai tashin algaita duk inda ka hanga police ne da dogarai, sai ga
motar Uban kasa har gaban ‘tent’ din da iyayen amarya ke ciki, dogarai suka zagaye ta ana
kirari “Barka da sauka magajin garin Ilorin, barka dai sarki dan sarki jikan sarakuna. Gaba
salamun baya salamun. Abdulrashid dan Idrisu jikan Akanni. Jikan Ummaru Jalloh Uban kasar
Gombe…”.
Abdulrashid yana mota jin ana masa wannan kwakwazon ji yayi kamar ya nitse, cewa yake
“don Allah sarkin dogarai kace su bari” yace masa “toh kawai”.
Sai ya yunkuro zai fita, dogarawa suka baje riga aka bude kofar, ya fito. Uncle Abdulmajid ma
ya fita, yara ‘yan unguwa da matasa sai ihu ake …. kyau kam iya kyau Hamma Prince ya sheka
shi.
Baba Barau da Baba Yunus suna inda suke zaune kowa yana tasbihi ga Allah a zuciyar su,
dan lallai ya bawa diyar su miji nagari, wanda bashi da makusa. Ga nasaba ga addini. Kuma
Allah ya mallaka mata zuciyar sa.
Sai kawai Baba barau yaji sanyi a zafin sa da yake ji. Ya tashi suka wuce suna nuna masu
wurin zama.
Sarkin dogarai ya wage baki da murya yace “mai martaba Uban kasar Gombe ne ya wakilta
dan sa yazo ya wakilce shi a wannan daurin aure na Maryama. Ya kuma bayar da auren a
madadin sa”. Da ya kai aya sai dogarawa suka wuce dasu goro da dabino alawa ana ta
jibgewa.
Ashe a cikin gida ma ana ta sauke su lemu da ruwa da dai kayan daurin aure. Baba Barau
ya tabbatar cewa lallai an karrama shi, an karrama autarsa Maryam.
Nan aka zauna Abdulrashid ya gaishe su, zai duqa kenan Sarkin dogarai ya tare shi, ya ce
“Yallabai Uban kasa fa kake wakilta, kai ne sarki yau”. Baba Barau yace kul ka tsugunna, muje”.
Aka wuce ciki aka bashi waje duk suka zauna. Sarkin dogarai a ran sa yace. “wannan Yarima
na zamani, ba abinda ya sani a kan sarautar gidansu”. Nan dai aka fara shirin sallar Jumma’a. Liman yace gudun kada yayi laifi, ko Galadima zai yi
limanci? Sai Uncle Abdulmajid yace da Prince yayi. Nan kuwa Prince ya tashi yayi huduba mai
ratsa jiki, sannan ya tayar da sallar jumma’a.
Da aka idar aka daura auren Maryam da Angonta Yusuf, Kehinde yayi walicci aka bayar da
Maryam bisa sadaki naira dubu dari lakadan. Sai fatan Allah ya basu zaman lafiya
Ana gamawa kowa yana so ya gaisa dashi, nan duk ya tsaya aka gaisa akayi hotuna, Prince
ya matsu su wuce gida saboda cikowar jama’a irin wadda bai zaba a ciki ba, ga rawanin nan ya
ishe shi da zafi, duk ya gaji kamar yasa kuka.
Zasu shiga mota kenan sarkin dogarai yace wa Mal. Yunus zasu shiga su gaishe da Umman
Aisha da matar Baba Barau. Malam Yunus yace “toh ba matsala”.
Su mata acan cikin gida al’ajabi ya ishe su, ance sarki yazo daurin auren Maryam, toh ta
yaya? Ita dai Aisha jikin ta duk yayi la’asar. tun da taji ana “jikan Akanni” kuma ta jiyo muryarshi
yana khutbah…Mal. Yunus ne ya shigo yace da matar Baba Barau da manyan Aunties din
Aisha su kimtsa Uban kasa ya turo ai musu Allah sanya alheri. Ai sai suka yafa mayafai, aka
taho falon.
Suna shiga ya koma yayi musu iso, masu algaita zasu fara kirari Hamma ya daga hannu sai
suka yi shiru, da algaitar suka shigo gidan.
Amman babu wanda bai ce masha Allah ba, wanda suka gansa shekaranjiya ma basu
gane shi bane, suka shiga falo dasu Galadima aka gaisa, da su Baba Barau duka, aka kuma
sake fatan alkhairi, sannan suka ce zasu wuce. An karramasu, sun gode.
Karaf! Hamma sai ji yayi Waziri yace “toh a bisa al’ada, in sarki ya bada aure, komi na
gararauren shi zaiyi, dan haka ga kayan gara nan na Maryama Uban Kasa yace a kawo….”.
A dari da sittin Abdulrashid ya kalli Waziri,