Showing 6001 words to 9000 words out of 40544 words
Chapter 3 - Aishah-Saddiqa 4 end Complete Novels by Sumayya Takori.pdf
yaji don Aisha tace da bakinta bazata bishi ba. Har ta samu
abin adarwa a gaba.
Fatima na komawa dakinta ta kira Aunty Taiwo, tana mayar mata da yadda aka yi, da irin
gwasale tayin binsa gidansa da Prince yayi ga Nenne da Aisha, sai Taiwo tace da Fatima, “ewo,
to dama nifa na san Kehinde sarai, nafi kowa saninsa, saninda ko Nenne bata yi masa ba, ba
son zama da yarinyar nan yake ba, biyayya yake yi musu don a rabu lafiya da kafaffun
iyayenmu da basa shawara, su Nenne ke faman cusa masa ita kamar dusa, kamar ance
lafiyayyun mata ‘yan asali na manyan gida sun gama karewa a duniya.
Na rantse idona idonta a Lagos ko Ilorin in ta sake tazo, sai nayi mata wulakanci da
kaskancin da bazata kara kuskuren zuro jiki cikin zuri’ar Akanni ba, balle ta wani kwashi siraran
kafafunta tazo mana biki irin wannan na girma”.
A dakinta na baya wato dakin Kiki aka sauketa, kafin ta kwanta saida ta kira Ummanta ta
gaya mata saukarsu lafiya a Lagos, sannan ta kira Hamma don tayi masa saida safe ta kuma
bashi hakuri da kalamai, amma sai ta samu ya kashe dukka wayoyinsa.
Haka ta kwana da tunani da damuwar Hamma a ranta.
Washegari da safe ita da Nenne ne suka shirya abin karin Dade da Hamma, sai wajen
karfe goma na safe Prince yazo gidan kuma a gurguje suka karya shida Dade zasu fita, bayan
yabi Nenne dakinta sun gaisa, yanaso ya tambayi Aisha amma ya dake. Sai gata tana shigowa
dakin Nennen dauke da lemun tuffah da sassanyar madarada tanbulan na tangaran akan
karamin tray, ta gefensa ta wuce zuwa ciki, taci ado har ta gaji gabadaya ta saje da ‘yammatan
amarya da suka cika gidan tun jiya.
Ta ajiye a gabansa, don tun safe take dakon shigowarsa duk ta damu, tace a ladabce
“Hamma ina kwana?” Yayi mata wani kallo yace “lafiya kalau, yaya gajiyarki?” Nenne aka kirata
a waya sai ta fita daga dakin tana amsa wayar.
Aisha bata yi aune ba taji Prince ya kamata ya mikar daga durkuson data yi a gabansa ya
jata zuwa kusurwar dakin ya matseta sosai a jikinsa, sannan ya manne ta a kirjinsa da wata
zazzafar hug, ya rage tsaho ya sumbaci lips dinta lightly, yace,
“Aisha jiya banyi barci ba isashshe saboda rashin ki a gadona Aisha, I missed you and your
sweet lips, me yasa kika yimin hakane wai?”
Ya yi mata wani kallo na so da sha'awar da baisan yaushe ya fito daga idanunsa zuwa nata
ba, saida Aisha taji tasirin kallonnan har spine dinta, tsigar jikinta saida ya tashi yarrr, Hamma
ganin haka ya sake manne bakunansu wuri guda yana kissing lips dinta hungrily, wannan karon
zazzafar kiss yake extending Wanda ya rikita Aisha bakidayanta. Duk da haka tunanin a inda
suke ya hanata nutsuwa ta amshi sakonnin nasa. Aisha ta soma kokarin kwatar kanta tana
fadin.
“Please don Allah Hamma ka bari, ka sakeni kada Nenne ta dawo. Dakin Nenne ne fa!”.
Hamma yace “I don’t care, ai gara ta gani ta san yadda kuka taru kuka kwareni jiya, I missed
your warmth, shine jiya kika ce nan zaki zauna ko? Don kawai kinga ina shirin angwancewa?
Wannan ai mugunta ne Aisha.
Hummm! Ni na manta ma I am pissed at you na tsaya Ina romancing dinki”. Aisha tayi wani
murmushi kawai ta kalleshi “ni dai don Allah Hamma ka sakeni kunya nake ji” ya sake mata kiss
a kasan wuyanta sannan ya saketa jin kamar motsi a bayansu. Ashe Firdausi ce ta shigo
neman Aisha, ganin abinda ke faruwa tayi maza tayi excusing kanta da gaggawa ta juya tana
murmushi.
Firdausi na fita Nenne ta dawo, sai Aisha ta gusa ta basu wuri. Har Hamma ya gama gaisawa
da Nenne ya fita daga gidan, wanda ya soma dinkewa da baki musamman kawayen amarya
dana Nenne, bai kara ganinta ba. Kuma a washegarin ranar first flight ya tashi dasu zuwa Ilorin,
shida Dade, Nenne, Aisha da amaren domin su samu addu’ar arba’in kuma a dauro auren a
fadar Ilorin.
Da hantsin ranar suka shiga Ilorin Emirate, Aisha tana like da Nenne duk inda tasa kafa
nan take mayaswa. A yanayin kalar fatar jikinsu da kamanninsu na Fulani sai suka fita dabam a
gidan, kamar ‘ya da uwarta. Wadanda basu san matar da aka aurawa Prince bama a gidan a
ranar suka ganta, masu yabawa nayi haka masu gatsinen yarbawa na kankantar Aisha. Amma
maganar rashin wayewa ya fara barin jikin Aisha ta yi fes da ita ta kara cikowa ta fara cika
idanun mai kallonta. Prince yana can fada tareda Uncles dinsa do a ranar ne ake shawarar
wanda za’a bawa sarauta a cikin ‘ya’yan Emir. Idris Akanni y ace a’ah, ko dama Emir ya dade
yana gaya musu su cire Idris da dan sa daga sha’anin sarauta. Basu kara yarda da hakan ba
sai yau da Dade ya fitittike yace bazai karba ba, baida ra’ayin sarauta ko kankani, don haka ya
barwa kaninsa mai bi masa wato Abdulyaqeen Akanni wanda shine Turaki of Ilorin.
Da wannan aka bar zancen cewa washegari bayan addu’a arba’in din za’a zarce da bikin
nadin sarautar da daurin aure.
Da farko a dakin da Nenne ta sauka Siddiqah take amma da Aunty Taiwo tashigo yiwa
Nenne barka da zuwa, suka gaisa, ta tambayeta Hakeem tace yana fada, tana kallon Siddiqah
a kaikaice, taga alamar a dakin Nenne take nufin zata sauka sai tace da Nenne cikin yarbanci
da tayi tsammanin Siddiqah bata ji sam. “Nenne keda surukar taki daki daya zakuyi sharing ne? Ai ba’a yin haka a gidannan, ta tashi
ta koma cikin matan ‘ya’ya, haba Nenne don Allah ki dinga jan ajinki akan yarinyar nan”. Nenne
tayi sakatoto tana duban ‘yarta Taiwo kafin ta samu abin cewa Aunty Taiwo tace da wata baiwa
dake gefe ta dauko kayan Aisha ta kai dakin da ta sauka. Jin tace a kai dakin da take yasa Nenne tayi shiru bata tanka ba, koba komai zata so a samu
shakuwa da fahimta tsakanin Murjantu da Aisha, bata son yadda Taiwo ke treating matar kanin
nata.
Taiwo tace Aisha ta biyo ta, kamar kada ta mike don ba tun yau ba jikinta ya gama bata
Aunty Taiwo bata sonta ko kowa bai gaya mata ba. Amma jin Nenne bata ce a’ah ba, kuma
Taiwo dinnan diyar Nenne ne da bata da maraba da Hamma, sannan Maman Kikinta sai kawai
ta zari hand bag din ta da mayafinta tabi ta nata dakin. Babban bedroom ne a wani sashe na cikin gidan sarautar, dakuna ne a jere wasu na
fuskantar juna duk iri daya, yawanci matan Uncles din Abdulrasheed da matan ‘ya’yansu in
suka zo sha’ani duk anan suke sauka, dakin da suka shiga da Aunty Taiwo ya ji kayan alatun
rayuwa na gargajiyar sarauta dana zamani, ga iya kwandishin mai ni’ma nata aiki, akwai
tafkeken gado da wardrove, Aunty Bola matar wani Cousin dinsu da Aunty Iyabo matar Turaki
da Fatima da Firdausi ne a dakin suna hira lokacin da suka shiga dakin. Jikin Aisha a sanyaye
matuka don yarbanci kawai kake ji yana tashi a gidan da sauran dakunan, koda suka shigo ma
duk ta tsangwami kanta duk da Firdausi na tsokanarta da fulatanci tana cewa duk ta wani
takure, tafi son koyaushe gta like da Nenne, tace ta saki jikinta nan duk iyayen Hamma ne sai
su kannensa. Fatima ta Harari Firdausi tace da turanci don kowa yaji “in taga dama ta daure
jikin don Allah, kinsan bata son shiga cikin yarbawa kada su cinyeta, ba abin raini a wurin
yarinyar nan irin Bayerabe. I wonder yadda na jita shiru kamar an aiki bawa garinsu tun isarta
gidan Hamma kuma”. Ifedayo ta zaro ido tace “kamar yaya bata son yarbawa? Ewoo! Bata son
kabila ta auri dan su, dan ma babban jikan sarkin Ilorin da muke fatan ta zama uwa ga kowa
namu watarana?”
Aunty Bola tace “ke ko Ifedayo! Ai ‘yammatan hausawa ba don so suke aure ba, kwadayin
su ba inda baya kaisu. Balle taji sarauta zam, taji Prince na kasashen turai ai nan ‘yammatan
hausawa dana fulani suka fi kauri. Sai an yi auren kiga ba soyayyar da zata dauwamar da farin
ciki a cikinsa”. Kamar an yiwa Aunty Taiwo kunni, ko kuwa allura akan gyambon ta, ta dubi Aisha ta kyabe
baki, tace “ku bar ganin laifinta, iyayenta ne manyan kwadayayyu da basu san darajar kansu ba
balle na abinda suka haifa, amma ba ita ba, tunda ita batama san shi ba ko kafin a auro ta, su
da suka dauki wannnan teenager suka aurawa Kehinde wanda a haife ya haifeta sune suka
fiddo kwadayinsu da zalamarsu fili, ta yaya zaka aurawa danka wanda baka ko taba gani a
zahiri ko a hoto ba? Sai kawai don jin su waye iyayensa.
Wai daga haduwar kan hanya aka baiwa Nenne sadaqarta ta aurawa danta saboda an ga
mamora a jikinta.
Ni tunda nake ban taba jin aure na rashin mutunci irin haka ba, ban taba ganin auren rashin
sanin darajar Da irin naki ba, ai a al’adarku ana lefe, ana yiwa amarya kayan hana gori, amma
ke ko lefen bana jin an yi miki, ke suturar da zaki saka ma a gidanmu mu muka yi miki, da
tsummokara kikazo, ko wanka babu, aka bi aka asirce mana uwa, bata zance sai naki, amma
ku duba kuga daga shan jar miyar Ewedu har ta fara washewa, ku kuke kayan daki amma ke
haka aka daukoki zikau! Aka kawo mana.
Mun miki komai domin mu suturtaki, mai nuna sadaqarki suka baima Nenne ta likawa
Kehinde ta karfi da yaji.
Kuma shi ba so yake ba, ya fada ya kara bashi da lokacin soyayyah, bazai taba son ki ba
saboda ya dade da gama soyayya tun a kuruciyarsa, akwai wadda yayi shekara da shekaru
yana so tun samartakarsa har girmansa bai aureta ba. kuma har gobe ita zuciyarsa ke so.
Ni nasan Kehinde wallahi, babu kuma wanda zai gaya min waye Kehinde, ko a kafa aka
daura masa ke nan gaba kadan zai kwance ya yar.
Kawai kun ga arziki da sarauta kun nace, watakila ma kuna tunanin Kehinde zai yi sarauta
ne, to in gaya miki gaskiya inma wanan kukewa keda iyayenki to kije ki gaya musu Kehinde
bazai yi ba.
Da aka aura masa ke aka kawoki guidanmu saida ya jingineki kusan shekara guda, saida su
Nenne suka gaji da ajiyarki a daki ne suka tattara ki suka danna masa ganin wankin hula zai
kaisu dare.
Da zuwanki gidansa na fahimci kun soma juya masa kai, iyayenki nata surkulle ga dukkan
alamu, har wani dora ki yayi a status baya ko jin faduwa a ganshi dake a matsayin mata.
Nayi rantsuwa ni Taiwo abokiyar tagwaitakarsa, inma asirinku ne ya fara cinsa ko zan daina
barci sai na warwareshi da karfin addu’a, in asiri kuke shiga jeji kuna jefa masa mu addu’a
muke kwana yi, yadda kuka ganshi haka zaku kyaleshi. Kakan kakanmu Shehu Alimi, ya dade
da tofe zuri’ar shi da kul’aquzai, daga duk wani sharri na masu nufin Kehinde da wani surkulle
na magauta da irinku makwadaita”.
Duk maganar nan Taiwo na yinta ne cikin sassaukan turanci da fulatanci ziryan, don ma
Aisha ta fahimta sosai.
Siddiqah dai tana zaune banda kallon bakin Taiwo ba abinda take yi. Kirjinta yana
harbawa zuciyarta na matsewa. Fuskarta na rinewa daga yellow zuwa jazir.
Saida Aunty Taiwo ta gama cin mutuncinta tas, su kansu su Fatima da Firdausi
wadannan maganganu na Yayarsu Taiwo sun san firgitasu domin sunji sun yi zafi da tsauri
sosai. Firdausi jikinta rawa ya fara yi ta soma cewa “haba-haba Aunty Taiwo? Haba ke kuwa
don Allah Maman Kiki? Wannanba girmanki bane”. Ganin yanayin da Aisha ta shiga ya firgitasu.
Babu ko digon hawaye a fuskarta amma tsigar jikinta duk ta tashi yarr, tsokar fatar bakin ta har
raurawa takeyi amma ba kuka ba.
Taiwo zata wuce toilet ta bar su a wurin suka ga gabadaya jikin Aisha ya dauki kyarma,
idon nan ya koma kamar garwashin wuta ya kada yayi jazur… Ga dukkan mamakinsu Aisha ta
mike da hanzari ta sha gaban Aunty Taiwo dake neman wucewa toilet wato ta gama zagin
banza, ta sha lafiya zata wuce harkokin gabanta. Aisha ta tsaya gaban Aunty Taiwo, gabadaya ta koma Aisha-Siddiqarta fitinanniya,
masifaffiya, ta Billiri ikon Allah! Gang leader mara tsoron kowa, sannan mara kara wato mai
keke - da kekenta da kowa ya sani, ta kalli Aunty Taiwo cikin ido ta soma magana cikin
sarkewar numfashi. “Na rantse yau kinci albarkacin haihuwa, kin ci albarkacin Kiki a wajeana, kinci albarkacin
dimbin qaunar da ‘yar ki ta nuna min.Sannan kinci albarkacin girma da shekaru.
Sannan kinci albarkacin Nenne, mafi girma kuma kinci albarkacin tarbiyar da iyaye na suka
bani akan wanda ya girmeni!!!
Kinci zarafin dattako da tarbiya da kamalar da Nenne take dashi kuma ta baku ku ‘ya’yanta,
kin ci amanar tarbiyyar data baki!!!
Aunty Taiwo ta saki baki galala! Tana kallon yarinya karama haka kamar diyarta Kiki, ta
tsaya a gabanta tana maida mata da martani, yarinyar da bata wuce second born dinta Kiki ba,
duka mutanen dakin ma su Ifedayo da Aunty Bola sun sha mamaki domin basu zaci zata iya
tankawa Taiwo ba sam, da yake cikin turanci take maida mata martanin duk suna ji, kallonta
suke, shock duk ya kamasu.
Firdausi ta soma bata hakuri daman tunda Taiwo ta fara zuba rashin mutuncin Firdausi tana
ta cewa “haba aunty Taiwo, ki bari bai kamata ba” Taiwo ta ce mata “shut up malama! Kada ki
kara saka min baki in ina magana”.
Ganin haka gudun kada akai ga duka sai Princess Firdausi ta dauki wayarta jikinta nata
kyarma ta yiwa Hamma text, tace maza ya bar duk abinda yake yi yazo don Allah ga Aunty
Taiwo na cin mutuncin Aisha tana neman wulakantata a gaban dangi”.
A take Hamma ya kira Firdausi immediately, ai kuwa Firdausi ta saka masa a handsfree,
yana iya jin muryar Taiwo na karasa wassafa ma Aisha… “ki dake ni mana ‘yar Mallam Shehu!
Shine zan san kinyi fushi na zagi makwadaitan iyayenki da suka yi miki auren sadaqah.
An zagi iyayen naki, wata tsiya ne su? Ko zaki rama eh? Ke a karan kanki da dan hankalinki
kinga dacewar ki auri Kehinde?
Banda kankanba irin ta talakawa da kai kai inda Allah bai kai ka ba, ina ke ina zuri’ar
Akanni?
Ai da kin tafi kin auri mai kora shanu a kauye shine daidai ke…. Amma ba dan Sarki babban
jikan Sarki ba…”.
Hamma be kashe wayar ba a haka ya karaso hankalin sa a matukar tashe. Aisha ta wuce ta
gaban Taiwo a zuciye, ko ganin gabanta bata yi. Wani irin tafasa zuciyarta keyi. Babu kuka ko
digo a idonta zuciyarta ta bushe. Bata so ta kara wata kalma bayan wannan don zuciyarta na
iya bugawa a lokacin. Firdausi ta kula da hakan ta taso ta biyo bayanta da sauri tana Siddiqah tsaya don Allah….
ko jinta batayi ba ta bude kofa, sai karaf! Tayi karo da mutum tsaye a bakin kofar.
Data daga kai ta kalle shi da idanunta kamar gauta sai ta kawar da kai, ta sake juyowa tana
kallon Taiwo data biyo bayanta…. ganin Kehinde yasa Taiwo tsayawa standstill. Wani irin
bayyanannen bacın rai ne a fuskar sa, zata iya rantsewa tunda take da shi bata ta a ganin
wannan yanayin a tare dashi ba. Ya bude baki zai yi magana sai jin Aisha yayi ta juya tana cewa da Auty Taiwo….
“Kuma kamar yadda kike ta tutiya kan cewa baya sona, haka zalika nima baya cikin lissafina
balle na irin mazan da nake so, ki tambayeshi kiji biyayya duk mukayiwa iyayen mu, saboda sun
isa da mu. Daga yau na bar miki shi. Gashinan ki jika shi ki shanye….”.
Tana gama fadin hakan ta wuce ta bar musu dakin, ga dukkan mamakin Taiwo sai taga
Prince ya bi bayanta yana “Aishah Please wait…Don Allah tsaya…” ko kallonsa Aisha bata yi
ba ta kara sauri, ta kara da gudu-gudu, shima ya daga kafa ya bita yana “please listen to me
Aisha….”. Yayi sa’ar riko gefen gyalenta, Aisha ta juyo a fusace tace “cikani, daga yau na gama
wannan auren”.
A lokacin sun kawo kofar dakin data baro Nenne. Kalaman Aisha na karshe a kunnen Nenne
suka sauka, inda tace.
“na gama auren nan, na barwa Aunty Taiwo dan uwanta Kehinde ta jika ta sha, har abada
baa auren!”
Da sauri Nenne ta taso suka game ita dasu a bakin kofar, ganin yanayin da Aisha ke ciki da
rudewar dake fuskar Hamma saida gaban Nenne ya fadi.
Ta kama hannun Aisha suka shiga cikin dakin Prince