Showing 24001 words to 27000 words out of 40544 words

Chapter 9 - Aishah-Saddiqa 4 end Complete Novels by Sumayya Takori.pdf

sannan ya kalli Baba Barau, sai kawai ya rufe ido,
a ransa yace “shikenan, daman can Taiwo tayi masu gorin arziki, toh yanzu Baba Barau cewa
zai yi shi da kansa yayi musu, amma dai ba’a kyauta masa ba…”.
Prince yana cikin wannan tashin hankalin sai ya ji Mal. Yunus ya ce, “sun gode”, ya kara da
cewa ayiwa Uban kasa godiya, Allah ya kara girma, ya saka da alkhairi”.
Ya kuma kallon Baba Barau, sai yaga dai fuskarsa normal. Suka mike daganan aka tashi
za’a shiga mota.
Suna gaba sun fito kenan kamar ance ya kalli gaban sa, sai ya hango Aisha da wasu
‘yammata biyu suna dawowa.
Cak! Hamma ya tsaya ya dan kalle ta, duk da hijab ne jikin ta amman abinka da farar fata
lallen nan ya fito, yatsun nan sunyi jajawur kamar jini, ita ashe tunda taji muryar sa ta fice ta tafi
gidansu, tace taje dauko wasu kaya.
Shine Furairah matar Baba Barau tayi waya tace ace Aisha ta dawo bakin sun tafi. Tsayawa
sallama da mutane yasa har suka dawo suka cimmasu a kofar gida.
Ba wanda ya lura ita yake kallo, don tana daga nesa. Amman Prince ya ganta, itama kuma ta

ganshi. Da kyar ya shige mota dai suka wuce
Hamma yana shiga mota yace ma Kawunsa Abdulmajeed bazai yarda a qara saka shi wakilci
ba, Uncle Abdulmajeed da Sarkin dogarai suka yi ta dariya.
Da suka koma gida Prince ya kwabe Rawanin a falon Oumana ya shige nasa dakin dake
sassanta yayi wanka ya kwanta. Zuciyar sa na hasko masa Aisha. Shi a idonsa kamar ma kiba
yaga ta kara.
Yace a ransa wato yarinyar nan babu ma abin da ya shalle ta dani, gashi nan tana ta shan
lalle tana yawo a unguwa, shi kadai ake yi wa boyon ta. Takaici hana shi hutawar da yayi niyya.
Yadda tayi kyau dinnan haka nan take ta yawo a cikin unguwa da gari kowa na kallon lalle ya
masa kyau kowanne gardi yana kyasawa a ransa.
Ai sai ya mike ya saka jallabiya ya wuce parlon Nani Oummana. Nan ya samu Nenne da
Oummana sun idar da isha kenan. Tace “yaya dai Hamman su? Ko a kawo fura? Na ga ko
abinci baka ci ba. Yace “Oummana yaushe zaku gidansu Aisha ne?” ta ce “ba ance sai gobe ba
yau biki suke tayi?” Yace “ai na ganta tayi lalle sai yawo take a gari kowa na kallonta”. Nani da Nenne suka hada baki suka ce “kayi hakuri, gobe sai aje, in sha Allah. Amman kar
ka fada masu za’a zo”.
Washegari sauran yan yinin biki duk suka watse. Kafin la’asar gidan ya zama ba kowa sai
‘yan tsirarun mutane. Nenne ma ta kira Umman Siddiqah suka gaisa amman bata ce mata tazo
Gombe ba. Tayi masu Allah ya sanya alkhairi a uren Maryam, suka gaisa da matar Baba Barau
ma. Nan tace “anata yinin biki” Furairah tace “ai tun jiya suka kai amarya. Yau can gidan ta zasu
yi yini, nan dai an gama komi. Nenne tayi masu fatan alkhairi sukayi sallama. Nan take ce ma
Oummana ga yadda sukayi da Haj. Zainab da matar wan Baban na Aisha. Suka ce toh a bari
zuwa bayan isha tunda Uban kasa yace dashi za’a je.
Da aka yi magriba, Hamma ya kira Mal. Yunus suka gaisa, yace “ya gajiyar jiya?” Yace “ai
baba akwai ta, saida nayi ciwon kai na rawanin nan, ai nace baza’a qara wakilta ni komai ba”
Mal. Yunus yai dariya yace “ayi haka kuwa Abdulrashid?” Yayi murmushi. yace “baba kana gida
ne?” Yace “eh, ina gida amman yanzu zani gidan Yaya Barau yace in zo”. Prince yace “toh
shikenan Baba a dawo lafiya”.
Ana idar da sallahr isha Uban kasa yayi badda kama dashi da Dade a mota daya da sarkin
dogarai sai driver Malam Buhari.
Nenne da da Hamma da Uncle Abdulmajid mota daya suma suka shiga sa Jeka da Fari.
Gabadaya Abdulrasheed ya bade su da sassanyar kamshin turarensa Boss Intense. Yau dai
jallabiya ce jikinsa coffee, da hula irin ta saudi dinnan. Ya saka slippers din ‘LV’ da ‘counter’
haka a hannun sa. Sai ya fito yaro sosai, yau kamar ba shine basaraken jiya ba.
Shi yayi sallama gidan Baba Barau. Ai kuwa Auwal ya fito ya ganshi, ya shiga ya fadawa
Baba Barau.
Baba Barau yace “kai wannan yaro ya cika naci. In ba bashi yarinyar nan nayi ba cinye ni
zaiyi, haba!” Auwal ya rike dariyar sa shi da Malam Yunus. Yace “amman yau sai naci masa kan
wannan naci da yake yi min, je ka shigo dashi”.
Baba Barau yana zaune ya bata fuska, yana jiran shigowar Prince, sai ko gashi nan ya ga ya
shigo, sai ga Uncle Abdulmajid ma, yace “ah ah, kai ya sake dauko…” kafin ya kai aya sai ganin
Uban kasa yayi da Nenne. Yace “la’ila ha illahu…” suka tashi su dukkansu, yace “dan Allah ku
zauna. Ai yau ba maganar sarauta, biko nazo wa Da na wurin Baba Barau, ayi mana afuwa”.

Baba Barau kamar ya nitse, kunya duk ta kama shi, wato gabadaya kowa kallon bala’e’e
yake masa. Yunusa ya zame kansa ya barsa da kunya, yace “Allah ya taimake ka”.
Suka zauna dukkansu aka gaisa, Mal. Yunus yace Auwalu yaje ya dauko Umman Aisha.
Auwalu ya tashi ya tafi, sai matar Baba Barau ma ta shigo suka gaisa, suna ta jinjina saukin
kai na wannan sarki, da kuma irin son da suke ma Aisha da Kehinde.
Umma tazo, akai rungume-rungume ita da Nenne, tace “baki ce min kinzo ba dazu da
mukayi waya”, Nenne tace ai tun jiya muka zo, da naji ana biki nace sai kun gama.
Nan Uban kasa ya basu hakuri yace ayi wa Prince uzuri. Yace kuma yara ne ka haife su
baka haifi halin su ba, amman tun ba’a je ko’ina ba itama tayi dana sani, gashi da ita suka zo.
Taiwo ta basu hakuri, tace sharrin shedan ne ayi hakuri. Nan dai akayi sulhu, Aisha ma tace ta
haqura. Zuciyar Hamma wasai yau. Mutuniyar dai ko kallon sa batayi ba. Saida aka gama Baba
Barau yace “toh Aisha dai an siya mata jamb form, zata yi anan Gombe sati mai zuwa”. Nenne
tace “ba komai, tayi abinta a nitse, bayan jamb din sai ta koma”.
Kehinde dai yayi shiru. Sai Mal. Yunus ne yace Aisha ko zaki hakura kiyi a can, dan nasan
Abdulrashid kamar sati biyun da aka debar masa zai kare cikın satin nan mai zuwa”.
Nan Siddiqah tayi maza tace “ah ah Malam don Allah, inaso nayi, dan in samu cigaba da
karatu na”. Nenne ma tabi bayanta. Baba Barau ya kallo Hamma, sai ya bashi tausayi, yace
“kuyi shawara dai”. Koda Hamma ya kalle ta yaga tana wani cin magani yau shiru bai ce komi
ba. A haka aka gama hirar. Baba Barau yace sunga sakon jiya an gode. Uban kasa yace ai diyar
shi ce, an zama daya yanzu. Akayi ta hira ta dattaku kafin akayi sallama, duk suka shige
motocinsu suka koma. Kowa tashi zuciyar fessssss.
Aisha ta dauka Hamma zai tsaya ya lallashi ta sai shiru taji ya ware tareda iyayensa.
Prince ya dan ji haushin yadda Aisha ta kafe ita sam sai tayi jamb zata koma. Shi kuma
yasan dole ya koma Alhamis sabida Argentina zai fara tsayawa, akwai abinda dole zai dauka ya
manta gidan su, inyaso Friday ya wuce Qatar ya dan huta, Monday ya koma aiki.
Yanzu Aisha naso ta jiqa masa aiki. shi kuma (he wouldn’t beg….) don ya ma lura har wani
kiba tayi ta kara haske, ba abin da ya dame ta….
Prince ya shiga damuwa, kada fa yarinyar nan ita (nothing has changed in her feelings
towards him, shin shi kadai ke rawar sa da tsalle or what….?
Ire-iren tunanin da yayi tayi kenan yau, sai ji yayu ana kiran assalatu.
Yayi sallah ya godewa Allah, kuma ya rokar musu dukkan alkhairinSa.
Da safe sai wajen 11:30 ya tashi. Yayi wanka ya sa kananan kaya ya shigo falon Oummana,
ya gaishe su ita da Nenne, sai Taiwo dake zaune itama sun gaisa.
Oummana na tsokanar sa wai daga sulhu sai yau ya qara zama yaro. Prince yayi dariya
kawai yace “ai Oummana Aishan tace ita sai tayi jamb zata koma don neman magana. Su
Nenne kuma sun bi bayanta ni kamar bani da mai bin bayana sai Babanta”.
Nani Oummana tace “ai jan aji ake maka, ka san Indo Aisha ba daga nan ba”. Hamma ya
girgiza kai yace “ai na shaida. Ayi jarrabawa lafiya.” Tace kai dai yau ka shirya kaje zance, daga
nan ka gwada sa’ar ka, yace “uhm….”.
Aisha ana can gida, tun jiya dama da suka tafi iyayenta suka sake yi mata nasiha ta zaman
aure suka ce kuma ta gode Allah ya bata surukai na kwarai da mijin da yake matukar son ta.

Dan an gwada shi ta ko’ina kuma yaci gwajin. “Duk wasu experiments da suka dora jikan
Akanni bai fadi ko daya ba!”.

Dan haka suka ce ta kawar da maganar Taiwo daga ranta ta fuskanci aurenta da mijinta da
iyayen mijinta. Ta kyautata musu ta kuma rike su da kyau.
Baba Barau yace “tunda naga ya matsa ma Indo ko zaki hakura ki bar jamb din ne? Ban ga
amfaninta ba tunda kasar zaku bari fa.” Tace “Baba gara inyi, ko ba komi dole zan koma
makaranta, ina so in cigaba”.
Baba Barau yace “toh bakomi”.
Addar Kumo tace “gara dai ki kara satin kema, sai ayi miki shirin amarya, kamar yadda akayi
ma ‘yar uwarki Maryam. Yanzu ne za mu kai diya, dan wancan kaiwar daman dai yin sa kawai
akayi”.
Ummanta tace “nima zanfi son haka”. Aka ce “toh shikenan. Allah ya masu albarka”.
Toh dazu bayan azhar tana tsakar gida sai ga Baban ta ya shigo yace Hamma ya kira shi
yace zai zo anjima ya musu sallama sabida gobe daga Litinin ze wuce Lagos, jibi zai tafi
Argentina. Aisha tace “toh” tayi ciki.

Ta ma rasa me take ji. She is happy, kuma har ranta abin da ya faru ya wuce, amma kuma
sai tana jin haushin Hamma yace zai tafi. Wato bai ma damu ba, da tace baza ta bishi ba.
Hmmm! Da Haseena ce kila kuka zai yi tayi…mtsw…..
Satin nan da tayi a gida, quite sure tasan Hamma bashi da laifi, amman kawai dukansu taji
sun bata haushi daga Taiwo din har shi. But daga baya tana dan missing dinshi.
Amman jiya yadda taji Baba Barau yana bata labarin nacin da yayi tayi akanta, ya dawo
Gombe ma gabadaya duk sai ta ji tausayin shi da so me girma.
(She always want to be loved) sosai irin haka, toh gashi itama dai kamar Prince ya fara
sonta.
Amman wannan cewa da yayi zai koma be matsa su tafi tare ba, ya bata haushi. Ta sake
kwana a gidan Baba Barau dai, ta dawo gidansu tayi kwance har akai magrib.
Daman tun yau da safe aka fara mata gyaran jiki itama. Ummanta tasa an mata halawa dazu
dasu dilka, tace baza a qara ba.
Toh yanzu ana ida magrib Umma ta miqa mata diye tace taje ta durje jikinta dashi ta hada
mata lalle da khumra kuma tace ta dauraye jikin dashi. Aisha tace “toh”. Ta shige toilet tayi ta
gama ta fito. gaba daya dakin har waje kamshi ke tashi. Tace “Umma nidai mura zanyi in
kullum zan wannan wankan”. Haj Zainab bata tanka ta ba dai, tace “yi ki shirya ko Hamma yau
zai zo zance” tace “kai Umma, ina tsoho ina zance” Umma tace Patel kenan, ana so ana kaiwa
kasuwa. Ni je ki shirya kyaji da gulmar ki”. Ta wuce ta barta a wurin.
She is so nervous, a haka ta tashi tai sallahr isha. sai ta dauki kulaccen da Ummanta ta bata
ta shafa, da tasa undies dinta black ta ma rasa kayan da zata sa, akwai wata abaya da
Ummanta tazo mata dashi daga Hajj bata taba sakata ba daman suka tafi Lagos da Nenne. Ita
ta dauka tasa, white and silver haka kuma cif-cif jikinta. Sai ya kwanta lubb! A jikinta, kugun nan
nata ya fito masha Allah.
Tace ta san dai tayi kiba saboda abayan kamar yanaso ya matse ta, karin kibar nata har
haka ne? data gama ta dauko ‘yan hannun gold din da Nenne ta bata na Makkah ta saka su,

tasa ‘yan kananan ‘yan kunne na gold suma ba sarka. Tayi parking kitson ta tayi gammo da
gashi. Sai ta dau gyalen abayar ta yafa. Tana zaune taji ana gaisuwa a tsakar gida, gaban ta ya
fadi….
Shi kuma Prince tun da akai magrib ya dau wanka. Ya dai ma kasa cin abinci. Yayi sallah
yana zaune da jallabiya har akayi isha, sannan ya shigo cikin sassan Oummana, Nenne tace
yazo yaci abinci yace a koshe yake. Bari ya shirya zashi gidansu Aisha zai masu sallama tace
“toh” ya shiga ciki ya dauko kananan kaya sai kuma ya mayar, yace gidan surukai ne. Sai ya
dauko wata baqar (voile lace) na maza. tana da shara shara haka sai daukan ido kyallin ta
yake. Wando da riga irin iya cinya dinnan cip jikin sa dinkin. Sai karamin hannu haka ba dogo
ba iya gwiwar hannu. Haka Hamma ya shirya tsab, ya dauko hular sa Tonak ya saka baka
itama, da design din silver a jikinta, ya zuba turaren ‘Tomford Oudwood’ ya kuma dauko ‘Francis
Kurkdjian Baccarat Rouge’ ya fesa.
Wani sanyayyan kamshi na tashi daga jikin Prince ya dauko ‘black hermes’ ya saka ya daura
‘rolex’ dinsa ya fito.
Ai yana fitowa sai Taiwo tasa guda har ma dai yaji kunya, su Nenne duk suka juyo, yace
“meye haka Taiwo?”, tace ko dai mu dauko mayafi mu bika naga daukar amarya zaka yau” yace
“kash!” Ya wuce.
Nenne da tayi murmushi dan tun bai fito ba suke jin kamshi. Lallai Aisha Siddiqa ta ciri tuta.
yau Kehinde ke ta wannan rawar kafar haka zai je zance. “Alhamdulillah” Nenne ta gode ma
Allah.
Yace musu se ya dawo ya fita. ya dau mallam Buhari suka wuce.
Prince ya yi sallama gidan su Aisha, Mallam Yunus yana tsakar gida suna zaune da Umma,
ya amsa ya ce “shigo mana Abdulrashid”. Ya shigo ya gaishe su. Sun burge shi. Domin sun
shimfida katuwar dadduma ga abinci nan a gefe, ga sallayar Umman Aisha da hijabinta akai.
Nan tayi sallah kenan. Tana gefen Mal. Yunus suna hira tana dama fura. Shikuma ya kishingida haka kan tuntu.
They look so simple and very in love. Masha Allah kawai yace a ransa, ya karaso suka gaisa
yace Oummana na gaishe su. Mal. Yunus yace suna amsawa ina Dade? Yace ai ya koma
Lagos tun dazu. su Nenne suma jirgin safe zasu bi gobe. Suka ce “toh Allah ya kai su lafiya”.
Akayi shiru, Umma tace “shiga palo Hammansu, bari in kira Petel”.

“Petel!!!!”
Umma ta kwada mata kira, ta amsa daga cikin dakinta tace “na’am” tace ga “Hammanku
yazo, ki debo ruwa da abinci ki kai masa. Hammansu akul kayi min fulako” yayi dariya yace
“Umma ai daga gida nake, furar kawai zan sha”. Tace “toh bari ta kawo maka” yace “toh”.
Ta nuna masa kofar falo ya shiga, ya zauna yana jiran gimbiyar tasa.

Can sai gata ta fito, Ummanta tace “dau fura da yamri a fridge da kindirmo duk ki tafi dashi,
wanda yafi so sai ki dama masa”. Tace “toh Umma”. Umma duk sai ta ga wani kyau diyarta yau
ta tatso, tace “uhm lallai… Aisha dai an girma, masha Allah”.
Tayi sallama ta shigo, fuskar dai a gimtse, da dan nisa tsakanin falon Baban nata da cikin
gida. Prince ya amsa mata, ta shigo, ya daga ido yana kallon ta.
Tashi yayi don ya taya ta da kayan hannunta amman sai ya kasa. Wani kamshi takeyi da ya

rasa wane iri ne tun shigowarta, ta qara cika, ga wata abaya nan ta saka ta kwanta jikin ta,
gabadaya surarta ta fito waje…. shi yarinyar nan take so ta jiqawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login