Showing 18001 words to 21000 words out of 40544 words
Chapter 7 - Aishah-Saddiqa 4 end Complete Novels by Sumayya Takori.pdf
a ransa, ya tabbatar ya kuma kara yarda bai aurawa Aisha mijin
banza ba tunda gashinan hakikanin gaskiyarsa yake basu hakuri, yake kuma Allah wadai da
halin ‘yar uwarsa wanda shi kansa Malam Yunusya san tabbas wulakanci ba halinsu bane.
Amma still he is so proud da Aisha ta nuna musu iyayenta ba abin wasa bane don haka bazata
dau wulakanci ba.
Sannan kuma ya ga girma da soyayyar Aishaa idon YarimaAbdulrasheed wanda yasa ya
kara jin dadi, amma duk da haka yace bazai shiga maganarsu da Baba Barau ba. gara yaje
Baba Barau ya kara wana shi amma zancen kashe aure yanzu babu shi in sha Allahu.
Baban Aisha nan take yace da Sunusi ya raka su gidan Baba Barau din. Sunusi ya saka
takalmansa ya shiga gaban mota, Prince na owner’s side, Malam Buhari yaja motar suka tafi,
don gidan Baba Barau ba nisa sosai, layi biyu ne tsakaninsa da dan uwansa.
A zaure suka tadda Baba Barau yana cin abinci, ga fura mai sanyi a gefe an ajiye masa a
kwanon silba a gefe. A nutse Prince ya yi sallama a zauren. Baba Barau ya amsa duk da bai
taba ganinsa ba, don haka da fara’a sosai Baba Barau yake wa hamshakin bakon nasa da bai
san ko waye ba barka da zuwa, ya ce. “Zo nan bisa buzuna ka zauna”.
Prince har da cire hula bayan ya cire takalmansa ya ki hawa buzun ya zauna a kan kafafunsa
tankwashe a gabansa. Ya fara gaishe shi da hausarshi da ba ta da kwari.
Baba Barau ya ce, “Ban gane dan nawa ba, daga ina kenan?”
Nan Prince ya gabatar masa da kansa da cewa shine Abdulrasheed daga Lagos. Baba
Barau ya kara neman karin haske, don har lokacin bai gane ba, Prince ya kasa magana sai da
kyar ya iya cewa “Mijin Aisha-Siddiqah”. Ai nan da nan Baba Barau ya hadiye duk wani annuri
da ke fuskarsa, Prince ya kara gaishe shi a ladabce, ya bashi hakuri akan zuwan Aisha. don
yana da labarin Baba Barau a bakin Aisha, wani Yayan babanta da ba ya daukar wargi kuma ba
ya yarda ko Babanta ya bata mata rai. Yadda Baba Barau ya maida walwalar fuskarsa ne ya sa
Prince jin wata irin shakkarsa. Amma hakan bai hana shi fadan abin da ke gabansa ba, ya fara
da bada hakuri sannan ya ce masa wallahil azeem shi Aysha tafi karfin wulakanci a garesa.
Dalilin ma da ya bari sai yau ya taho kada cece-kuce yayi yawa ne cikin taron bikin. Ya kuma
tabbatarwa Baba Barau ya magance matsalar Taiwo. Kuma yayi alkawarin baza’a kara ba. a
wannnan gabar Baba Barau kansa ya yaba da hankalin Prince. Ya ce “naji, amma dai a hakura
kawai da aurennan, kaima daman ba so kake ba itama haka, to kuma kaga akwai mutunci
tsakanin iyayenku mata kada auren nan ya zama silar matsalarsa”.
Murya na rawa Prince yace “Baba ni ia son Aisha…” Baba Barau ya dakatar dashi yace
“Abduulrasheed maganar gaskiya yaranmu basa auren wulakanci, munada hakuri amman
banda wulakanci, kuma abinda yasa Aisha dawowa gida haka to babba ne, inda duk za’a taba
maka iyaye bazakaso zama ba. so ina bayan Aisha kan duk abinda ta yanke, kaje zan neme ka
zanyi shawara”.
Jiki a sanyaye Abdulrashid yace “toh Baba, nagode, zan iya ganinAisha yanzu?” Baba Barau
yace “a’ah”. Sai yayi shiru na dan lokaci cikin damuwa daga bisani yace “to shikenan Baba zan
tafi nagode”.
Suka koma gida, ya kwashe komai na yadda sukayi da Baba Barau ya gayawa Nani
Oummana.
Da kyar Nani ta rarrashe shi ya dan ci abinci ya yi mata sallama ya wuce gidansa.
Nani sai ta dau waya ta kira Nenne suka gaisa, Nani ta yi mata ban gajiyar biki da ta hidima,
Nenne ta ce, ai har sun dawo Legos, ta kansile da yawan events din bikin da ba su zama dole
ba saboda Taiwo data bata ciwon kai. Tana son kashe auren Hammansu babu gaira babu dalili.
Nani ta ce, “Amma Dadensu ya kyauta min da ya wanke ja’ira mai halinsu na yarbawa, mu
dai kam Murja ba ta dauko mu ba, can musu cikin Akannin”.
Nenne ta ce, “Ai ko a Akanni babu irin Taiwo. Ita kadai ce da halinta, mijinta ma hakuri yake
da nature dinta ba tun yau ba. Tun yana kawo kararta ana sulhu har ya gaji ya yi nesa da ita, sai
ya yi watanni uku bai waiwayo ta ba”.
Nani ta ce, “Addu’a za ku dinga yi mata da nasiha ba fushi da ita ba. A shekarunta dai ta yi
girman banza”.
Sun dade suna tattaunawa a kan sha’anin Taiwo, har Nenne ta ce, “Ban da abin Murja ma
Aisha ba ta ki Hammansu ba saboda ratar shekarun da ke a tsakaninsu sai shi ne zai ki Aisha?
Aisha son kowa kin wanda bai samu ba, na bi sarauta da kudi da gudu, na kama wa Hamma
Aisha ne saboda nagarta da iyaye na gari, idan kuwa har Aisha ta fada wa iyayenta abin da
Murja ta yi mata, to abu ya baci. Don ba kowa zai yarda a taba mutuncinsa a wanye lafiya ba,
shi ya sa daga ni har Dade muka ce babu mu a 'yan biko wai ido da kunya. Shi da ya bar Murja
ta ke taka rawa cikin rayuwarsa sai ya nemo ta ta yi masa biko”.
Nani kuma ta ce, “Hamma meye laifinsa? Ana hora shi ne kawai da laifin da ba nashi ba. Ya
je bikon ai ga shi ya dawo ba nasara, ya yi min shame-shame a falo kamar gawa. Duk sonsa da
fura tunda ya zo bai sha ba”.
Nenne ta ce, mu kyale shi ya yi ta bikonsa shi kadai, ya fi sanin darajar wahalar da aka yi
masa aka yi masa aurenta babu ko kobonsa”.
Nani kuma ta ce, “A’a za ta sa uban kasa ya shiga maganar, idan Abdulrasheed ya kasa.
Kwanan sa biyu a Gombe. Rana ta farko da yaje ga yadda suka kwashe da Baba Barau, don
haka ya sake kwana a Gombe. Washegari ya sake komawa wajen Baban Aisha da Umman ta,
ya gaya musu yadda sukayi shi da Baba Barau, ya Kuma roki Abban Aisha don Allah ya taya
shi baiwa Baba Barau haquri. Malam Yunus ya lallashe shi ya ce ya koma gida zai ma Yayansa magana, dan har ga Allah
yaji tausayin sa.
Prince ya saki jiki da iyayen Aisha kamar ba jiya ya fara zuwa ba. Sukayi developing good
bond. He is open minded, ga kuma hankali. Amman kana ganin sa kaga damuwa.
Abban Aisha yace masa kar ya damu yaje gida zai saka baki. Kuma kada yaje gidan baba
Barau yau tunda jiya ya je, zai neme shi da kansa, yace yayi haq9uri har ya neme shi din.
Prince ba yadda ya iya haka ya dawo Lagos bai san makomar aurensa ba.
A daren ranar yana tareda iyayen sa a falon gidansu. Dade ya tambaye shi "toh ya akayi a
gomben?" Nan Prince ya fada masa komai, yace murya ba kuzari "nidai Dade ba don Taiwo yar
uwata bace da na mata Allah ya isa, finally i have a glimpse of happiness, ta lalata min shi,
wannan wani irin rashin sa’a ne?" Prince ya fadawa Babansa in a heartbreaking manner. Yasa hannu ya dafe kan sa. Sai ya ba Dade tausayi matuka. Suna haka aka kira shi daga
Qatar, Dade yana jin sa yace musu bashi da lafiya su qara mashi 2 weeks.
Sai bayan ya aje wayar ne Dade yace masa "toh ka koma mana sai ka dawo daga baya? By
then itama ta huce Aysha din". Prince yace "Dade ko na koma bani da nitsuwar yin aikin, gara
dai inyi ta fama ko zata haqura. in kuma taqi haqura sai na koma din.
It seems that’s the life my own twin thinks i deserve, a lonely, sad life, unworthy of pure
happiness… and apparently you and Nenne too....".
Prince ya furzar da numfashi me daci a kasalance ya tashi zai wuce gidansa. Dade yace
"why will u say that?" A marairaice Prince yace "toh ba cewa kukai ba ruwanku ba Dade? Ni
iyayen aysha basu sanni ba ku suka sani. And if we are being honest I am nothing but good to
Aysha.
Ita in yarinta ya debe ta ba se a duba ni ba. Ni da ba ni nayi laifin nan ba and also ba ni nasa
Taiwo ba. Amman duk laifin ya dawo kaina kuma kunyi shiru kunce ba ruwanku. Gaskiya i won't
forgive Taiwo for this Dade she really did hurt me…." ya tashi zai tafi ya juya kenan sai kuwa
sukayi ido hudu da ita. Taiwo. Jikinta yai sanyi, tazo ne immediately don Dade ya aika a kirata
dazu.
Ko kallonta Prince baiyi ba ya fita ya tafi gidan sa.
Nan iyayen sukayi mata tatasss, don Nenne ma taji me yace ma Dade tana daga dakin Dade
din, kamar yadda Taiwo taji itama tana shigowa. A ranta ta fara nadama. Ga nasihar da iyayen
ke mata suna kuma nuna mata ta butulcewa son da Kehinde yake mata in har itace zata saka
shi a wannan halin. To duk wannan ya taru yasa Taiwo ta damu, a lokacin ta baiwa iyayensu haquri ta koma gida
ta wuce ta sai tiket din tafiya UK.
Bayan fitarta ne Dade da Nenne suka kara tattauna maganar, suka aje lallai Friday zasu je
Gombe takanas suyi bikon nan da kansu. Alamu sun nuna fa Hamma yana ta iyo a kogin
soyayya. Babansa kuma yasan basu iya so ba, gara ya taimaki magajin sa. Nenne har sallahr
nafila tayi ranar ta godiya ga Allah ganewa data gama yi Hamma Abdulrasheed yana son Aisha,
ga kuma irin matakin da ya dauka kan Twin dinshi Taiwo da cikinsu da ita kanta Taiwo din babu
wanda ya zaci zai iya hakan akan Taiwo. Ta san ko da wasa bazai kara barin wani ya taba
Aisha ba, dan haka zasu shirya nan da kwana uku suje Gombe, yau talata, toh ranar Friday ko
Saturday zasu je gombe.
Shi Prince bai sani ba ya tafi gidansa haka ya kwana zuciya ba dadi. Sai asubahi ma bacci ya
dauke shi, yana tashi yaga ba amfanin zaman Lagos. Bari kawai ya koma Gombe din sai yayi
jiran hukuncin Baba Barau a can.
Nan Hamma ya hada 'yar akwatin tafiyarsa ya kira nenne a waya yace zai koma Gombe.
Nenne tace ko lafiya ince ko? Prince yace "toh Nenne ai gara ina can in yi ta matsa musu kawai
Nenne. Idan Kuma har lokacin basu yarda ba zan tafi inyi reporting wurin aiki…
Tawakkaltu Alallah… na fawwala wa Allah".
Nenne sai taji ta kuma jin tausayinsa masa je ka Hammansu Allah ya ba da sa’a kaji, Allah
kuma yai albarka albarka Annabijo".
Prince yace amin Nenne". Ya tafi a ranar ya hau jirgin Gombe.
Oummana sai gani tayi baqon shekaranjiya ya dawo. Tace "yaya dai Abdulrasheed?" Sai
yace "nan zan zauna, sai an bani matata" Ommana sai ta fashe da dariya tace, "ah lallai Indo ta
murza kambu, sarauta ta fadi" Prince yace "ai Oummana warwasss! Sarautar nan ta fadi.
Aisharku itace mai mulkin". Me Oummana zatayi ba dariya ba. Tace "sai ka shirya kaje ai" Prince yace "dole ai
Oummana… ki mun addu'a ni ko ganinta ma na samu nayi yau". Zuciyar Oummana fessss!
Yau ace Abdulrasheed yasan martabar mata a gare shima babbar nasararsu ce. Prince yana
fita tasa ai mata kiran uban kasa. Da Uban kasa ya tashi fada sai ya zarto sassan mahaifiyar tasa, nan Oummana ta fada masa
komi da ya faru har dawowar Hamma Gombe yau. Uban kasa yace "wannan ai abu ne me
sauki Oummana, ai dan nasan abinda ya faru kenan dana aika tun ranar da tazo. Wulaqanci ba
dadi amman sai ayi la'akari da ba laifin sa bane. Ayi masa afuwa".
Oummana tace "ai ina sane da ban fada maka ba. So nake shima yaji a jikin sa, kuma inga
gudun ruwan iyayen sa, in har zuwa karshen mako naga babu wani canji se kuje da auta
(Abdulmajeed) dan Allah ayi mana bikon Aisha".
Uban kasa yace "bakomi Oummana ".
Shi kuma ya tafi ya sake daukar wanka, yau ma cikin brown filtex yadi, ya daura hular
manyan matasa na zamani wato 'Tonak' kalar kayan, ya yi fes cikin shiga ta kamala, zati, haiba,
kwarjini da kamala duk sun bayyana tare dashi, ko makiyin sa ya ganshi a wannan lokacin sai
yace "fatabarakallahu ahsanil khaliqeen". Domin yau Hamma a ruwa biyunsa ya fito, Malam Buhari ya daukoshi zuwa Jeka da fari.
Prince yai sallama a gidan su Aysha Baba yunus ya fito yace "laaa Abdulrasheed kai ne
tafe?" Yai murmushi yana dukar da Kai, suka gaisa da Baban Aisha, yai masa iso zuwa ciki,
Abba ya tambayi su Dade. yace "inace shekaranjiya ka tafi ko baka tafin bane?" Yace na tafi
Baba. dazu na dawo". Yace ina Ummanmu?" Abban Aisha yace ta je gidan Baba Barau bikin
'yar sa Maryamu akeyi. Jibi Jumaah za'a daura auren bayan sallar Jumaah. Sun tafi jere wai.
Malam ya dubeshi Yana murmushi ya ce "ka san mata da hidima".
Prince yayi shiru. Cikin damuwa. Malam Yunus yace "Abdulrasheed ba nace zan kira ka
ba?". Yace "Babanmu kayi haquri wallahi ko na zauna Lagos bani da nitsuwa, gara dai in dawo
Gomben in zauna jiran hukuncin Baba Barau". Malam Yunus yace "ba ance ana ta kiran ka
wurin aiki ba?" Yace "na basu excuse sun qara min sati biyu, shiyasa nace gara na dawo nan
din". Sai yayi shiru.
Malam Yunus ma duk sai yaji wani iri, yace ba damuwa in an jima zani gidan nasa daman,
zan masa magana kaji?"
Prince yace "toh Baba. Nima wai da zuwa zan yi in gaishe shi". Yace "toh babu laifi".
Yana barin nan yace wa Buhari ya kai shi gidan Baba Barau. Ai kuwa ya samu gida makil da
jamaa ana ta hidimar jere yau da kawo lefe.
'Yan uwan mijin sun tafi kenan Prince yai sallama, dan Baba Barau ya fito yaje ya fada masa
mijin Aisha yazo. Nan aka masa iso zuwa ciki.
Wato duk hayaniyar da ake a gidan Malam Barau Hamza, jikake kamar anyi ruwa an dauke
tsit!!!!! akayi. Lokacinda Prince ya keto jamaa ya ya wuce zuwa falon Baba Barau, kwarjinin nan
na masu sarauta, gashi dai ba girman kai, amman ana ganin sa an ga basarake, haiba, mulki
ado, kai komai ma!!! Hamma yayi tsugunno a gaban su Baba Furera yai masu gaisuwa jama’u (in general).
Auwalu babban Dan Baba Barau da ya shigo dashi yace dasu "mijin Saddiqah ne"". Ga dangin
Aisha gabadayansu sun hadu, nan aka sake gaisawa, ya miqe zuwa cikin falon Baba Barau.
Nan aka bar 'yammatan family dinsu Aisha da kawayen amarya da santi da lashe miyau,
Saddiqah na tsaye jikin window taji muryar sa, ta juyo tana kallon sa ta tagar, har wata rama
taga Hamman nasu Firausi yayi, amman ya zuba kyau Masha Allah.
Tana ganin yadda 'yan banzan cousins dinta sai kallon sa suke tace kamar mayu, a ranta ta
ce "mayu kawai, mtsw". Da taji ya Auwalu yace mijin SIDDIQAH ne she was proud!!!!
Sai daga baya ta tuna tace fa ta gama auren. Sai ta koma ta zauna a gefen gado, ta fara
tunani.
Prince ya isa palon Baba Barau ya zauna a kasa ya gaishe shi cikin girmamawa, shima ya
amsa. Ya tambayi su Nenne yace suna lafiya suna gaishe shi ya sunkai da kai. Baba Barau ya
dauka zai masa maganar Aisha yaga bai ce komi ba.
Yace "Babanmu ashe biki ake yi". yace "eh wallahi, wa ya fadi maka?" Yace "Baba ne ya fada
min dazu. Allah ya basu zaman lafiya. Yaushe ne daurin auren?" Baba Barau yace "jumaa ne in
sha Allah". Prince yace "toh Allah ya kaimu. Allah yasa ayi damu", Baba yace "Amin".
Zuwa can kuma Prince yace "Baba inzo daurin auren?" yace "ah me zai hana in kana nan
kazo". yace "ai ina nan ma in sha Allah".
Baba yace "toh Allah ya kaimu". Yai shiru dai, can kuma yace "Baba zan tafi kuma dan Allah
ina kara baka hakuri. Waman gaddarallahu hakka qadrihi…. Allah ne ya qadarta faruwar abinda